Showing 72001 words to 75000 words out of 78880 words

Chapter 25 - YAR KANCE free pages na Maman Abdallah.doc

Allah'n ba zai aikata abinda shi YallaSai ya faWa, a yau koda tare aka haife ku da mutun baka shaidar sa akan abinda idanunka basu gani ba, ballantana kuma ni da Allah ne ya haWa ni dashi rana tsaka, a wata ranar Laraba da sayin safiya naje gonata ta bakin mashigar gari, yayin dana tura ?an matasan yarana zuwa wata gonar, ina tsaka da aiki na sai hangen wani abu mai kama da mutun nayi a can gefe a yashe, wanda a alamu babu alamun yana motsi, da dukkan ?arfina na saSashi a kafaWa, na nufi gidan mai gari dashi, ba tare dana ji wani War ba na gabatar dashi a gaban magabatan gari, duk da nima tun a lokacin nake jan ragamar limanci a babban masallacin garin. Da taimakon Allah da taimakon su jama'ar dake fada wannan bawon Allah'n nunfashinsa ya dawo gangar jikinsa, sai dai an Wauki sa'o'i kafin ya iya buWe idanunsa, lokaci Waya kuma yana mai dafe kansa. A ta?aice dai a ranar muka gane mutumin nan baya gane komai, haka ya manta komai, yanzun komai ya zamar masa sabo. Na Wauki nauyin tafiya dashi gidana dan kulawa dashi a gaban Maigari, ya kuma bani goyan baya akan hakan, tun ma anan fadar na fara kiransa da suna Usamatu, ya kuwa amsa, kafin muka wuce gida da sabon ba?ona mai sabon suna da sabuwar rayuwa. Daga kwana aka fara lissafin mako, kafin aka koma lissafa watanni, daga nan aka zarce shekara, a haka har aka Wauki tsawon shekaru Usama bai tuna komai na daga rayuwarsa ta baya ba, maganar aure kuwa babu yadda bamuyi dashi ba, amma duk sanda aka yi masa ita kai tsaye yake barin ma mutun wurin, shifa'u barshi da yawan ibada, 6ana da ?o?ari sosai akan duk wanin abun dana koya masa, wannan ita ce rayuwar da Malam Misbahu ya yi a matsayin Usama'', Malam Liman ya kai ?arshe yana mai tabbatar musu.

Jinjina kai dayawansu suke yi, ba ya kamar Baban su Yusuf da har ?ar ?wallar tausayin malam Misbahu ya zubda, abun da matu?ar damuwa ace mutun ta Wauki tsawon shekaru ba tare da yasan koshi waye ba, gashi kuma shi ba haka yake ba, Allah mai iko.

A wannan gaSar ne kuma Malam Usama ya buWe bakinsa da ''tabbas kamar yadda YallaSai ya faWa hakan ne, sunana Misbahu, sannan kuma ni na kasance direba a gidansa, Dr mutumin kirki ne, sannan kuma yana zaune da kowa lafiya cikin girmamawa, kama daga kan ?an'uwa, abokai kai harma da ma'aikata, zan iya ce wa a lokacin YallaSai ya maida ni kamar abokinsa, dan ko tafiya muke yi a mota haka zaka dinga ji yana sakoni cikin firarsa, haka ma baya gajiya dayi min hidima, duk da kudin albashin aikinsa da ake biyana akan lokaci YallaSai yakan yin kyauta akai-akai, daga ?arshe har muhallin zama masai da YallaSai ya yi niyyar kyautatawa, duk da ina biyan kuWin hayar gidan da nake a duk wata, kuma a haka ma har inyi hidima dayawa da rarar kuWin da nake samu daga gareshi.
Wata rana ina tsaka da goge babbar motar dana fiddo farfajiyar gida, wacce zamu fita da YallaSai da ita, naga ficewar wata mata ta gabana ta nufi babban falon gida, har ga Allah tun ganin farko ban yarda da yanayinta ba, dan kana ganinta zaka fahimci a tsorace take. Washe gari ma na sake ganinta a irin yanayin, gashi ko kaii waye kayi kaWan ta amince ku haWa ido da ita sai dai a bisa kuskure. Ranar da ya cika kwana goma a gidan nan naga ta fito tana ta rarraba idanu, ashe wai yanayi da kuma yawan mutanen dake farfajiyar gidan take dubawa, duk babu wanda yasan ?udurinta a gidan, to tun daga ranar na fara fakon ta, ina lura da duk wani motsi na shiga da fitarta, a saboda ita na ?ara lokacin tashi na a aiki, nakan zauna har sai naga Maigadi yana shirin rufe gida irin ?arfe goman daren nan kafin in yi masa sallama in nufi gida, a hakan ma ina taraddudi kar aje matar ta zanbaci amincin da mutanen gidan suka bata, ta cutar dasu cikin dare. Har ga Allah bansan nufinta akan akan ?ar jaririyar gidan bace, sai a wata ranar Talata da safe misalin ?arfe goma da ?an kai, fitowata daga banWaki kenan naga fitowarta rungume da wani abu a gaban hijabinta, da hanzari naga ta fice daga gidan, dubana na maida wurin mai gadi, sai naga bacci ya Wan fara shurarsa na sanyin iskar furannin dake kaWawa a tsakiyar gidan. Duk da bansan ko miye a tare da ita ba haka nan nabi bayan ta, amma ni nafi zaton ko wani abun ne ta sato.
Duk da sauri take haka na cimmata, na Waya baki da nufin yi mata magana kawai naji kukan ?arinyar nan, a mugun razane ta juyo dan ganin ko wani baiji kukan yarinyar ba, sai kuwa ta ganni, yan na fara takowa inda take haWi da mi?a mata hannu da nufin ta bani yarinyar, dan nan take zuciyata ta haskomin abinda ta aikata. Nan fa ta fara yin da baya da baya, kafin in ankare tuni ta zabga da gudu, nan kuma na bi bayanta, ashe ta ajiye Wan sahu a kwanar gidan, nan kuwa ta shige ta barni ina halin gudun da nasha ba shiri. Nan take wata dubara ta faWo min, nima da gudu na koma cikin gidan na faWa mota mafi kusa da ni, dama key a jikin ake bari, mahaukaciyar odar da nayi ita ta tashi Maigadi a firgice, ya wangalemin ?ofar a kiWime ba tare da yasan dalilin fitar ba, daga nan nasa kai da gudu na karya doka, fama kawai nake in cimmusu. Da hannu guda nake tu?in, Waya kuma wayata ce a hannuna ina ta gwada kiran YallaSai amma baya shiga. Nasha wahala sosai kafin in gano su, gashi lokacin da suka shige cinkoson jama'a sai na dauka a motar ina duba su, wayata a kunnena ina ta ?ara gwada kiran maigida, to ?an Islam gari nada yawa, kowa da abinda ya fito nema, a lokacin dai wani Sarawo ya zaren wayar ya zura da gudu, in na bishi na rasa damata na hangota da nayi a cikin wata motar da take shirin tashi. Ai kuwa da hanzari na koma mota dan in cimmusu, kuma Ni wallahi a lokacin na manta maganar kururuwa ma, na tabbatar a lokacin da na nusar da jama'a akan yarinya ta sato da babu shakka jama'a sai sun kawo min Wauki.
Kamar wasa sai gani ina bibiyar wannan motar da ta kama hanyar barin gari, kalmar da asiri haka nayi ta bin bayansu, haka muke ?etare ikuna nakan hanya amma bakina ya kasa furta kalma guda Waya akan matar, sai nake tafiya a matsayin matafi nima. Tafiya dai mai tsayi aka yi, koda an tsaya a inda ya kamata ta fito daga motar ta nemi abinda zata ci ko ta bawa yarinyar to bata fitowa, ?ila sautu take badawa a shigo mata da koma mene ne. Tafiya tayi nisa sosai, duk da bansan inda zamu je ba amma nasan koma dai ina ne muna daf da isa.
Mun shigo muka wuce ta wani babban gari, kafin muka kuma Waukar wata hanyar, a lokacin duhun dare ya fara, gashi kamar man cikin motar ya ?are, duk da motocin gidan YallaSai cikasu dake da mai a koda yaushe amma sai akayi rashin sa'a na wannan motar iyakarsa nan, sai na ratse a gefen titi da nufin ajiye motar, ashe a wani kududfufi na afka, wanda da ?yar na iya buWe murfin motar na fito, nan na kamahanyar dana ga motar ta nufa, na shiga tafiya a ?afa, ga banyi sallar magariba da isha'i ba, ga duhun dare, ga kuma ba haske koda na tocila ne a tare dani. Tafiya nake har bansan inda nake saka ?afata ba, kaina ya juye, gashi dana a sanin garin nayi ba, ban lura da wata ?aton dutse ba, ?afata ta harWe na faWi a wurin, wanda kaina ya yi mugun buguwa da wannan dutse, ban kuma gane inda kaina yanke ba, sai a ?an shekarun baya bayan nan, na fara mafarkai bakatai da suke nuna min fuskokin iyalaina, hakama da sunan YallaSai da yake yawan zuwar min a cikin kwakwalwana.
Sai kuma yanzu dana ji ya kirani da asalin sunana, na gama tabbatarwa yanzun na dawo cikin tunanina.''

Shuru wajan ya Wauka babu mai ce wa komai, kowa al'ajabin wannan abu ne ya rufe shi, ba ya kamar Gwamna da yake jin kamar yanzu matar ta bayyana a gabansa, da shi kaWai yasan irin abinda zai yi mata, tabbas yana time da lokacin da Abby ya sanar masa ?arsa ta koma wa mahaliccinta, amma koda wasa bai ce masa sace masa ?a aka yi ba.

Hum! Baba ya sauke ajiyar zuciya, da muryar tausayi ya ce ''ashe dai abinda ya faru kenan! Allah mai iko da buwaya, wallahi mu duka a yarinyar ta rasu muka Wauki abun, ashe wannan mummunar ?addarar ta sameta, gaskiya Alhaji kunada tawakkali da t???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?awali'u, nayi mamaki ?warai dajin wannan labarai, ashe dai har masu rufin asiri suna iya jurar ?unci bayan suna da hanyar samuwar warakar damuwarsu? Tabbas wannan abu babbar darasin rayuwa ne da mutane ya kamata mu lura dashi, Allah ya datar damu.''

Da amin suka amsa kafin Gwamna ya ce ''to yanzu abinda ake san ji a nan shi ne yarinyar tana raye ne ko kuwa? sannan idan tana a raye yanzun tana ina?'' ya faWa ba wasa, fuska cike da tsare gida.

Malam Misbahu ya kalli malam Liman da neman karin bayani game da tambayar Gwamna, dan shi bayada sani akan komai.

''Eh to maganar gaskiya dawan jama'ar garin mu kan fita yawan cirani, kuma sun ma fi yawan zuwa arewa e nan, dan yanzu haka dayawansu suna can, wasu matan tare da mazajensu, wasunsu kuma sun bar mazajen a gida. Da abu Waya ne tal za'a iya gane wannan matar, shi ne idan har zaku iya gane fuskarta'' ce war malam Liman.

Abby ya karSe shi da ''ni na tabbatar muku Baga matar a Agadez watanni biyu da suka wuce, kuma na tabbata a yanzun haka tana can, domin kuwa an baza hotunanta ta kora ina a hannun jami'an mu, zata iya ficewa daga garinnnan ba face an kamata kuwa, ta kota wane irin hali kuwa, daboda haka zamu tafi can mu cigaba da nemanta, in sha Allahu nan kusa za'a samota, shi kuma malam Misbahu Allah ne ya ?addara sai ya rayu daki na tsawon shekaru, shi ya nufa ya biyota har garinku, ya kuma mantar dashi koshi waye, duka wannan yana cikin ?addarmu baki Wayanmu, ada kam mun munana zato akanka, dan har iyalanka saida suka yi gudun kar abinda la aikata ya shafe su, haka ta Wauki yaronta suka gudu, amma cikin ikon Allah yanzun haka muna nan tare dasu a gidana, zaka riskesu cikin aminci.''
Abby ya Wora da ''yanzun nasan an gama dai-daita komai sai tafiya, bansani ba ko zaka bi su Malan ne ku tafi, ni zan wuce gaba daganan bazan fasa ba, idan kuma za'a barka anan kaWan kintsa ne sai kaje daga baya to shikenan'' Abby ya faWa yana famar rura hannu a aljihun babbar rigarsa.

Malam Liman ne ta ce ''a haba! Taya ma zaice ba zaije yanzu, shi ba wasu iyalai ba bare ace sai ya dai-dai wasu abubuwan, ai kawai dashi za'a tafi, shima yaje cikin iyalansa daya rabu dasu na tsawon lokaci.''

Nan Abby ya cika malam Liman da alkhairai, ya kuma bawa malam Misbahu wasu kuWi ya ce ya ri?e a hannunsa, su haWe a gida. Nan suka yi musu sallama suka fice, dan saura kaWan Abby'n ya makara zuwa airport, wai dan ma yanzun zasu iso Damagaram, tunda hanyar ba cinkoso, gashi kuma manya ne akan hanyan doke ake matsawa a basu wuri, nan danan suka iso gidan gwamnati, inda Abby ya kuma Waukar wanka sai airport, bayan sun yi sallama da abokinsa Gwamna, wanda har rabuwarsu alhini abinda ya faru da Abby'n bai ba....

Sai ?arfe sha Wayan rana suka kama hanyar Agadez, bayan gama dai-daita komai, Malam Liman da Malam Misbahu harda Wan kukan su na rabuwa da juna, inda Liman ya yi wa malam Misbahu alkawarin zai zo yaga mazauninsa da zaran komai ya dai-daita.

A motar da Abdallah yake tu?awa Ishaq ne a gaba zaune kusa da Abdallah, sai Yusuf

?ayar motar kuma Amarya ce da ?an rakiyarta mutun uku, Wayar ?anwar Mamanta ce Tanti ?ausiyya, sai kuma Wiyar babbar yayarsu Baba mai suna Indo, ta ukun kuma Shamsiyya ce a kusa da amarya sai sha?iyanci take mata Anty Indo na kama mata, sai Tanti ?ausiyya ce mai ?are ta.

?ayar motar kuma Baba ne kujerar baya, sai malam Misbahu a kujerar mai zaman banza
Baba da malam Win sai zancen abinda ya faru suke yi, a haka har suka bawa direba haske akan maganarsu, har shima ya shiga zancen tsundum.

''Amma naga abun al'ajabi, wai dama ashe abinda ya faru da ?anwarka kenan Abdallah? Amma duk aka rufe mu akan ta rasu! Ashe wai saceta aka yi'' ce war ango Yusuf.

Abdallah ya ce ''kai ka bari kawai, nima bai fi watanni biyu da sanin ba rasuwa tayi, saceta ?ar aikin gida ta yi ta gudu da ita, da farkon an yi zaton ko tafiyarsu Waya da wannan Direban, ashe ma shiWin ceton yarinyar ya je.''

Ishaq ya ce ''to amma yanzun ta ake ciki game da labarin yarinyar?''

''Eh to gaskiya har yanzu ta?amemai ba'asan ina ita matar ta kaita ba, an dai tabbatar KANCE ta zo da yarinyar a lokacin, sannan kuma watannin baya-bayan nan Abby yaga matar a wurin wani taro a Agadez, kuma tana ganinsa ta gudu, hakan ya tabbatar ita ya gani ba gezau ba, kenan ba za'a san inda yarinya take ba har sai an kama wannan matar, ita ce tasan komai'' ce war Abdallah.

''Allah ya kyauta yasa a dace'' Yusuf ya faWa cike da kulawa. Suka amsa shi da Amin su duka, kafin Abdallah ya kira number Ummy'nsa. Sun Wan taSa fira, har take faWa masa Abby ya faWa mata ce wa anga malam Misbahu, kuma harma kuna hanya yanzun haka tare da shi, nan Abdallah ta tabbatar rmtama da zancen ya kuma ?ara da kwantar mana da hankali da ce wa ''karki damu Ummy, in sha Allahu za'a ganta, kuma dole ne ta faWi yadda tayi da rayuwar yarinyar'' dan shi har ga Allah yafi badawa kawai yarinyar ta mutu tun tuni, dan a nasa ganin taya za'a raba ?a da uwarta tun tana da wanni uku kuma ace zata rayu, bayan yaWan yaron da aka sace daga gaban itayensa zai yi wuya ace an ita cire kuWi an siya masaafara dan ya rayu.

Wani kiran ya tura wa number Talatu bayan sun yi sallama da Ummy, har yanzun dai a kashe, rai ba daWi ya ci-gaba da tu?i, Allah Allah yake suyi su isa Agadez ya wuce gida, yaje daga Noor Winsa, wacce tunanin halin da take cike ya fara shirin zautar dashi.

Agadez
Ummy suna gama waya da Abdallah ta mi?e ta nufi sashen su Baaba Balki, da sallama ta tura ?ofar falon ta shiga, wanda ya yi dai-dai da fitowar Inna Balki daga kicthing Win, wanda tana tsaka da aiki ne taji sallamar Ummy.

Da fara'a a fuskarta Baaba ta ce ''laa Hajiya keda kanki? Ai da kin ce inzo sai in zo har ciki ina sameki.''

Murmushi Ummy ta yi haWi da zama a kujerar da Baabar ce tayi mata tayi, kafin ita ma tazo zata zauna a ?asan Wan madai-daicin carpet Win da aka saka musu a tsakiyar kujerun falon, wanda gwargwadon karfin mai rufin asiri dai sun ishe shi zaman gidan duniya. ''a'a dan Allah, ki zauna a kujera magana za mu yi'' Ummy ta faWa tana mai yi mata nuni da kujerar kusa da ita.
Ba musu kuwa ta zauna tana sauraron bayanenta, tuni hawayen farin cikin bayyanar mijinta ya wanke mata fuska, cikin kuka ta ce ''yanzu baban Al?asum yana kan hanyar zuwa gidan nan? Allah mai iko! Wallahi ni na gama cire rai da zuwansa Hajiya.''
Ummy ta ce ''ai bawa baya cire rai daga rahamar Ubangiji, a kullum muna sarai akan abubuwan alkhairi, sai Allah ya ida mana nufi akan burikanmu.''

''Tabbas wannan haka yake, ku Win nan dai mutanen kirki ne, Allah ya yi muku mafiyin abinda kuke mana, ya dubi lamurranku...''

Sallamar Al?awum ta katse wa Baaba zancenta, nan ya gaishe da Ummy cikin girmamawa, ta amsa shi cikin farin ciki, haWin da ce wa ''yarona wata babbar bazata za ayi maka yau a gidan nan, Baabarsu karfa ki faWa masa, na bashi wannan bazata a matsayin kyautar jarabawar da yaci ta baya bayan nan, wacce Allah bai bani damar yi masa kayuta ba'' ta kai ?arshe tana ?ar dariya.

Ita ma Baaba dariyar ta yi tana ce wa ''in sha Allahu kuwa bazan faWa masa ba Hajiya.''

Harararta Ummy ta yi jin dai kiranta da Hajiya take ta?i ta fasa, bayan a kullum haka take ce mata ta kirata da sunanta Gaisha, ko kuma tace Ummy'n yara.
?asa dakai Baaba Balki ta yi tare da ce wa na daina Ummy'n yara.
''yawwa ko kefa'' ce war Ummy tana ?o?arin tashi. Sallama ta yi musu tana mai barin sashen, Uwar da Wants suna yi mata godiya.

Al?asum ya matso kusa da mahaifiyarsa ya ce Baaba wai miye za'a yi min bazatar dashi ne? ?an Allah Wan faWa min.''
Cikin farin cikin daya kasa Soyuwa akan fuskarta ta ce ''Wan nema, miye yasa ita baka tambayeta ba? Wato nice sa'arka kenan ko?'' ta faWa tana zungure masa ?yeya cike da shau?i.

''Allah Baaba Ummy'n ce ba wasa, da wuya mutun ya iya kwalo-kwalo a gabanta, tana yin ?warjini ne sosai wallahi, gashi ina masifar jin kunyarta, Allah Ummy da ?a?anta gare ta sai na zama sirikinta.''

''Ka jika da zancen banza, an kuwa Al?asum kana ajiye kanka nan kusa kuwa? Anya kana tuna kai waye kuwa? Idan ba haka ba ta yaya kake tunanin koda suna da ?a ta kasance mallakinka, a irin hakan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login