Showing 12001 words to 15000 words out of 78880 words

Chapter 5 - YAR KANCE free pages na Maman Abdallah.doc

da ita daga faWawa komar Wan caca mara albarka.


Cikin ?asa da murya ya ce da malam Usama ''Ni kuwa inada abunyi idan har kun yarda da ni a matsayin ku na magabata a garin nan'', kafin ya gama faWin abinda ke ransa malam Usama ya bashi haWin kai Wari bisa Wari, inda ya bashi tabbacin zai fahimtar da malam Limam da duk wani mai faWa aji na wannan ?auyen kuma yasan zasu fahimta.


?auyen Matamay
A Wan Sarawon baccin daya fizge shi kusan asubahi ya tashi da kalmar Kance a bakinsa, da gudu Ishaq da fitowarsa daga bayan gida ya ajiye butar ya nufo inda yake, cikin tashin hankali yake girgiza Yusuf tare da faWin ''lafiyar ka qlau kuwa Yusuf? Mi ya faru kana jina kuwa, Yusuf kayi magana mana''.


Shi dai Yusuf kalmar Kance kawai yake ?ara maimaitawa kafin ya mi?e tsaye yana karkaWe kayan jikinsa dan rabin shi duka a ?asan Wakin yake zaune rabi a gefen katifa a haka har bacci ya dauke shi.

Galala Ishaq ya yi yana kallon ikon Ubangiji ganin Yusuf Win ya shuri butar daya ajiye ya faWa bayan gida a gurguje.

Saida Yusuf yayi alwala kafin shima Ishaq ya yi, a daidai nan Kawu ya shigo zagayen cikin jimamin da suka kwana na rashin dawowar Abdallah, ya yi mamakin sosaiganin su a falke har sunyi alwala, kasancewar har kusan asubar su duka suka shigo gidan ba tare da nasarar ganin Abdallahn ba.


Mamaki ne ya kusan kashe Kawu ganin mirmushi akan fuskar Yusuf, cikin kokwanto Kawun ya nuna sa da hannunsa na dama mai ri?e da tsarbi, da rawar murya yake faWin ''Ina fatan dai kana lafiya lau dai ko?''.

Dariya ce taso kubcewa Yusuf ganin daga Kawun har Ishaq sun tsorata dashi amma ya gince, cike da samun tabbaci daga zuciyarsa ya ce da Kawu ''Yanzu nasan inda Abdallah yake Kawu''.


Tsabar mamaki har kusan haWa baki suke wajan tambayar ''Kamar ?a?a kasan inda yake?''.


Suna tafiya a hanyar masallaci Yusuf ya basu labarin ?ar Kance yarinyar da suka taSa haWuwa dasu a bayan gari, sannan ya tuna lokacin da yake faWawa Abdallah cewa ma?wabtan ?auyan su ne, bayan wannan bai tuna wani abun da ya taSa haWa Abdallah da wannan yarinyar ba, amma kuma ko tamtama bayayi acan zasu same shi.


Ana gama sallahr asuba Yusuf, Kawu, Ishaq da wasu dattawan guda biyu suka kama hanyar Kance a motar da suka zo da ita garin, amma basu kai ga isawa cikin garin ba suka hangi mutun da wani abu a kafaWar sa, fitilar motarsu ita ta tabbatar musu ko waye wannan mutumin, ga kuma kamar mutun ne a kafaWar sa, kuma ma mace, da alama kamar bataso daukan ba tunda sai wutsil-wutsil take da ?afafuwan ta.

Burki Yusuf yaja ya tsaya ganin Abdallahn yana shirin raSawa ta gabansu ya wuce dan baisan su Win bane a daidai wannan lokaci.

Murfin motar ya buWe ya fita da tarin al'ajabi a tare dashi.

kamar daga sama Abdallah yaji sautin muryar abokinsa yana faWin ''Yarona Ummy sai ina haka kuma daga ina? Wace wannan?''.

Juyawa ya yi cike da mamakin ganin Yusuf Win, tsayuwar da ya yi ya bawa yarinyar damar wuntsilowa daga kafaWarsa sai gata a ?asa dirshen tana turje ?afafunta, kasan cewa duka ?afar da hannu saida ya ?ulle su, ya kuma ?ulle mata baki da wani kwalle da zata iya kira da adikonta, hawaye ne fal ida nunta ga kuma wanda suke kan zirarowa akan fuskarta.


''Babu shakka ita ce yarinyar'' ce war Yusuf lokacin dasu Kawu suke firfitowa daga cikin motar suma.


Ishaq ne ya ?araso kusa da Abdallah yana taSa fuskarsa wai zai tabbatar ko shiWin ne.

Ri?e masa hannu Abdallah ya yi dan baya cikin yanayin wasa a yanzu, gefe ya maida kafaWar Ishaq Win kafin ya fara takowa har inda su Kawu suke.

BuWar bakinsa da ya yi sai ce wa ya yi ''Kawu dan Allah ku mini alfarma mu koma ?auyen nan daku yanzu, zai fi kuji daga bakin wayanda za kufi yarda dasu''.

Jinjina kai Kawu ya yi tare da ?o?arin komawa cikin motar dan har ga Allah yana jin tsoro a ransa ce wa kar aje sato yarinyar nan ya yi, dan ga dukkan alamu bada yardarta ba ya Waukota tunda harda ?ulleta ya yi.

Suma sauran jama'ar komawa suka yi cikin motar, Kawu a kujerar mai zaman banza, haka suka kukkutsa aka samawa Abdallah da Talatuwa waje, dayake motar ba ?arama bace haka har suka isa cikin garin Kance.

A daidai ?ofar gidan malam Limam yayiwa Yusuf umarnin ya tsaya, ba musu kuwa ya tsaya yayin da kowannen su ya fito daga cikin motar, amma banda Abdallah da yake ta faman ya cicciSo yarinyar ya fito da ita amma tana zillewa, a mugun hasale ya fincikota tare da saSata a kafaWa kamar yadda ya yi mata a farko data kawo masa wasa.

A dai-dai nan malam Usama ya dawo daga massalaci bayan har gari ya kusan gama waye wa, turus ya yi ganin rafkekiyar motar zamani a ?ofar gidan, duk da ba wanna bane farko amma a kurkusa bai ga irin wannan motar a duka wannan ?auyan nasu ba.


?arasowa ya yi inda suke ya fara basu hannu suna musabiha, sai yanzu ya lura da Kawu cikin fara'a ya ce ''Malam Abdu ko na ma?wabtan ?auyan mu, idan ban manta ba kamar a Matamay kuke ko?''.

Shima Kawun da murmushi ya amsa shi da ce wa ''Ni ne kuwa malam Usama kwana dayawa yasu malam Limam Win shima an daWe ba'ayi katari mun haWu da shiba''?.


''Ai kuwa dai sai...'' bai gama jawabin daya Wauko ba ganin Abdallah tsaye sumgume da yarinya a kafaWarsa, da sassarfa ya karasa kusa dashi cike da mamaki ya ce ''Yaro dama baka tafi ba? Ya kuma ka dawo da wata damuwar ne? Tare dasu kake dama? Ko kana da ala?a dasu ne?'' kai tsaye malam Usama ya jerowa Abdallah wayan'nan jerin gwanon tambayoyin a jajjere.


Dai-dai nan malan Limam ya fito daga gida dan dama tun tsayuwar su wani yaron gidan ya sanar da shi ya yi ba?i a ?ofar gida, ison da ya yi musu zuwa cikin gida bai bar Abdallah ya bawa malan Usama amsoshin tambayoyin sa ba.

A turakar Limam suka yada zango bisa jagorancin sa, bayan gaisuwar data gudana a tsakanin su Kawu ya gyara zama ya ce ''Malan jiya da yamma na samu ba?untar Wan yayana dake zaune a Agadez, sai kuma suka zo da rakiyar abokansa guda biyu, bayan sallahr isha'? kawai sai neman Abdallah mukayi muka rasa har asuba babu shi babu labarin sa, to yanzu sai shi Yusuf Win yake faWa mana ya tuna inda za'a samesa, muna zuwa mashigar garin nan sai ganinsa mukayi Wauke da wata yarinya, tun kafin mukai ga tambayar sa sai ce wa ya yi mu koma garin nan, a kuma ?ofar gidan ka yaja linzamin tafiyar tamu, shi ne na ce koda abunda ka sani game da ala?arsa da yarinyar da muka gani a tare dashi?''.

Murmushin manya ne ya bayyana a fuskar Limam cike da dattako ya ce ''Eh gwarai inada masaniya, hasali ma nine jigon labarin nan, nan malam Limam ya bawa su kawu labarin
duka abinda ya faru tun daga shigowar Abdallah ?auyen da zuwansa masallaci duk ya faWa musu, har alfarmar daya nema wajan malam Limam Win bayan malam Usama ya gabatar dashi a wajansa kafin jama'ar gari su taru.
A harabar masallaci suka sameni da maganar, inda wannan yaro ya ce dani ''Malam naji abinda yake shirin faruwa da yarinyar kuma sam banji daWi ba, har ga Allah na shigo garin nan ne dan inga irin rayuwar da yarinyar take ciki ganin nazo har kusa da garin su, sai kuma na iske wannan abu, Malan shin ku kuna goyan bayan Ado ya aure ta eh ko a'a?'' ya tambaye ni.

Dama nida duk wani mai hankali a garin nan mun kasa yarda da ce war da Ado ya yi wai ba yarsa bace, duk da dama ana Wora ayar tambaya akansu daga shi har matarsa ganin yanayi kama da kuma halayyar yarinyar sam basa kamanceceniya da nasu, nan take na amshi da ce wa bana goyan bayan wannan zaluncin da kuma dabbacin, dama Ni a nufi na idan safiyar Waurin auren ta yi inWaura auren da yarona Iro da bayanan nan garin, yana garin Magarya acan yare rani bana, to sai ga wannan yaron albarkar da maganar shi idan zan bashi auren zai ?arSa, ya faWa mana cikekken adireshen gari da gidan su, ya kuma faWa mana su waye iyayen sa, ya bani har number sa data magabatan sa, saidai ya ro?i alfarmar kar Iyayensa su ji daga nan idan yaje da kansa zai faWa musu yadda zasu fahimce sa, ban sake yarda da shi ba saida ya tura mini photunansa dana iyayensa dan cire shakku daga zukatan mu, samun tabbacin zai kula da yarinyar ne yasa na yarda na Waura auransa da Talatu batare da ita kanta tasa ni ba, bamu bata zaSi ba dan a yanzu ba tada shi ko kaWan, malam Usama shi ya yi masa jagora zuwa gidan su yarinyar bayan Waurin auren, sun kuwa iske Ado bai kwana a gida ba wata kila yana makwabtan ?auyan nan akwai wani gidan caca a can, kuma a mafi yawan lokuta dama yakan kwana acan Win, ba jimawa ya naWo yarinyar a kafaWa ganin zata basa matsala, kuma idan har ta ce ba zata bisa ba zata ji?a mana aiki ne, shima da yake ba?o baiji ?yashin yi mata gata ba sai ita ce zata masa butulci, Ni nasa Usama ya rakashi har mafitar gari, wannan shine abinda muka sani gaskiyar magana''.


Kamar gumaka haka Ishaq da Yusuf suka kasance, Abdallah ne ya yi aure a garin da ba nasu ba, ba sanin wani nasa ba kuma ?ar yaren su ba, to mi zasu ce da Ummy da Abby? Wannan ne basu sani ba.


A cikin su Kawu babu wanda bai yaba jarumta irin ta Abdallah ba, sai dai duk da ya yi jahadi yayi kuskure babba, fatan su dai Waya ne Allah yasa Iyayensa su fahimce sa yadda ya kamata.


Sallama suka yiwa su liman kafin suka kama hanyarsu ta dawowa Matamay, a wanna karon da ?afafuwan ta shiga mota bayan taji ko waye ya sunkuto ta ba wani ?arin bayani, ta kuma gane cewa yanzun ita matar aure ce amma ba da Baba Ado ba kamar yadda ta kwana tunanin mi gobe zata haifar bayan Waura aurenta da Ado, ta gudu ta shiga duniyar data gujewa shiga ko kuma ta nemi wata mafitar, har suka iso ?ofar gidan Kawu kuka take ?asa-?asa mai ban tausayi, inda Kawu ya kira Rammatu data tafi da Talatu Wakin su kuma a bata makari dan gari ya gama wayewa, cike da ladabi ta asma baban nata tare da kama hannun Talatu suka shige cikin gidan, inda su su Yusuf suke a tsaida ba?o..............


Page 6
________A zahiri hankalin sa kwance yake danna wainar hatsin da aka kawo musu a matsayin karin kumallo, ya yin da tarin tsoro da fargaba suka cika cikinsa fam, ko abincin da yake ci yanzu ba wani sanin WanWano ko daWinsa yake jiba, innalillahi kuwa ya yi yafi cikin kwandon tumatur, tun daga lokacin da ake faWin an Waura Auren Abdallah Abdul-?adir da Nana Talatu Ado akan sadaki jika ashirin da biyu(22k) zuciyarsa ta tsinke, gudunta ya nunku sau ba adadi a ce war sa, yau shi ne da Aure rana kai tsaka ba umarni balle shawara, shi ne ya auri yarinyar da ko matsayin ?ar aikin gidansu bata isa takai ba, yarinyar da ko cikekken sunanta babu wanda ya sani, duka taron jama'ar dake zaune a masallacin nan aka gaji da cigiyar ko akwai wanda ya san asalin sunan yarinyar nan na yankan rago? Kowa sai ya ce bai sani ba, har yanzu maganar wani dattijo ta na masa ansa kuwwa a kunnuwansa lokacin da yake ce wa ''a gaskiya kaf garin nan babu wanda zai ce yasan asalin sunan yarinyar nan, tunda ba a nan aka haife ta ba, sun fita yawon rani wane gari ne ma?'' Ya yi shiru yana nazari ko zai tuna garin da su Ado da Balki suka tafi cin rani a shekarar da suka dawo da ?ar malekar ?arsu wacce suke kira da Talatu, daga nan kuwa sunan yarinya ya bita hakan nan.
Haka aka gaji da neman sunan a lokacin kawai sai aka Waura da sunan Nana Talatu, dama ya tabbata ce wa duk Mace ta duniya sunanta Nana, shi kuwa Namiji Mamman.


Uban tsakin da Yusuf ya ja ne ya yi sanadin dawowar Abdallah cikin duniyar masu matsakaiciyar lafiyar daya faWa, dan yanzun ba lallai a kira sa da mai cikakkiyar lafiya ba, ya dawo daga nisan kiwon da ya yi a duniyar manazartan da abun yi ya ?are musu.

Kallon Yusuf Win ya yi da ayar tanbaya game da tsakin daya rattaSo yanzu, suna haWa ido Yusuf Win ya kauda kai daga garesa, lokaci Waya kuma ya fidda hannunsa daga samirar wainar da suke dannata da iya karfinsu badan tana musu daWi ba su duka ukun, labulen Wakin ya Waga tare da ficewa daga Wakin gaba Waya.

Shi ma Abdallah a jiye sauran wainar daya soma gutsura a cikin ta tun kafin ya fara wannan dogon tunanin ya yi, wani wawon ajiyar zuciya ya ne ya sauke tare da jingina bayansa da jikin katangar Wakin, idanusa ya rufe lokaci Waya ya fara imagine yadda zai fuskanci ?alubalen daya taryarwa kansa, ko ma ya ce ya siya da kuWinsa, dan ma lokacin da aka nemi da ya bada sadaki da ya duba aljihunsa iya jika ashirin da biyu(22k) nan da ya bada su kaWai ne a jikinsa.
A hankali ya buWe idonsa yana mai maida duban sa ga Ishaq da ya zama mutun-mutumi yana kalonsu tun lokacin da Yusuf ya yi tsakin farko, cikin wata iriyar muryar da ya aro ya ma?alawa kansa ya ce da Ishaq Win ''yanzu miye laifi na dan na bi umarnin zuciyata fisabilillahi, ka duba yadda Yusuf yake so ya juya mini baya lokaci guda! Ita Win abun tausayi ce, ni fa kawai taimakonta na yi ba wani abu ba'' kamar zai yi kuka haka ya ?arasa maganar.

Dai-dai nan kuma Yusuf ya Waga labulen Wakin ya shigo, dan dama daga banWaki ya ke, wannan shigarsa na biyu kenan bayan da wowarsu gida cikin mintunan da ba lallai su ?etare arba'in ba, gudawa yake wanda yasan sarai tashin hankalin da Abdallah zai saka su a ciki ne sila, ko ma ya ce ya saka su tunda mai afkuwa ta afku.

Kusan a tare Ishaq da Yusuf suka Wauko zance, sai shi Ishaq Win ya dakata dan sauraron Yusuf da abinda zancen sa zai ?unsa.

Kamar daga sama suka ji Yusuf yana ce wa ''to ni miye ruwana a cikin wannan zancen Malan Abdullahi da har kake tunanin zan juya maka baya? Ai ka yi daidai malan, abu Waya na fahimta kazo Matamay ne dama dan kaje Kance ka auro wannan yarinyar, kunyi da ita cewa ta tafi garinsu kai sai ka biyo bayanta, tun da kasan idan har a Agadez ne babu wanda zai yarda ka auri yarinyar nan daga Ammy, Abby, kai harma da su Dady babu wanda zai yarda ka auro bare, baren ma kuma ka rasa wacce zaka Wauko musu sai ?ar Kance, kuma wani rashin galihu ba uwa ba uba ba aboki, babu kowa za kaje a ka Wauro maka aure saboda kaine kafi kowa sanin miye soyayya a duniya? Hum kai tsaye bazan iya ce wa kayi kuskure ba amma ba za'aci amanar su Abby dani ba, idan har ban faWa musu a waya kafin mu isa ba to ka tabbatar muna isa Agadez zan sanar dasu duk abinda yake wakana tun daga ranar da muka fara haWuwa da wannan yarinyar, in yaso idan sun nemi ?arin bayani kai sai ka ?arasa musu labarin ta yadda aka yi kuka tsara har hakan ya kasance'' ya ?arasa maganarsa da janyo kwanon wainar sa ya ci-gaba da dannawa a baka kamar da gayya.

Kamar sa?ago haka Abdallah ya kasance, sai Ishaq ne ya yi ?undunbalar yin magana da ce wa ''kafin in kai gundarin maganar da zanyi dole anan in magantu'' ya faWa yana nuna kwanon wainar da Yusuf ya kusan cinteta saura guda biyu a mayin cinye ta da ya fara.

''Eh ban koshi ba dama kashi naje yi'' ce war Yusuf cikin halin ko in kula dan yau baya jin akwai wani abu wai shi sassauci a duka lamarinsa.

Sai da Ishaq ya gince dariyar data taso masa ta hanyar danne ?ofar bakinsa da duka hannayensa biyu.

Abun mamaki anan shi ne Abdallah mai raha, murmushi, da dariyar ?eta har da ta banza yanzun ko gezai bai yi ba, shi sai yaga ma kamar da gayya Yusuf Win yake so ya tunzura sa da kalaman daya jefe sa dasu yanzun nan, sai dai ba yadda ya iya dole yabi shi a hankali dan baya so su Ammy suji wannan zance kamar yadda Yusuf Win ya ce sai ya faWa musu.

''Yanzun yaushe ne zamu koma gida? Ce war Ishaq.
Gyatsa Yusuf ya yi tare da hamdala ga Ubangiji yana ce wa ''da gaskiya sai mun yi kwana biyu muWan zaga ?auyuka da gonakan da bamuda su a can garin, amma yanzu kam zance ya sauya tunda munyi abinda ya kawo mu, mi ye muke jira kuma? Kawai mu shirya zuwa azahar mu kama hanyar komawa gida, dan gudun kar a saSa ranar tarewar Amarya da Ango really?'' ya yi maganar yana kallon Abdallah cike da tarin iskanci da kuma ?atoton takaicin sa fal ciki da ransa.

''Ya isa haka Yusuf! Na ce ya ishe ka haka! Kai baka san lokacin wasa bane komai? Tun Wazu nake so ku fahimceni amma abu ya gagara, kai baka fahimceni ba kuma ka?i bari wani ya saurareni, zan faWi a ko'ina kuma a gaban kowa ce wa ban aikata ba dai-dai ba kamar yadda kake kallona a haka, Ni jihadi na yi fisabilillahi kuma Allah yasan da haka, mi yasa kake so sai ka ?ure Ni ne iye? Ba na so ka daina, idan har ba zaka mini fatan alkhairi ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login