Showing 66001 words to 69000 words out of 78880 words

Chapter 23 - YAR KANCE free pages na Maman Abdallah.doc

ne, ya jigata ainun, ya susuce.
A razane ya Wago da kansa jin wata uwar tsawa da wani jami'in dake tsaye a kansa ya yi masa.
Baba Ado ne, duk ya koWe yayi ba?i, ya fi ce a hayyacinsa,. Tun ranar daya kama hanyar zuwa Agadez daga Kance dan gujewa abin da zai je yazo kamar yadda Balki ta faWa bayan ya sanar da ita halin da ake ciki na auren Talatu da wani matashin saurayi ya yi ya tafi da ita, a hanyar tausayi da mugun katari suka afka masa.

''Kai zaka yi mana bayanin ina kuma wa zaka kaiwa kayan nan ko sai mun maidaka hannun madaka sun kuma canja maka kamanni?'' wannan jami'in ya wurga masa tambaya a kausashe.

Da ?yar yake Waga bakinsa da ce wa ''yo ni ina na sani YallaSai? Wallahi ba jakata ba ce, na faWa muku wani mutum ya bani in ri?e masa'' ya faWa yana mai ficiccika ?ananun idanunsa da suka ?ara shigewa lungu.

''Ofisa'' wannan jami'i ya kira wani mutumin na daban, ya Wora da ''ku koma dashi, da alama bai shirya faWar gaskiyar ba, shi yasa har yanzu ya?i ya samawa kansa mafita'', yana kaiwa nan ya bar ofishin zuwa wani sashen.

Ba Sata lokaci aka maida Baba Ado cell, aka maida ?yaure aka rufe.
Wani kuka ne ya suSuce masa a lokacin, cikin yanayin da bai iya tantance na saduda ne ko kuma na samun kai a ?angin rayuwa ne ya shiga faWin ''yau ina ganin jalala ni Adamu, tunda nake yawan duniya ban taSa rufe kwanaki uku a hannun Kwalawa ba, sau tari akan kama mu akan laifin shaye-shaye, rigima a kan caca ko faWa irin na ?an duniya wanda ba za'a rasa ba, yau sai gani a hannun mahukunta a bisa laifin fataucin miyagun ?wayoyi, wanda ba laifinsa bane. Haka kawai fa nazo tasha zan shiga Mota, muka haWu da wani salihin bawa mai shige da mutanen kirki, har tanbaya ta ya yi ina zanje, nace masa Agadez, nan faffira ta Sarke tsakaninmu, har ya shaida min shima can ya nufa, dashi muka kama hanya, a garin Tanout muka tsaya direba ya Wauki wasu kaya, haka harda fasinja guda muka samu ?ari, daga Wan ri?emin jakana in zagaya wannan munafukin ya barni da jaraba,ashe jakar tasa ma?are take da tabar wiwi, wayyo Allah na ni Ado naga ta kaina.''
Haka Baba Ado ya yi ta sumbatu yana zuba shi kaWai ransa, yana ta kara maimaita zancen da ya daWe da hardaceshi jerosa kawai yake, dan tun a lokacin da jami'an bincike hanya suka yi ran dashi yake maida musu yadda aka yi da yadda abun yake, amma har yanzu ya kasa ceton kansa, domin kuwa an nemi mutumin daya zana siffofinsa kaf amma an rasa, hakan ya nuna kenan kaya nashi ne.


Agadez

''Naga kina ta raha miye labari ne?'' Abdallah ne da magana lokacin da yake kallon Talatu da fuskarta ke ?awace da kyaukyawan murmushi, sanye take da riga da wando na sanyi, kasantuwar yau an tashi da mugun sanyi a gari, kanta sanye cikin hular kayan, wacce bata iya rufe duka gashin kanta ba?i wulik mai santsi da tsayi ba, wanda martabarsa ta ainahi ta fito ne bayan da Abdallah ya cika da sabulan wanke gashi kala-kala, haka ma mayukan gyaran gashin babu kalar da bai siyo ya kawo mata ba.
''Yaya shayi na haWa irin naku, nasha naji ya yi daWi sosai, in kawo maka zaka sha?'' ita ma ta tambaye shi.
?ar dariya ya yi haWi da kamo tafin hannunta yana murzawa ya ce ''dama a shayi da banbanci ne? Na hukunce irin namu'' ya kai ?arshe lokaci Waya yana mata tafiyar tsutsa a hannun.

Dariya ta shiga yi tana so ta ?wace hannunta amma ya ri?e a ?arshe ma sai ?arasa kamota ya yi gaba Waya ya Wora a kan cinyarsa, ya yin da shi kuma yake zaune a bakin gadonsa na bacci.

''Uhum! Ina jinki fa'' ya faWa yana mai tsareta da ido.
Cunno baki tayi gaba tana faWin ''to yaushe ka bani damar da zan baka amsar.''
Hannu yakai yana kewaye Wan mitsitsin bakinta da yatsarsa manuniya kafin ya ce ''yana min kyau sosai Noor'' ya faWa a marairaice.
?an buge hannun tayi haWi da kamo kyakkyawar fuskarsa da duka hannayenta kafin ta ce ''zaka saurareni ne ko kuma Waukar hankali'' ta faWa haWi da kalla masa harara.
Fuskarsa ya ?wace yana sauke wani gwauron nunfashin da tasan miye ma'anasa, baya san tana ta?ura mata. A ?an kwanakin nan sam baya barin mata baki ya huta, dasun haWu daya haWe bakunansu, tun abun baya tasiri a gareta har ta hardaceshi.

Kamar wasa sai gani ya yi ta kuma kamo fuskarsa a karo na biyu, ta dai-dai dai-daitonsu kamar yadda taga yana yi mata, kafin ta Wora laSSanta akan nasa, ta shiga bashi lafiyar sumba mai kyau da ?awa.

Abdallah abun nema ya samu, ai bai san sanda aikin ya koma nashi ba, daga ?arshe dai maganar shayi tasha ruwa, dan kam an manta babin ta.

Washe gari da da dare yake faWa mata gobe da safe zasu kama hanya zuwa Matamaye, Waurin auren Yusuf.

Da har Abby ya ce zai ce, amma fur baban Yusuf yace wallahi ba za'a Worawa kowa mauyi ba, kawai shi da yara sun isa suje a Waura auren su kamo hanya, to shima da zai je Win dan shi ne alwalin Amarya, bawai Yusuf ya auri Rammatu ba, ko wani ne ya ganta zai aura dole dai Baban shi ne mai bada aurenta.

Talatu tasha kuka da asubahin ranar, lokacin da ?yar Abdallah ya iya cireta daga jikinsa, cikin kuka ta ce ''har sai yaushe zaku dawo Yaya Abdallah?''
Shafar sumar kanta da kullu yaumin take ?ara bashi mamakin kasantuwar bahaushiya da irin wannan suma tasu ta ainihin buzaye yake, cikin kwantar da murya ya ce ''idan muka je yau tuni zamu tarar suna tsaka da shagulgulan bikinsu, gobe da safe ana Waura Aure zamu kamo hanya, a ta?aice dai kwana Waya ne da wuni biyu ?anwata.''
Wani kukan ta fashe dashi harda bubbuga ?afa a ?asa, ''Yaya kwana da wuni biyu! Harma faWa kake kamar ba komai bane'', cikin rigima take magana.
Da ?yar dai ya samu ya lallaSata yai mata wayo, haka kuma ya yi mata tuni da wayar dake hannunta, zai na kiranta kai da kai dan jin ya lafiyarta.

Harma kusan makara ya yi, dan sun yi zasu fita kafin bakwai, inma an samu jinkiri kar a wuce bakwai Win, sai gashi sai kusan bakwai da arba'in ya baro sashensa, shima sai da ya tabbatar Talatu ta yi barci, kafin ya lulluSeta ya ja mata ?ufar da?in. Daya fito daga falon ma key ya yiwa ?ofar kafin ya faWa Sangaren iyayensa.

A Wan gaggauce suka gaisa da iyayen nasa, in da Ummy take masa ?orafi akan ya makara, bayan anan dakin taki jiya suna tsara yadda ya kamata tafiyar ta kasance.

''Sorry Ummy, bacci ya Waukeni ban ankara ba'' ya shiga bata uzurinsa.
''Ai fa! Ai kai kam yanzu ka ?ware wajan bawa mutun uzuri, ga makara akan komai, saSanin da da komai kakan yi shi ne akan lokaci, Allah dai ya shirya min kai.''
?an murmushi ya yi kansa a ?asa, kafin yana ji ta Wora da ''nasa an saka muku kulolin abinbi a bayan mota, zai ishe ku ku karya gaba Waya, dan mai Wan yawa na haWa.''

Godiya ya yi mata sosai yana shirin barin jikin Abby da dama tun shigowarsa yaje ya raSu a jikinsa, in da Abby'n yake zaune a cikin kujera, yayin da shi kuma Abdallah'n ya zauna a hannun kujerar, ya kuma Wora kansa bisa kafaWar Abby'n nasa.

''Yarona da direbobi guda biyu zaku je, kowannensu ya tu?a mota Waya, kai kuma sai ka tu?a Waya, an duba lafiyarsu sosai na kira injiniya Mukhtar yazo har gida ya duba su, Allah ya tsare hanya'' Abby yakai ?arshe da shafar kan Wan Wan'uwan nasa mafi soyuwa a ransa.

Rungume Abby ya yi yana mai godiya, kafin ya saukewa kowannensu sunba a goshi ta fice daga falon da sassarfa, jin motsin watarsa dake faman nusar dashi da kiran da yake shigowa.

Magana ya yiwa direban daya hanga ya fito daga banWakin ma'aikata maza dake a farfafijar gidan, ai da sauri ya yi wa Wan'uwan aikinsa magana kan ya fito su wuce. Hakan kuwa aka yi, motar Abdallah ce a gaba, sai guda biyu dake bin bayansa, basu tsaya ko ina ba sai ?ofar gidan su Yusuf, wanda da ganin ido kawai ya isar maka?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ka gane da sha'anin da ake yi a anguwar.

Cikin girmama Abdallah ya gaishe da Baba, da yake dama Abby ya yiwa Baba bayani kan kar su nemi abin hawa Abdallah zaiji da komai, sai zuwan motoci uku na alfarma bai basu mamaki ba, kawai sai ma shirun tafiya da suka yi, nan da nan suka kama, sai fatan Allah ya dauke su lafiya.

A Takuku suka tsaya suka tsaya suka karya da abincin da Ummy ta yi musu, wanda har ya yi saura dayawa wanda ba'a taSa ba, harma zai iya kasancewa har sukai Matamaye ba lallai su siyi abinci a hanya ba, tunda kalolin abinci mabanbanta kala uku Ummy'n tayi, haka kuma duka dayawa ba laifi.

Sun sha dariya da aka zo komawa mota dan ci-gaba da tafiya, cikin siyasa Baba ya canja mota, ya shiga wacce direba ke tu?awa a madadin ta Abdallah'n daya zaSaSSen ya darje ya shiga tun a ?ofar gida. Sai dai tun ba'a je ko'ina ba ya fara salati da sallallami kan irin gudun da Abdallah yake shatatawa,shi ne yanzu ya fece da hujja.


Acan gida kuwa ?aran wayar daya sa?ala mata ita a hannun bayan tayi barci ne ya tashe ta, a hankali ta dade kanta da rabi ya Wan sara mata, Wan kukan nan da tayi ne ya haddasa mata.
Sai da ta zauna WoWar akan gadonsa kafin ta Waga kiran ta kara a kunne, tunda dai tasan kiran nata ne, tun ranar da wayar nan ta zama na a wurinta take wabi kira bai kuma shigowa ba idan da daga gareshi ba, irin ya fita haka zai kirata suyi ta fira tana masa shirme.

''Assalamu alaikum'' ta faWa murya a sanyaye.

Ajiyar zuciya ya sauke a bayyane kafin ya ce ''Amin wa'alaikissalam, ?anwata, kin tashi a baccin ne?'' ya faWa kamar da raWa.

''Kai!! kai!! Kai!! Munafunci yanzun nan magana kayi?'' ce war Yusuf dake a bayan motar, bai ankara ba kuma Ishaq ya zare wayar dafa matsetan da ya yi tsakanin kaii da kafaWarsa, katse kiran yayi yana wurga masa harara ya ce ''wallahi yadda kake kashe muryar nan ba zamu zira maka ido ka kifar damu akan hanya ba, haka kurum!idan kai kasan miye auren ai mukam sai kayi mana asara kafin mu karance shi.''

Kicin-kicin Abdallah ta yi da fuska yana yiwa Ishaq kallon ?asa-?asa, irin ka matu?ar rainani Win nan, a she?e ya ce ''wannan dai shiga ha??i ne, kasan da wana nake magana kuwa?'' ya wulla masa tambaya.

Dariya Yusuf ya yi kafin ya ce ''yi da waye ya wuce wannan yarinyar, al?ur'an ni ba tun yau ba na gama gane ta canja ka tas, gaba Wayanka ka zama wani baban soyayya.''

Shima Abdallah dariyar ya yi da ce wa ''Wan da ido, kace rayuwata kake kallewa fes ka hardace.''

''To da me kake tunani? KaWai yi a hankali wallahi, kar rawar kan nan da kake yi yasa Ummy ta gano ka da wuri, kuma yana kamata zuwa yanzu ace ka samu mafita Abdallah, babu fa'ida a zamanka da yarinyar nan a haka fa, rayuwar aure a Soye! Abun da matu?ar wahala da, wai danma kai ne wallahi, nikam da ni ne ai tuni akagama gano n'' ce war Yusuf.

Cikin damuwa Abdallah ya ce ''wallahi nima abun ya fara damuba Yusuf, yanzun da wata biyu watannibiyj muke shirin rufawa, amma har yanzu jiya iyau, waccen mafitar dai Waya da nake ganin ita ce hanya mafi saurin da zanbi in magance damuwar nan ita kaWai ce, kuma in sha Allahu muna gama hidimar bikin nan zan yiwa Abby magana kan zancen auren Angel, asa a kurkusa kawai, ni kuma a ranar Waurin auren zan faWa musu komai game da Noor, nasan a lokacin zasu fahimceni, za kuma su karSi auren kodan biyayyar auren zaSinsu da nayi ba dan ina so ba.''

Fatan alkhairi suka yi masa kafin suka canja wani maudu'i a fitar tasu.


Talatu

Mi?ewa ta yi haWi da sauka daga gadon tana mi?a, ayyanawa take a ranta ?ila network ya hana shi jin amsar da ta bashi daya yi mata tambayar, daga ?arshe ma sai kawai tafa kiran ya katse.

Cikin nutsuwa ta fara gyara shinfiWar gadon, kafin ta Wore da gyara masa Wakin, duk da ba wata ?ura ko WauWa yake da ba, kawai dai yanzun ba kullum yake bawa ma'aikata damar gayara masa Wakin ba, musamman idan a nan Wakinsa suka kwana, sammako yake yayi babakere a falo, koda anzo iya falon kawai ake gyarawa yace ya wadatar.

Wayarta taje ajiyewa kan Wan ?aramin sib Win dake gefen gado, sai kawai ta sirce ta faWa baya. Cak ta Wauke shi ta ajiye a gefe kasancewar ba wani nauyi gareshi ba. Wayar ta Wauka, sai kuma taga wata enveloppe babba a shinfiWe a wurin, wacce da gani ita ma faWa wa ta yi kamar yadda wayarta ta faWa a yanzu. Hannu takai ta Wauki envelope Win kafin ta maida sib Win wajensa.

Haka kawai ta kwaWaitu da san ganin abinda ke cikin envelope Win nan, irin kamar idan taga tana da ya?inin zata iya karantawa idan har ya kasance rubutu ne. Tabi umarnin zuciyarta lokacin da take zama akan sib Win, da bismillah ta zaro abinda ke ciki wanda saida ta sa hannu ta iya gane takarda ce.

Ras! Gabanta ya faWi, hankalinta ya tashi ainun, ganin fuskar Innarta zane a wannan takarda, innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, miye haWin Inna Balki da Abdallah da har yake da cofin fuskarta? Ita dai yasan a zamansu dashi na tawon wata biyu wata magana mai kama data innarta bai taSa haWa su ba.

''To ya aka yi haka?'' ta tambayi kanta.
Ganin batada amsa kuma babu mai bata ita a lokacin sai kawai ta mi?e cike da jimami da taraddudi, ta ajiye zanen akan sib Win ba tare da ta maida shi cikin envelope Win ba.
Jiki a saSule ta gama gyaran Wakin, kafin ta wuce nata Wakin ta gyara, a ?arshe ta faWa toilet dan yin wanka, tunani kuwa yi take tana kwancewa, amma ta barwa ranta abun zuwa dawowarsa, in yaso sai taji ta yadda aka yi har ya samu hoton Inna Balki.


Matamaye

?arfe biyar na yamma suka iso garin, da ace tu?in Abdallah aka bi da tuni suka tsufa da isowa garin nan, dan wani irin gudu ya dinga tsalawa kamar yana cikin sahara, sai ya bawa su bana tazara mai yawan gaske, kafin ya tsaya ya jira su iso, haka kuma zai sake buWe wuta, daga ?arshe dai Baba ya dokawa layinsa, cikin Sarin rai ya ke faWin ''Abdallah zan Saci ranka wallahi, shin bakada hankali ne kome?'' dama Baban su Yusuf badai zafi ba, to sai a sannan ya nutsu yake tu?i dai-dai gwargwado, a haka har suka iso.

Anyi musu tarba ta musamman, Kawu Abdu ya rasa inda zai ajiye Wan'uwansa dan murna, haWi da dattawan direbobin nan.

Suma su Yusuf masaukinsu aka kai su, inda tuni gari ya kuma katsamewa da hayaniya, dan kuwa albarkacin uban lefen da aka nunawa jama'a na Rammatu, shi yasa dayawan mutane suka Wauka har auren ma zai kasance na musamman, kamar yadda kayan lefenta akaf garin babu wacce ta taSa samun irin su ko a tarihi.

Rana na faWuwa duka dattawan nan suka haWe a masallacin kusa da gidansu Rammatu, inda ana gama sallar magariba aka fara karatu, kamar dai yadda yake faruwa a mafi yawan sabgar al'ajirar makaranta ?ur'ani, musamman masu karatun warash (wato karatun allo). Sauka aka Wauki tun daga fatiha, in da za'a kwana ana yi, har zuwa lokacin Waurin aure.

Hayaniya kota ina, ?an'mata da samarin gari ana ta ciriniya, an shirya gagarumin invitation dan wannan aure, wanda ya haWa da gayyatar wasu matasan daga makwabtan garuruwa.

A ?ofar gidan su Shamsiyya ake hidimar, dan ita ta Wauki nauyin komai, haka na tuni ta gama ?ulle katanga tsaf dan da ita za'a je rakiyar amarya zuwa Wakinta.

Abun gwanin ban sha'awa, aka kunna ?arancin rediyo mai sauti, ana ta ra?ashewa da wa?ar (Ali acibilli), wata wa?arsa mai taken Aisha.
Amarya da ango zaune a gefe sai love Winsu suke zubawa, dan tuni suka yi zurfi a soyayyar junansu cikin watanni biyun nan.
Shi kam Ishaq ya zama abokin Shamsiyya, dan duk inda ta Wauke ?afa anan yake ajiyewa. Babu laifi Shamsiyya tanada ?ar wayewarta, dan har tama fi Rammatu sanin dayawan abubuwan zamani, daya ke tana da yayarta dake aure a can Damagaram gari, to takan kai mata zira lokaci bayan lokaci, shi yasa take da wayo sosai, gata da barkwancin tsiya.

Tsaki yake tafanan bugawa yafi a ?irga, tun Wazu yake tura kira wa layin Talatu amma ko fita kiran ya?i yi bare yaje inda ya nufa, yadda hankalinsa ya tashi akan rashin jin yarinyar ko akan su Ummy bai tashi ba, dan har yanzu bai kira sunji ya suka sauka lafiya ba. Ya rasa yadda zai yi, ji yake kamar ya saki kuka a tsayen nan, gashi babu halin yasa a duba masa lafiyarta.
A karo na barkatai ya kuma tura kiran, sai kuwa ya tafi, amma wani rashinsSa'a sai aka ce masa wayar a kashe, saura kaWan ya dangwaza tasa wayar a ?asa, sai kuma wata zuciyar ta haneshi.
Yana shirin tura wani kiran kiran Abby ya shigo masa, a saSule ya Waga da sallama a bakinsa.....

Wallahi na gaji, mu kwana anan gobe sai mu Wora da yardar Allah.

Gashi dai Talatu taga zanen fuskar Innarta a Wakin Abdallah, wanda wannan ya tabbatar mata da wani abun da bata sani ba.

Shin ya zata kaya ne? Mi kuke tunanin zai faru idan Talatu ta tunkari Abdallah da maganar zanen da ta gani?

To kodai Talatun Inna ita ce Talatun Abdallah!
Yanzu aka fara wasan, sannan saura pages biyu book one ya ?are, wanda shi ne free.

Karki yarda mu fara two

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login