Showing 75001 words to 78000 words out of 78880 words

Chapter 26 - YAR KANCE free pages na Maman Abdallah.doc

ka ja mana matsala a wancan garin ko? To waccar ma tafi ?arfin ajinka ina ga ?ar nan gidan? Kar in kuma jin irin wannan batu, dan bai yi kama dana mai hankali ba'' ta faWa rai a Sace.
Ha?uri ya bata haWi da yi mata al?awarin kiyaye harshensa, sai dai shi har ga Allah baiga wani abun data faWa ba dai-dai ba.

Talatu
Tunda ta tashi da asubahi ta wuce kicthing dan samawa kanta wani abun, Wan ji tayi kamar babu hanji a cikinta.
A gurguje ta dafa taliyar yara ta haWa da soyayya kwai, a kicthing Win taci ta ?oshi kafin ta fito ta hau gyaran sashen, batada shakka ko tsoron kar wani ya ganta, tunda tana da tabbacin ta datse ?ofar ta ciki, haka ma yace mata zai kulle ta waje, kuma zai tafi da Wan makullin ne, dan haka babu mai shigowa nan koda kuma wanene, shi yasa take shaglinta. Tana sa ikon gyaran da ba wani dattijo tana ?issima irin kukan da zata yi masa da iya lokacin da zata Wauka tana yi, na?in kiranta da yayi tun jiya da safe.

Ta gama da falo ta faWa daki, nan ma ta gyara ta feshe ko'ina da turaren Waki.

Ta koma Wakknta ta kwanta tana mai kallon wasu videos Win da bata gama kallonsu ba, wasu na abinci ne, wasy kuma na juice, wasu na kalolin da ake haWa a samu dressing Win da zai bada kala, a ?arshe dai sai gata a video'n ta da Abdallah ya Wauka a wancan filin, gata nan tsaye ita da suwaiba a filin bolo. Dum! ?irjinta ya buga, ta kuma shiga kwokwanto game da lamarin mijin nata.
''Ya naganni a wayarsa, bayan a lokacin ko sanin da banyi ba! To wai miye ala?arsa dasu da har yake da hoton Inna Balki, haka kuma yake da video'nta, wai danma Allah yasa ba wani hayaniya ko suturta nayi a Waukar ba, iyaka dai ina nusar da Suwaiba ne akan rayuwarta ta yau da kullum'', ta faWa a bayyane.

''Joma dai minene zan sani ne bayan e anayi masa tanbayoyi'' ta kuma faWa a bayyana tana gyara kwanciyarta nan take bacci ya yi awon gaba da ita.
Ba ita ta farka ba sai uku ta gota, sosai tasha mamakin irin barcin da tayi, nan ta faWa toilet Win Wakinta ta Wauro alwala, ta gabatar da sallar azahar da aka riga aka yi, kafin ta Wora da la'asar da taji an fara kiraye-kirayen a wasu wuraren.
Ta Wan jima a zaune tana tilawar karatunta, kafin daga bisani ta tashi ta nufi madafa dan yin girkin dare, tunda dai na rana kam ya wuce ta.

Farar shinkafa ta dafa sai ?ar karamar sauce ta albasa da kifin gwangwani. Talatu da sanyin jiki, sai gashi Wan aikin nan ya kaita har daf da faWuwar rana.

Bayan ta gama sallar isha'i ta zubo abincin dai-dai wanda tasan zai isheta ta dawo falo, ?arfata Waya kan Waya ta Wora plate din akan cinyarta, Waya hannunta a cikin abincin, yayin da Wayan ke da littafin ?awa'idi, inda take duba dai-dai wurin da ya Wora mata kafin ya tafi, cikin nutsuwa take karatunta, haka kuma ta gama gane ma'anar ba?aken da aka haWe suka zama kalma, wacce ita ta bayyanar da hukunce-hukunce kala daban daban da rabe-raben su dan gane addini, da kuma yinshi yadda ya dace.

***********************

''YallaSai alfarma za kayu mana, dan Allah ku taimaka ku barmu mu wuce, tunda muka iso nan ai sai a barmu mu ?arasa, dan Allah YallaSai, kaga ai dare bai yi sosai ba.'' Baba ne ke ro?ar Waya daga cikin jami'an dake tsare hanya na Darvisanate, in da idan har baki manta ba anan ne su Abdallah suka kwana wancan lokacin dawowarsu daga Matamaye, gashi yanzun ma tarihi yana so ya maimaita kansa, wanda ko kowa ya Wauka Abdallah baya jin zai iya Waukar wannan ibtila'in, eh ibtila'i mana! Tunda yadda yake ji a ransa a yau idan har bai yi tozali da Noor Winsa ba to tabbas da matsala ?atotuwa.

BuWe murfin motarsa ya yi ya fito zuwa ga su Baba, da sallama ya karasa inda suke, ya buWe daki da ''Baba wai ?i suka yi su barmu mu wuce? Grand fr?re a dubemu da idon rahama, amarya muka Wauko ga kuma dattawan iyayenmu, haka ma ni Win nan wallahi ina da abinda yake nan jiran zuwana, Oga idan ban shiga Agadez ba a yau da damuwa wallahi, ya kai ?arshe yana mai kama kunnensa da du?awa ?asa alamar tuba.

Yadda jami'an nan ke dariya haka masu Yusuf dake mota, Ishaq ya ce ''Wan iskan can ya iya siyasa aradu, ka duba yadda ya ajiye matsayi da girmansa ya wani du?a musu! Tab lallai yaro yaso zuwa gida.''

''Baka da dama Ishaq, da alama ?uruciya ke damunka'' ce war Yusuf yana wani shan ?amshi wai shi gashi babba.

Fiddo ido waje Ishaq ya yi baki sake, takaici ya hana shi ce wa Yusuf Win komai, saima maida dubansa da ya yi zuwa ga su Abdallah. A lokacin tuni jami'an nan suka ha?ura, amma dan goman dare bai rufa bane, da babu wani zancen alfarma dole ne su kwana anan komai yawansu kuwa.
Bayan har an buWe musu hanya sai Abdallah ya koma mota, wajan ajiya dake motar ya buWe ya Wauko rafar ?an Wari-Wari,wanda ko shakka bana yi zasu kai jika hamsin na cefa, ya basu yana mai godiya da fahimtarsa da suka yi. Suma godiyar suka yi masa kafin suka koma bakin aikinsu, suma suka yanki hanya sai Agadez.

Hikimar Abdallah na ?in basu kuWi tun farko zai iya zama ya basu cin hanci ne, su kuma suna ?arSa sun zama ?an rashawa, sai ya yi hikimar ro?onsu har suka yarda, bisa faWin kansu bawai dan kuWi sa ba suka buWa musu hanya, wannan kuWi kuwa daya basu ihsani ne Allah ya ?wata musu.

Jikinsa har wani karkarwa yake ganin sun shigo garin Agadez tarau idon Kado a ruwa, sai faman sakin murmushi yake wanda babu wanda yasan ma'anarsa sai shi da ya yi kayansa.

?arfe goma sha biyu da mintuna goma sha uku suka iso ?ofar gidansu Yusuf, anguwar shuru kamar ba mutane, kowa ya shigewarsa gida ya killace kansa da iyalansa, tare da fatan Ubangiji ya ara masa damar wayar gari cikin ?oshin lafiya, dan ci-gaba da shagulgulan gabansa inma na alkhairi ne ku kuma taSewa. Allah ka raya mu cikin aminci, ka amintar damu, ka shirye mu ka shiryi bayar mu, kasa mu dace duniya da ?iyama, kasa muna daga cikin bayinka masu rabo na alkhairi.

Abdallah, malam Misbahu, da sauran direbobin nan guda biyu ne a motar Abdallah, inda aka bar wa?ancan motocin guda biyu fake a ?ofar gidan su Yusuf, kasantuwar da kayan amarya da sauran kayan amarya da aka lodo akansu, wasu ma har cikin boot duk amsa da kaya. Dama duk p abu da aka san zai bada wahalar jigilarsa ba'a tarki siyansa acan ba, kama daga kan gado, kujeru da katifu duk anan Kawu Abdu ya turo aka siya mata, ?an kayan kicthing ne da sauran kayan anfani kawai suka zo dasu.

Sai daya sauke kowannensu a ?ofar gidansa, ya kuma tabbatar ya shiga gida cikin aminci kafin ya kama hanyar gida shi da malam Misbahu.

Ummy tana tsaka da mafarkin mijinta sai ga kiran Abdallah ya tashe ta. A dabirce ta tashi tana salati, dan wallahi batasan lokacin da barcin ya yi awon gaba da ita ba, suna fira da Abby a waya, wanda bai samu ya dawo a yau Win ba kamar yadda yaso, shi ma jin tayi barci ne kawai sai ya katse kiran yana murmushin halin yarinta irin na Ummy, har kullum baya gajiya da duk wani abin da zata zo masa dashi, Gaisha ta daban ce a ce warsa.

''Ummy gamu mun iso''taji muryar Abdallah bayan ta Waga kiran.

''Kai ma sha Allahu! Amma gaskiya tafiyar tayi muku sauri sosai.''

Mi?ewa ta yi bayan jin yankewar kiran da yaron nata ya yi, ''Yarona kenan, mai hali kala daban daban'' ta faWa tana mai buWe ?ofar falonta, wanda ya yi dai-dai da danna odar da Abdallah ya yi a ?ofar gida, ga kuma Baaba Balki da Al?asum da suka fito daga nasu bangaren suna masu zuba ido. Ita Baaba Balki ta zira ido ne taga fuskar mijinta da tayi mata wahalar gani na tsawon shekaru, shi kuma ?asum yana so me yaga bazatar da ta hanawa idanunsa bacci tun bayan da Ummy ta yi masa albishir Win ta.

Ba Sata lokaci mai gadi ya wangale ?ofa bayan daya le?a ta ?aramar ?ofa ya san ko waye.

Cak yaja ya tsaya a bakin ?ofar motar, wasu yake hanga kamar mata da kuma Wansa, lallai yau zai kwana yana gode wa Ubangijin daya hukunta sake saduwarsu, ya kuma hukunta ya samesu cikin aminci.

Bakin Baaba Balki har rawa yake wajen faWin ''Malam'' ta faWa ta rasa in da zata tsunduma ranta ta ji dai-dai.

?asum me ya tako zuwa gare shi, sai da yazo daf dashi kafin ya ja ya tsaya, hawaye fal idanunsa, bakinsa ya kasa buWuwa ya yi magana, sai kawai ya faWa jikin mahaifinsa yana mai sakin kuka mai ban tausayi.

Bubbuga bayansa malam Misbah yake shi ma ya kasa magana, a haka har Ummy ta tako kusa dasu, inda ta dafa kafaWar Abdallah daya jinginar da bayansa a jikin motar, ita Ummy a nata tsammanin ko gajiya ce da tausayin uba da Wan nan suka kamashi dayawa, ya yin da shi kuma yake so yaga ya sallami kowa, ma'ana ya tabbatar da shigar kowa Wakin barcinsa a matsayinsa na wakilin mai gidan tunda baya nan.

''Yarona ya hanya?'' ce war Ummy, kafin ta juya ga Malam Misbahu tana yi masa sannu da zuwa cikin girmamawa.
Cike da kunya ya amsa a ransa yana kuma tabbar da kirki da karanci irin na iyalan gidan nan, gashi dai ko bayan shekaru masu yawa bata canja gmdaga yadda take gaishe shi ba.

Sai a lokacin Baaba Balki ta iso wurin, kanta a ?asa wai ita kunya take ji, ai kuwa sai da Abdallah ya dara cikin barkonci ya ce ''Baabarmu kai a ?asa wai?'' hararar wasa ta wurga masa duk kunya ta isheta.
Cikin nutsuwa ta ce ''sannu da zuwa Malam.''

Ummu ce ta katse su da ce wa ''Baabar yara dare fa ya yi sosai, ku isa daga cikin sai ku gaisaa nutse, kai ma kaje ka huta ko'' ymta kai ?arshe tana kallon Abdallah.

Sallama suka yi musu tare da shigewa sashensu, ?asum ma?ale da mahaifinsa kamar wani yaro, Wakinsa ya shiga dashi dan yin wanda, kafin ya fito ya ajiye masa jallabiya a bakin gado wacce a cikin kayansa ya daukota, da ya ke malam Misbahu baya da jiki irin sosai Win nan,sai rigar tazama masa kamar tasa.
A falo ya samu Baaba Balki da abinci da ruwa ta sa a gaba tana jiran fitowarsa. Cikin farin cikin da ya kasa Soyuwa akan fuskokinsu suke kuma gaisawa da junansu, duk inda ?asum zai yi idan malam Misbahu akansa, wanda daga karshe ya kasa ha?ura sai da ya ce da Baaba Balki ''taya kika iya rainon yarona haka? Gashi ya zama mutun abun mangari, Allah ya biya ki da aljanna.''

Abun nema ya samu, nan fira ta Sarke tsakaninsu, inda Baaba Balki ta fara da bashi labari tun lokacin da aka bemesho aka rasa, har zuwa yanzu da ya dawo gare su. A takaice dai a zaune suka kwana a nan falon.


''Zaka ci abinci ne ko baka jin yunwa?'' Ummy ta tambayi Abdallah.
Ya amsa ta da ''a'a Ummy, bana jin yunwa sai dai bacci, zane in yi wanka in kwanta in huta.''

Shafar kansa ta yi tana mai saka masa albarka kafin ta koma falo, yana tsaye har yaji ta sakawa ?ofar sakata kafin ya nufi Sangaren sa.

Key ya saka ya buWe ?ofar, ya tura ?ofar ya jita a rufe daga ciki. Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana, to yanzu idan ya dace da yarinyar nan tayi nisa a bacci ya zai yi?

A hankali ya shiga bubbuga ?ofar cike da tsoron kar Ummy ko wani a gidan ya ga yana bubbuga ?ofa, bayan kowa ya kwana da sanin shi kaWai ne a sashen,haka kuma bai bar kowa a ciki kafin tafiyarsa ba.

Cikin barci take jin ?aran buga ?odar ?asa-?asa, dama saboda hakan ta kwanta a kujerar falon, tsoro ta ji kar taje ta buWe sakatar ace ?an gidan suna da key Win falon, wani ya ce zai shigo idan aka yi rashin sa'a aka ganta akwai damuwa. Haka kuma idan da ace a Wauki take baccin nan ba lallai ta iya jin yana bugawa.

Mi?ewa tayi tana hamma alamar baccin take ji da gaske, kai kace bata yi baccin rana ba.

Ajiyar zuciya ya sauke jin motsinta a jikin ?ofar, nunfashi haka ya fesar bayan da ta zare sakatar gaba Waya.
Yana shigowa ya sunkuceta ya yi sama da ita yana juyi da ita tun daga mashigar falon.

''Eyeeeee gani na dawo gani na dawo'' haka yake ta faman faWa yana juyi da ita.
?an?ame shi tayi sosai jin kanta ya fara juyawa, wani jiri na Wibarta. A hankali takai bakinta saitin kunnensa ta ce ''ka bari dan Allah, ina jin juwa fa'' ta yi maganar kamar mai raWa, wacce ba ?aramin taSa Abdallah ta yi ba.

A kasalance ya sauke ta ?asa yana mai zama akan kujera, ita ma biyosa tayi ta faWa jikinsa jin har yanzu bata fasa jin jirin ba.

Nan kuwa ta tuna da kukan da tace zata yi masa, ai kam ta fara kamar da wasa, a hankali sautin muryarta yake shiga cikin kunnensa, wanda yake jin kukan kamar da sarewa take yinsa. Matseta ya yi sosai ajikinsa idanunsa rufe, dan wani kalar abu yake ji akanta na daban da sauran kwanakin da suka rayu a tare da ita. A hankali ya ce ''kina so ki tayar min da hankali ko?''
Cikin kukan ta ce ''to wane irin laifi nayi maka daka shareni tun jiya ka?i ka Kura ni, kuma nima koda nace zan kira ka baya ma fita bare har ya isa gareka'' ta faWa tana ?ara yiwa kanta masaukinsu a bisa ?irjinsa, nan take lissafinsa ya fara kwancewa.

Ta kuma ce wa ''shi ne zaka ?yaleni, dama kenan da gangan ne ka?i kirana'' ta turo baki gaba a ?arshe. Wanda ya yi dai dai da buWe idanunsa da ya yi, sai ko suka sauka kan bakin nan daya zamar masa abun so da ?auna.

''I na jin ki'' ya daWi kalamar ina jinki a rarrabe, dan da gaske a lokacin ji yake kamar ba shi ba, kamar ba Abdallah jarumi mai juriya ata wannan fannin, amma yau a fili yake iya gane gazawarsa.

Yarinyar ta ta kasa barinta ta iya hango abinda ke cikin idanunsa, ta yi tamanin Waya ce yana jinta Win nan kawai ya bata dama ta zube masa duka ?orafin ta, in yaso ya duba sai ya gyara na gyara.
Ta kuwa sake buWe ba ki ta ce ''sannan kuma naga hoton Inn...''

Bata gama fadar Innar ba taji ya haWe bakunansu.

Nan ya shiga sanar da ita yada dawo daga tafiyar da ya yi. Ta kuwa shaida sosai dan harjikinta ta amsa.
Sama da mintuna ashirin Abdallah yana abu Waya, kafin da?yar ta isa ?wace bakinta tana kwaSe fuska kamar zata saki kuka, cike da shagwaSa ta ce ''Allah har yaji-yaji take min.''
Tsafka ya kai mata ta goce tana mai nufar Wakinta tana dariya, kafin shima biyo bayanta yana tangaWi yana raba hanya.
Tun a hanya ya fara cire rigarsa, haka ma wandon shaddar tun a ?ofar Wakinsa ya cire, ya faWa toilet hadi da sakarwa kansa ruwa wai ko zaiji dama dama.

Ita ma data shiga Wakinta bandaki ta faWa, har tayi wanka ta ta fito Abdallah yana banWaki bai fito ba
Bisaa umarnin zuciyarta wajen shafa turare ta haWa da wanda Mamar su Rammatu ta bata ranar da zasu taho nan, amma tun ranar data ajiye shi akan gaban madubin nan bata sake waiwayarsa sai ba, sai dai idan zata goge wajan ne takan gusa su gaba Waya da sauran tarkacen.
Sosai ta kama jiki duk ta murje da wannan turare wanda ita kanta jin ?anshinsa take har cikin kwanyarta.
Ta shige cikin wasu kayan bacci riga da wando masu sulSi, irin manyan nan ne wanda ake Waure rikar da igiya ta zagaye mutu, sun kuma karSe ta sosai duk da ba wani tsiraici suke nunawa ba.

Tana shirin barin gaban madubin yaji shigowarsa Wakin, juyawa ta yi tana sakar masa murmushi ta ce ''ko in haWa maka wani abun ne?'', takowa ya yi ya saka ta a jikinsa ya zagaye tare da faWin ''bana jin ci ko shan komai a yanzu Noor, sa'o'i zuwa safe in sha Allahu.'' Yana kaiwa nan ya sunkuceta ya nufi Wakinsa da ita, ya shinfiWeta kamar wata ?ar baby, kafin ya kashe musu wuta kamar koda yaushe, ya hauro gadon yana shirin kwanciya a kusa da ita.

Tunma kafin ya dai-daita kwanciyarsa tayi wa kanta masauki a kan faffaWan ?irjinsa, inda take ?ara cusa kanta wai sai taji ?arshen ?anshin turarensa, ita kuma bata san wani aikin daban take yi ba bawai wanda yake a nata tunanin ba.

Bakinta ya lalubo ya jone da nashi, inda hannunsa kuma kasa tsayuwa a guri Waya kamar da can,yau salon na daban ne, karatun mai tsauri ne, wanda iya gane shi sai wanda aka karanta domin sa.

Tuni ta fara gane ma'anar zancen, yadda taga ya susuce dajin yadda albarkatun ?irjinta suke azahiri, duk tsawon kwanakin nan bai taSa gigin koda Wora hannunsa akai bane sai yau,sai yau da yake tunanin mai kankat zai yi.

Ni dai jin Talatuwa tamu ta fara kuka da babbar murya nace to bari in tattara tarkacen na inyi nan, da tarin tunaninnika fal raina, shin miye Abdallah yake yi wa gaggawa da bazai bar ?ar mutane sai ta girma ba? Sai tunanina ya tsaya cak jin ya fara karanto wata addu'a mai kama data saduwa da iyali. Ruf na rufe musu ?ofar da dama tuni na daWe da ficewa daga dakin.

Na dawo falo ina jiran gawon Shanu.=??

Kar ki yarda ki zauna jiran gawan Shanu tawan, koda zaki samu na banzar ba lallai ki samu akan lokaci ba, mun fara dake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login