Showing 57001 words to 60000 words out of 78880 words

Chapter 20 - YAR KANCE free pages na Maman Abdallah.doc

ido kamar mai san ya gano wani abun.

Sunne kanta tayi ?asa tana mai wasa da hannunta ta cikin hijabin dake jikinta. Bata iya ce masa komai ba, dan har yanzu yanayin jikinta bai gama dawo mata dai-dai ba tun sanda ya canja, ita dai batasan miye dalili ba, koda hannunta bawan Allah'n nan ya taSa to in sha Allahu sai taji yanayin jikinta ya canja.

''?an jira ni ina zuwa'' ya faWa yana mai yin hanyar ?ar ?aramar kicthing Win dake Sangaren nasa.

Wuri ta nema ta zauna tana ?are wa falon kallon, yau shi ne rana ta farko da ta taSa ganin falon a nutse, dan ko ranar da suka zo gidan nan bata samu damar kallonsa har haka ba, dan a lokacin Abdallah yana neman kai da ita, ma'ana yana famar ya yi ya Soyeta kar wanda ya ganta.

Tana wannan tunanin ne ya dawo da plate a hannunsa, haWe da cups guda biyu da ruwan gora mara sanyi, ajiye wa ya yi tare da yin bismillah ya zauna.


Lokacin da zai fara zuba abincin a plate har ta yun?ura da niyyar zuwa ta amsa ya dakatar da ita ta hanyar Waya mata hannu, a hankali ya ce ''ina zuwa Noor.''

Komawa ta yi ta zauna tana kallon yadda yake zuba komai da kuma yadda ya dace a duban, ''shi kenan! Wannan kam ta gama koyarsa, ba gaba'' ta faWa a cikin zuciyarta.

''Yawwa zo ko'' taji ya faWa haWu m da mi?a mata hannu, cike da kunta ta ?ara so ta mi?a masa nata hannun ya kama, a maimakon taga ya taya ta zama a gefensa kawai sai ya yi mata wuri a kan cibiyoyin sa, rintse ido tayi tsabar kunyar da ta hana mata buWe su.

''Miye haka? Wai kunya na kike ji komai? Ai kam dai ?wara ki daina tun wuri gaskiya, dan ni a irin wannan tsarin nake so in gina rayuwar iyalina tun daga tushe gaskiya.''

''Iyalinsa? Tun daga tushe! Kenan hakan na nufin ya gama Waukarta a matsayin mata duk da bata kai ba? Hakan na nufin zai zauna da ita kina yanzu ba?''

''Eh! Har abada ke Win ta Abdallah ce Noor, abadan! Abada!''

Taji ya bata amsa kai tsaye, wannan shi ya tabbatar mata ce wa ba zancen zuci tayi ba, a zahiri ta yi magana kuma ya ji, tunda gashi nan har ya bata amsar da har abada ba zata taSa iya mantawa ba.

Ai batasan lokacin da ta faWa jikinsa da dukkanin nutsuwa da sakankancewarta ba.


Yau Win ma dai kamar kullum haka yaji abu ya to?are masa ?irji, a ransa ya Warsa ce wa yau sai ya tabbatar shin na gaske ne ko kuma dai....


Shima ?an?ameta ya yi yana mai sauke ajiyar zuciya, dai-dai da saitin kunnenta yakai bakinsa kafin ya ce ''ba nace a fasa sa hijab idan ina nan ba, dan Allah Madam'' ya ?arshe kamar zai yi mata kuka.

Kuma rintse idanunta ta yi a karo na biyu, duk jikinta ya mutu murus, sai ta ji ko yunwar ma da take ji yanzun bata ji, kuma bata san ina ta fece ba.

Lokacin da yake ?o?arin cire mata hijabin bata hana shi ba, duk da kuwa tana cikin matsananciyar kunya da zai ganta hakanan babu hijabi a jikin.

Humm, jama'a Abdallah shiWewa ya yi na wucin gadi ganin Talatuwa ba hijabi da ranar gari, gasu daf da juna, koma ince tana zaune a jikinsa.

Hannu takai ta rufe fuskarta cike da jin kunya, yayin da shi kuma ya kasa cewa komai, banda tasbiji babu abinda yake yiwa Ubangijin daya halicci wannan baiwa tasa mai Soyayyan kyau na masifa, gashi ya cire ma yarinyar ababen wasa tun da wannan ?ananan shekarun nata, tab! To ai wallahi sai yake ga Noor kamar ma tafi Angel cikar diri na halittar mace, dan sau tari ko a cikin hijab Win nan yakan ce bari ya yi ?iyasin yanayin yadda surarta yake, sai ma yaga tama wuce yadda yake ?iyasta ta.

Shi dai a nasa hangen ma sai ya ce Noor ta fi sa kyau nesa ba kusa ba, shi sai dai ace fari ne, dan wallahi sai yanzu ne ma yake ?are wa kyaukyawar fuskarta kallo, haWi da Wan madai-daicin surar jikinta wanda ya yi dai-dai da shekaru goma sha biyar Win da gareta a duniya, tabbas anan babbar mace Allah ya halitta ya ajiye anan, ba lallai dayawa su gane hakan ba, amma yau da gobe lokaci zai nuna wa mai nisan kwana.

Hannayensa yasa ya zagaye wuyanta dasu, ya yin da ya haWe goshinan su wuri, haka hancinsa suka samu damar goguwa dana juna, cikin harshen buzancinsu ya ce ''zaki rayu dani na duka rayuwarki? Ni kam ina nan a tare dake, kuma ina ?aunarki, ina sanki har abada Noor.''

Idan ka cire Noor Win nan babu abinda ta fahimta a zancensa, hira Waya ta Waga masa haWi da turo Wan bakinta gaba da ce wa ''to da hausa fa? Ai kasan sarai ban iya yarenku ba, abu Waya na sani a yarenku, kuma na ri?e shi a kaina tun ina yarinya, ''mani bararan?''

Tuntsirewa ya yi da dariya haWi da ce wa ''to kenan miye ake nufi da wannan Win?'' ya tambaye ta.

Ture shi tayi ya yi baya, ya yin da ita kuma ta yi baya haWi da sauka daga jikinsa, ita ma tana ?ar dariya, a haka suka fara cin abincin suna rafa, yana kuma janta da firar da tasa murmushi ya kasa barin fuskarta.

Ana haka ne yaji shigowar kiran Ummy, daram! Ya ji gabansa ya yi musu faWuwa hakan nan tunma kafin ya Waga kiran.

Kallonta ya yi yana mai gyara zamansa kafin ya Waga ya ?ara wayar a kunnensa.

''Assalamu alaikum Ummyna.''

''Wa'alaikassalam, kai wai miye kake yi a gefen hanya ka tsaya da mota anan?'' ta jefa masa tambaya bayan ta amsa sallamar da ya yi mata.

Idanu waje yake kallon Talatu da lumar abincin da ya Wauko a hannunsa wacce ya kasa ?arasa saka ta cikin bakinsa.

''Kiyi mini shiru.'' yaji ta kuma magantuwa daga Sangaren ta.

Gyaran murya ya yi haWi da dai-daita nutsuwarsa kafin ya ce ''mota kuma Ummy? A ina kenan?'' shima ya jefa mata tambaya.

''Bana san iskanci Abdallah, miye yasa zaka maido mini tambaya bayan nima tambayarka nayi, zaka faWa mini ne ko sai nasa Direba ya koma inda naga motar ne, in yaso sai in ganewa idona abinda yake faruwa'', ta faWa a kufule.

A sanyaye ya ce ''kiyi ha?uri Ummy, ai da farko ban fahimci zancen ba ne, eh motata ce, ai tun jiya take nan a ajiye, na dawo daga ma'aikata duba yanayin aiki ina kawowa nan ta tsaya ba gaba ba baya, to shi ne da nake so in kira mai gyara anjima ya duba ta, amma kuyi ha?uri dan Allah'' yakai ?arshe da ?as?an da kai gare ta, bayan ya zuga mata ?arya kawai dan ya samu mafita, idan ya ce mata ya bar motar ne haka kawai ya dawo gida gaskiya da matsala, dan ko wa ya yi masa tsaye sai ya faWa mata dalilin komawarsa gidan, bayan kuma ya ce a gaggauce yake su Ishaq suna jiransa.

Ita ma a nata Sangaren nunfashi taja ta fasar haWi da faWin ''Allah ya kyauta gaba, amma kasa a duba ta da wur-wui, babu wani fa'idar barin mota a gefen titi hakan nan kawai a ajiye, bye sai mun haWe a gida.''

Da ''in sha Allah'' ya asma kafin ta katse kiran daga Sangaren ta.

Ajiyar zuciya mai karfin gaske ya sauke yana mai tsurawa Talatu ido, da ita ma kanta ta kasa ci-gaba da cin abincin ganin ya sa?e hannu yana waya a cikin yanayin da da gani baya jin daWin maganar da yake yi.

''Tabbas abun ba ?arami bane kamar yadda ya Wauke shi, yanada wahalar gaske idan ba'a ganoshi a nan kusa ba, dan wallahi a yadda Ummy'nsan nan take da bin diddigi a komai zai yi wuya tafiyar nan ta yi tsayi, abunyi anan kawai shi ne in maida hankali game da zancen Angel Win nan, in yaso idan na cika musu nasu burin sai nima ina zo musu da zancen Noor, na tabbata zasu fahinceni a wannan lokacin.''

Maganar zuci yake yi, ya yin da idanuwansa suke yawo akanta, kanta a ?asa ta kasa Waga idanu ta kalleshi, sai take jin kamar duka dan ita ne rayuwarsa take sun ta sukurkuce, gashi ma har ?arya yake yi duka a sanadin, eh! ?arya mana, sai yanzu bayan tayi wa kowace magana tasa fashin ba?i ta gane ma'anar inda zancensa ya dosa, ''a kwai matsala gaskiya.''

Shi ne abinda yaji ya fito daga bakinta bayan dogon nazarin da yaga tana yi.

Cike da damuwa ya ce ''a kwai matsala kuma? Miye damuwarki a yanzu?'' ya jefa mata tambaya.

?agowa tayi tana kallonsa da kyawawan idanunta wanda suka ciko da ?walla ta ce ''tunda na shigo rayuwarka ka rasa samun nutsuwar ka, kai kullum kana kan yi mini hidima, kana kula dani, kulawar da tunda nake a rayuwata ban taSa samun makamanciyarta ba, to amma kai ta yaya zaka samu farin ciki idan kana tare dani? Kullum kana cikin fargabar kar wani ya ganni, saboda haka san abinda zaka ce musu ba, tunda komai yazo maka a bai-bai ne, kayi ?o?ari sosai,sannan kuma kayi jihadin rabani da wancan Baba Ado'n da ya yi niyyar illata mini rayuwa, kayi ha?uri ka kaini can wurin sansaninmu, in ci-gaba da zama a matsayin Talatuwa ta zai gi maka kwanciyar hankali'' ta ?arashe maganar da wani ?aramin kukan da zai iya zuma zuciyar mai sauraronsa.

Janyota ya yi ta faWa jikinsa, inda ya matseta gam kamar wani zai kwace masa ita, da muryarsa ta Abdallah sak ya shiga faWin ''Allah baya Worawa rai abinda ba zata iya ba Noor, akan ki nikam zan iya, shi yasa ya haWa ?addarata da taki wuri guda, ta yadda za suyi sanadin haWuwarmu kamar dai haka, babu wata nasara da zata samu mutun a rayuwarnan face sai ya ?etare wahala da gwagwarmaya kafin zuwanta, miye ma ya faru? Ai babu abinda aka yi yanzun ko? Ki kwantar da hankalinki, ki nutsu ki maida hankali wajan koyan duk wani abu da kika san zai anfaneki, kafin in samu sararin saka ki a babbar makaranta Noor, in sha Allahu sai kinzama abar kwatance a cikin mata, wannan al?awarin Abdallah ne.''

?an nunfasawa ya yi kafin ya Wora da ''kinga ko abincin ma bakici na kirki ba, maza buWe baki Ni da kaina zan baki.''

Kamar yadda ya ce, cike da kunya take karSar abincin daga garesa, saida ya tabbatar ta ?oshi kafin ya tattara kwanika da sauran abincin ya zuba gwandon, yayi mata sallama ya fice bayan ya nuna mata kicthing Win da zata kai plate da cups Win da suka Sata, rufe sashen ya yi ta waje kafin ya faWa wata motar ya fice daga gidan.


Wasu almajirai ya gani a hanyarsa ta zuwa gidansu Yusuf, tsayawa ya yi ya basu suka sauye sauran abincin nan, ya ?ara musu da kuWi yace su raba su siyi omon wanki kafin ya yi gaba.

A gidan su Yusuf ya samu Ishaq, sai bayan da ya gaida su Mama da Anna kafin ya dawo inda suke a Wakin Yusuf Win.

Wata shegiyar harara Yusuf ya wurga nasa haWi da cewa ''ba farau keda zafi ba wallahi, ramau'', dariya Abdallah ta yi yana mai faWa wa kan katifar Yusuf Win da ce wa ''sai aka yi rashin sa'a Ni ba Bahaushe bane, ban ma san mi ka faWa ba ehee.''

Cofin robar dake hannunsa Yusuf ya wulla masa tare da ?arin wata hararar bayan waccen, Abdallah ya ce ''jai ya da haka Malam? Ka wani sani a gaba kana harara kamar k wasu wani yaron shagonka dan ban fito da wuri ba, ka manta niWin mai iyali ne? Mai iyali! Dole sai na sallami Madam da suka hidundumun ta kafin na wani gardi ato.''

A wannan karon dariya Yusuf Win ya yi har Ishaq na taya shi, cikin dariyar ya ce ''kasan Allah ni mantawa nake da maganar auren kan nan idan ba zancwn aka yi ba, Allah sarki ashe da mai iyali nake magana, Sorry! To ya aka baro Madam Win? Fatan tana cikin ?oshin lafiya.''

A kufule Abdallah ta ce ''to da a tunaninka bata lafiya?tana nan garas Malam, kuma wallahi ku daina yi wa wannan aure nawa sha?iyanci da dariya, dan sai ya zama abun alfaharinku wata rana in sha Allahu, matu?ar a zaman tare akwai taya Wan'uwa murna, alhini, jimami da kuma farin ciki.''

?an nisawa Ishaq ya yi haWi da faWin ''kuma fa haka ne, to Allah ya tabbatar da wannan Aure ya kuma inganta shi, yasa muyi alfahari dashi duniya da lahira.''

Da ''amin'' Yusuf ya amsa shi kafin suka mi?e da nufin barin gidan.

Bayan Yusuf ya yi wa iyayensa mata sallama akan sai sun dawo suka kama hanyar kasuwar toll, a cewarsu su fara da ita.


Ma sha Allah! A shagon farko da suka shiga saida suka haWa atanfa, leshi, shadda dadadi masu yawan gaske, da da farko iya abinda ya tsara zai iya siya Yusuf ya tsaya, amma sai Abdallah ya yi ta ?ara Wauko wasu yana jibgewa, bayan sun gama lissafi Abdallah ya karSi account detail ya turawa mai shagon ya tura masa ma?uddan kuWaWen sa, wanda da Yusuf Win ne zai biya to babu shakka zai iya bada illahirin kuWin dake aljihunsa, amma duk da haka ba lallai su biya kuWin wannan tulin suturar ba.

Kallonsa Yusuf yayi tare da Waga baki da nufin yin magana, girgiza masa kai Abdallah ya yi haWi da yin gaba ya barsu a shagon, suma biyo bayansa suka yi, bayan Ishaq ya faWa wa mai shagon da a zuba musu kayan a jakunkuna, idan sun gama siyayyar sun zo su Wauka.

Haka suka yi ta yawo a kasuwar nan, kusan komai na haWa lefe sun siye shi, akwati ma guda shida suka siya, a madadin guda ukun da Yusuf ya yi niyyar siya, kai komai da yayi program Win siya saida aka nunka shi, abun dai sai wanda ya gani.

Da Yusuf ya yi wa Abdallah magana akan hidimar yayi yawa hakan nan, dan wallahi ba ?ananan kuWaWe aka kashe ba, kawai sai ya ce masa daga Abby ne, shi ya zuba masa kuWi akan ya bashi, shi kuma ?arya ma ya zanbaWa, tabbas Abby ya ce zai tura masa kuWi, to amma fa bai turo ba, ?ila yaje suna shan fira ko ayyuka da Dady ya manta, duka hidimar nan a aljihunsa ya yi ta, kuma hakan ba zai sa account Win sa yayi koda ciwon kai ba.

Kusan a kasuwa suka yi sallar azahar, kafin suka kamo hanyar komawa gida, bayan an sha?e musu bayan motar Abdallah da kaya ni?i ni?i.

Ishaq sai dariya yaje ?asa ?asa, Abdallah yasan dashi yake amma ya yi shiru ya maida shi banza.

Wai sun shiga shagon kayan ado da kwalliya na mata, a Wauko wannan a ajiye wancan, anzo kan breziya da tambayar mesure(awo) na dai-dai yadda za'a Wauko, Yusuf ya a
sunne kai saboda kunyar abokansa dake wurin, shi kuma gogan ba sai isa inda tulin breziyar suke ba, ya fara Wagawa sama yana dubawa, hankalinsa kwance zuciya zaune, idan ya Wauko ta Waga sai ya girgiza kai alamar bata yi ba, su dai suna gefe suna kallon ikon Allah, saida ya Wauko wacce yake tunanin tabbas taza yi masa abinda take so kafin ya ce ''yawwa ni dai-dai da wannan tayi min, samun dozing uku a leda Malam.''

Bawai su Yusuf ba, hatta mai shagon sai da ta dara, tare da faWin ''Maigida dozing uku ai sunyi yawa, a nawa gani.''

Ko a kwalar rigarsa ya ce ''to sa mini dozing biyu.''

Ishaq ne ya yi ?undunbalar faWar ''wai duk mi zaka yi da wannan abun Wan gidan Abby? Naga kai dai ba lefe kake haWawa ba'' ya karashe da ?ar dariya.

Juyowa ya yi garesa da ce wa ''ban tashi haWa lefe ba yanzu tukuna Malan, amma ai kasan kafin hakan nake da iyali'' harda murguWa masa baki a ?arshen maganar kamar wata mace.

A wannan karon harda mai shagon saida ya dara, cikin dariyar ya ce ''ikon Allah! Dama ana aure har a kira mutun mai Iyali kafin haWa lefe? Ya abun yake Wan'uwa?''

Kashe masa ido Waya Abdallah ya yi tare da ce wa ''abun wani sirri ne, su sunsan zancen ai.''

To wannan abun da ya faru ne ta yi mugun bawa Ishaq dariya, ashe dai abokin nasa bada wasa yake ba, tunda har yasan akwai abinda za'a sakawa breziya harma da sanin ma'auninta.

''Allah ka hore mana dai muma muyi auren nan muji abinda yakw a cikinsa'' ce war Ishaq.

Dariyar sha?iyanci Abdallah ya yi km amsa kafin ya ce ''Wan iska kawai, ko yau ka fito da matar aure wallahi zamu wanke ka mu bata kai, dan naga so kake ka lalace tunma kafin a aurar da kai.''

A haka suna zolayar junansu har suka iso bakin ?ofar gidan su Yusuf.

Sallallami da salati Mama da Anna suke ta zubawa, tun bayan da aka gama jibge musu ubannin kayan da su Abdallah'n suka tulo a matsayin lefen mutun guda Waya.

''Kai amma abu yayi kyau wallahi! Ki duba kiga kaya kamar ba a garin nan aka siyo ba, lallai komai kace babu to baka nemeshi ba'', faWin Anna dake ta faman WaWWaga kayan.

BuWar bakin Maman Yusuf sai ce wa ta yi........


?AR KANCE

Page 18

________''Haba Kursiyya(Anna) ai wallahi wannan da gani kasan hidimar wannan yaron ne Abdallah, Yusuf ina yaga kuWin da zai yi wannan uwar siyayyar, abun ai dayawa.''

Murmushi Yusuf Win ya yi kansa a ?asa ya ce ''wallaho kuwa Mama, bi har Nana rasa da bakin dazan yi musu godiya, a kullum hidimarsu agereni ?ara daWuwa take, da nayi nasa ?orafi tun a lokacin da muke kasuwar sai ce wa ya yi in ji Abby ya ce ya bani, Mama a taya ni godiya da w....'' bai ?arasa maganar daya Wauki ba yaji an buge masa baki, tana Wagowwa yaga Abdallah ne da wannan aikin, sai kawai ya faWa jikinsa suka rungume juna, a hankali ?ar ?wallar da Yusuf yake ta faman ri?e wa ta gangaro ta faWa a kafaWar Abdallah, yana jin haka ya raba jikinsa da nasa haWi da tura sa baya tare da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login