Showing 63001 words to 66000 words out of 78880 words

Chapter 22 - YAR KANCE free pages na Maman Abdallah.doc

kamar zata yi kuka.
''Na ?oshi da gaske, iya abinda zan iya ci kenan, kafin zuwana nan sai da na ji ba wuri a cikina'' ya bata amsar tambayar data jefa masa.

Mintuna uku kawai ya ?ara bayan wannan ya mi?e tsaye yana gyara wuyan rigarsa, ''zan tafi ni kam, amma baki bani amsa akan lokacin da kike son ayi hidimar ba.''

Kanta a ?asa tana wasa da yatsun hannunta ta ce ''koma yaushe ne, ni dama a shirye nake'' ta faWa yana mai rufe fuskarta wai ita kunya.

?an murmusawa ya yi ba tare da ya kuma ce mata komai ba ya ajiye mata rafar kuWi a kujerar daya tashi, tare da zato wasu da bansan ko nawa bane ya dam?awa Auta haWi da yi mata raWa a kunnenta.

Da gudu yarinyar ta nufi Wakin mahaifiyarsu tana faWin ''Mama kiga kuWin da yaya Abdallah ya bani, ya ce in faWa muku zai tafiyarsa gidansu.''

Ba Abdallah ba, har Angel sai da maganar ta bata dariya, wai zai ficewarsa gidansu, irin kamar nasu gidan ya gundire shi, bayan shi ba haka ya ce mata ba.

''To Madam Ni zan wuce, sai kin jini'' ya katse musu shurun da furucin sa.
''Sai na jika ko sai ka jini? Ka faWa kamar wanda zaka kira ni'' ta faWa tana wani shagwaSe masa fuska.

A dai-dai sa'in Mama ta fito, wanda dama ita Win yake jira suyi sallama ya fice, sai da safe ya yi musu tare da godiya, in da ita ma ta bashi sau?in gaisuwa kan ya gaishe da su Ummy.

Har bakin motarsa Angel ta taka masa, ba tare da ya sake ce mata komai ba yake ?o?arin buWe murfin motar, ''na gode sosai da hidima, Allah ya tsare hanya ya maida ka gida lafiya, a gaishe min da Ummyna'' ta faWa ata rufe fuska haWi da juyawa cikin gida da sassarfa.

Jinjina kai kawai ta yi kafin ya shige ya bar gidan, da tari tunaninka a ransa. Anya wanna hanyar ita ce hanyar daya kamata ya raSu da ita dan warware matsalarsa kuwa? A nashi gani yarda da auren Angel shi kaWai zai bashi damar bayyanar da ala?ar dake tsakaninsa da Talatunsa, ''Allah gani gareka'' ya faWa a bayyane yana mai shafar kansa da hannunsa Waya, ya yin da Wayan yake akan matu?in motar.

Tunani ya shiga yi sosai akan samun mafita, a haka ya tsaya a hanya ya siya musu tsiran tukunya mai Wan yawa, haWi da wata sabuwar madara Alkausar, kafin ya wuce gida.

A lokacin goma baifi saura mintuna biyar ba, ya tsayar da motarsa a farfajiyar gidansu, wanda ya ?awata da haske mai Waukar hankali.

Filin gidan shiru babu kowa, da alama wasunsu duk sun kama gobe.

''Ummy na dawo, naga dare ya yi sai da safe.''
Wannan shi ne sa?on daya tura mata ta waya kafin ya fito daga cikin motar.

Can ya hango Al?asum zaune a ?ofar sashen su, da alama karatu yake yi, dan da littafi a hannunsa.

Tattaki Abdallah ya yi har zuwa in da yake, ganin ya doso wurinsa sai Al?asum Win ya mi?e da murmushi akan fuskarsa, har isowar Abdallah wurin yana murmushi.
Hannu ya mi?a masa suka gaisa, Abdallah ya ce ''na ganka anan! Ko kana hutawa ne?'' ya jefa masa tambaya.

''Eh to gaskiya ina karatu ne, gobe muna da jarabawa ne, da ina zaune a falo ne, sai kuma na fito nan'' ya amsa shi cike da girmamawa, tamkar yaya haka ya Wauki Abdallah'n, dan a washe garin ranar da suka dawo gidan Abdallah ya kai shi makaranta bisa umarnin Dady, tunda dama yana karatunsa ba wani alfano a zamansa hakan nan, shi ne yanzun ya ci-gaba da karatunsa hankali kwance, wanda a yammar yinin yau Win nan Dady yake tambayarsa, shin yana so direba ya ci-gaba da kai shi makaranta ne ko kuma a nema masa abin hawa? Kunya ta hana ya amsa, sai kawai Dady'n ya sallameshi kan za'a siya masa moto (babur) na zamani irin na matasa ?an makaranta.

Fatan alkhairi Abdallah ya yi masa kafin ya ce ''in sha Allahu gobe za'a kawo maka motonka har gida, dan mata biya kuWinsa har da na kawowa. Godiya Al?asum ya yi masa kafin suka bar wurin kusan a tare, shi ya faWa sashensu cike da murna, shi kuma Abdallah ya nufi nasa Sangaren.

Sai sakin murmushin da ya kasa gane ko na minene, shi dai yasan aduk sanda ya kusanta kansa gareta dai yaji kamar babu yashi a duka faWin duniya, ''mi nake ji akanki ne Noor?'' ya faWa a bayyane bayan ya rufe ?ofar falon, ya jingina da ?ofar haWi da kulle idanunsa.

''Nima ban sani ba'' kamar daga sama ya ji sautin muryarta a kunnuwansa.

BuWe idon da zai yi sai ganinta ya yi zaune a Waya daga cikin kujerun falon, ta tallafe fuskarta da duka hannayenta biyu, fuskarnan a kunbure kamar wacce aka mammara.

Da wani irin sauri ya ?ara so inda take bayan ya yi wurgi da ledar dake hannunsa.

Akan giuwoyinsa ya zube a gabanta yana ?are mata kallon cikin tashin hankali, ''Noor wani abun ya sameki bayan barina gida? Me ya faru'' ya cilla mata tambaya yana mai dafa kuncinta da suka Wan fi da fitowa sakamakon kukan da tasha.

Buge masa hannu ta yi daga taSatan da yake, cikin wani kukan da yazo mata ta ce ''ni kar ka kuma taSani bana so, ka je can ka koma in da ka fito'' ya faWa yana ?o?arin fincikewa daga ri?on da yake ?o?arin yi mata.

Maganarta ta Wauke masa kai sosai, kamar ya ya koma inda ya fito?
Sakata ya yi a jikinsa tare da matseta sosai yana shafa bayanta.

''Bamuyi haka dake ba Noor, ban ce miki a zaman mu zaki dinga zubda hawaye ba, miye dalilin kukan nan dan Allah, wani abun ya faru ne? Ko wani ya ganki ne bayan bana nan?'' ya dinga jero mata da tambayoyi.

Da dubara ta zare jikinta daga nasa tayi Wakinta, har yanzu muryar Ummy tana yi mata amsa kuwwa a kunnuwanta.

Kamar wasa ta ce bari taje Wakinsa, lokacin da ta shigo yana wanka, sai ta Suya a bayan labule, haka ma lokacin daya fito daga wanka sai rufe idanunta tayi, duk da ba tsirara ya fito ba, lokacin da yaje zantuttukan nan akanta bayan gama shiryawarsa duka tana kallonsa, a dai-dai gaSar da ta yi nufin bayyana a gabansa a lokacin ta ji fatin Ummy, da sauran maganganun da suka yiwa hankali da tunaninta fashin ba?i zuwa ga gane manufar shirinsa da inda zaije, da kuma wacce ya Wauki wankan domin ta.

A Wakin suka barta ba tare da sun san da wanzuwar ta a ciki ba, ya yin da shi Abdallah ya ji haushin tusa shi gaba da Ummy tayi, kafin ya nuna wa Noor Winsa wanka da ya yi, ya kuma faWa mata inda zaije.

Jiki a saSule ya tashi ya bi bayan ta, amma ga mamakinsa sai ya iske ba sakawa Wakin key, ya Wan bubbuga yana kiran sunanta ''Noor ki buWe please, ki faWa min abinda ya tashi hankalinki, ba zan samu nutsuwa ba alhali kina cikin ?unci'' ya ?arashe da ?ara narke murya kamar zai yi kuka.

Batasan dalili ba, haka kawai ta tsinci kanta cikin ?unci tun bayan da ta fahimci zance zaije, kenan aure zai yi? Shikenan ya manta da ita a rayuwa, ya daina kulata, tunda dama a bayyane abun yake shiWin ba sa'anta bane, ga kuma yadda ?addarar rayuwa ta haWa su, sai take jin kamar ta gudu tabar gidan da ?afafunta tun ma kafin ya wofintar da ita, a yadda suke zaune shi ne yake kula da ita da duk wani motsi nata, taya idan ya samu mai kula da shi ba zai manta ta ba?
Wani kukan ya kuma suSuce mata wanda har yanzun ta kasa sanin ainihin dalilin yinsa, taimako ne dai Abdallah yayi mata shi, tunda ya raba ta da auren wannan Baba Ado'n, kuma ko yau ya ce ya sake ta bai yi laifi ba, haka kuma bai kamata ta ?ullaceshi ba, amma me yasa take jin kamar idan ta rasa shi ta rasa wani giSi na rayuwarta?
''Saboda shi ne gatanki a yanzu'' zuciyarta ta bata amsa. Ta ci-gaba da tuna irin alkhairansa gareta, da yadda ya Wauki kasadar aurenta, yadda yadda yake raba farin cikin sa biyu ya bata rabi, da yadda suke share lokacinsa wajan kula da duk wani abun da ya shafe, tabbas baki kyauta masa ba, ta yaya zaki barshi yana buga ?ofa amma ki ?i kula shi?'' zuciyarta ta nusar da ita a karo na biyu.
Zunbur ta mi?e tana share hawayenta ta nufi bakin ?ofar da har yanzu bai daina mata magiyar ta buWe ba. Tana buWe wa ta juya da nufin komawa ciki, amma sai taji ?afafuwanta sun tsaya, wano irin by ya tsarga mata tun daga ?o?uwar kanta zuwa tafin ?afafunta, jin ya rungume ta ta baya, ya haWe ta da jikinsa sosai, ya yin daya Wora haSarsa tsakanin kafaWa da wuyanta, duk da ya fita tsawo nesa ba kusa ba, amma hakan bai hana shi rankwafawa ya Wai-Waici tayinta ba.

Sarrrr ta ji wani abu mai kama da hawaye suna Wigar mata a kafaWa, da wani irin sauri ta juyo ta fuskanceshi da tarin mamaki da al'ajabi, tabbas kuwa hawaye ta gani a idanunsa, ta tabbatar ne a sanda takai Wan yatsarta ta dangwalo hawayen a gurbin idanunsa. ''Kuka! Ya Abdallah kuka kake yi? Kuma saboda ni? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un'' ta faWa lokaci Waya wani sabon kukan ba?inci da tausayin kanta na zuwar mata, a lokacin kuma ta faWa jikinsa ta rungume ?an-?am.

''Yi shiru kinji, ji?anki na tayar min da hankali Noor, zan tuhumi kaina akan na kasa baki kulawar daya dace, bayan al?awari na Waukar wa Malam Liman da kuma Malam Usamatu akan zan kula da rayuwarki, ba zan barki a ?unci ko damuwa ba, shi ne zan ganki kina kuka! Wani abun nayi miki ban sani ba?'' ya kai ?arshen maganar da jefa mata tambaya.

Shirun tayi kamar yadda ya ce, sai ta saka kanta cikin ?irjinsa ta Soye, sai yanzu kunyar kukan da bashi da dalilin da ta yi tayi ya sakata jin kunya.

Sunfi mintuna biyar a tsayen nan, amma ta kasa Wago da kanta sama, haka kuma ta kasa bashi amsar tambayar sa.

Hannunta ya kama suka isa bakin gado, ya zaunar da ita kafin shi ma ya zauna, ya fuskanceta yana mai kallon yadda fuskarta ta canja.
''Ba zaki faWa min abinda ya saka kula ba Noor? Kina so ki ganni cikin damuwa ko?''

LangwaSar dakai tayi gefe haWi da marairaicewa kafin ta ce ''nima bansan dalili ba Yayana, haka kawai naji ?unci ya lulluSeni dana ji zaka je....'' tiryan-tiryan ta bashi labarin shiga Wakinsa da ta yi, da yadda wankan daya Wauka ya yi matu?ar yi masa kyau haWin da tashin hankalin da ta shiga lokacin da taji zaije zance.

Shi abun dariya ma yaso ya bashi, lokacin da take fada masa wai tana fargabar kar ya yi aure ya manta da ita, kar ya samu mai kula da shi ya watsar da ita.

Kama hannunta ya yi ya saka s nasa ya ce ''wannan ba abinda zai iya faruwa ba ne abadan Noor, ki saka a ranki har abada Abdallah ba zai manta dake ba, kuma koda bautar da zai miki zata iya zama silar rayuwarsa bazai fasa ba, haka kuma babu zancen gajiya, ina jinki daban da sauran, idan kika cire iyaye da ?an'uwana na jini, kece ta farkon wacce nake ji da ita a can ?asan raina, kar ki kuma yin irin wannan tunanin Noor, dan ba zai taSa faruwa ba, kuma ko a mafarki kar ki kuskura kina irin wannan, dan babu shakka babban saSo ne jin hakan daga gareki'' ya kai ?arshe yana mai matse hannayenta da Wan ?arfi.
?arar shagwaSa ta saki haWe da yarfe hannun a lokacin daya sake mata shi tana faWin ''Yayana da zafi fa! Ko duk cikin horon ne?'' ta faWa tana ?ar dariya.
Sai a lokacin hankalinsa ya kwanta, ganin ya sauke te harma tana dariya. Abu Waya daya fahimta anan shi ne Noor Win da na kishinsa, to yaushe ta fara sansa ne? Dan babu kishi a inda babu so ko ?auna.


Bayan mako Waya.

Dady ya koma Algeriya kwanaki biyu da suka wuce, ya samu kiran gaggawa kan wani abu daya taso, kuma suna da tabbacin shi ne kawai zai iya nuna yadda ya dace ko kuma ya aiwatar da kansa kafin matsalar ta dai-daita.
Ya bar Agadez da Wan sauran ayyukan daya rage ba'a ?arasa ba, ga manya-manyan zaSuka na ?asa na dinfarowa, inda ya rage saura watanni hudu a gudanar da zaSe.
Harakar ginin ofishin jam'iyya tuni aka hamada, harma an gama zuba duk wani abinda ya dace, kama daga babban Wakin taro, ofisoshin jiga-jigan jam'iyya, mangazar (store) na ajiye kaya da kuma farfajiyar ajiye ababen hawa da makamantansu.
Masana'anta ne dai a na kan aiki, abunka da ba ?aramin aiki ba, shi yasa zai Wauki lokaci kafin a gama.
Burin Dady da Abby, bayan gama gina wannan masana'anta su samawa dubban Matasa ayyukan yi, nasu salon tafiyar daban ne, hatta iyaye mata da dattawa maza an shigar dasu cikin jerin wa?anda zasu samu abin dogaro da kai.

Note:
Jama'a wani sa'in tunaninmu na kwancewa wajan ganin matasa ne kawai ya kamata a inganta rayuwarsu a sama musu aikin yi ba, bawai ina ja da hakan ba ne a'a, amma a yadda zamanin nan ke tafiya magidanta manya su suka fi shan wahalar rayuwa, mutun ya girmanta, ga yawan iyali ma sha Allah, amma haka zaka samu bayada ri?e??en aikin yi sai kama nan kama can, abubuwa duk su taru suyu masa yawa, gashi zamani ya kawo mu ?arnin da ba kowane Uba ko Uwa ne kanyi dacen Wa nagari wanda zai maida damuwarsu tazama nasa, ya Wauki nauyinsu da duk wani abun nema na daga bu?atunsu.
Dayawa matasa koda sun samu aikin yin ma tofa kansu kawai suka sani, daga ?an matansu sai mata da yaransu, dayawansu su kan manta da nauyin kula da iyayen da Allah ya Wora musu, a wani sa'in har ?ara ?a mace, ita kam idan kaga bata taimakawa iyayenta ba to gaskiya bata da shi ne, ko kuma marasa rabo daga cikin mu. Allah ya yi mana mai kai.
?aukar dattawan da suka manyanta aikin da aka san zasu iya yi ba ?aramin tasiri zai yi wurin samuwar sassaucin rayuwa irin wacce muke fuskanta a yanzu, Allah yasa mu dace.

A Sangaren Angel babu laifi yanzun suna Wan gaisawa da Abdallah, sadai tun ranar daya zo gidansu bai kuma dawowa ba, ko ta wayar ma ita ce da ?o?arin kiransa, shima basa fin mintuna uku yake rasa abun faWa, sai dai ya yi mata sallama ya katse kiran.

Shirye-shiryen auren Yusuf suke ba wasa, in da Yusuf Win ya gama ginin gidansa dake anguwar Misrata, bayan babban masallacin jumma'a na Kaddafi.
Gida ne dai-dai na zaman mace Waya, ciki da falo ne, sai dai falon babba ne sosai, a tsakar gidan da madafa a gefe, da kuma bishiyar darbejiyar (maina/bedi) daya daWe da dasa ta tun lokacin daya siyi filin, haka kawai iccen yake birgeshi, ko na cikin gidan iyayensa daya gama rufe gidan da inuwa shi ne ya faWa shi tun a shekarun baya, cikin ikon Allah kuwa sai gashi ko runfa babu a gidansu yanzu, saboda maina/bedin ya gama rufe gidan.


Matamaye

''Kai amma Rammatu kekam kin gama yin dace wallahi, kiga irin wannan uban kayan da aka kawo a matsayin lefe? Yi ai wannan ko duka kayan shagwon Nuhu aka haWa ba zasu kai yawan wannan ba, wai karma ake ga zancen farashi, Allah ya baku zaman lafiya yasa abokin rayuwarki ne.''
Wata ?awar Rammatu ce mai suna Shamsiyya da wannan maganar, inda take zuzuta irin kayan da juya da yammar nan ne suka iso, da su Abdallah har sunce zasu ke sukai har can Kancen, amma sai baban Yusuf ya hana suyi hakan, a ce warsa hidimar ai tayi yawa, kuma abun da gajiya sosai, suje sukai lefe sannan kuma nan da kwanaki goma masu zuwa suce zasu je Waurin aure? Kawai a tura kayan ba sai wani yaje ba, haka kuwa aka yi, suka sako kaya ababbar motar sufuri tsakanin jihohi wato Bus, daga Agadez zuwa Zinder, dama tuni Baba Abdu (baban Rammatu) ya aiko da wani yaronsa Iro nan Damagaram, da nufin mota na isowa ya karSi kayan ya isa dasu Matamaye.


Kance.

''Kanta! Agadez nake son zuwa kwanakin nan, ko zaka je ne?''
Sulemanu ne da kanta zaune a ?ofar gidan su kanta suna cin gwaWa amaro, ya yin da Sulemanun ke yiwa Kanta wanna magana.

Watsa gwaWar daya Sara ya yi a baki duk da uban yawanta kuwa ya fara taunawa yana magana ''Yo Manu ai ?afarka ?afata wallahi, dama ni tuni na faWa wa baba ina so bana mai fita nema, amma a lokacin ban faWa masa inda nake son zuwa ba, kaga tafi gidan sau?i, kawai muyi tafiyar mu Agadez Win.

?an muskutawa Sulemanu ya yi haWi da faWin ''ni kasan saboda mi wai? Wallahi kawai saboda inje ko zanga Talatu da irin yadda rayuwarta ta canja, sannan inga ya ta ?are tsakanin baba Ado da inna Balki'' ya faWa yana Waya kai sama alamar tunani, ku kuma hasashen yadda abun zai kasance.

''Hhhh, ai kaima kasan mai raba wannan Innar ta Talatu da Ado sai Allah wallahi, kawai hali ne zasu haWu suna rabawa a garin da ba nasu ba, koda yake yanzun ai Inna Balki yafi dacewa a kirata da ba'abzina, tunda ta zama ?ar can'' in ji Kanta.

''Mu saka rana kawai abokina, mu tafi can Win kawai, Allah ya bamu sa'ar nema.'' ce war Manu.


Damagaram (Zinder)
Ofishin hukumar hana fataucin miyagun ?wayoyi.

Yadda yake a kwanannaWen nan a cure guri guda zai yi wuya daga nesa ka gane ce wa mutun ne, ya jigata ainun, ya susuce.
A razane ya Wago da kansa jin wata uwar tsawa da wani jami'in dake tsaye a kansa ya yi masa..........=ض?=ض?

Waye wannan? NI kaina bansani ba.=??
Wai kin fahimci ina labarin nan ya dosa kuwa?>??

Kar ku bari a baku labari Habibtys=?
?d'?=؞?=ؕ?

Maman Abdallah taku. '?

?AR KANCE

PAGE 20

Damagaram (Zinder)

Ofishin hukumar hana fataucin miyagun ?wayoyi.

Yadda yake a kwanannaWen nan a cure guri guda zai yi wuya daga nesa ka gane ce wa mutun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login