Showing 45001 words to 48000 words out of 78880 words

Chapter 16 - YAR KANCE free pages na Maman Abdallah.doc

kai alamar a'a, badan ransa yaso ba haka ya zauna.


Da gudu Malan Misbahu wanda shi ne direban Abby ya taso yana mai buWe wa Abby ?ofar gida tun ma kafin mai gadin ya yi yun?urin yin hakan Win, ?ifar motar ma shi ne ya buWe masa gidan baya, tare da buWe gidan gaba ya zauna a mazauninsa na direba, da yake dama Abby ba wani kashe motar ya yi a lokacin da yazo ba kawai sai suka bar ?ofar gidan, da addu'a a kunsa, da kuma fatan samun sau?i ga uwargidan adalin mai gidansa, wanda ya zama gatansa shi da iyalansa, ba zai gushe ba a kullum yana mai yi masa addu'ar Allah yasa ya gama da duniya lafiya ya kuma ?ara masa buWi da zuciyar imani, ya azurtashi da zuri'a Wayyiba.


Aiki sai mai shi, ba'a Wauki mintinan biyar bayan isowarsu asibitin ba sai ga idanun Ummy sun buWu, a kuma raSin sa'a aka gama gane matsalar ta, abun nema ne dai ya samu, wato tana Wauke da ?aramin ciki na tsawon makonni uku, tab-Wijan! Zance murna da farin ciki ba'a maganarsu, a yadda Muhammad ya rikice a lokacin daya tabbatarwa kansa ce wa matarsa tana da cikinsa a jikinta, sai ya zama abun kallo tun daga asibitin nan, sauran jami'an lafiyar dake a ?ar?ashin sa manya da kuma ?anana sai taya shi murnar suke ana yi masa barka.


Wata ?ar ?warya-?waryar walima ko kuma in ce liyafa aka shirya wa samuwar cikin nan, wanda ?asa ya ?asa haka mutan Algeriya suka zo aka yi wannan shagalin dasu, wanda murnar da Dady da Mamma suka nuna sai mai gani da sauraro yace sun ma fi masu abun ?aunarsa, uwa uba Dady da tun lokacin daya samu kiran da Wan'uwan nasa ya faWa masa sun kusan samun ?aruwa ya kasa samun sukuni, mintuna biyu uku sai kaji ya ce ''idan Allah ya bawa ?anwata lafiya'' da yake haka yake ce mata ?anwata, ko kuma kaji ya ce ''nima na kusan samun ?ata ko yarona.


Kusan wata biyu suka Wauka a Agadez kafin suka koma, a hikimar Dady na tsawon zaman kawai saboda Gaisha ne, a ce warsa har sai ta gama laulayin farko mai wahala kafin su barta, idan har za ta yi irin na ?ar'uwarta ne to ba lallai ta yi rainon ciki ya bata wahala ba, dan a lokacin samuwar cikin Abdallah basu sha wata wahala ba, idan aka cire yanke jikin da tayi ta faWa, wanda shi kuma shi ne ya yi sanadiyyar gano da wanzuwar cikin.


Wata Waya-Waya sai da cikin nan yakai watanni bakwai Ummy tana lafiya, bata wani ciwo ko kuma wasu ?an ?ananan lalurori irin na masu ciki irin wannan, matar likita ce ita, dan haka take samun cikakkiyar kulawar daya dace.

A gefe Waya kuma Abdallah kullum yana ma?ale da jikin Ummy, a wani sa'in haka zai zauna yana ta zuba zance shi kaWai, wai shi yana magana da ?ar ?anwarsa da take cikin ne, a wani lokacin kuma har hannu yake kaiwa saman cikin uwartasa ya shafa yana mai ce wa ''sai yaushe ne zaki zo gareni ne ?anwata?''.

Ita dai Ummy sai dai tayi murmushi kawai, wani sa'in kuma ta shafi sumar kansa da ce wa ''waye ya ce maka ?anwa za'a haifa maka ne yarona?'', yakan ce ''haka kawai Ummyna, ina ji a raina kawai abokiyar fira za'a kawo mini, Ummy! Dama kar ku manta nine zan dinga yi mata wanka ina shirya ta, Ummy har wanki ni zan dinga yi mata, sai ka maida ita ?ar gata babua' mai taSa ta a gabana ya zauna lafiya, Ummy kuma koda ta girma nine nan zan ci-gaba da rainonta, ni zan na koya mata karatu, ta yadda za ta zama hazi?a sananna wacce kowa zai santa a ?asar nan'', ire-iren wa?an nan dama makamantansu sune suka zama wuridin Abdallah a duk sanda ya zauna, koda makaranta yaje to Allah Allah yake ya dawo ya zauna a daf da Ummy'nsa, ta yadda yake kula da zama da tashinta, kaWan yaga ta yun?ura zata tashi daga zaune zuwa tsaye, ko kuma gurin zama taWan kuskure ta zame kodai wani abun da ya yi kama da wannan, haka zai iso wajan jiki har yana masa Sari, randa ya kasa ha?urin jurewa haka zai ce da Ummy ta dinga kulawa dan Allah.

A lokacin da Ummy ta shiga watan haihuwa ita kuma Mamma tana can tana fama da rainon cikin data samu, wanda a lokacin yana da watanni shida, to wannan ya Wan so yazo mata da damuwa, wanda har aka hana ta garaje ko kuma wawan motsi a asibiti, ko irin ayyukan gida amhaka aka ce na nema mata wanda zai dinga yi mata su, dan ana bu?atar ta zauna Wam, saboda tun farkon samuwarsa da wata biyu da ta fara ?an ciwace- ciwace, ana zuwa asibiti likita ya shaida musu ce wa bakin mahaifa a buWe yake, dan haka suna wani wawan garaje cikin zai iya Sarewa a koda yaushe. Wannan shi ne dalilin Waya hana wa?annan ?an'uwa biyun haWuwa guri guda a lokacin da Waya take gwagwarmaya akan guiwa, wato a lokacin da take kan gadon haihuwa a Agadez, ita kuma tana can zaune cikin falonta na alfarma dake babban birnin ?asar Algeriya, inda duk wata addu'ar da yazo mata a baki yi take yi, dan nemawa ?ar'uwarta sau?i da sassauci a gurin Ubangiji.


Cikin ikon Allah mintinan arba'in bayan zuwansu asibitin Ummy ta santalo ?arta mace mai she?in haske da annuri, abinda ya yi matu?ar bawa mutane mamaki shi ne yadda Uba, Uwa, da kuma sauran jinjirar suke farare tas da su, sai dai farin na wani tafi na wani, amma ita jinjirar ba za'a iya ce wa fara ba ce kai tsaye, ba kuma za'a iya kiranta da ba?a ba.

Wannan kalar ta yarinyar ita ta kuma tafiya da Abdallah lokacin da aka fito da yarinyar sanye cikin wasu lasassun kayan da suka kasance na zallar auduga ne ga laushi, kafin Dady da aka mi?awa yarinya ya kai ga karSa tuni Abdallah ya caSe abarsa yana mai kai mata sumba a goshinta, abinda ya fara fitowa daga bakinsa shi ne ''Allah ya yi miki albarka ?anwata, ya kuma yafe miki kurakuren da za kiyi na duka rayuwarki'', wannan addu'a ta WaWa jama'ar dake a kewaye dashi, a dayawan lokuta idan aka yi mana haihuwa mukan ce Allah ya raya akan sunna, wannan ita ce addu'a mafiya yawa daga cikin mu, amma shi Waya san zata samu irin wancan salon addu'ar daga bakin jama'u, sai kawai ya sanya wa rayuwarta albarka, ya kuma nema mata gafarar Ubangiji a ranar data diro duniya a matsayin na baiwar Allah.


Kuma Mamma ta saka wa Dady a waya ita a dole sai tazo taga jaririya, ba zata iya jira har sai ta haihuwa nan da watanni uku kamar yadda Dady'n ya faWa.

Ba zai iya jurar jin muryarta tana kuka ba, ba kuma zai iya katse wayar da suke kallon juna da fuskar ta ba matu?ar baiga farin ciki akan fuskarta ba, bazai iya barci ba matu?ar ya tuna ce wa matarsa a yau tayi kuka saboda neman wata bu?atar da ta nema a gurin shi, zai yi iya bakin nasa ?o?arin wajan ganin ta samu abinda take so matu?ar dai bai fi ?arfinsa ba, saboda hakan nema ya yi mata al?awarin zuwa dan su taho tare da ita, ta kuwa ji daWi fiye da kima, wanda har sai da yaga dariyarta kafin ya yanke kiran.


?arfe goman safe ma data buga yana Alger ne, in da ya wuce ofishinsa ya yi wasu ?an ayyuka mn na awannin uku kafin ya nufi hanyar zuwa gidansa.

Bayan sun tashi daga barcin rana da suka Wan taSa ne ya ce ta gama shirya wa, ana yin sallar la'asar za su tafi, wani daWi ko kuma ?arin bazatar ma ba'a jirgin kasuwa ko gwamnati za suje ba, a jirgin Waya siya da guminsa domin ?ara fadaWa ayyukan kimiyyarsa ya siye shi, ya fara ?era wani jirgi marasa matu?i ne, siyan wannan zai bashi damar karantar duk wani abinda ya kamata ace ya sani kafin haWuwar wancan jirgin ya zai kasance na musamman ne domin hukuma.


Arziki ya ci uban na da, likafa ta ci-gaba, badan rashin Magabata da kuma Iyaye da suka yi ba, da wa?annan iyalan ba lallai suce jiya ba yau ba a yadda komai yake zuwar musu fiye ma da yadda suke zata, farin ciki da soyayyar junansu ne a mamaye dasu wanda ganin idanunka ba zaka iya ?iyasta adadin ?aunar da suke yi wa juna ba, sai fatan Ubangiji ya dawwamar da farincin dake a tattare da su idan yaso.


Kwanaki bakwai na haihuwar bikin suna ya gudana, wanda yarin ta ci sunan kakarsu wacce ta haifi iyayensu wato Fatuma, haka kuma sunan yayar mahaifiyarta wato Mamma.


Taron ya ya cika da awannin jama'u daga Sangarori mabanbanta, manyan mutanen da suke tare da Abby, da kuma mutanen Dady, ga dangi na sha Allah ta ko'ina.

Har ma da ma'aikatan gidan da matayensu duk sun zo, ciki kuwa harda matar direban Abby Misbahu, wanda ita ma ta samu zuwa gurin bikin bisa jagorancin maigidanta, tare da yaranta guda biyu a lokacin, Wan yaro namiji da kuma mace wacce take goyo, wadda ba za tafi watanni biyar zuwa shida da haihuwa a ?iyasi ba.



Da yamma sosai bayan taro ya fara watse wa suke zazzaune a falo, Abdallah ne ya shigo ya Wauki yarinyar ya Wora a cinyarsa kasancewarsa a zaune, kallon fuskar yarinyar da take ta barci abunta yake, ya yin da fuskarsa ta yalwata da wani murmushi, shi dai har ga Allah wannan haihuwa shi aka yi wa, yana ?aunar ?anwar nan tasa fiye ma da yadda yake san kansa, a kwanaki bakwai Win nan babu ranar da zata fito ta koma bai daWi hakan ba, abun har mamaki yake bawa Ummy.

''Ni Abdallah a matsayina na yayan wannan babyn ya samo mata inkiyar suna mai daWi wanda ya yi dai-dai da yanayin ta, na kira ta da suna Noor, wato haske'', ya Wora da ce wa ''Ummy sunan na ?anwata ya yi daWi kuwa? ni dai ya yi mini daWi sosai, dan dama ba tun yau ba na ajiye shi a cikin zuciyata a domin ta, ina jiran zuwanta ne in kira ta dashi, nasan idan ta girma sunan zai yi mata daWi sosai'', nan kuwa falon Ummy ya Sarke da firarrakin sauran jama'ar da basu watse ba game da abinda ya ce Win, da kuma yaba daWi da ma'anar sunan da ya yi wa ?anwartasa.

Murmushi Ummy ta yi masa tare da faWin ''ai kam ba wai ni kaWai ba, kowa ma dake nan wannan sunan na yaya zuwa ga ?anwarsa ya yi mana, Allah ya ?ara girma yaya Abdallah'', a karon farko tun bayan daya fara hankali ya ji Ummy ta kirasa da sunansa, sai abun ya Wan bashi kunya, hannu yasa yana Wan sosa ?eyarsa da ce wa ''Ummy bara in je in raka su Yusuf in dawo, yanzu fa zan dawo, a kula mini da ita ajiya na baku'', ya faWa da murya mai Wauke sauti, dan yana tafiya ne yana magana.


Kukan da yarinyar ta saka ne ya sa kowa dake falon hankalinsa ya kai gare ta, hannu Ummy ta Waga tana mai yafito ta da nufin tazo gareta, ba musu kuwa yanar jikin mahaifiyarta dake zaune a kujera mai zaman mutum biyu, da waya a hannunta da alama tana duba wani muhimmin abu ne, dan ko lokacin da ?artata ta fara kuka bata ko kalle ta ba.


''FaWa mini yarinyata! Miye ya saka ki kuka ne?'', ce war Ummy ta faWa tana mai tambayar yarinyar da ba zata wuce ?ar kimanin shekara huWu haka ba.

Cikin wani kukan yarinyar ta ce ''to Tanti ba shi bane ya yi wa b?b? sabon suna ba, kuma yana ta Waukarta tun Wazu, ni kuma ko sau Waya bai Wauke ni ba'', ta faWa tana mai turo Wan ?aramin bakinta gaba.

Shafar kanta Mamma dake kusa da Ummy'n ta yi tare da faWin ''?ata Angel akwai rigima, to ai kema ganan naki sunan da daWi, harma yafi na baby'n fa'', ita ma Mamma'n ta turo bakin a karshen maganar kamar yadda yarinyar ta yi, ai kuwa ba shiri yarinyar ta yi dariya ganin abinda Mamma'n ta yi, ta koma kusa da mahaifiyarta tana tsalle tana dariya, kafin zuwa dare kowa ya watse, ya rage sai su ya su kawai.


Kwanaki uku bayan suna su Dady suka koma Alger a jirginsu kamar yadda suka zo, maganar zuwan Ummy wanka gida kuma kamar yadda al'ada ta tanada Abby ya ce babu shi, bai yarda taje ko'ina ba, sai dai wata ?anwar mahaifiyar su Ummy'n ce ta zauna a gidan dan kula da lafiyarsa, a hakan kuwa har sai da suka yi watanni biyu da haihuwa kafin tabar gidan.

A wannan watan biyu idan kaga Noor ba zaka ce ?ar watanni biyu bace, yarinyar ta yi bul-bul abunta, harshen kalar fatar ta kuwa sai ?ara fita yake daban da nasu, ita dai ba fara bace, ba kuma ba?a bace, tsayin hancinta dai-dai misali, bakin Wan tsinini dai-dai da kwanakin ta, da kyar da dibara ake raba Abdallah da ita ko gun kwanciya, wani sa'in sai dai a barshi yaje Wakinshi da ita, idan aka dai-daici ya yi barci a Waukota, haka tun asuba zai dinga mitar an Wauke masa Noor Win sa.


?arin wani watan Waya bisa biyun da suka yi da haihuwa shi ya bada watanni uku kenan, a kuma dai-dai wannan lokacin ne Mamma ta haihu a can Algeriya, ta samu ?arta mace, a ranar da aka yi haihuwar da safe, da yamma jirgin ?anwar mahaifiyarsu wacce ta yi wa Ummy zama zai tashi zuwa can, dan da farko so aka yi ma ta isa tun ma kafin a yi haihuwar, to sai bata samu dama ba, sai yau da aka yi haihuwar.


Sabon abu dai a ko'ina sabo ne, jin Mammarsa ta haihu yaji shau?i dasan zuwa yaga yarinyar da aka haifa ya kama shi, sai Abby ya ce su tafi da (Anna) haka suke kiran tsohuwar dashi, ina yaso idan suka je bayan biki sai su dawo tare.


Sai da yammar ta yi yaga da gaske tafiya zai yi ba tare da haskensa ba, sai kuma ya ce shi ya fasa tafiyar, nan kuwa Abby ya ce ?arya yake kuwa, dole tabi Anna su tafi.

A Waukar ?arshe da ya yi wa yarinyar tana ta harba ?afa abunta hankali kwance, sai wasa take yi da Wan ?aramin bakinta kamar wacce take san yin magana, baki yakai ya sumbaci baki da koshinta, yana share ?ar guntuwar ?wallarsa wacce Ummy ta rasa ko ta wane iya shegen ce, a haka dai ya bada ta badan ransa yaso ba, a ya kusan barin falon na haka yace da Ummy, dan Allah kar su daWe basu je ba, a yi a kai mata ?anwarsa.


Ashe wannan shi ne ?arshen ganin da zai yiwa yarinyar da yake mutuwar so a matsayin ?anwa, yake ?aunarta fiye na da kima.

A washe garin ranar da su Abdallah suka tafi, a ranar Abby yaje asibiti, kusan acan ma ya kwana, akwai wa?anda aka yi wa aiki ne, har kusan taran safe bai dawo ba.

Haka ta gama shirya kanta da kuma ?arta tana zaune a falon da mai aiki ta gama gyara shi tsaf, a ranta take faWin ''gaskiya wannan sabuwar mai aikin harma tafi Baba Balaraba iya gyara waje, a ?an makonnin da basu wuce uku da tayi a gidan ba ta gane ?arewarta, da tana ce wa za'a nemo wata wacce za ta dinga kama mata aikin dan kar ya yi mata yawa kafin dawowar Baba Balaraba daga ?auye su, ta Wauki hutu ne ta tafi gida, in da zata aurar da ?arta Lamunde kafin dawowarta, yanzun haka ta faWa musu ranar Waurin auren, sai dai ta yi dai-dai da lokacin suna Algeriya ne, tunda a lissafin da Ummy ta yi ranar auren zai kana a washe garin bikin sunan Anty Fatuman tane, sai dai suyi mata fatan alkhairi da addu'ar Allah yasa ayi bikin a gama lafiya, ya kuma bawa ma'auratan zaman lafiya da zuri'a Wayyiba, sun cika ta da tarin alkhairai kafin tafitarta.

To a ranar da suka tafi ne da yamma mai gaWin wancan lokacin ya shigo har falo yana faWa mata ce wa da wata matar da yazo tana neman aiki, ba tare da jira ba Ummy ta ce ya shigo da ita.


A waya kawai Ummy ta kira Abby tana faWa masa sun sami ?ar aiki, shima ba tare da wani bincike ba kawai ya ce ta karSe ta idan har ta yi mata.

Sunanta kawai Ummy ta tambaya, a lokacin matar ta ce mata sunanta Fatsume, a hakan kuma ta Wauka, wannan shi ne farkon shigowar Fatsume a rayuwar gidan Dr Muhammad Ousman, in da ta share makonni uku tana aiki tu?uru, harma uwar Wakina nata take yaba wa ?o?arin ta, shi ne a ana gobe zasu tafi Algeriya bikin nan, a zaman falon nan da Ummy take da yarinyarta bayan sun Wauki wanka suna jiran Abby, sai Ummy taji ?arar wayarta dake a Waki, da har ta tashi da yarinyar a hannunta, sai kuma ta maida ita ta shinfiWe ta a kan kujera, filullakan kujerar ta jera kusan guda uku ta kare ta gudun kar ta faWo, yarinya tana halbe-halben ?afa tana wasan ta Ummy ta barta ta shige Waki, inda ta tarar da kiran Abdallah ne da Mamma, in da yake tambayarta ajiyar daya bata a ce warsa, daga nan kuma suka Wore da fira, in da ya mi?a wa Mamma wayar bayan Ummy ta ce dashi ta gaji da surutunsa, duk tabi ya cika mata kunne da zancen ?anwarsa.

Kusan mintuna goma sha biyar tayi akan wayar nan, ganin firar ya?i ya kare yasa ta taso ta fito falon da wayar a kunnenta, amma sai maganar da ta Waukowa Mamma ya tsaya mata a iya ma?wogwaronta ganin babu yarinyar a inda ta shinfiWe ta, tashin hankalinta bai gama ninkuwa ba sai bayan data gama buda duk wani lungu da sa?on dake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login