Showing 9001 words to 12000 words out of 78880 words

Chapter 4 - YAR KANCE free pages na Maman Abdallah.doc

har kunne haka suka ta nuna zallar farin cikin da suka shiga dangane da karar da yayi musu, duk da sunada Wan rufin asiri a yanzu amma hatta iyayen su sun ji daWin yadda Abdallah da Yusuf suka tsaya aka yi komai na bikin tare dasu kamar ciki Waya suka fito dukkanin su, masha Allah haka akayi taro aka watse, dangi da sauran yan'uwa suka mai?a amarya Wakinta tare da bada amanar ta ga miji da kuma danginsa.


Kwana biyu da kammala biki iyayen Amarya suka bar gari sai garin da aiki ya maida mahaifin su, sun bar gari cike da kewar babbar ?arsu mace Waya tilo ?wallin ?wal.

Ranar da suka fitar Wan tafiya ?auyen su Yusuf tayi, Abdallah bai wani samu matsala daga iyayensa ba dan yanzu ya wuce ace an hanashi tafiya matukar bata saSawa mahalicci ba, cikin farin ciki suka bar gida a babbar motar gidan da Abby ne yace zaifi dacewa ace sun tafi da ita bawai su shiga motar haya ba, su Ummy harda guzirin danbun nama tayi musu, yayin da Abby yasa aka cika musu bayan motar da tsaraba kamar ance idan sunje sai sun rabawa duka jama'ar garin, Yusuf ya rasa bakin yin godiya, sai dai Ishaq ne ya fanshe shi da yi wa su Abby addu'ar Allah yasa a gama da duniya lafiya, tare da fatan samun nasarar rayuwa da kuma samun cigaba mai dorewa, Ummy ce take amsawa da ameen ya yin da Abby yake ta mirmushin farin ciki da godewa Allah, alhamdulillah kawai yake haWa shikan yagodewa Allah da ni'imomin da ya yi agaresa, tabbas ya cancanci yabo da kirar, Allah mai bayarwa da kuma hanawa, ya bawa wanda yaso ya hana wanda yaso kuma alokacine dayaso, gashidai Allah bai hukunta zai rayu da da Wa ko ?arsa ta cikinsa ba, amma ya azurtashi da yaran da zasu na yi masa fatan alkhairi, cike da jin daWin addu'ar Ishaq din ya ce ''kuje kunga kar rana ta take sosai, Allah ya yi muku albarka ya yi muku jagora, yakai ku inda bakwa tunanin zuwa, Allah yasa kaima ka sama mana surukan acan duk mu gama mu wanke ku'' ya faWa yana kallon Ishaq.

?an sosai ?eya Ishaq ya yi yana sunne kai kamar yaganshi a gaban surukai ya ce ''Abby ai Abdallah ne a gaba kafin ni, tunda ya bani kusan watanni uku a lissafin ranakun haihuwa'' ?ar dariya Ummy tayi ta ari bakin Abby wajan faWin ''ai kai kaWai ne baka samuba yarona, dan Abdallah ma kuna dawowa za'akai nagani inaso'' su duka biyu idanu suka fiddo suna kallon Ummy da mamaki jin ta ce Abdallah ya tsayar da mata har manya zasu shiga maganar, Yusuf ya juyo da kyau baya kallon Abdallah kallon taguma, irin na neman ?arin baya Win nan.

''Ummy Abby na sai Allah ya maidomu, zamuyi magana dazaran mun isa insha Allah'' Abdallah ya faWa lokaci Waya yana barin falon.

Da mirmushi duka suka amsa kafin daga baya suma su Ishaq da Yusuf suka bi bayansa da tarin tambayoyi a cikin rai da bakunansu.

Tafiya suke akan hanya sai tsula gudu Abdallah yake kamar yana saman gaWon Wakin jatumarsa, sosai yake gudu kamar dama yasan hanya, alhali da Google yake aiki wajan ganin mi?akkiyar hanyar da zata kaishi har kauyen Matamay direct, tun Wazu Yusuf yakeso ya yi masa tambaya game da zancen da yaji Ummy tana yi game da neman auren nan, kallon Abdallah ya yi da yake dama shine a kujerar mai zaman banza, shi kuma Ishaq yana bayan motar a kwance da alamu ma bacci yake, cikin zolaya ya ce ''wai dan Allah abokina miye gaskiyar maganar danaji Ummy tana yi, ka fara neman aure shi ne ko ka faWa mana? Ka kauta'' yayi ?wafa lokacin da yake ?arasa maganar.

Basarwa Abdallah ya yi kamar ba zai tanka masa ba, anfi mintuna uku kafin ya ce ''kana ji ko! Kawai su Ummy'n ne suka ta?ura mini akan maganar wannan yarinyar Angel take ko waye, ganin kamar basu ji daWi ba shi ne kawai na ce dasu na amince, shi ne asalin zance kaji daga tushe'', da mirmushi Yusuf ya amshe zancen da ce wa ''ai kuwa dai ?ara mu aurar da kai mu huta, ina goyon bayan su Abby''.

Wata iriyar dariya Abdallah ya bushe da ita yana nuna Yusuf da yatsutsan sa na duka hannayensa, da sauri Yusuf ya taka burkin motar yana tallare ?eyar Abdallah.

Tsayar da motar da Yusuf ya yi ne ya yi sanadiyar farkawar Ishaq dake rangaWa baccin sa hankali kwance, kamar zai yi kuka ya ce ''wai har mun iso ne haka ina bacci na mai Wan karan daWi kun tashe ni''.

Yusuf ji ya yi kamar ya zagaya ya yi ta jibgarsa haka yaji, cikin shan fuskar shanu yana kallon Abdallah ya ce ''Dan an ce za'a mini auren dole bashi yake nufin na ha?ura da rayuwata ba, kai kuma kake zancan kana bacci mai daWi wallahi da saidai ka ganka a wata duniyar sheka??u badai wannan ba, badan na taka birkin motar nan ba Allah da tuni ya kifar damu duka wai yana dariyar iskanci da iya shege'' ya ?arasa da kallon sashen da Ishaq Win yake.

Kallon tuhuma Ishaq yabi Abdallah dashi kafin ya ce ''Yaron Abby ba zaka barmu muga jikokin ?a?an mu na biyar bane? Ka ke faman kashe mu tun a matakin farko na shekarun samartakar mu?''.

Cikin dariyar maganar Ishaq Win Abdallah ya ce ''Kawai fa dariya nake masa jin ce wa muma so yake a mana aure irin nasa, shine dai kawai'' ya faWa yana buWe ?ofar fita daga motar.

A hasale Yusuf ya ce ''Ina kuma zaka je wai?'', cikin Waga murya yake faWin ''Atsawi zanyi malam ko a motar zanyi'' lokacin da yake buWe bayan motar ya Wauki ruwa na gora dan tsarkake jikin sa bayan tsiyaye abinda ya faWa zai yi.
Koda ya dawo Yusuf yayi masa musayar wuri, dan a ganinsa tu?in Abdallah lahira salamu alaikum ne.


?arfe huWu na yamma suka iso garin Matamai, daidai an gama sallahr la'asar.


Da karamci da kuma girmamawa irin na dangin mu na ?auyuka aka tarbe su, kafin suyi sallah tuni aka cika musu gabansu da irin kala da kala na abincin mu na gargajiya irinsu Wan wake da mai da yaji burabusko da miyar yakuwa, salati( salade), ?agalashe dadai sauransu.

Mutanen gida kuwa daga manya har yara sai shigowa suke suna musu sannu da zuwa kamar yadda ya kasance al'adar sune girmama ba?o koda ka girme sa ne.

Zuwa karfe shida na yamma kowannan su yayi wanka ya canja kaya, ya yin da suka yi alwala dan jin ana kirare kirayen sallar magariba.

Bayan sun yi sallar isha'i kuma aka yiwa Yusuf iso dan su tattauna da yarinyar da aka zaSa masa mai suna Rammatu, ya yin da Ishaq ya samu wani matashin yaron gidan mai suna Ma'azu ya fita dashi wai zasu zaga gari a ce war sa.


Zaune yake yana danna wayar sa da alama game yake dan bai jima da gama waya da Iyayen sa ba, kamar wahayi haka sunan garin ya faWo masa a rai, KANCE, ba jimawa maganar Yusuf a waccan ranar ta dawo masa a ?wa?walwar sa ''?an kance kenan, sune ma?wabtan ?auyan mu wato tushe na'' kenan idan ya fahimta garinsu wannan yarinyar nan kusa yake da wannan garin kenan? Ya tambayi kansa.


Bai gushe daga wannan tsananin ba maganar yarinyar ta yawo masa a kansa ''Inaga kawai zance ta turani ?auyan, da in bi hanyar da take so ?wara kawai naje na zauna da Babana''.

Shiru yayi yana ?ara zurfafa tunaninsa kafin ya mi?e tsaye kamar an mitsinesa yana saka takalmansa tare da barin gidan........


Page 5
____________Tafiya yake hannayen sa duka biyu a aljihunsa, hasken watan dake sama ne ya ?awata sararin samaniyar duniya, yayin da garin ko ina da haske irin na wata a kwana goma sha huWu zuwa sha shida.


Tafiya yake har ya fara barin gari, zuwa lokacin sanyi da iske irin na bayan gari sun fara ziyartar sa.

Wasu matasan maza guda biyu dake akan sharet da mara?e( Wan saniya) ne suka zo giftawa a kusa dashi, har sun Wan bashi tazara ya ?arasa garesu da sassarfa, da sallama ya fara kafin yayi tanbayar sa garesu ''Dan Allah ?an'uwa anan kusa akwai wani gari wai shi KANCE?'' ya tambaye su.

Kusan a tare suka bashi amsa da cewa ai nan kusa ne kuma ma garin su ne yanzu ma daga cin kasuwa suke wani ?auye zasu koma gida.


Saida gabansa ya faWi haka kawai jin yana kusa da garin, cikin kamewa yace ''Dan Allah ko zamu iya tafiya tare daku nima can zani amma ni ba?o ne''.


Da yake suma wasu masu zance ne yasa suna tafiya a hanya suna ta?alar sa fira jefi-jife, har suka kisan isa ?auyan Kance mamaki bai barsa ba wai yau shine a saman sharet abinda yake ganin mutane suna mu'amala dashi ta gilashin motar sa ba tare da wani kwakwaran dalili ba, Wan nunfasawa yayi ya kalli Wayan wanda yake mazaunin shine direba, eh direba zai iya kiransa dan shine a gaba kusa da mara?in, kuma shine da bulalar saka mara?in a hanya da zaran ya fara wasa yace ''Dan Allah ko kunsan wata mai suna Talatuwa a garin naku?''.


Da tarin mamaki matashin ya kalleshi yace ''YallaSai a irin wannan ?auyen namu zaka tanbaya da mai sunan Talatuwa! Ai kuwa suna da yawa, saidai idan kasan sunan mahaifi ko mahaifiyarta, wai ma babba ce ko yarinya? ya kamata in sani kafin insan wacce Talatun kake magana''


?an jim Abdallah yayi kafin yace dashi ''Eh to zadai a iya kiranta da yarinya dan ba zata wuce shekara sha huWu zuwa sha biyar ba, wata da suke zuwa Agadez da Mahaifiyarta ko zaka tuna ta'' ya ?arashe da masa cikekken kwatancen ta yadda zai iya ganewa.


Kafin yace wani abu tuni Waya abokin tafiyar nasu ya magantu da cewa ''Wai Sulemanu ka gane wace Talatu yake magana, ?ar gidan Ado Wan caca fa ita yake nufi, kuma ma ai bata jima da dawowa daga can birnin da faWi sunansa dai-dai ba, ku acan ta baro uwarta ta dawo wajan fa?irin ubanta mai matacciyar zuciya, Sulemanu anya Ado zai san duniya ta faku kuwa, wai ashe ba shine mahaifin Talatu ba, babu wanda yasan da wannan rufeffen al'amarin saida ya Sullo da wata magana a jiya jiyan nan, waishi da bashida hankali wai zai aure ta, kuma fa yarinyar bata wani rasa masoya ba tunda ba laifi tana da hankali sosai'', Wayan ne ya amshe da cewa ''Ai kai dai bari Kanta! Kuma wallahi nima nasoyyarinyar nan tun tana ?ar ficikar ta, da na buWe baki ina jiran dawowar su a wannan shekara in sanar mata da abinda ke raina, sai kuma ta dawo ita Waya ba tare da mahaifiyartan nan mai shegen san abin duniya ido rufe, sai kuma gashi wannan mashayin Wan cacan yana shirin yin wuf da ita''.

Sulemanu ne ya amshe da cewa ''Amma da qnce yarinyar bata so, kuma yanzu haka akwance take bata da lafiya jin wai wa?an'da ta ri?a a matsayin iyaye ba suba suka haife ta ba, Allah sarki yarinyar kirki, babu yadda ta iya haka tana ji tana gani zata auri ubanta, ita uwar tana can tayi garau da ha?ora wai ita ta turo yarinya gida, batasan shegen mijinta na shirin kwance musu zani a kasuwa ko ma ina ce ya kwance Win'', daga tambayar su ko sun san Talatu kawai sai matasan suka Suge da fira abunsu, duka Abdallah yana sauraren su kuma yanafa himta, idan har kunnuwansa sun saurara dai-dai ita wannan yarinyar ce suke magana akan ta.


Daidai da isowar su cikin ?auyen ne Wayan yace ''YallaSai mun iso cikin gari a ina zamu sauke ka?''.


Saida wani Wan murmushi ya suSuce masa wai sun iso gari, yanzu wannan shine gari wai, a gajeran tunanin sa zasuyi daidaito wajan ma'auni da bayan garin daya fara ganin wannan yarinyar da har gobe ya kasa sanin dalilin da yasa yake bibiyar lamarin ta.


Saukowa yayi daga sharet Win yace da wanda yayi masa tambayar wato Kanta yace ''Na gode da da wannan taimako, ina godiya sosai Allah ya biyaku, amma dan Allah yaushe ne daurin auren kuma inane gidan su?'' ya kuma tambayar su dan ?arin sani.


''Eh kamar naji an ce gobe da ?arfe bakwan safe, bawan Allah injin dai ba wani abu Talatun tayi ta gudo daga birnin ba, dan da alama kaima daga can kake, gashi kuma mu mun buWe baki munyi ta sakin zance a gaban ka, Allah yasa dai ba ka da nufin cutar da ita bane dan wallahi abun tausayi ce, gashi an kasa samun ko mutun Waya acikin iyaye da magabatan mu wanda zai musawa Ado game da ?udurin sa akan Talatuwa'' cewar Sulemanu yana share hawayen tausayin yarinyar daya gama kama zuciyarsa sa.


?an bubbuga kafaWar sa Abdallah yayi tare da bashi tabbacin cewa ''Karka damu abokina, niWin amintacce ne! Kuma insha Allah bazan cutar da ita ba ba kuma zan bari wani ya zalunceta ba ko kuwa shi kanshi Adon ne, nayi maka al?awari'' ta ya tabbatar masa da hannun sa kamar yadda indiyawa suke Waukan al?awari abun cikawa.


KuWi ya ciro daga aljihun wandan sa wanda zasu kai jika ashirin (20k) ya basu tare da ?ara jaddada musu godiya, bai gushe ba sai da suka nuna masa babban masallacin garin kafin suka rarraba.


Matamay

Zaune suke sunyi jigum-jigum ganin shiru har ?arfe goman dare ya rufa ba Abdallah babu dalilin sa, a irin wannan lokaci na sanyi a ?auye ba'a nisa da gari, kasancewar duka matasa maza da mata na cikin garin duk sun tafi cikin birane rani, to a lokacin yawan Sarayi da kuma malalatan mutane suke baza komar su, sanin ba matasan da zasu kare iyaye da matayen su a gari.


Ire-iren waWannan tunanin jama'ar gidan suke kodai ya haWu da Sata gari ne.

Cikin tashin hankali Yusuf yace da surukin sa na gobe wato Malam Lamin, kuma Wan uwan baban Yusuf Win ne ta Sangaren uwa yace ''Kawu kaga fa har yanzu wayarsa bata shiga yanzu ya zanyi, mi zan faWawa Ummy da Abby dan Allah'' yayi maganar kamar zararre.


Kawun ne yace dashi ''Ka kwantar da hankalinka Yusufa! Wata kila ko yayi wajan bayan gari ne, amma karka damu zai dawo da ?afafuwan sa insha Allah''.


Kamar zai yi kuka haka Ishaq yayi kalar tausayi tare da faWin ''To Kawu mi zai hana abi bayansa! Ina nufin mu bazu a rarraba kota ina, kunga sai a ganshi d wuri koda bayan garin ne ya tafi''.


Basu Musa shawarar da Ishaq Win ya jawo ba suka bar bazu neman Abdallah.


Wasa_wasa wankin hula yana shirin kai su dare, dan har kusan ?arfe sha biyun dare suna kan nema da cigiyar Abdallah amma shiru ba labari, gashi kuma wayarsa har zuwa wannan lokaci bata shiga.


Cikin tashin hankali Yusuf ya danno number Abby da nufin antaya masa kira a tsakiyar daren nan.


Kwace wayar Ishaq yayi yana kiran ''Ba kada hankali ne komai Yusuf, wai su Ummy zaka kira ka tashi hankalin su tun da wuri haka, ai dai duk rinci ka bari idan safiya tayi in har ba'a gansa ba kafin ka kira ka faWa musu, amma ba yanzu''.


Komawa Yusuf ya yi ya zauna a bakin katifar da aka kawo musu ?an madaidaita har guda uku wato kowa da tasa, dafe kansa ya yi da yake shirin darewa gida biyu, cikin tsananin tashin hankali kamar ya fashe da kuka ya ce da Ishaq ''Ishaq dole hankali na ya tashi, ka duba fa ?arfe Wayan dare ne take shirin rufawa har yanzu bai dawo ba, wa yasani a garin nan, ina yaje bai faWa mana ba, wallahi ji nake kamar nayi hauka, Allah ka tsare sa a duk inda yake alfarmar Annabi da al?ur'ani'' ya ?arasa da haWe hannayen sa biyu waje guda tare da Waga kansa sama.


Yadda suka ga rana a hanyar su ta zuwa ?auyen haka suka kwana a bin lungu da sakon cikin ?auyen ko Allah zaisa su ganshi, amma har asuba shiru ba labarin sa.


A ?auyen Kance
A babban mallacin garin ya kwana bisa jagorancin wani bawan Allah mai suna Usama, wanda shima a nan yake kwana akasarin rayuwarsa, ba wani babban mutun bane can_can amma zai kai shekaru arba'in haka, bashida iyali dan asali ma har yanzu bai tuna shiWin na ina bane ba bayan shekaru goma sha biyar da aka tsince???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?sa a bayan gari gaSar ruwa a yashe, malam Limam yasha wahala sosai kafin mutumin ya dawo kamar ko wane mutun, saidai ko ya farfaWo ya mance komai daya danganci rayuwar sa, haka yaci gaba da zama a gidan malan Limam a wani Wakin daya kasance nasa ne, inda kuma Limam Win ne ya saka masa suna Usama, yanzu haka shine ladanin wannan masallaci, shi yasa a mafi yawan lokuta yake kwanciyar sa a masallaci har asuba hi.

Bisa rantsuwar da Abdallah ya yi masa akan shi ba macuci kuma ba azzalumi bane kamar yadda yanzun duniya ba tabbas ne da ita ba, yasa ya bashi masauki a nan.

A kuma nan suka kwana ibada kamar yadda hakan ne al'adar malam Usama, sai kiran sallar asubahi suka tsagaita, ?ara kusanta kansa Abdallah ya yi da malam Usama yadda zai ji kuma ya fahimce shi, bai Soye masa komai ba game da zuwan su ?auyan Matamay har iso warsa Kance da ya yi, ya kuma tambayar sa ce wa wai da gaske a safiyar yau za'a Waura wa yarinyar aure da baban ta na bogi.


Da yake labari komin ?an?antar sa baya Soyuwa idan aka ce maka ?auye ne, tuni kowa ya sani a Wan ?an?anin lokaci.

Ha?i?a da kuma tabbatarwa Abdallah ya samu daga malam Usama, sam baiji daWi ba, baya jin kuma zai bari wannan mummunan abun ya faru da yarinya ?arama haka, ta gudo daga Agadez ne dan tare kima da darajar ta na ?a mace da uwarta take so a dole sai ta zama watsatsatsiya, ashe data zo nan Win ma bata tsira ba gashi ana shirin cutar da ita, bashi da lokacin tambayar Ado idan ba shine mahaifinta ba ina asalin Iyayen ta, amma yanada lokacin da zai kuSutar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login