Showing 39001 words to 42000 words out of 78880 words

Chapter 14 - YAR KANCE free pages na Maman Abdallah.doc

Balki da yaronta Ummy'n ta kuma basu mazauni a falon kafin a gama gyara musu wajen.

A Warare suka zauna a ?asan lallausan carpet Win dake falon, yadda Al?asum ya ruWe da ganin falon nan ko Innarsa bata nuna wannan ?auyancin ba, ?ila kodan dama ita tasan falon ne tun dacan a baya oho, sai dai zubin kayan da kuma launin pentin daya banbanta da wanda ta sani a baya. ''Baba! Ai nayi tunanin babu falon da yakai falon wancan gidan tsaruwa, ashe wancan duka wasa ne, ku kalla kuga wannan gidan kamar ba'a cikin ?asar nan yake ba'' Al?asum ya faWa ?asa-kasa yadda yake tunanin babu wanda zai iya jinsa idan ba mahaifiyarsa da yake yiwa raWar ba.

Sai dai kam tuni Ummy mai kunnen mesa ta jiyo shi, a lokacin da ta dinfarosu ne da nufin ce musu su taso ta tayi musu iso zuwa ga masaukinsu.

Note:
WANNAN AIKIN DA ZATA IYA SAKA ?AN AIKI SUYI MATA SHI NE, FIYE MA DA HAKAN TANADA FAWAR DA ZATA IYA SAKAWA AYI MATA FUK ABINDA TAKE SO, AMMA DA YAKE TASAN MUHIMMANCIN GIRMAMA BURI DA KUMA MURADIN MIJI, HAKAN YASA TAKE ZARTAR DA KOMAI KAMAR YADDA YA CE, BA TARE DA TA Yi LA'AKARI DA HALIN JIMAMIN DA TAKE CIKI BA, TAKE TAFIYAR DA KOMAI YADDA YA DACE KAMAR DA, BABU WANI AIKIN DAYA KASANCE ITA TAKE YIN SHI DA A YAU BATA YI SHI BA, DUK DA KUWA HALIN DA SUKE CIKI. WANNAN ITA AKE KIRA DA (MA CE TAGARI), MAI YIN KOMAI CIKIN NUTSUWA DA KUMA DUBA CANCANTA, MAI MAYE GURBIN BA?IN CIKINTA IZUWA FARIN CIKI DOMIN SAMUN WALWALAR MIJINTA.


*
Cike da jin kunya Baba Balki ta sunne kai a ?asa ganin Ummy na daf da isowa inda suke, a cikin zuciyarta kuwa ce wa take yi ''babu shakka ta ji maganar da wannan yaron ya yi, Allah ma yasa ba aibata su ko kushe su ya yi ba.''

''Yawwa ku taso mu tafi ko, an gama gyara sashen, sannan har kayanku an kai su can'', Ummy ta katse wa Baba Balki maganar zucin da take yi.

Da to kawai suka amsa tare da mi?ewa suna masu biye da bayan ta, a haka har suka isa sashen.

''Wannan shi ne Sangaren da Abby ya ginashi domin ku shekaru goma sha biyar kenan, ana daf da gama ginin ne wannan tsautsayin ya gifta, za ki zaSi Wakin da ya yi miki, tunda dama Wakunan guda uku ne, in yaso shi ma yarona sai ya shirya kayansa a Waya, ku saki jikinku, ku zauna anan Win na tsayin rayuwa, babu abinda zai gagara in sha Allah'' Ummy ta yi maganar tana nuna musu Wakunan da suke guda biyu a jere, sai kuma Waya da bai kai wa?ancan girma ba daga gefen su, da madafa a sashen, ga kuma banWakuna a kowane Waki, da yake akwai sib-drawer irin wannan mai haWe da asalin ginin nan da ake yi, a lokacin da ake ginin nan ba ?ananun kuWi suka tafi ba, kai kace Wa Abby'n zai aurar yake gina masa wajen da zai zauna, ba wai ginin domin direbansa ba.

Da ?wallar mamaki da kuma tarin farin ciki da kuma ?unar rai duka a lokaci Waya Baba Balki ta ce ''wallahi ni har kunya nake ji Hajiya, ba wai ni ba! Ko shi Babban Al?asum Win ba lallai ya taSa tunanin yana da irin wannan matsayi har haka ba, na tabbata da ace ya sani da bazai yi tunanin aikata makamancin abinda ya aikata ba, bayan gudun hijirar da muka yi na tsawon shekaru, gashi mun dawo har yau dai a matsayin iyalansa, a maimakon ku wula?anta mu sai ma wurin zama kuka bamu, a madadin ku kore mu sai kuka jamu a jikin ku, babu shakka akwai waliyyan Allah a Soye a cikin al'ummar zamanin nan'', ta fashe da wani irin kuka a ?arshen zancen ta.

Hannu Ummy ta sa ta dafa kafaWarta tana mai girgiza mata kai alamar ta daina kuka kafin ta ce ''bai kamata kiyi kuka ba gaskiya, sannan kuma bana san wannan sunan wai Hajiya, ki kira ni da sunana na gaskiya wato Gaisha, ko kuma ki ce dani Ummy'n Abdallah, kar ki damu kanki dayawa dan Allah, ni da ke da kuma sauran jama'ar da abin nan ya shafe su babu wanda yasan abinda Ubangiji ya rufe game da wannan dawowar taku nan, ta yiyu Allah ne zai kawo wata kyakkyawar mafitar da za ta yi sanadiyar dai-daituwar nutsuwar zukatanmu, da kuma kwanciyar hankulan mu. Na tabbata da yarona Al?asum bai faWa soyayya da yarinyar wancan gidan ba, to da yanzun ba kuyi tunanin zuwa nan ba, faruwar hakan kuwa ya warware mini wani kokonton da yafi caza mini kai a baya, kafin zuwan wannan rana a kullum zargina akan maigidanki ?ara ?aruwa yake, amma sai wani tunanin na daban ya faWo cikin kwakwalwata a yau, koma dai miye Allah'n daya kawo wannan ranar shi zai kuma kawo wata wacce zata fayyace mana komai da yardar sa'', Wan nunfasawa ta yi kafin ta kuma ce wa ''bara in koma na bar aiki a kicthing.''


Daga Uwar har yaronta da ido suka bita, sun kasa kuma ce wa komai, a wannan lokacin Baba Balki ji take a zuciyarta ce wa matu?ar dai ya tabbata maigidanta ne da aikata wannan laifin, to ko ita ba zata yafe masa ba.


**************

Burkin motar ya ja ya tsaya a dai-dai wajen da ya ?udura a ransa za suje.

Shiru kake jin motar babu mai ce wa komai, sama da mintuna biyu suka yi a haka, kafin daga ?arshe Abby ya buWe baki da faWin ''Yaya anan ne aka yi taron da safiyar yau Win nan, kasancewar ina daga cikin manyan ba?i mune a can cikin lungu san dandamali, daga nesa na hangeta, kuma na gama tantancewa ita Win ce a lokacin da muka haWa ido da ita, kafin in ce na kutso ta tsakanin mutane tuni ta arce ta bar wajen, da yake dama tana daga mashigar hall Win ne, banban miye ya kawo ta ba, amma nasan bazai wuce sunsamu labarin ana taro na manyan mutane suzo ko Allah zai sa su dace da samun alkhairi daga gare su.''


Shuru Dady ya yi masa kamar ba dashi yake ba, sai ma danna waya da yake yi da alama da abinda zai yi da ita.

Kira ya tura zuwa ga wata number, yana mai kara wayar a kunnensa, bugu Waya a na biyu wanda aka kira ya amsa kiran, cike da girmamawa ya ke faWin ''barka da wannan lokaci ?allaSai, ashe yau Agadez tana da manyan ba?i kasancewarku a cikinta, ?allaSai naga lambar ?asarmu kuka kira da ita, yaushe a gari?''

Sai da ya Wan nunfasawa kafin ya ce ''kuma duka a lokaci Waya nima zan baka amsar duka wa?annan tambayoyin fisabilillahi, yaushe ka canja aiki daga Lauya zuwa ?an jarida? Uhum faWa mini in ji'', ce war Dady da afakaice ya juye tambayoyin da Barister Jallo Ahmed ya yi masa ya maida masa makamantansu.

Ba Jallo ba, hatta Abby dake gefe saida ya murmusa dajin rikicin Dady, daga can Jallo ya kuma ce wa ''yau kam ?ar jayayya ce da gani, to Allah ya huci zuciyar Alhajin Allah, Alhajin Agadassawa, kuma Alhajin jama'ar Algeriya'', ''zan Wan jima a cikin garin nan, akwai ayyuka da yawa a gabana, nasan za kayi duk abinda ya dace'' faWin Dady daya kawar da wancan zolaya da kirarin da Barister Jallo ya yi masa.
''Ok to ba damuwa, zuwa gobe da safe sai in shigo idan ba damuwa.''
Da to kawai Dady'n ya amsa shi kafin ya kaste wayar.

Dubansa ya maida zuwa ga Abby da ce wa yanzun na gama fahimtar duka laifina ne a duka lalacewar lamurranka, da a ce na tsaya wajan gina ka da baka garkuwa a matsayina na babba agareka da wasu abubuwan ba zasu taSa faruwa ba, koda bazan iya kare ka daga abinda Ubangiji ya hukunta a kan ka ba amma nasan zaka samu garkuwa sosai, duba da abinda ya faru shekaru sha biyar da suka wuce, da a ce akwai securitys dayawa da kuma makaman kariya a gidanka a waccan ranar da ba'a fita da yarinya sukutum daga gidan ba tare da ansani ba, haka kuma a yau da ace akwai masu tsoro a tare da kai da matar vata gudu bayan ka ganta da idanunka kuma ta Sacewa ganin ka, akan wannan ina jin tsoron Allah ya kamani ?anina, yayin da ni ina can 8na rayuwa kamar wani shugaban Nahiya bama ?asa ba, ace ?anina Waya tak tilo yana yawo da damuwa na tsawon shekaru amma na kasa magance masa wannan damuwar, babu shakka a yau abun ya dameni sosai, bazan bar garin nan ba har sai naga rayuwarka ta canja yadda ya kamata, ita kuma waccan matar nayi maka al?awari matu?ar tana cikin garin nan bawai ta fice ba sai na gurfanar da ita a gabanka cikin mako Waya, wannan al?awari na ne, sannan kuma kalma ta ce.''

Kallonsa kawai Abby yake da zallar ?aunar Wan'uwansa da a kullum take ?ara ?aruwa a cikin ransa, shi yasan hakan a cikin ransa da ace wani rai zai iya fansar da nasa ran akan rayuwar wancan ran to da yayansa ya sadaukar da ransa dan dawwama da nasa ran na har abada.


Cike da shau?i da kuma murya mai cike da rauni Abby ya ce ''madallah da Wan'uwa nagari kuma mafi nagarta a cikin ?an'uwaye na wannan zamanin, Allah ya ?ara maka lafiya Yaya ya baka ladan Wawainiyar da kake yi dani da duk wani wanda yake a ?ar?ashina, Allah ya ?ara maka wuyan Wauka ya ?ara girma da lafiya mai Worewa da anfani, ya albarkaci zuri'a ya kuma shirya mana su bisa kan tafarki madaidaici'', da amin Dady ya amsa yana mai kama hannun Wan'uwan nasa ya ri?e ?am kamar wanda za'a sace masa shi kafin ya ce ''in sha Allahu wannan Muhammad Win nawa sai ya zama alfaharin wannan garin, wannan ?asar, kai harma a lafiyar Afirika dole a ambaci sunansa, da yardar Ubangiji daga gobe za'a fara kaWa gangar siyasar ka, ina fatan ka shirya wa hakan, ka dage, ka kuma jajirce, a wannan karon bawai jama'ar dake kewaye dakai bane suke ro?on da ka shiga harkar siyasa ba a'a, Yayanka ne yazo ma da tayin da yake tunanin ba zaka juya masa baya ba, zan tsaya maka da iya ?arfin da nake dashi, alfarma da duka abinda nasan inada shi, ni dai abu Waya nake so in ji daga gare ka shi ne eh yaya na karSa.''

Sai da Abby ya share ?wallar da ta taru masa a kwarmin idanunsa kafin ya Waya baki da ce wa ''na karSa Yaya'', ya faWa kamar yadda Wan'uwan nasa ya ce yana san ji daga garesa.

''Ma sha Allahu, to Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa, kuma ya yi mana zaSin alkhairi, ya shiga al'amarin ya kuma sa jama'ar da zamu faWa harakar domin su su anfana'', da amin Abby ya amsa shi.

A hanyarsu ya komawa gida ma Dady sai kiraye kiraye waya yake ta yi, wani kiran idan yayi zai bada umarni ne, wanin kuma kana jin yadda yake amsa maganar kadan da wasu wa?anda suke jin suma wasu ne ya ke magana, dan ko kai waye dole ka samu wanin a sama dakai wannan ?a'ida ne, idan da babu fifiko a tsakankanin mutane babu shakka da babu wanda zai samu nutsuwar yin cikakkiyar ibada, a ?addara duka mutanen duniya talakawa ne basada komai, to suwa ye zasu sadaka, suyi kyauta, suje Hajji dan sauke farali, waye zai fitar da Zakka? Dadai sauran ababen da dayawan lokuta sai mai dashi ne kawai yake iya zartar dasu. Idan kuma aka ce duka Mutanen duniya masu kuWi ne su waye zasu zama Malamai, waye zai yi kiwo, wa zai noma abincin da za'a ci a rayu? Su waye zasu na sada zumunci? Waye zai juri zama da Wan'uwansa? Ta yaya za su yi kasuwanci? Idan sunada kayan kasuwar ina zasu kai su? Su waye zasu siya idan yana samu wajen da zai tallata hajar tasa?.........

Babu wani abinda Allah ya halitta a duniyar nan da bashi da manufa a halittarsa ba, komai ka gani da amfaninsa, takala da tasa rawar ganin, haka mai mai akwai, abu Waya ne anan shi ne kowa ya maida hankali ya nemi duniya da ?iyamarsa.(Inji ni) =??


Ana daf da kiran sallar magariba suka koma gida, wanda ya yi dai-dai da tsayawar motar Abdallah da shima shigowarsa kenan gidan, dan Wazun yana ajiye su Baba Balki ya kuma fita daga gidan, bayan ya ji sa?on Abby daga bakin Ummy.

A tattare kusan su huWu suka tafi masallaci, Dady, Abby, Abdallah da kuma Al?asum daya fito daga sashen da za'a iya kiran sa da bangarensu shi ma da nufin zuwa masallaci.


Bayan dawowar su babu wani wanda ya zauna a falo, kowa Wakinsa ya wuce dan yin wanka, haka ma Abdallah ya tura ?ofar falonsa ya shiga da sallama a bakinsa, duk da yasan babu kowa a falon yin sallama a kullum kafin shigowarsa bai kasa zama Wabi'arsa ba, ko da can baya kenan, bare kuma yanzu da yasan da wani ran a sashen koda ma ba a falon take ba.

Sai da ya shiga Wakinsa ya yi wanka ya zira jallabiya mai gajeren hannu tare da feshe jikinsa da turare kafin ya nufi ?ofar Wakin da take, a hankali ya Wan bubbuga ?ofar.

Lokacin fitowar ta daga banWaki kenan ta ji ana buga ?ofar Wakin, a wannan karon ma kallon jikinta ta yi, yanzun ma wanka tayo bayan ta gama sallar magariba, ita wannan abu ya yi mata dai-dai ta wani Sangaren a cewarta, dama can ita Win ma'abociyar san yin wanka ce, amma a mafiya yawon lokuta Innarta take hanata yi koda kuwa ta yi niyyar yi, a da lokacin tana yarinya wanka ta ke yi koda ruwan ro?o ne, kuma a lokacin tafi haka kyau da Wan haske, yanzu a ?an shekarun nan da hankali yazo mata, ta kai matakin da Innartata take tunanin yakai ta mora daga kyau, haske da kuma surar jikin da Allah ya bata sai ya kasance ita Innar da kanta ne take so tana Waukar wanka, wai dan tayi kasuwar da zasu na samun kuWaWe bawai tunanin samun mijin aure ba, a lokacin duk bata san ce wa akwai wata kitumurmurar da Innar take kullawa wajan san ganin rayuwarta ta lalace ba, a lokacin kawai tana ganin san duniya ne uwartata ta Worawa kanta, amma bayan faruwar komai na daga zuwanta Kance, da yadda Baba Ado'n da take yi wa kallon uba mahaifi ya furta zance ya yanke akan lallai sai ya aure ta tasan da sauran kallo, kwatsam sai ga wannan bawan Allah'n ya kawo mata Wauki da tallafi a lokacin da tafi bu?atarsu sama da komai, babu abinda za ta yi masa ta biya shi hallacin da ya yi mata a wannan rayuwar.

''Ina yini'', ta faWa tana bashi hanya bayan ta buWe masa ?ofar ya shigo.

Saida ya zauna a bakin gado kafin ya ce ''lafiya ?alau ya kike?'', ya tambaye ta.

Kanta a kasa aWan nesa kaWan da inda yake ta ce ''dadama alhamdulillah.''

Nazari ya yi na wasu ?an sakanni kafin ya yi mata nuni da gefen shi da yatsa, sanin abinda hakan ya ke nufi yasa ta fara takowa zuwa ga cika umarninsa, haka kawai idanuwansa suka sauka akan yatsun ?afarta lokacin da take takowa, ?an madai-daita dasu ?an das, da fararen faratanta da babu ko digo Waya na sauran lalle ko wani abun na daban a tattare da su.

Ajiyar zuciya ya sauke tare da fuskantar ta, yadda yaga ta wani Wosanu ta zauna kamar daga ance arr ta arta da gudu sai abun ma ya bashi dariya.

Da murmushi a kan fuskarsa ya ce ''wannan zaman fa Madam? Kamar mai jin tsoro.''

Gyara zaman kawai ta yi ba tare da ta ce dashi komai.

''Kiyi ha?uri kinji, abubuwa suka mini yawa, na barki ke kaWai a sashe ga kuma kaWaici'' ya yi maganar kamar wanda yake tare da wata zankadeWiyar macen da takai ya zauna da ita har haka.

Cikin muryarta ta nutsuwa ta ce ''to ai dama ba lallai sai ka zauna a tare dani ba, kanada abun yinka, kana tare da iyayenka, kaga dole ne ka tsaya akan al'amuran ka kamar da, bazai yiyu daga taimakona da ka yi ka rarraba hankalinka akai na ba, iya hakan ma na gode sosai, Allah ya saka da mafificin alkhairi.''

Shiru ya yi yana nazarin kalamanta, sai dai shi sam har yanzu bai ji a ransa ce wa wai ya aure ta ne dan ya taimaka mata ba a'a, kawai ya yi hakan ne bisa umarnin zuciyarsa, koda yanzun bai yarda da abinda tunaninsa ya fassara masa game da hakan da ya yi ?undunbalar aikatawa ba, yasan zuwa nan gaba kaWan zai fahimta ne, kafin nan zai bata kulawar da duk ya dace ace ta samu, zai zame mata garkuwa kuma bango majinginar dafawa, zai zame mata inuwa dan shiga taji sanyi a ranta, kuma in sha Allahu sai ya gano komai daya danganci rayuwarta kafin komai ya dai-daitu masa, wannan al?awarinsa ne.

''Kar ki damu, in sha Allah za kiyi farin ciki anan Win, ni dai abinda kawai na ce shi ne ki taya ni Soye kanki a tanan, kar ki yarda wani ya ganki bisa ganganci, bayan wucewar duk wannan zan sanar dake wani muhimmin abun da yakamata ki sani, yanzun zan tafi masallaci ne, idan na dawo zan shigo miki da abinci, kafin shima in san abun yi, dan ba zai yiyu in Waukoki in ajiye anan bana baki cikakkiyar kulawa ba'', ya faWa cike da jimamin rashin kyautawar da yake tunanin ya yi mata, na keSanceta daga cikin mutane, rashin sha?ar iska da kuma tauyeta ta wasu fannonin da ya kamata a ce ba hakan ne ya kasance ba.

''Laa wallahi karma ka kawo mini dan bana jin yunwa, na ?oshi, ni da cin wani abun kuma sai gobe in Allah ya kaimu'', ta faWa tana kai hannunta saman cikinta tana mai yawo dashi.


Ita abinda take yi daban, ya yin da shima ya shiga wani tunanin na daban,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login