Showing 69001 words to 72000 words out of 78880 words

Chapter 24 - YAR KANCE free pages na Maman Abdallah.doc

ba dake ba.

200? GA ACCOUNT NUMBER=?I? Shaidar biya ta wannan layin=?I?
Maman Abdallah taku =?
?>??


?AR KANCE
Labari da rubutawa
By
Khadijah Bashir
(Maman Abdallah)

Page 21

''Yarona shi ne ba waiwaya baya?'' Abby ya tambaye shi bayan ya amsa sallamar da ya yi masa.

''Ba haka ba ne Abby, wallahi abubuwa suka sha kaina, ya gida ya dare? Ummyna fa? Fatan tana cikin ?oshin lafiya'', ya faWa lokacin da ya yiwa kansa wuri jikin katangar wani gida, nesa kaWan da wurin dasu Yusuf suke.

?an murmushin manya Abby ya yi kafin ya maimaita abubuwa, cikin watanni biyun bayan nan zai iya ce wa abubuwa sun yi wa yaronsa yawa tabbas, dan daga yadda yake gudanar da wasu al'amurran game hankali zai iya gane hakan, amma shi sam Abby ba mutun ba ne mai yawan tutsiye mutun, ko kuma tsunduma kai a komai, sai dai idan ta yi dalili ne, a ganinshi koma dai miye yake Wawainiya da yaron nasa to tabbas ba mai Waga hankali ba ne, dan da damuwa ce tabbas su zai fara tunkara, dan sune farkon abokan firarsa, haka kuma dasu ne kawai yake raba matsalolin sa, su kuma nemo masa mafita a matsayin su na manyan sa.

Abby ya ce ''gaskiya bana kusa da ita a yanzu, zaifi ka kirata a layinta, dan zan Wan jima kafin in koma gida.''

Mamaki ne ya kama Abdallah, jin Abby ya ce baya gida, haka kuma zai daWe a waje kafin ya koma, idan da Dady yana ?asar ne sai ya ce ya shiga wurinsa firar dare, ''to ina Abby'n ya tafi ne?'' ya tambayi kansa.

Ganin kamar ya shiga wani abun na daban yasa Abby ya kuma ce wa ''kana ji na kuwa? Naji kayi shiru.''
Cikin sanyin murya Abdallah ya amsa shi da ''ina jinku Abby, in sha Allah yanzun zan kira ta.''

Basu wani yi firar arziki ba Abby ya yi masa sallama ya katse kiran, nan take ya tura kira wa layin Ummy, bugu biyu ana uku ta amsa, lokacin fitowarta daga bayi kenan.

''Ummy ya naji muryar ki haka! Ko bakida lafiya ne?'' ya tambaye ta bayan gama amsa sallamarsa da ta yi.

Ajiyar zuciya Ummy'n ta sauke kafin ta ce ''ina kuwa lafiya yarona? Baka nan, haka ma Abby, wallahi duk gidan ya gundureni'' ta faWa kamar za tayi kuka.

''Abby baya nan? To bulaguro ya yi ne komai? Shi ma haka ya ce min baya gida yanzun da nace ya baki waya? Dama tafiya zai yi ne?'' ce war Abdallah cike da mamaki.

''Ok wai dama bai faWa maka ba? In na fahimta kenan bazata yake san yi maka, to ai shikenan, zan gudu bacci nake ji'', Ummy na kaiwa nan ta katse kiran, haWi da ajiye wayar a inda ya dace, kafin ta kashe wutar Wakin da addu'a a bakint.
Kwancinta kenan sai ga wayar Abby, ya kira su sha love a waya, tun da yau Win dai ya yi nisan kiwo.

Kasa?ai ya yi da waya a hannunsa, a bayyane ya ce ''to kodai wani abun ya faru ne bayan barina gida?'' ya tambayi kansa. Cikin hanzarin ya kuwa tura kira wa layin Talatu, yanzun ma a kashe ya ji, kamar wanda kwai ya fashewa a ciki ya kama hanyar komawa gidan su Amarya.

Yusuf bai lura da ficewarsa daga wajen ba, sai Ishaq ne ya hangi bayansa lokacin da yake tafiya, cikin hanzarin ya biyo bayansa yana tambayarsa ina zaije, Abdallah bai ita Waga baki ya yi magana ba, Wan ji ya yi bakin ya yi masa nauyi.

Tare da Ishaq suka dawo masaukinsu, jiki a saSule ya zuba ruwa a bokici ya je ya yi wanka, ai kam kafin ya fito daga banWakin ma zazzaSi ya rufe shi, yana rawar Wari ya shigo Wakin da gudu.

Da taimakon Ishaq ya iya zira wata ba?ar jallabiya daya naso a ?ar jakar baya, sai site guda Waya na shaddar da suka yi su uku wacce zasu sa ran Waurin aure, wacce shi ya zuba manya kuWi ya siya musu, shi kuma Yusuf ya yi hidimar Winki.

''Sannu ka kwanta sai in samo maka magani'' ce war Ishaq da duk jikinsa ya yi sanyi da ganin abokin nasu a wannan yanayi.

Gyara kwanciyarsa ya yi akan katifar da tuni Ishaq ya lulluSa masa bargo ya fice da sauri dan nemo maganin zazzaSi.

Tunda Ishaq ya fice daga Wakin Abdallah ya lula duniyar tunani, miye yasa wayar baya shiga idan ya kirata, a ace network ne ai bazai samu Ummy ba, wai in ma ance Abby baya gida. To kodai Ummy ta shiga sashensa taga Talatu ne? A'a, idan da ta ganta lallai zai fahimta a wayar da suka yi. Haka dai yake sa?awa ya kwance, ahaka har Ishaq ya dawo da maganin zazzaSin, Yusuf ne a bayansa.

Sun bashi magani yashadda ?yar, danaAbdallah baya san shan magani ko kaWan, duk ranar da Ubangiji ya Wora masa koda ciwon kai ne tofa a ranar akwai darga a gidan Abby, dan bayasan maganar shan magani, a mafiya yawan lokuta sai dai Abby ya haWa allura ya yi masa, ita kam ko guda goma za'ayi masa lokaci guda baya shakka, tsaf zai mai?a hannu ko baya a zanbaWa masa a wuce wurin.

Abu ya yiwa Yusuf da Ishaq lami sosai, Yusuf ne ya ce ''to miye yake damunsa ne? Haka kawai zazzaSin ya rufe shi?'' ya tambayi Ishaq.
Ishaq ya ce ''wallahi nema haka kawai na ganshi, da farko na hangosa yana waya, daga baya kuma sai ganin ya kama hanyar dawowa gida nayi, shi ne ya biyo bayansa, ashe ma zazzaSi ne a jikinsa, kuma muna zuwa ya yi wanka.''

''Allah ya kyauta, ya bashi lafiya cikin gaggawarsa wacce bata cutarwa'' ce war Yusuf. Da amin Ishaq ya amsa shima yana hayewa kan katifarsa, ko Shamsiyya bai yiwa saida safe ba, haka kuma wallahi sai dai su kwace a goben idan da rai, a ce warsa.

Yusuf kam sai da ya tabbatar da shigowar Amaryarsa cikin gida kafin ya samu sukunin yin wanka shima, ya zo ya kwanta da addu'a a bakinsa.
Asuba tagari.

Talatu
Tun data gama dafa abinda zata ci da rana take zaman jiran kiransa, haka ta tusa dafa dukar shinkafar da tayi a gaba tana kallo, jimawa kaWan sai ta kalli screen Win wayar, Badan tana jin daWin abincin ba haka take tsakura tana watsawa a baka.

Wasa-wasa har magariba bata ji kira daga Abdallah ba, hankalinta ya tashi, tunani kuwa ta yi kala da kaloli akan dalilin da yasa ya?i ya kirata. Har kiransa ta gwada amma sam kiran ya?i fita, har isha'i tana abu Waya, ko abincin dare bata girka ba, dama bata jin yunwa, kuma ta saka a ranta kawai zata sha madara ne idan zata kwanta.

Kwance take a kan gadonsa tana sha?ar ?amshin turare da daya gama kama ilahirin zannuwan gadonsa, cike da damuwa ta ce ''to kodai ta yi tunanin ni ce na katse kiran da ya yi min da safe'' ta tambayi kanta.
''Amma kuwa ba bai yi min adalci ba, idan har ya yi tunanin hukuntani da hana ni jin muryarsa'' ta faWa tana juyi akan gadon ciki damuwa.

Duba lokaci ta yi a fuskar wayar taga har goman dare ya yi, jiki ba ?wari ta tashi ta faWa toilet, itama wankan ta yi ta haWi da maida kayan dake jikinta, dan bayan magariba ne ta yi wanka haWi da zuwa doguwar riga mai dogon hannu.

Haka ta kwanta duk ba wani daWi, ga kanta dake Wan sara mata, rungume da wayarta a ?irji bacci ya Wauke ta.

Abinda Abdallah ke tunani daban, haka ma Talatu.
Shi dai tunaninsa ya fi karkata a ko batadda lafiya ne, shi ne ma dalilin da zazzaSi ya rufe shi lokaci guda. Ita kuma a nata Sangaren lokacin da ta Wauki wayarta daga ajiyetan da tayi bayan gama gyara masa Waki da ta yi, bisa kuskure hannunta ya danna wannan alamar jirgin dake can saman wayar, wanda ke nuna ka dakatar da layinka daga aiki na iya lokacin da zaka cire wannan alamar. Kuma a duka karatun da take mata na fannoni da dama, Allah bai nufa ko sau Waya ya taSa nuna mata anfanin wannan alamar.

Matamaye
?arfe bakwai na safiya tuni ?odar gidansu Rammatu ya cika da mahalarta Waurin aure, ?anluwa da abokan arziki duk sun halarta, haka ma daga makwabtan garuruwa jama'a-jama'a sai shigowa suke, ciki kuwa harda su Malan Liman da Malan Usama da sauran tawaga, a kurkusa dai sai ince babu inda Kawu Abdu bai aika takardar gayyata ba, shi yasa ?ofar gidansa ya zama na ba masaya tsinke a yau.

Abdallah a nannaWe a bargo har su Yusuf suka gama shirinsu tsaf. Ishaq ne ya ce ''Abdallah da ka Wan ?o?arta ka mi?e, ciwo fa baya san san jiki, sai kace wata mace.''

Yadda Abdallah ya fito da kai ya murguWa masa baki kai ka rantse ma en ne kamar yadda ya ambata, bai ce dashi komai ba ya mi?e ya fito daga bargon yana mi?a, da cinin ido ya yi wa Ishaq nuni da Yusuf da sai ?ara duba madubin da babu wanda yasan ya sakosa a kayansa.
Dariyar Ishaq ce ta ankarar da Yusuf ya gane suna gulmarsa, cikin wasa ya ce ''ai fa sai ka shiga tsokana tunda ka samu sau?i, Allah banyi tunanin abun naka zai zo da sau?i haka ba, da har nayi fara tunanin zaka sa min sabga tayi lami, dan ka sani koda ace she?awa kayi ba zan yarda a Waga min ranar aure ba, ?o?ari Waya zanyi in bi jama'a a kaika gidanka na gaskiya.''

Naushi Abdallah ya kai masa sai Yusuf Win ya kauce yana dariya, Abdallah ya ce ''Wan ba?i ciki, wato kai naka lokacin ya yi shi ne ka ke ba?in cikin kar wani ma yaga nada ranar auren kamar haka, to wallahi ?aryarka, nan kusa zaka ga ina baza babbar riga ana kira na da Ango'' ya faWa yana mai barin da?in, ya nufi banWaki da Wan kuzarin da yake ji a jikinsa ya samu.

Alhamdulillah! Rana bata ?arya sai dai uwar Wiya ta ji kunya, ana shelar a nutsu za'a fara Waurin aure sai ga jerin gwanon motoci na alfarma, haka suka fara fakawa Waya bayan Waya a nesa kaWan da kofar gidan, nan kuwa kallo ya koma kan wa'yannan motoci, dai-dai da fitowar Abdallah daga cikin gida yana gyara zaman farin gilashin daya sa?alawa idanunsa. Ganin zai tsaida su Yusuf su makara gaba Waya yasa ya ce su su fara fita, in yaso shi idan ya gama shirin sai ya fita.

Turus ya ha ya tsaya ganin wani mai kama da Abby'nsa ya fito daga mota, tabbas yasan suna da irin wannan motar, amma kuma numbobin dake gaban wannan motar sunsha banban da nasu.
Cike da mamaki ya ce ''Abby kuma! Kenan dama zai zo Waurin auren ne? To amma ai Baba ya ce ya bari ya yafe masa.''

Yana tsayuwar tunani har baisan an tarbo su Abby ba an basu wurin zama, inda ake ta faman mi?a musu gaisuwar bangirma. Duk da kasantuwar Abby babban mutun ne, amma ba lallai ace anan kwakwkwahen an san dashi ba, amma babu wanda zai dubi na kusa gareshi yace ya kasa gane shi, duk wanda yakwan ya tashi a garin Damagaram da yankunan ta, yasan da wanzuwar Dr Dawood Zailani Kango, wanda shahararren mai kuWi nw, shi ke Waukar lanba ta uku a jerin sunanayen masu kuWin garin Zinder, haka kuma a yanzu shi keda mu?amin gwamnan jihar.

Dr Dawood abokine ga Abby, duk da basuyi karatu a ?asa Waya ba amma abotarsu ta samo asali ne tun a shekarar farko ta kama aikin kowannensu, a wani taron ?ara wa juna sani daya gudana a babban birnin ?asa Niamey, anan suka haWu, kuma abota mai ?arfin gaske ta ?ullu a tsakanin, to Waya ne ya haWu da Waya, bima'ana kana da naka ina da nawa, irin wannan abota bata tare da duk wata mishkila.

Cike da mamaki Baba ya ce ''Amma Alhaji ka shammace nk dayawa, ashe dai sai da kazo.''
Shima Abby'n da murmushi a kan fuskarsa ya ce ''to ai kaima faWa ne da bata baki, taya za'a Waura auren yarona kace kar nazo, ai ko lokacin da ka faWa jin?ai kawai nayi, tun jiya da yamma ma na iso Damagaram, yanzun kuma muka iso nan.''
Godiya sosai Baba yayi wa su Abby da gwana, Kawu Abdu kuwa baki har kunne, shikan wannan abu bana a manta bane, a ce zai aurar da ?a har Gwamna ya samu halarta, kai gaskiya abun sai dai Allah ya sa a gama lafiya.

Babu Sata lokaci aka fara Waura aure, wanda dayawan Jama'ar dake wajan suka shaida Waurin auren Yusuf da amaryarsa Rammatu akan sadakin da babban Aminin da zai iya kiransa da Wan'uwa kai tsaye ya biya, babu yadda Yusuf ya iya haka ya amshi kuWin daga hannun Abdallah, shi dai bashi da abinda zai ce wa Abdallah da iyayensa sai fatan Allah yasa a gama da duniya lafiya, ya biya musu bukatunsu na alkhairi, ya ji?an magabatansu.

Wani ?arin abun al'ajabi'n bai wuce yadda Abby da abokinsa suka saka hannu suka karSi goro dabino da ?an sauran ababen da sukan raba a taron Waurin aure da kansu ba, suka kuma sanyawa auren albarka, kafin suka ce zasu taf, dan Abby jirgin ?arfe goma gareshi, wanda daga nan Maradi ya nufa, dan halartar wani zama na manyan ?an kasuwa masu masana'antu da za'a gudanar da misalin ?arfe Wayan rana. Yana da ran kuma a yau zai koma Agadez matu?ar ya gama abinda ya kai shi akan lokaci.

Kamar ance ya juyo bayansa lokacin da Abdallah ya buWe masa murfin motar a madadin body-gayd Win Gwamna, bayan
Gwamnan ya fara buWe wa ya shiga kafin ya buWe wa Abby. Karaf idanunsa suka sauka akan su Malan Liman dasuka tarbi Kawu Abdu suna yi masa sallama, bayan da suka dawo daga rakiyar su Abby.

Jikin Abby har karkarwa yake, hakama bakinsa har rawa wajen kiran suna........

Caji ya yi wa wayana ?aranci, wallahi ba anan maso tsayawa ba, amma muyi ha?uri mu kwana nan, zuwa gobe da yardar mai duka.

Shin waye Abby ya gani har jikinsa yake kyarma?? Ina jiran amsoshin ku please =?O?
Karki yarda mu fara two ba dake ba.

200? GA ACCOUNT NUMBER=?I? Shaidar biya ta wannan layin=?I?
Maman Abdallah taku =?
?>??

?AR KANCE
Labari da rubutawa
By
Khadijah Bashir
(Maman Abdallah)

Last free page

Page 22

_____Jikin Abby har karkarwa yake, hakama bakinsa har rawa yake wajen faWar ''Ma ma Malam Misbahu.''

Ras! Malam Usama yaji kansa ya dara masa, duk da ?ar tazarar dake tsakaninsu da Abby ai hana kunnuwansa jin wani sunan da yake tunanin nasa ne bawai yau ba, ya jima tabbatarwa kansa Misbahu shi ne sunansa na asali, sai dai ba zai iya tuna ina sunan ya samo asali ba, sai a duk dare na Ubangiji yakan yi mafarkai barkatai, zai ganshi a wani gari daban ba KANCE ba, kuma gashi cikin wasu mutanen daban basu Malan Liman ba. Haka ma wani yaro yana yawan zuwar masa a cikin barcinsa, a kullum haka yake ceasa yaushe zai dawo ne.

Ri?eshi Malam Liman ya yi ganin ya dafe kansa dake barazanar sara masa, dama gashi gwanin ciwon kai, bawan Allah idan ya fara ciwon kai sai kowa dake kusa dashi ya tausaya masa.

''Sannu! Sannu Usama, da wani abun ne?'', malam Liman ya faWa a kiWime lokacin da yaga Usaman ya sulale yabi ?asa.

Shi kuma Abdallah Abby ya kalla da mamaki, da al'ajabin daya wanzu akan fuskarsa ya ce ''Abby kasanshi ne?'' shi duka a nasa tunanin ko Abby yasan ala?arsa dasu Malan Liman, wai ko sun kira wayar Abby'n ne, tunda dama saida ya basu numbersa, amma ya nemi alfarmar kada su kira shi har sai ya faWa musu ya kama dai-daita komai.

Sakin murfin motar Abby ya yi, ya nufi wurin su malam Liman da tuni aka fara rufe su ana tambayar ba'asi faWuwar malam Usama.

Shima Gwamna fitowa ya yi ya bi bayan abokinsa, nan take kuma tawagar masu bada tsaro suka rufa musu baya.

Ajiyar zuciya ya sauke bayan da aka zuba masa ruwa, suma ya yi na wucin gadi, tsabagen yadda zuciyarsa ta shiga ruWani da razana.

Dai-dai da isowar Abby daf dashi ya buWe idanunsa, kalmar farko da ta fito daga bakinsa ita ce ''ku taimaka min kar su gudu da ita, dan Allah jama'a ku taimake ni.''

Nan jama'a suka shiga kallan kallo, ciki kuwa harda Dr Dawood sai da ya yi wa Abby kallon me yake nufi, tunda ya lura da wani abinda Abby ya sani game da mutumin da ya kira da suna Misbahu.

Cikin sanyin jiki Abby ya ce ''magana ce mai tsayi gaskiya, ga dukkan alamu kamar baya cikin hayyacinsa, dan Allah ko zaku iya bamu wuri?'' Abby yakai ?arshe yana kallon jama'ar dake kewaye dasu.
To dama tawagar Gwamna basu yarda da kasamcewarsa cikin cinkoson nan ba, dajin maganar Abby suka fara bawa mutane umarnin su fice daga nan, babu musu kuwa aka watse kaf, ya rage daga su sai su, sai kuma Malam Liman daya kasa fahimtar komai a yanzu, so yake kawai Usamatu ya Waga baki ya yi magana, a ransa kuma addu'a yake Allah yasa ya dawo cikin tunaninsa, yasan ko shi waye, abinda ya daWe yana addu'ar Allah ya kawo ranar da zai faru.

Cikin mintuna ?alilan Abby ya basu labarin abinda ya faru shekaru sha biyar da suka wuce a ta?aice ya Wora da ''a yanzu hakan nan muna kan binciken neman matar ne, dan baifi watanni biyu dana ganta da idanuwana a wurin wani taro ba, sai dai har yanzu an kasa gano inda take, bare a kama ta.''

Kukan Malam Usama ne ya cike Wan madai-daicin gidan magwatansu Kawu Abdu da aka yi musu shinfiWa a can dan zaman tattaunawa.

Malam Liman ya ce ''a gaskiya biri ya yi kama da mutun, duk da bazan gas?ata ko ina ce wannan bawan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login