Showing 15001 words to 18000 words out of 78880 words

Chapter 6 - YAR KANCE free pages na Maman Abdallah.doc

to karka ?ara aibata ni kaji na faWa maka'' Abdallah ya faWa kamar zai fasa Wakin tsabar takaicin Yusuf.

Shima cikin Waga muryar Yusuf ya ce ''duka na zaka yi komai? Na ce dukana zaka iya yi da har kake Waya mini murya haka? Gaskiya ce dai kuma dole a faWa maka ita ko kana so ko baka so, kuskure ne ka riga da ka yishi sai ka nemi hanyar warware shi''.

''ku dakata dan Allah miye haka wai fisabilillahi, kamar wasu yara zaku na Waga murya a gidan mutane? Ha ba abi komai a sannu man...'', bai gama maganar da yake yi ba Abdallah ya katse da da ce wa ''a'a ni ba gidan mu ba dai zaka ce, ai shikam nan gidansu ne kuma shima hakan yake ?o?arin nusar sani na fahimta, garinsu nazo kuma gidansu! Kaga duk abinda ya yi mini ni nazo da kafafuwana, dan haka ka barshi kawai''.


Dafe kansa Yusuf ya yi da sauri saboda mugun sara masa da ya yi, dai-dai nan Abdallah ya tashi zai tsallaka su ya fi ce daga Wakin, ri?e ?afarsa Yusuf ya yi kansa a ?asa ba tare daya Wago ba, tsak Abdallah ya tsaya amma bai juyo ba, har kusan second talatin suna a haka, jin hannun Yusuf ya yi sanyi wajan ?a??arfan ri?on da ya yi masa da farko yasa Abdallah juyowa dan gani ko neman dalilin da yasa ya ri?e masa ?afa, sai dai abinda ya gani ne ya yi mugun Waga masa hankali, ''Yusuf kuka kuma? Ya yi masa tambayar cikin matu?ar razana.
da sauri ya dawo kusa dashi ya zauna tare da sa hannu ya Wago kansa Wan ya tabbatar da gaske kukan ne yake yi, ai shi ma bai san sanda hawaye suka fara zarya akan fuskarsa ba.


Kallon wannan drama ta kukan gardawon samari ne ya cika Ishaq da takaici, ba zato suka ji ya zagayo ta bayansu ya gwara kansu waje guda ji kake gumm, da ?ar dariya ya ce ''banzaye na ce kuyi mai dalili'' ya faWa yana harararsu ganin zasu cika sa da iskanci.


Ai kuwa ya yi nasarar saka su dariya kamar yadda yaso, dan a tare suka yi dariya tare da murza goshinsa duka a lokaci guda, a kuma sa'i Waya suka furta kalmar ''sorry'', wata dariyar suka kuma yi a wannan karon harda Ishaq, shima cikin dariyar ya ce ''ko ga ku fa, amma kun tsaya kuna mana kuka kamar ?wailayen Amare''.

Harararsa Yusuf ya yi tare da faWin ''da Ni kake ko da shi faWi gaskiya ina sauraronka''.

Shan kunu Ishaq ya yi ya na mai ce wa ''kaji na kira sunan Mutun anan ne? Ni Amare na ce ban kira wani gardi ba''.

Samirar (kwanon) da suka gama cinye waina Yusuf ya jefa masa kaWan yana gota shi yadda yasan ba zai kai gareshi ba.
Kaucewa ya yi da murmushi a fuskarsa ya fara magana kamar haka ''Yusuf komai ya zo a yadda ba'ayi zato ba, faWa wa su Ummy da wuri haka ba lallai ya haifi Wa mai ido ba, amma kai Abdallah miye ka tsayar daga gareka ne?''.

?an nisawa Abdallah ya yi tare da faWin ''ni dai so nake kar wanda ya faWa musu dan Allah, zan bi komai a sannu da sannu har zuwa lokacin da nake tunanin zasu fahimce ni kafin na sanar da su, ku tayani rufe wannan abu dan Allah nasan zaku iya, zan ajiye ta a sashe na tunda akwai Waki har guda biyu banda wanda nake ciki, ba tare da kowa ya sa ni ba daga ni sai ku sai Allah, sai kuma ita dazan gindayawa sharaWin ko ?ofar Wakin dana ajiyeta kai ta fito, har zuwa lokacin da Allah zai kawo mini mafita'' ya karasa maganar da geste( nuni) alamar ro?o.

Ajiyar zuciya Yusuf ya sauke kafin ya ce ''ban ?i wannan ba amma ya za'ayi ka ajiye yarinya a gidan nan ba tare da su Abby sun ankara ba? A yadda kuke gudanar da rayuwar ku cike da soyayya, kulawa, da kwakwaran bin diddigin nan ta ?a?a kake zaton shirin ka zai yi aiki?''.

''Ni ma shi na gani'' ce war Ishaq, ba tare da Sata lokaci ba Abdallah ya faWa musu duk wasu tsarurrukan da yake tunanin zasu fiddashi ya zayyane musu.
Sosai suka masa fatan alkhairi tare da fatan samun goyon bayan Iyayensa cikin gaggawa, ya kuwa ji daWi sosai da yadda suka sauke ransu suka karSi zancen sa musamman ma Yusuf da ya Wauka da zafi da farko.


?arfe sha Waya kowa ya yi wanka a cikin su, ita ma Talatuwa tayi wanka a cikin gida bisa jagorancin Rammatu, kuma ita ta bata kayanta ta saka dan bata wani fita sosai ba, sai dai a shekaru za'a iya ce wa Rammatu ta girme wa Talatu da kusan shekara Waya da Woriya.

Yusuf ya faWa wa Kawunsa ce wa daga sunyi sallar azahar zasu kama hanya.
Sam kawu bai ji daWin wannan abu ba, dan so ya yi suyi musu koda kwana uku zuwa huWu ne a kaWan, amma tunda haka duka ce shi kenan, ta yi yu ko da wani mai ri?e??en uzuri a cikin su, ko kuma shi Abdallah wanda yasamu babban uzuri kamar daga sama.

Yusuf sun kuma zama da Rammatu kafin su tafi, in da a nan ne ma ya yiwa yarinyar kallon tsanaki, babu laifi tanada kyau dai dai misali, sannan ga yadda ta amsa Mahaifinta cike da girmamawa Wazu da safen nan zai tabbatar maka ce wa yarinyar ta samu tarbiyya gwargwadon iko, gashi har yanzu ta kasa bari su haWa ido dashi tun da suka zauna, amma yana gani kuma yana jin tasirin idanunta aduk sanda ta kalleshi a sa ce.

Kyautar bazata daga Abdallah, suna tsaka da wannan zama da Rammatu Abdallah ya yi kiransa a waya wai yazo ya ga wani abu, ba musu kuwa ya nemi exuse ya ta fi, ai kuwa dai abunda shi Yusuf ya manta ne Abdallah ya yi masa wato waya, sam shi yama manta da ce wa ya kamata ya zo mata da waya tunda Baba ce wa ya yi auren saura wata biyu kacal, gashi har an cinye fiye da mako a cikin jerin kwanaki sittin Win da aka yanke wa lokacin auren nasu.
?aga baki ya yi da niyyar yi masa godiya Abdallah ya Sale bakin da yatsarsa, bai kuma bawa Yusuf wani damar magana ba ya ce ''Malan jeka sallame ta kaga lokaci yana kuma gabatowa''.


Rammatu ta yi murnar samun kyautar wannan zunbuWeWiyar wayar da ta yi, za ta iya cewa a kurkusa babu mai waya wacce takai girman wannan, tabbas yanzu wayoyin endroid suqn barbazu ko'ina da ina, da ?ar jikarka biyar (5k) sai ka sami ?ar karama ta hannu ka siya abinka, yau gata da waya a hannunta ?irar INFINIXE harda jakarta da komai da change, sabuwa dal a kwalin ta.

Yusuf ya yi nazari da tunani game game da zancen layi, sai kawai ya cire Wayan layin wayarsa ya saka mata a cikin wayar, nan ya nunnuna mata ?an abubuwan da za ta yi anfani dasu nan kusa irin Waga kira, tura kira da dai makamantansu.


Tsarabar ?auye kam kamar bayan motarsu bazai Wauke ba, busheshiyar KuSewa, Wake Daddawa, Barkono, Cukui, Nono kindurmu, Yakuwa da sauran su, Hatsi ma kusan bahu biyu aka haWe musu a mota kaya ni?i-ni?i, bayan alkhairin ya Yusuf ya yiwa dangin nasa wanda Abdallah ne ya bashi kaso uku daga cikin abinda ya basu.

Jama'ar gidan da makwabta ne suka fito har ?ofar gida dan yi musu rakiya da fatan alkhairi, Rammatu na ri?e da hannun Talatu suka fito daga gidan bayan ta shirya a cikin wasu kayan wanda suma na Rammatun ne, kanta a ?asa har suka iso bakin mota, Maman Rammatu ce ta kama hannunta tayi wani gefen da ita tare da bata wani abu a leda ta ce ''?ata na rasa abinda zan baki kasancewar abu yazo a bazata kuma gashi yanzun za ku tafi, wannan turare ne ki adana kinji ko, Allah ya saukeku lafiya''.
Da murnar ta ta ?arSa tana wa Maman godiya Wan ita mutun ce mai tsananin son ?anshi, sai dai Allah ya kawo ta a muhallin da ba lallai ta samu yin rayuwa cikin nutsuwa bama bare har ayi tunanin wani kwale kwali.
Jin maganar Kawu yana ce wa ''ki barta hakan nan tazo su tafi, hanyar tasu ba kyau ne da ita ba gashi za suyi tafiyar maraice, Allah dai ya tsare ya maidaku gida cikin aminci''.


Yusuf ne a mazaunin direba Ishaq kuma a kujerar mai zaman banza, ya yin da Abdallah da Talatu suke gidan baya.

Abun al'ajabi har zai tashi motar sai kuma ya fice da hanzari ya koma cikin gida kamar wanda ya yi mantuwa, lura da hakan da Kawu ya yi ne tunda dama duk suna tsaye a wajan da nufin son ganin tashin su yasa ya ce da Rammatu da ke tsaye a kusa da mahaifiyarta ce wa su wuce cikin gida, shi ma gaba ya yi abinsa dan dama akwai wajen da zashi, ba musu kuwa duka wajen aka fara watse wa, sai ya rage sai Yara wanda su kuwa ba'a rabansu da inda a kwai mota musamman a ?auye, idan har ba ganin suka yi ta bar wajan ba ba lallai su gusa ba.

A cikin gida kuwa Yusuf yana shi ga ya ja ya tsaya kusa da bishiyar Warbejiyar dake kusa da ?ofar Wakin da aka saukewa a ciki kamar mai jiran wani abun, ganin Rammatu ta shigo yasa ya saki fuskarshi tare da gyara kolar rigarsa cikin shau?in da ya rasa dalilin shigarsa cikin sa, daga idon da zai yi sai kuwa suka haWa ido da Mama ta shigo gidan ita ma, da yake dama kusan a tare suka shigo da Rammatu, sai dai ita ta riga Maman nata shigowa ne sakamakon ri?e hijabin Mama da ?yauren ?ofar gida ya yi.
?asa da kansa ya yi yana sosa ?eya alamar yaji kunya.
Kamar bata gansa ba Mamar ta yi tana mai yiwa Rammatu alama da ido kan ta tsaya ta saurareshi, ba musu kuwa taja tunga ta tsaya ya yin da Maman nata ta shige cikin gida.


''Yaya Yusuf ka manta wani abun ne dama?'' ta faWa cikin sassanyar muryar ta wacce ko kaWan ba zakace a ma'abota zaman wannan ?auyen akwai mai nutsuwar murya a zance kamar haka ba.

?ago da kansa ya yi ba zato idanunsu ya sar?e dana juna, cikin sakin fuska ya shiga ce wa ''eh na yi mantuwa ne ?anwata, kuma abun ma a wajan ki yake ai, baki ce kina sona ko a'a ba taya zan tafi in bar baya da ?ura''.

Kusan second sha biyar ta dauka tana nazarin kalaman sa, miye nufinsa a nan, to kodai ya gane tana sanshi ne yasa ya faWi haka, cike da matsananciyar kunya ta rufe fuskarta da tafukan hanunta tana mai ce wa ''ina sanka mana Yaya ba tun yau ba ma kuwa'' tana kaiwa nan ta shige cikin gida da sassarfa.

Shi ma da gudun sa ya fice daga gidan kamar ?aramin yaro, yana zuwa kusa da motarsu ya wani uban tsalle tare da faWin ''yesss'' lokaci guda kuma ya ?amewwaje Waya tuna saSaSar da yake shirin yi.
A gurguje ya shige Motar yana tama key da addu'a a bakinsa.

''Allah ya koro sau?i'' shi kaWai Abdallah ya faWa lokaci Waya yana kauda kai kamar ba shi ne ya yi zancen ba.

Ishaq ne ya karSe da ce wa ''jiya warahaka a hanyar mu ta zuwa garin nan babu cika bakin da mutun bai yi ba akan shi dai an gama dashi tunda za'a haWa shi da ?ar ?auye, gashi yanzu wai harda su tsalle alamar abu ya yi kyau, Allah ya shirye ka Yusuf''.

?ar dariya kawai ya yi bai ce dasu komai ba ya cilla Motar kan titin da zai sada su da babbar hanya wacce a kanta zasu mi?e har daSen da zasu fuskanci hanyar komawa Agadez.

Ita dai Talatu kanta a ?asa yake tun shigowar ta motar, sai matsewa da tayi a guri Waya kamar mai jin sanyi, alhali kuma tunani ne fal ranta na abinda zata taras wanda bata taSa zata ba, mutumin da bata taSa sani ba, taya a kayi har yasan ta kuma har yaje garinsu ya aure ta, a abinda taji Kawu ya faWa wa malan Limam da jawabin da Liman Win ya yi wa su Kawu ya tabbatar mata ce wa daga Agadez suke, sun zo ne dan Yusuf ya ga Rammatu a matsayin zaSi Iyayensa, su kuma wayan'nan abokanan sa ne suka yi masa rakiya haka ne? Ta tambayi kanta, ganin ba tada amsa yasa ta Wago kanta a karo na farko ta dubi sashen da yake, dai-dai da ya ciro wayarsa a aljihunsa ya fara latsawa.

''Assalamu alaikum Ummy barka da rana, ya gida ina Abbyna yake ne?''.
Daga Wayan Sangaren Ummy ta amsa shi da ce wa ''wa'alaikas-salam barka dai Yarona! To ya ?auyen kuma? Abby gashi nan shigowarsa gidan kenan yau yawo ya tafi''.
Cike da tsokana kamar wanda baya cikin damuwa Abdallah ya ce ''to ko ya amsa gayyatar cin abincin rana daga wat..'' bai gama maganar ba Ummy ta katse kiran dan dagani hawan jini Abdallahn yake so ya saka mata game da haWa Mijinta da zancen wasu matan daban ba ita ba.

?ar dariya Abdallah ya yi tare da sumbatar wayar yana faWin ''Ummyna rigima''.

Haka kuma a lokacin nan ne ya tsargu jin kamar ana kallonsa, juyawar da yake sai suka haWa ido da ita, wani irin azabebben fargaba da tsoro ne yaji sun kuma rufesa, yau miye ya daukowa kansa magana domin Allah, ta ina yarinyar nan ta yi daidai da tsarinsa? Ba sai ma an kai ga Iyaye da dangi ba, a shi karan kansa yasan wannan yarinyar ba ajinsa bace.


?asa ta kuma yi da kanta saboda wata iriyar kunya da taji ta rufe ta, na kama ta da ya yi tana satar kallon sa, a karo na farko ta shiga abinda bai shafe ta ba, ta ?uresa da ido har saida ya ranfo ta, cikin in-ina ta ce ''yi yi yi ha?uri''.


Kamar bai ji mi ta ce ba ya share ta, sai ma shiga firar su Yusuf da Ishaq da ya yi.

A haka suke wuce garuruwa har aka kira sallar la'asar, lokacin sun shigo zinder anan suka tsaya suka yi sallah kafin suka kuma kama hanya, wacce gadan-gadan Agadez aka nufa ba wata kwana.

Ganin kamar gudun da Yusuf yake bai wadatar ba yasa Abdallah ce wa ''Yusuf ka ?ara gudu ko kuma Ni in yi tu?in nan, a haka yaushe zamu kai Agadez fisabilillahi? Koda gudu muke ba lallai mu isa goman dare ba, gashi idan daren ya yi sosai hukuma ba zasu bari mu shiga gari ba koda kuwa muna hango shi daga inda mike ne har sai gari ya waye''.

''Tab-dijan wai Ni in baka tu?i ka je ka kifar damu? Ai ?wara in daWa gudun da kai ka daWa, ko banza Ni idan naga abun ba mai yi yuwa ba ne zan iya ragewa kai fa?''.


Ishaq Sarkin bacci tuni ya fara gyangyaWi daga zaune, Yusuf ne ya kalli inda yake tare da faWin '' mesa Sarkin bacci! Allah mutumin nan sai a sace shi ba tare da ya sani ba garin wannan baccin nasa da bashida salansa''.

A garin Takuku magariba ta kamasu, hakan nan suka tsaya suka gabatar da ita kafin suka ci gaba da tafiya, a kuma wannan lokacin sai da Abdallah ya siya musu abinci anan garin, wasa-wasa ?arfe goman dare ya shuWe ana shirin sha Waya amma babu alamar zasu hango mashigar gari bare a yi zancen isa gida, ganin har wannan lokacin bataci abincin daya ajiye a gefenta ba ya buWe baki ya ce da ita ''ki Wauki abincin nan ki ci'', cikin baccin daya Wan fara fizgarta ta ji shi lokacin da yake maganar, Waukan ledar ta yi tare da juyawa Wayen sashen, dafa dukan shinkafa ne sai rabin kaza a saman ta, da bismillah ta fara cin shinkafar a hankali cikin nutsuwar da ta gama zame mata jiki, ba wani mai yawa ta ci ba dan dama ita Win ba mai yawan cin abinci bace, koda sun je gidan biki sun samo dayawan abinci wani sa'in ba ci take ba, sai dai idan ya burge Innarta takan Wan tsakura iya wanda zata iya ci, sauran kuma omo (klin) ake siyowa a wanke shi tas, ruwa biyu uku har huWu ma idan abincin mai mai?o ne, a haka kowannensu yanada tabarmar kaba irin ta shanya Win nan, wayan'da basu da ita kuma a bahu suke shanya nasu wankekken abincin, bayan ya bushe sai a sauye a mazubi a adana, wa?anda Iyayensa suke ?auye sai su tura musu idan ?anzon ya taru, wa?anda suke gari kuwa dayawa sayarwa suke kwano Waya dala Wari 500f.

Lura da ta gama cin iya abinda zata iya ci a abincin ne Abdallah ya mi?a mata ruwa a robar faro.
KarSa ta yi tasha tare da faWin ''alhamdulillah'' a sarari, cikin lokaci ?an?ani bacci ya Wauke ta, suu ta sulale sai akan cinyar Abdallah.

FaWuwar gaba haWi da wani irin firgici ne suka ziyarce sa lokacin da jikin yarinyar ya haWu da nasa, hannu ya saka zai cireta sai kuma wata zuciyar ta hane sa, tunawa da ya yi ce wa yanzun shi ne bango majinginar yarinyar, idan bata raSe shi ba ina zata raSa, shi ne komai na ta a yanzu kuma al?awari ya yi zai kula da ita, kuma in sha Allahu sai ya sama mata ingantacciyar rayuwa wacce ko a mafarki bata taSa tunanin samu ba, sai ya ?ure ?aryar Iyayen nan nata mutanen banza, ida har sun sauka lafiya daga gobe zai fara bincikar wannan Innar tata, game da sahihancin zaman??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????su iyaye ga wannan yarinya, kuma dole ya tuhumeta akan ce war da Ado ya yi zai auri Talatu, yasan tabbas ba wani gushewar hankali irin na masu ?an surSe-surSe ba ne, akwai dai hujja ko dalilin da yasa ya ce ba ?arsa Sace kuma zai aureta, ya zama dole ya binciki Inna sosai, har ya tsara a ransa yadda zai tafi da komai har ya cimma nasara, ba kuma zai bari tasan yana da ala?a da Talatuwa ba bare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login