Showing 51001 words to 54000 words out of 78880 words

Chapter 18 - YAR KANCE free pages na Maman Abdallah.doc

na tashe ki kina bacci'' ya faWa lokacin da ya yi arba'in da fuskarsa bayan ta buWe masa ?ofar.

Murmushi kawai ta yi tare da nufar banWaki, alwala ta Wauro ta fito ta sameshi zaune a bakin gado.

''Baki yi sallar isha'i ba ne?'' ya jefa mata tambaya.
''A'a na yi, dayake ina yin sallar dare ne, kuma naga kamar lokaci yayi'' ta faWa cike da nutsuwa.

''Ai kam lokaci bai yi ba, yanzun ?arfe sha biyu ma bai yi ba, yanzun dai zo ki zauna ki Wan sha wannan, kafin ki kwanta ki huta, kinga mungaji sosai a wunin nan, wallahi ni sai yanzu ma nake jin muguwar gajiya a tattare dani'' ya faWa a shagwaSe kamar yana gaban Ummy da Abby'nsa.

Sai da ta saki murmushi ganin yadda ya wani narke kamar ?aramin yaro.
Ba tare da ta musa masa ba ta zo ta zauna a kusa dashi kamar yadda taga yana da muradin hakan.

Yadda take lakato madarar da ?ar ?aramar cokalin robar dake hannunta tana kai wa a baki sai abin ya yi matu?ar ?ayatar dashi, sai kawai ya zuba mata ido yana kallo kamar wani wawa, Allah babu abinda ba zai iya yi ba, a yadda ya halicci yarinyar nan a cikin babu da rashin gata sai kuma ya sama mata nutsuwar da bai bawa wa'yanda aka haifa a cikin akwai da wadatar ba, babu shakka Allah gagara misali ne wanda yafi misali.

''Ko zaka sha ne?'' A hankali muryarta ta daki dodon kunnensa.

Wata irin kunya ce ta rufesa ganin har yarinyar ta lura da irin kallon ?urullar da yake mata.

Bai iya buWe baki ya yi mata magana ba, sai kwanciya da yayi akan gadon yana mai kallon sama, tare da zuciyarsa dake masa bugun da bai yi kama dana da kafin ta shigo rayuwarsa ba.

Rufe sauran ta yi tana mai komawa banWaki ta kuma kurkure bakinta kafin ta dawo, sai dai a wannan karon tsaye tayi a bakin gadon ba tare da tasan abinda ya dace tayi ba.

''Ki hau ki kwanta mana, ko bakya jin bacci ne?'' ta ji ya jefo mata tambayar.

A yadda yake kwance ya kalli sama kuma idanunsa a rufe, kai sai kace barci yake, ashe idonsa biyu yana sauraronta.

''To! to a ina zan kwanta?'' ta faWa a Wan Warare.

Tashi ya yi zaune yana mai fuskantar ta da ce wa ''a ina kuwa idan ba akan gado ba, ko ya yi mana kaWan ne gadon a tunaninki bazai wadacemu ba?'' ya faWa ko a jikinsa.

Idanuwa ta fiddo waje tana kallonsa da ce wa ''wai anan zaka kwana?'', bata ma san ta yi masa wannan tambaya ba sai da taji ya biyo bayanta da amsar ''eh! Anan zan kwana gaskiya, a Wakina ina jin tsoro.''

Sake ?walalo idanu waje ta yi da mamaki fal a ranta, ba tare da ta kuma ce masa komai ba ta fara ?o?arin Waukar bargon dake kan gadon dan ta nemawa kanta wurin da zata kwanta, amma dai ya dakatar da ita ta hanyar ri?e bargon yana kallonta.
''Ki kwanta akan gado in ji ni, kuma bana san musu dan Allah Noor.''

Sakin bargon ta yi jiki a sanyaye, yau shi ne karo na farko da zata taSa kwana a Wauki Waya da namiji, kuma namijin ma baligi ?ato kamar Abdallah, gashi ya zo mata da wani zance na ta kwana akan gado kuma tare dashi, to amma ya za tayi? Ita dai rufin asirinta Waya ma daya kasance mijinta ne, koda dai....
''Ki rage hasken nan ta hanyar danna wancan Wan madannin, nikam sai da safe'' ta kuma jinsa da wani batun daban ba wancan ba, wanda a wannan karon har ya dai-daita kwanciyarsa a kan Sangarensa na dama, sai ma da shafe jikinsa da addu'a.

Haka ta yi kamar yadda ya ce, ta rage hasken Wakin kafin ta kwanta a gefen gadon, wanda da za tayi ?wa?waran motsi to sai dai ta ji ta a ?asa warwas.

Da yake ita ma ta gaji sosai tana kwantawa barci ya Wauke ta, yana jin saukar nunfashinta ya canja ya san tayi baccin, mirginawa ya yi zuwa gare ta, ya matso da ita tsakiyar gadon kusa dashi, samun kansa ya yi da kallon kyaukyawar fuskantar mai Soyayyan kyau.

''Wai har baccin ma da hijab kika yi, miye yasa ba zaki cire kisha iska ba? Daga yanzun kar ki kuma kwanci da hijab a jikinki dugun samun matsala'' ya faWa yana mai yaye mata hijabin dake jikinta kafin ya Wora da ce wa ''kulawa dake wajibi na ne, in sha Allahu sai kinga haske a cikin rayuwarki, haka kawai naji zuciyata ta nutsu da shiga al'amarin ki, ki taya ni kula da kanki kinji Noor, sannan kuma! A kullum mu kasance a tare gaf da juna kamar dai haka, kwana a wuri guda, ke muyi komai a tare idan a hali, zan yi farin ciki idan har ya kika kasance a tare dani, zan yi miki komai dai-dai da ?arfina in sha Allahu.''

Duka wa'yannan maganganu da yake yi a kunnenta, sai dai ba lallai ya lura ba saboda ta bashi baya ne, amma sosai take mamakin wannan bawan Allah'n, to amma miye ma'anar wannan? Shin tun yaushe ya santa haka da har ya shirya zama da ita kamar yadda yake faWa yanzun? Wannan ba komai bane face ikon Ubangijin da baya barci kuma gyangyaWi baya Waukarsa, Allah gagara misali wanda yafi misali, wanda shike mulkar duka zukatan bayinsa nagari dama koma bayansu, ''alhamdullillah'' shi ne abinda ta faWa a ?asan zuciyarta, bayan nan bata kuma sanin inda kanta yake ba, barcin na gaske ya yi awon gaba da ita, barci mai cike da tarin gajiya da mafarkai barkatai.

Haka ma a Sangaren Abdallah sai da ya yi mafarkin wai ga waccan Noor Win tasa ?ar jaririya tana kwance akan cinyarsa tana ta ?wel?wela masa dariya, abinda bai taSa yi ba tun bayan da aka ce masa Fatuman ta rasu sai yau Win nan

Bayan kwana biyar

Kamar wasa Dady ya fara aikin daya da kansa, tuni aka kai kayan aiki wancan filin da ya yi sanadiyar haWuwar Abdallah da Talatunsa, inda aka zuba ma'aikata kamar ba da kuWi za'a biya su hakkinsu na aikin da zasu yi ba, dama tuntuni Abdallah ya gama zama taswirar yadda ya kamata wurin ya kasance, ba Sata lokaci aka fara aiki gadan gadan.

Da sa hannun Barister Jallo Abby ya cike takardar tsayawa takara, in da suke faman kafa jam'iyyarsu, su bada wasa suka zo ba, dan haka ba za suyi wasa a harakar ba, komai nasu na musamman ne.


*********************
Zaune yake akan kujerar dake ofishinsa da tarin takardu da kuma na'urar mai ?wa?walwa dake gefe, sai kuma wayar tafi da gidanka irin ta kiran gaggawa wa wani ko kuma isar da sa?o.
Ajiye al?amin dake hannunsa ya yi wanda rubutu ne yake dashi kafin ya Waga wannan wayar tafi da gidanka ya tura kira..... ''Tariq!'', iya abinda kawai ya ce ya ajiye wayar, kafin ya cigaba da aikin dake gabansa.

Bubbuga ?ofar aka yi alamar neman iso, sai da ya bada umarnin shigowa kafin wani matashin saurayi wanda shima fari ne ya shigo haWu da sarawa Ogan nasu.

''Tariq an dawo daga shari'ar ne?'' expecteur Muhsin ya tambaye wanda ya kira da suna Tariq.

''Eh YallaSai sun dawo, kumar dai yadda kayi hasashe hakan ne ya faru, kotu ta karSe wa'yannan kuWaWen, an zuba su a baitul mali'' ya faWa yana mai ?ara ?amewa wuri guda.

''Yanzun suna ina ne?'' ya jefa masa tambaya.
''An maida su cell YallaSai'' ya bashi amsa cike da girmamawa.

''To miye ake kira dasu da za'a ajiye su? A cike musu takarda a sallamesu'' ya tambaye shi haWi da bada umarnin a sake su. ''To ?allaSai'' Tariq ya faWa yana mai sarawa maigidan nasa kafin ya wuce.

''Amma Allah ya isa tsakanina dai, Mugu Azzalumi, Annamimi mai haWa mutun da hukuma ba tare da ya yi laifin komai ba, wallahi ban yafe maka ba, kuma dai kaga sakamakon cutata da kayi'' Inna Balki ce da wannan maganar bayan da aka sallamesu daga hannun ?an doka, bayan an karSe komai dake tare dasu.

''Ai Mugu shi yasan makwancin Mugu, da kinsan kina da gaskiya ai da kin Waya baki kin faWi inda kika samo kuWin a lokacin da aka yi miki tambaya a kotu, dan haka babu abinda Allah ya isar ki za ta yi min wallahi, maza ?ara ba, aje a Wora daga inda aka tsaya, ni nayi nan'' wannan ?arawon ya faWa yana mai barin wajen, yabar Inna Balki tsaye a wurin sai warin dauWa take, yau kwanakinsu biyar kenan a hannun iko, gashi yau Allah ya nufa sun sake su amma ba ko ?wandala a jikinta, sai ma dauWa da taban cizon sauro da ya kusan cinye rabin naman jikinta a cikin ?an kwanakin, nan musamman ma fuskarta daya kasance a buWe take, sauran jikinta kam da ragewa tunda tana sanye da kaya, amma fuskarta kam sai ha?uri, to a lokacin idan tace zata rufe fuskarta nunfashinta zai iya barin gangar jikinta, tunda wajan akwai zafi sosai, ga kuma masha?ar iskar ba yawa. A hankali ta ciri ?afarta ta bar wajan tana tunanin wurin zuwa, tsoro take yi ta koma can wurin zamansu abinda take tsoro ya faru, gashi kuma babu kuWin barin ?asa Bama ?asa ba, ko na cin abinci yanzun ba tada shi, yanzu har ma bata san yadda za tayi ba.

Barinta wajan kenan wata babbar mota ?ikar toyoya ta tsaya a bakin ofisoshin ?an sandan, sai bayan da Direban ya daidaita motar a inda ya dace kafin suka fito daga motar.

Tun daga ?ofar shiga ofishin suke karSar gaisuwa cike da girmamawa daga bakin Jam'ian dake wajan, a haka har aka musu jagora zuwa ga expecteur Bukar, wanda asalin sunansa Abubakar, amma ana kiransa da Bukar ne kasancewarsa Bazabarme, suna yawan kiran mai irin wannan suna da Bukar.

Mi?ewa ya yi tsaye yana mai yi musu ido da basu masauki a manya manyan kujerun dake cikin ofishin daga Waya Sangaren, dama an tanadesu ne saboda manya haka idan sun kawo ziyarar gani da ido haka ko dai wani abu makamancin wannan.

''YallaSai ai da kun kirani sai inzo har gida, fatan dai lafiya?'' ce war expecteur Bukar yana mai farin cikin ganinsu a ofishinsa.

Kallon Abby Dady ga yi, kafin ma yayi magana da bakinsa tuni Abby'n ya gane ma'anar kallon, sai ya tura wa Bukar envelope Win dake hannunsa, kafin ya Wora masa da bayani
kan ce wa suna so ne anaimo musu wannan matar dake jikin zanen nan.

?auka Expecteur Bukar ya yi yana mai buWewa, wata irin razana ce ta bayyana a fuskarsa ganin fuskar dake jikin photan.

Matar da ya bada umarnin a sake ta yanzun nan ita su dady suka zo naimo musu?

Cikin sauri ya Wauki wayar cikin office Win tura kira, Tariq din da ya bawa umarni da a sake su shi ne ya Waya kiran, ba jimawa sai gashi ya shigo tare da ?amewa agaban Expecteur.

Tambayarsa ya yi ''ina mutanan da nace a sallamai su ba jimawa?''
Cike da ladabi Tariq ya ce ''YallaSai ai sun tafi.''


Tashin hankali ne ya bayyana a fuskar sa ya ce ''maza aje a duba su yanzun nan'' da wata sarawar Tariq ya bar wajen cikin hanzarin dan cika umarnin ogansa.

Su dai su Dady shiru suka yi suna kallon Bukar, bakinsu fal tambaya, lura da hakan da Expecteur ya yi ne ya fara da ''ba jimawanna saka a ka sallami wannan matar ta jikin zanen nan ita da wani matashin saurayi, mun kama shi saurayin da laifin sata a gidan makwabtanmu, sai dai a inda muka je kamashi sai muka tardasu tare da wannan matar, kuma tabbas ita ce'' ya basu tabbaci, haWi da basu labarin yadda aka yi ya gane fuskar.

Nan suka shiga zaman jiran tsammani, in da Dady yake cike da farin cikin ce wa komai yana zuwa musu da sau?i, shi kuma Abby a nasa Sangaren shi ko da babu ?ar a halin yanzu, susan yadda aka yi ta salwanta shi ne burinsa domin kuwa babu shakka wannan ita ce Fatsumen da yake kyautata zaton zai ansamu ?arsa a tare da ita, ko kuma wani abun daya danganceta.

Babu in da su Tariq basu duba ba a kurkusa ba, amma babu su babu labarin
su.
Haka kuwa ya sanar da maigidan nasa basu gansu ba.

Saida rashin jin daWi ya bayyana a fuskar Dady da Abby, Bama ya kamar Dady da yaji aiki ya koma masa baya, amma babu komai, indai har irin hakan yana faruwa wata rana zasu kamata a hannuwansu ne.

Tabbaci akan zasu nemo ta Expecteur Bukar ya basu, bayan yaji Wan ta?aitaccen bayanin dalilin da yasa suke nemanta Win.

Sallama suka yi mada kafin suka bar wajan da ya?inin zai nemi ta Win kamar yadda ya ce, dan ba yau ba suka sanshi da kafiya da naci akan aikinsa, kuma ba laifi baya aikin rashawa an shaideshi.



?angaren Abdallah da Talatu kuwa a tare suke kwanciya waje daya duka jerin kwanakin nan, tun bata saba ba har ta saba, wani sa'in ma cikin barci sai dai yajita a jikinsa.
Hakan ba qaramin daWi yake masa ba, dan ko motsi baya sanyi saboda kada ta farka ta janye jikinta.

Ya dage dage sosai wajan koyawa mata karatu, kuma sosai take maida hankali wajan koyan. Alhamdulillah tana ganewa sosai abun har mamaki yake bashi, yadda da ya yi koya mata take daukewa, ba wani sa'in kafin ma ya faWa Wa mata bayani tuni ta fahimta, hadda kuma duk bayan sallar asuba sai ta kawo masa kuma ba tare da bata ba.

Kullum kayan dake jikinta basa wuce doguwar riga, dan ita kaWai ce abinda taga zata iya sakawa a irin kayan daya jibgo ya lode mata su, daga ?aramar riga sai gajeran wando, gashi ita kuma doguwar rigar ma dan babu yadda za ta yi ne take saka wa, haka kuma kunya take rufe ta a duk lokacin da ya shigo ya iske ta babu hijab, haka zata haWe jikinta har sai ya fice daga Wakin, ko kuma tayi dubarar da zata janyo hijab ta saka a jikinta.

A dan ?an?anin lokacin da suke samu suna karatun nan wata irin sha?uwa ta shiga tsakanin su, har takai da zaran ya fita sai ta zauna tunanin sa, haka shi ma yanzu tunanin yarinyar baya barinsa dai-dai da second Waya, haka zai yi ta ganin fuskantar tana yi masa gizo, fuskar da ta fara sauyawa dalilin sutun da ta su yanzu, eh! Shi iya fuskar zai iya tabbatar da sauyinta, domin kuwa ita kaWai yake iya gani, sai kuma ?afa da hannu.

Yanzu takai ko kwanciya barci Talatu bata iya yi sai ta raSu dashi. Dama can ta da san jiki sosai, kawai fi wuri na bata samu ba. Tun ana yar murginawa cikin bacci irin ba'a sani Win nan ba har takai da suna sane suke rungume juna suyi baccin su cikin kwanciyar hankali. Shi dai Abdallah yana jin abu yana dan tokare masa ?irji aduk sanda ya saka ta a jikinsa yayin bacci, amma har ga Allah bai taSa kai hannunsa jikinta da niyyar taSa ta ba,shi yasa har yanzun bai gama tabbatarwa wai da gaske ?irjin yarinyar ne da gaske.



An bawa mako biyu baya, ana wannan tafiyar ne yaga dai kawo mata abincin da yake yi fa Ummy takusa an karewa dashi, duk da ba koda yaushe yake kawo mata na Ummy'n ba sai dai ya siyo mata a gidan cin abinci.

Bayan ya zauna ya yi nazari da tunanin mafita, sai kawai ya yanke shawarar zai ajiye mata kayan abincin tarin?a dafawa da kanta, in yaso sai ya bata Wayar wayarsa, ya koya mata yanda zatayi amfani da ita, dayl yadda zata kunna Wi-Fi din gidan da kowa yake amfani dashi, ya sauke mata videos masu yawa na kalolin abinci daga internet, tana kallah tanayi har ta iya. HaWi da nuna mata yadda zata iya samun sauran abubuwan zamani wanda tana daga gida zata waye ta koyi abubuwa masu yawan gaske. Hamkalinsa kwance suka fara aiki da wannan tsari, sai dai a wayar da ya bata babu layi ko guda a ciki.

*************
Aikin gini dai ya kan-kama gadan-gadan, dan kuwa dai gini yayi nisa sosai an zuba ma'aikata wa?anda suka san makamar aikin su.


?angarori guda biyu ake ginawa, dayan Sangaren wata babbar ma'aikata da ta shafi ban garori da dama ake tsara za'a kafa, sai daya Sangaren inda ake gina ofishin jam'iyya.


Su dady sun dukufa wajan ganin sun gyara takardu na siyasa da fara campaign na Abby, inda suka ajiye takardar neman kujerar Gwamna, haka kuma Dady yayi alqawarin sai ?anen nasa ya zo da abubuwan da sauran jam'iyya basu zo da shi ba.

Yau kiran Ishaq ya tashe shi daga bacci safen daya koma, bayan ya dawo daga masallaci.

Kafe ta ya yi da ido yana kallonta, yadda har yanzun take zaune akan sallayar da ta gama sallar asubahi akai,anan ya tarar da ita dama, yana gama karSar hardarta ya ?ara mata karatun ya haye gado abinsa, a ce warsa bacci yake ji, dan jiya bai samu yayi cikakken bacci na awa biyu ba, sakamakon mutsu-mutsun da Talatu ta kwana tana yi masa ajiki, shi dai bai san dalilinta ya yin hakan haba, amma shi kam ta dama masa dalilin da ya kasa rintsawa na tsayin dare.

''Karatun kike yi har yanzu?'' Ta ji ya jefo mata tambaya lokaci Waya yana mai Waga kiran Ishaq din, ganin hakan da tayi dai kawai ta amsa shi da murmushi.

''To yane abokina?'' ya jefa wa Ishaq tambaya, lokaci Waya kuma yana mai mi?a wa Talatu hannu akan ta iso gareshi.

''Assalamu alaikum' ce war Ishaq.

?ar ?aramar dariya ya saki lokacin da yaji hakan daga gareshi, gashi ya yk dai-dai da isowar Talatu bakin gadon, hannu yasa ya kamata zuwa gare shi, inda yayi mata masauki akan mi?a??ar ?afarsa dake a mi?e akan gadon cikin laulayin bargo.

''Afuwan! Wa'alaikissalam'' ya amsa shi.

Dariya shima Ishaq ya yi daga Sangarensa kafin ya fara da ''mutumin ya kira ka kuwa? (Bi ma'ana Yusuf), yanzun ba jimawa ya kira ni akan yau zamu je haWa kayan lefe, wai baya so ya bawa su Anty Marya (kishiyar Mamansa) suyi masa shirme, ko kuma su siyo tsofaffin ya yi, dan haka mu zamu je da kanmu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login