Showing 6001 words to 9000 words out of 78880 words

Chapter 3 - YAR KANCE free pages na Maman Abdallah.doc

lokacin yarinyar ta fara tafiya dan ficewa daga wajan taron bikin, dama neman abinci tazo kuma ma ta samu.

Ganin kiran Ummy zai kace yasa ya Wauka da sallama abakinsa, gashi baya tu?i tana waya dole ya tsaya ya amsa kiran ''Assalamu alaikum Ummyna'', '' wa'alaikum salam yarona wai ina ka shige ne ka duba lokaci kuwa? gashi kuma ma munyi ba?i a gidan duka baka nan'' cewar Ummy da muryar ta wadda daga ji kasan tana cikin farin ciki.


''Ina lafiya Ummyna ai ina hanyar dawowa ne wani Wan abu ya rikeni, amma ganinan insha Allah'' ya faWa yana ?o?arin tayar da motar gudun kar yarinyar tayi masa nisa sosai har ta Sace masa gashi ya fasa hangenta, sallama ya yi wa Ummy akan gashinan zuwa tare da kashe wayar.


A guje yabar wajan wanda har saida ya tayar da ?urar da yasa jama'ar gidan bikin dake zazzaune yin tsaki wasu daga cikin su, wasu kuwa hauka suka kaWawa ma'anocin tu?i Motar game da buWe su da yayi da ?ura.


Saida ya Wanyi nisa kaWan kafin ya hangosu su biyu suna tafiya, kowacce da kwanon ta a hannu kamar almajirai, yana kallo suka sami inuwar katanga suka zauna, dayake a jikin wani gida ne inuwar yamma ta fara saukowa sai ya zagaya da motarsa ta gaban gidan, kasheta yayi tare da rufewa, ya fito da gorar ruwan faro a hannunsa ya nufi inuwar da suke zaune daga ge.

Yana sane ya yi haka kawai dan yaganta ya kumaji yau mi take ce wa yarinyar da suke tare da ita, tun lokacin da suka fito daga waccan gidan ya lura da fuskarta kamar bata cikin yanayin farin ciki, ko miye damuwarta oho!.


Alwala ya soma yi a Wan tsugunnen da yayi, a zuwan matafi yaga lokacin sallar azahar na gabatowa zai yi alwala, inda sallah takama duk sai ya yita.
Bai wani isheta kallo ba dan ba Wabi'ar ta bace shiga hurumin duk wanda bata saniba, kai wanda ta sanin ma bata shigo abinda bai shafe ta ba, dan yana daga cikin imanin mutun yabar abunda bai shafe shi, haka Annabi(S.A.W) ya faWa.


''Lami ina cikin damuwa sosai wallahi, jiya naga tashin hankali fiye da tunanin ki, kawai fa Innarmu dan na koma gida ban samo komai ba haka ta shiga zagi da tsine mini albarka, yadda saka mini albarka baya mata wuya hakama tsine mini ita, wannan Wabi'a tata ba ta mini daWi sam wallahi, dazaran na faWa mata cewa kar ta yimin baki haka zatace kar na cikata da tsinannan wa'azi na, kinga ai anan ma tayi tsinuwa ko, yanzu rayuwa tayi a haka? A kullum tana haWani da Suwaiba tafini zuciyar nema kuma tafini albarka da farin jini, a ?arshe ma ta bani zaSi guda uku kuma dole na zaSi Waya'' Talatuwa take fadawa ?awarta Lami wannan magana da halin da Innar ta take san saka ta a cikin.


?an nisawa Lami tayi cike da tausayin Talatun tace ''gaskiya Talatu Innar ku ta cika son abun duniya, wani sa'in idan tana wasu abun kamar ba tsikakkiyar uwa ba wallahi, babu uwar da zata so Wiyarta tana ?awance da Suwaiba, ko kuma ita uwar tana shigewa Maman Suwaiba din a matsayin ta na Hajiyan Yan Kance, kinga duk da Anty Balki ba itace mahaifiyar mu ba mu duka ukun nan, Ni da Ruma da Safara'u mu duka babu ?arta ko Waya a ciki, kawai ta Wauko mu daga wajan iyayen mu akan mu nemi kuWi muna ?aruwa da juna, zata nema nama gidan aikatau zakuma mu rinka neman abinci a gari da gidajen biki kamar dai haka'' ta faWa tana nuna kwanon abincin ta dage ajiye agaban ta kafin ta kuma ce wa ''ko ?an dabarun satar nan da nake ji ana koyawa wasu gada cikin mu Anty Balki ta hanemu da yi kuma ta horemu da rike gaskiya ako ina muka riski kanmu, idan an biyamu hakkin mu a gidan aikin da muke akan rabashi gida uku ne, Ni kashi Waya, ita kashi Waya sai kuma a turawa iyayena kashi Waya, kuma ba laifi duka mun gamsu da wannan tsarin tunda ba cutarwa a ciki, amma ke miye damuwar ki game da Innar ki?'' Lami ta tambayi Talatuwa bayan ta gama bata bayanan yadda suke zaune da Anty Balki uwarsu a wannan gari.


Cikin tsananin damuwar data kasa Soyuwa akan fuskar ta tace ''wallahi ni da kamar rayuwar ki na samu duk bazan damuba, tunda ko banza Anty Balki tana tayaku rike mutuncin kanku saSanin ni da mahaifiyata da kanta takeso taga rayuwata ta lalace, lami Inna taban zaSin kodai nayyarda ina kawo mana kuWi anan garin duk dare ko kuma na yarda a saka sunana a jerin sunayen jama'ar Hajiyan Suwaiba irin wanda take wa hanya zuwa kasar Algeriya da sunan neman kuWi, ko kuma ta turani gida wajan babana, kuma ita kanta batasan ranar komawar taba, kiban shawara wace mafita zan zaSa a cikin su ukun nan?''.

Bana don zuwa Algeriya saboda kowa yaji wannan zancen yasan ba abin kirki a ciki, ba kuma zan iya Waukar mata al?awarin zan dinga kawo mata kuWi duk dare ba tunda ba kasuwanci nake yi ba, sannan bana so ta turani ?auye wajan Baba dan ina jin tsoron sa sosai wallahi, shima dai kamar ita Innar yake koma in ce ya fita tunda shi mugunta yake mini kamar ba Babana ba, ki bani shawara dan Allah Lami''.


Cike da al'ajabin irin wannan rayuwa Lami ta ce ''tom nidai inaga kawai ki zaSi komawa gida, kinga shikenan ko banza kin tsira da mutucin ki, babu wacce za tace wai ta ?etare iyakar ?asarta zuwa wata ?asar da sunan neman kuWi batare data zubar da kima da mutuncinta na ?a mace mai daraja da kima ba, kuma ko acikin garin ma ba wani sana'ar da za kiyi wacce zaki dinga samun kuWi kullum idan har ba kin nemi kusanci da saSawa mahaliccinki ba, ki sani komawa Kance a wannan gabar shine kadai mafitar ki fatan kin fahimceni'' .


?afafuwan Abdallah sun kasa daukanshi mamaki ne fal aransa, wai dama ana irin wannan rayuwar da gaske, to anya ma wannan matar mahaifiyar tace kuwa, idan har ita ta haife ta miye dalilin ta na ganin sai taga lalacewar tarbiyyar ta wacce dagani ba daga wajanta ta sameta ba.


Haka yasami kansan dasan jin hukunci da zata yanke wa kanta dan ya Wora bisa mizanin daya Wora hankalin ta ya gani.
Maganar Talatu ce ta maidoshi cikin tunanin ta jin tana ce wa ''shikenan Lami in sha Allah zan faWa mata kawai ni zan koma can garin mu wajan babana, kinga shikenan idan naje bazan sake dawowa ba wallahi, kuma ma ai sai tayi kewata itama nasani'' cikin shaukin soyayyar mahaifiyar tata take magana.


''To ai shikenan kawai ki gaggawauta barin garin nan tun kafin suyi galaba akanki'' Lami ta faWa.
''Ai in sha Allahy hakan za'ayi'' a haka suka mike da kwanukan su a hannayen sa suka bar wajan.


A hankali ya mike kamar wanda kwai ya fashewa a ciki ya yi hanyar wajan da ya ajiye motar sa, tafiya yake maganganun su suna ?ara komo masa a cikin kwakwalwar sa a karo na barkatai, tab-dijan ana dara ga dare yayi, wacece wannan yarinya? Ya tambayi kansa, yana wannan tunanin har ya iso gida.


Ba?in Motoci guda biyu ya gani a gidan, bai wani tsaya tantance daga ina suke ba ya fice masallaci dan gabatar da sallahr azahar da ake ta faman kirar, dama yayi alwalar sa a wajan tsegumin firar su Talatu.

Saida yayi sallah kafin ya dawo cikin gidan jiki duk ba kwari, da sallama abakinsa yashiga falon.


Da gudu Litel Ummy ta iso garesa tana fadin ''welcome yaya Abdallah'', Wagata sama ya yi ya fara juyi da ita a kafadar sa, yarinya ce ?ar kimanin shekara huWu a duniya, Wiyar wani cusin din su Abby ne dake zaune a nan cikin agarin Agadez, suna kiran mahaifin yaran da oncle Alkhusaini, yaransa huWu kuma mai sunan Ummy ita ce karama, babbar ?arsa macece mai suna Djameela suna kiranta da (Angel) mai shekara goma sha tara a duniya, sai Sufyane da Aliyu, sai kuma auta Gaisha mai sunan Ummy.

Sunan mahaifiyar su Hajiya Fati, itama ?ar asalin ?abilar su ce kuma tare da ita akazo sosai Ummy take farin ciki aduk sanda ahalin gidan suka kawo masu ziyara, saboda wani ?uduri da tabarwa kanta sani, wanda take ganin yanzu lokaci yayi da zata fito da abun yake ranta kowa yasani, a ranta ta ke jin ce wa tabbas lokaci yayi.


Yana dauke da ita a kafaWa har suka iso tsakiyar falon, a kujera ya zauna tare da faWin wash, cike da yawan magana na wayan'da basu daWe dasamun baki ba Letle tace ''Yaya Abdallah ka gaji ko?'', gyaWa mata kai yayi alamar eh dan baya san yawan magana ahalin yanzu, daidai da fitowar ummy daga Wakinta tare da Hajiya Fatima tana faWin My takwara mun barki a falo ke kaWai k...? Maganar tace ta makale ganin Abdallah zaune ya lumshe ido kamar mai bacci, cike da kulawa ta iso inda yake tana faWin ''Yarona ashe ka iso, wai ina ka tsaya ne, wallahi har Yusuf na kira yake cemun ka daWe da baro wajan sa da sunan ka tafi gida''.

''Wai mi aka dauki yaron nan ne duk an ishemu da rakin bai dawo gida ba, kina ganin mutun ya kusa yani amma ake masa irin wannan tattali haka?'' Kafin Abdallah ya magantu sukaji maganar su Abby daga bakin ?ofar shigowa falo shida oncle Alkhusaini, Sufyane da kuma Aliyu sun dawo daga masallaci.


Kowa na falon sai da yayi dariya harda Angel da fitowar ta kenan daga dakin daya kasance na bakin ?an'mata ne, ga duk wacce tazo gidan da sunan ba?unta koda ta yini ce to anan take sauka, akwai komai na bu?atar mai shekaru shabiyar zuwa sama a cikin Wakin.


Tsaye Abdallah ya yi tare da tarbar su Abby dan girmamawa, haka suka karaso dasu ana ta gaisawa da kuma bayyana farin cikin ziyara, sai bayan sun ci abincin rana duka ana zaune Ummy ta kalli Aliyu tace ''ka kama hannun takwara ku tafi Wakina ku zauna a can zamuyi magana kaji Wan albarka'', ba musu suka muke har da Sufyane da Angel, ''a'a ke ki zauna'' cewar Ummy tana nuna Angel da yatsa, jin ance Angel daya girma da shekara takwas cib-cib da ta zauna harda ita za'ayi firar yasa ya fasa yunkurin tashin da yayi niyyar yi daga wajan zaman sa.


Su duka shuru sukayi suna jira suji ta bakin Ummy, ita tasa Abby ya gayyato su har gidan dan Sarke abinda ke ranta wanda koshi Abbyn bata taSa faWa masa ba, wayar ta ta ciro daga caji tare da lansawa surukin ta, mijin yayarta, kuma yayan mijinta kira.
''Assalamu alaikum'' muryar Dady Abdul?adir ta gauraye ilahirin falon dayake a handsfree ta saka wayar ta yadda kowa zai iya jin maganar da ake yi, amsa sallamar tayi cikin girmamawa kafin cikin mintuna uku tayi Wan gajeren bayaninta akan kudirin ta nasan hada Aure tsakanin Abdallah da Djameela.


Ras ras ras gaban Abdallah ya faWi, zuciyarsa tashiga buguwa da sauri-sauri, ba tare da an tambaye shi ba, bai kuma duba tsananin soyayyar dake tsakanin sa da Ummyn nasa ba, baiga girman Abby dake zaune agaban saba, bai ji kunyar oncle Alkhusaini da yake kusa dashi ba, bai kuma kalli idanun Hajiya Fati ba, ba'a kuma kawo kansa a zancan ba ya daga baki da murya yace......................


Page 4
________Kansa a ?asa yake magana ''Ummy ku gafarceni bazan bari kuyi magana yanzu sai tafiya ta yi nisa kuma na watsa muku ?asa a ido ba, niWin inada wacce nake so na aura''.
Ba su Ummy da Abby dake zaune ba hatta Dady Abdul?adir da Mammaa dake kan layi saida sukayi mamakin maganar data fito daga bakin Abdallah.


''Kana ji ko yarona, wannan abu ne mai kyau idan har ka ajiye hankalin ka, miye aibun Angel fisabilillahi, wallahi batun yau ba nake da wannan buri a raina ba, kawai sai yau ne nake tunanin yadace na faWa, kuma ma ai duka gidane yarona ka duba fa'' Ummy ta yi masa nuni da iyaye da ita kanta yarinyar dake zaune duk ta wani ta?ure waje Waya, harga Allah tana mutuwar son Abdallah, shekaru dadama take dakon soyayyar sa baji ba gani, kuma sai yanzu datake ganin Allah ya kawo mata mafita ta hanyar maganar Ummy zai ce bazai aureta ba, gashi kuma dama a ?abilar su da wuya kaga mutun ya auro bare, Angel Win dai itace dai-dai da tsarin tafiyar ahalinsa, saidai gashi gogan yanaso ya basu ciwon kai.

Har aka ?araci wannan zama Abdallah kansa a ?asa, zuciyarsa duk ba daWi kuma shi kansa ba lallai ya faWi dalili ba, kawai dai aransa yaji ce wa bai shirya rayuwar zaman aure da Djameelar ba, kuma badan bata tsantsanta ba a'a, kawai shi dai yasan yabi umarnin zuciyarsa.

Sai bayan la'asar lumus kafin ahalin gidan oncle Alkhusaini suka bar gidan A Muhammad Ousmane da bayyananan farin cikin daya danne ba?in cikin kiyayyar da Abdallah ya nuna wa ?arsu a gaban idon iyayen sa, ba ya kamar Angel da take ji kamar ta cire zuciyarta ta ?ar ta huta, Allah yagani tana son Abdallah, son daya kasa barin ta kula kowa a dandazon samarin da suke waricin neman soyayyar ta, tanada masoya dayawa amma bata wani kulasu, duk dan tana tunanin Abdallah, amma ba komai tayiyu shiWin ba abokin rabonta bane .

Tun daya koma sashen sa bayan barin su oncle Alkhusaini daga gidan bai kuma fitowa ba, tun lokacin yasami kansa dajin kunyar su Ummy, haka kawai yaji bazai iya auren Angel Win ba, kuma badan batakai ya aureta bane a'a, dalilin sa na faWin hakan ma bai saniba.

A masallacin sallar magariba suka haWu da Abby, shi dariya ma ya bashi wai sai sunne kai yake kamar yaga wani surukin sa, bayan sun fito ne Abby ya kama hannunsa har babban falon gidan, Ummy fitowar ta daga nata dakin kenan tana waya, shigowar su yasa ta kace kiran da cewa ''zan kiraki zuwa anjima Yaya'', zama Abby yayi akan kujera kuma har yanzu hannun Abdallah yana cikin nasa, alama yayi masa daya zauna , ba musu kuwa ya zauna kasa yana pasing Abby, a hannun kujerar da da Abby'n yake zaune Ummy ta zauna tare da Wora kanta saman kafaWar Abby, kallon ta Abbyn yayi da ido, wanda ta gama yiwa kallon fassara da kindai ji kunya.
Kawar da kansa yayi ya maida hankalinsa katsokam zuwa ga Abdallah yace ''Yarona muyi magana da kai please, miye dalilinka na?in yarda da maganar auren ka da Djameela, alhali kasan ce wa bama auren bare kaf ahalinmu, koba Angel ba yazama dole matar dazaka aura ta kasance daga wannan family take, akasin haka saidai yakasance yaren mu Waya da ita, ba zan Soye maka ba, sam bamuji daWin abinda kayi Wazun nan ba, kuma da baka santa ko baka san a haWa aurenka da ita ai zaka yiwa iyayen ta kara ko, ka duba yadda suka bar gidan nan cikin nishaWi, dan Allah abun bai baka kunya ba, wallahi sam abun bai yi kyau ba, wai sai kace kanada wacce kakeso zaka aura, a'ina? Kuma yaushe ka fara Soye mana abu Abdallah?'' Abby ya karasa da sakin hannunsa tare da maida bayansa ya jingina da kujerar dayake zaune.


Duk jikinsa yayi sanyi, sam baisan maganar da yayi zata Satawa iyayen nasa rai ba ''amma ai yanzu ma ban makara ba'' ya faWa a zuciyarsa, sashen da Ummy take ya kalla, zuwa yanzu a zaune take a Wayar kujera ta kusa da ta Abby, cikin sanyin murya yace ''Ummy na wai kema bakiji daWin abunda nayi ba ko, please dan Allah kiyi ha?uri, wallahi ba niyyata na Sata muku rai ba, kuma ba wata wacce nayi magana da ita, kawai inaga kuyi maganar ita Angel din shikenan, Allah ya tabbatar mana da alkhairi''.

Shuru sukayi masa su duka ba wanda yace dashi komai daga Ummy har Abbyn, rarrafawa yayi kusa da Ummy ya Wora kansa saman guiwar ta, cikin marairaicewa ya ce ''dan Allah kuyi ha?uri wallahi bazan juri fushi daga gareku ba musamman ma ke Ummy na, dan Allah ki dubeni kuma ai nace na yarda ko? Dan Allah.
Sosai taso ta Wan ja masa kafin ta sauka, dan tanaso ta nuna masa babban kuskuren da zaiyi na bijirewa auren Angel, yarinya mai nutsuwa da hankali kamar ta, ganin duk ya shiga damuwa yasa ta ce ''karka damu yarona insha Allah zakayi farin ciki da wannan haWin da yardar Ubangiji, muma duka a haka aka hadamu da iyayen ku maza, kuma muka yarda muka zauna dasu da soyayya da kuma girmama, gashi yanzu muna alfahari da junan mu kasantuwar mu a karkashin inuwa Waya wato aure, shi aure wata ni'ima ce da Allah ya ni'imta Wan adam dashi dan yayi rayuwa cikin inci da walwala, duk a halittun Allah wa kaga an halattawa aure inba jinsin mutun ba, ko a kabilu da yarurruka mabanbanta ansan aure kuma har gobe ana cikin yin da kuma haWashi, ka lura da kyau yarona mafiya yawon magabata da suka auri matayensu basu suka fitar dasu a matsayin zaSinsu ba a'a, saidai ayi auren haWi ko kuma a ace anbaka ?a, ko kuma an aura maka mata a Sagas'' Wan nisawa Ammy tayi ta kalli Abby ta kuma ce wa ''Yaronka ya amince da zabinmu, ka tayani nusar dashi miye aure da kuma abinda ya kunsa, sharuddan shi da kuma duba yanayi ko cancanta'' Abby shi dariya ma ta bashi, wai ya tayata yiwa Abdallah nasiha dan gane da aure, kamar yaune zasu mi?asa Wakin aurensa.

Abdallah yasami nutsuwa ganin ya dai-daita tsakanin sa da Ammynsa, dama baya tunanin zata iya yin fushi dashi koda na kwana Waya ne, kawai tana kauda kanta daga garesa ne irin na gyara kanka Win nan.


Washe gari
Tun safe suka shiga shirye shiryen walimar da Abdallah ne ya dauki nauyin ta Wan farantawa abokinsu Ishaq, kuma yaji daWi sosai dagashi har ango Umar, baki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login