Showing 3001 words to 6000 words out of 78880 words

Chapter 2 - YAR KANCE free pages na Maman Abdallah.doc

kenan har iyakar ?asa suke tsallakawa da sunan neman kuWi, to mace tabar garin su tabar jaha da kasar ta taje wata ?asa neman kuWi? Ya tambayi kansa, to wace iriyar sana'a suke yi idan sunje? Tabbas bashi da amsar wannan tambaya.

Zunbur ya mi?e tsaye kamar wanda aka tsikara, Ummy ce ta fara lura dashi dan Abby har yanzu suna waya da Dady wanda ya kirasa daga ?asar Algeriya.


''Yarona lafiya kowa?'' Ta tambaye shi ganin yana shirin barin falon.

Yana tafiya yake ba ta amsa da ce wa ''Ina zuwa Ummy nayi mantuwa a mota nane Wazu''.

Sakin baki tayi tana kallon bayansa lokacin da yake sassarfar barin falon zuwa wajan da yayi parking motar sa.


Har ya dawo falon ba'a gama wayar ba, saidai zuwa wannan lokacin Ummy ke gaisawa da Mammaa suna firarsu ta tsakanin aminai kuma ?an'uwan da suka gama sanin sirrikan junansu, kuma suke bawa junansu gudummawa wajan zama da mazajansu lafiya a matsayin su na ?an'uwa na jini.

Mamma itace babba a gidan su, sai mai biya mata Musa sai kuma Ummy.


Haka suka yi ta fira kafin daga bisani sukayi sallama akan zuwa safe zasu yi magana.

Hammar da Abby ya fara ita taja hankalin Ummy har ta raja'a akan tambayar da zata yiwa Abdallah akan miye damuwarsa, taga tunda ya shigo falon duk kamar a Warare yake, kamar mai sanyin wani abu kuma yana shakkar yi, kallon sa tayi kafin ta ce ''Yarona ka gaji sosai kaje ka kwanta kaji ko, shima mai zaman kallon new Win yau ba lallai ya iya jurar kallon ba, dan da alamu bacci yake ji'' ta karasa maganar tana kallon Abby da koyar idonta da yake kara kashe masa jiki da kara masa kasala.


Ba musu Abdallah ya mi?e daga inda yake, tattaki yayi har inda iyayen nasa suke ya sunbaci goshin kowanensu, cike da soyayya ya ce ''Allah ya bar mini ku Iyaye nagari, ina alfahari daku har kullum, Rabbi ya saka muku da mafificin alkhairi ya rayamu a aljannar firdaussi kamar haka''.

Cike da soyayya suka shiga amsawa, Abby ya Wora hannunsa akanshi yace ''Ubangiji ya albarkaci rayuwar ka yayi maka kamar yadda kake mana'' da ameen Ummy ta amsa kafin ya wuce sashensa.


''Ubangiji na gode maka daka hanani kuma ka bani, tabbas ka jarabceni kuma ka kawo mini mafita a kan lokaci, ko nace tun kafin jarabtar ta riskeni, Allah ka gani ancutar dani, badan ka haWani da makusanta nagari ba da naga ta kaina'' Ummy ta faWa da karyayyiyar murya kamar zata saki kuka.


Cimak taji an sunkuceta gaba Waya! Bai sauketa a ko'inaba sai a Wakin baccin su, a gefen gado ya zaunar da ita yace ''Idan nace zan lallashi ki a falo abun bazai yi kyau ba, gashi inajin bacci sosai, dan Allah uwargidan Muhammad Outhman ayi mini ha?uri, rigimar nan kar ta yi tsayi kinji matar aljannah'' Abby ya faWa yana kallonta da matattun idanunsa da suka kusan rufewa da abubuwa biyu zuwa uku.

Fahimtar manufar sa da tayi yasa ta cinye gundarin maganar data Wauko, ta sauya shaftar da salon da dukkanin su zasu fi ganewa, tabbas suna alfahari da junansu akoda yaushe, basu taSa duba da yawan shekaru ko girma wajan ganin sun faranta ran junansu ba.


?akin Abdallah

Yana shiga ya faWa makeken gadonsa da bismillah a bakinsa! Wayarsa ya fito daga aljihunsa ya shiga galeri inda yake tunanin ganin videon daya Wauka Wazu a filin nan.
Tun lokacin da Abby ya anbaci ?an Kance yake Allah Allah ya kalli videon dan ya ida tabbatar da kamannin su, tunda yaji Yusuf ya kirasu da suna Yan Kance.

Video
''Talatuwa!Talatuwa! zo kigani Allah yabani'', a hankali take takowa kamar batasan taka kasa, kayan jikin nan nata duk datti kamar mara hankali, wannan shine dalilin da yasa a lokacin Abdallah yayi tunanin ko dai mahaukaciya ce.
Kusa da wacce take kiran nata ta isa cikin muryar nutsuwa tace ''Inda nagani Suwaiba miye kika samu?''.

Cira ledar suka yi yan ?ananun tarkace ne a ledar a kulle, yan kunnaye da ribon da sauran kayan anfani na kwalliyar yara, wani ihu Suwaiba tayi tare da faWin saini Suwaiba ?ar gidan Hajiya Asama'u Hajiyar ?an Kance, Allah yayi yauma dawa yayi nama''.

Ri?e baki kawai Talatuwa tayi tana kallon ta kafin ta ce ''ki daina daga murya kina mace! Ita mace dukkanin ta al'aura ce, musamman a irin wannan wajen da muke mai cike haWururrukan rayuwa, ki duba fa ki gani a tsakiyar shara muke kuma kike irin wannan Waga murya haka'' .


?an Sata fuska Suwaiba tayi tace ''daWina dake shegen wa'azin tsiya wallahi, miye na wani yimin gargaWi kawai ni nafison duniya ta gaya mini, Allah na tuna nida nake da uwa kamar Hajiya ta, miye zai gagare ni, zanyi komai ba komai kawai ?an'mata'' ta ?arasa maganar da kashewa Talatuwa ido daya.

Allah ya shirye ki kawai Talatun ta faWa tana shirin yin gaba abinta dan komawa gida, jiya iyau ba wani sauyi, ita batama san yadda zasu kwashe da Innar taba yau Win nan, kafin ta fito sai da ta mata kwakwaran warning akan kar ta dawo mata gida hannu rabbana kamar yadda tasaba.

''Ki tsaya ki karSi kasanki'' taji amon miryar Suwaiba.
Tsayawar kuwa tayi dan ko banza tasami mafitar da take nema akan yadda zasu ?are da Inna.

Raba kayan tayi gida biyu ta ba ta kaso Waya tace ''gashinan kema kikai a saka miki albarka, dan Innar ku akwai iya banbadanci''.
Hararar ta Talatuwa tayi tace ''bana san iskanci Suwaiba, dan zaki bani abu bashi yake nufin kici zarafin babata ba, zamu sami matsala wallahi''.

Hakuri Suwaiba ta bata akan itafa bada wani manufa da fadi hakan ba, tayi mata uzuri dan ba yau suke tare da ita ba tun yarinta, kuma ta santa da rashin iya magana da kuma Sungurumar jahilcin dake cin kanta.
Duuuuuf videon ya tsaya iya nan, kuma a dai-dai nan ne su Abdallah suka neme su suka rasa.


Dafe kansa ya yi cike da bakin cikin karewar da videon tayi a dai-dai lokacin da yake ganiyar san ganin yadda take komai a cikin kamala da kame wa, duk da alamar babu da rashida suka bayyana a tare da yarinyar hakan bai hana ta zama cikin yara masu nutsuwar hankali a zance ba, gashi da alama tasan girman iyaye da girmama su duk lalacin su, duba da yadda ta Sata rai lokacin da Suwaiba ta aibata mahaifiyarta.


Shi a son ransa yaso yaga har gidan da suke rayuwa da yadda zasu kai wayan'nan kayan da kuma yadda iyayensu zasu karSa ba tare da sunsan daga ina ko wa yabasu su ba.


Har karfe ukun dare Abdallah ya kasa bacci, fuskar wannan yarinyar nan kawai take masa gizo, to ya akayi takeda sani bayan da gani da kuma yadda yaji Yusuf da Ummy na magana akan yan Kance Win nan ba lallai su sami nutsuwar neman ilimin addini ba, bama'a maganar boko.


Haka ya kwana ba tare da idonsa ya rintsa ba, dan lokacin da yaga baccin ya kasa zo masa sai ya tashi ya shiga ganawa da Ubangijinsa bai san ya akayi ba sai jin bakinsa yayi da yiwa yarinya adu'ar samun nasarar rayuwa, nema mata kariya daga sharrin shaidan da kuma fitinar zamani.


Sosai fuskar yarinyar take masa gizo lokacin da take nusar da ?ar'uwar tafiyar ta akan ta daina Waga murya tana ?a mace, wani tsadaddan mirmushi ne ya suSuce masa yana shafa gyararriyar sumar kansa, a hankali yace '' malama Talatuwa zanso na kuma ganin irin wannan tunatarwan naki a karo na biyu''.................


Page 3
________Washe gari da misalin goma da rabi na safiya suka nufi wajan Baban Yusuf dake kasuwar dabbobi, Wan kacari ne (irin masu sayar da kayan masarufin nan kamar su Masara, Gero, Alkama da dai sauransu) akan maganar da ya yi wa Yusuf din na ya sama masa matar aure a garin su, wai sunzo su bashi ha?uri tare da neman alfarma ta ?arshe.


Fafur Baba ya?i sauraransu, a cewar sa shima Abdallah Win idan yayi wasa zai haWa hardashi, haka kawai sai mu saka muku ido muna kallon ku, sai kun zama sa'anin mu kafin muyi muku aure komai? Ai da can Matamay Win muke da zama yanzu kamar ka ai kanada yara huWu koma biyar'' ya faWa yana nuna Yusuf Win da yatsa alamar shifa yayi magana kuma ta zauna, daga ?arshe ma rana ya sakawa Yusuf Win akan yaje can Matamay Win kwanaki biyar masu zuwa, dan ya gana da wacce zata kasance matarsa nanda watanni biyu insha Allahu.


Haka suka baro kasuwar duk jiki ba kwari musamman ma Yusuf da yake ji kamar ba'ayi masa adalci ba.

Lura da hakan da Abdallah ya yi ne yasa cikin muryar rarrashi ya ce ''Wan'uwa karfa ka damu da wannan hukunci da Baba ya yanke, abune mai kyau ace munyi aure zuwa yanzu, shekarun mu ashirin da bakwai kenan aduniya, kaga kuwa ya kamata ace mu da kanmu ne muka nemi da amana Aure, wallahi maganar Baba ta yanzu da yayi sai naji nima ina sha'awar nayi aure nan kusa, saidai bansan wace zan Aura ba''.

Ajiyar zuciya Yusuf ya yi kafin ya ce ''naji ban?i ta Baba ba amma kaga fa daga ?auye za'a dauko mini mata, dan Allah miye tasani a rayuwar Aure gaba Waya, ni wallahi da za'a bani damar dana samo anan cikin gari koma dai wani wajan daban, amma gaskiya matar ?auye za'a tauyeni dayawa'' ya faWa kamar zai yi kuka, dan shima shagwaSa batayi masa wuya kamar mace haka yake wani sa'in kamar Abdallah.


Sai yanzu Abdallah ya gane manufar abokin nasa na?in maganar Baba da yake san yi, wai ashe yana tuna yadda zai yi rayuwar love da ?ar ?auye ne, dariya sosai Abdallah yake yana kallon Yusuf, da tarin sha?iyanci ya ce ''wallahi mantawa nayi ban tambayi Baba sunan amarya tamu ba, da kasha kirari yanzu Malan''.

Hararar sa Yusuf ya yi yana ce wa ''zaka kalli gabanka kayi tu?i ko sai kasa munyi accident kana Waukan hankali? Ai dama nasan yanzu baka san farin ciki na ko kaWan'' yayi maganar yana kwafa tare da maida kansa Wayan gefen wai shi yayi fushi.


Tsagaita dariyar Abdallah yayi dai-dai isowar su bakin shagon Winkin Yusuf, wani abokin su Ishaq Laminu suka tarar yana jiran su, bai daWe da zuwa wajanba, da har zai bar musu sa?o sai kuma yace bara ya kiransu jin yaron shagon yace ogansu yace ba wani daWewa zasu yi ba.


Musabiha suka ya tare da tambayar bayan rabo, dan sun Wan dade basu haWuba, abokin su ne ta Sangaren Yusuf dan tare sukayi makaranta tun daga primary har lokacin da shi Yusuf Win ya bar karatun kota-kota, to haka suna haWuwa da Abdallah jefi-jife idan yazo wajan Yusuf din, koshi Yusuf din idan zai ziyarci Ishaq su kan je da Abdallah, saboda haka sai suka zama abokan juna dukkanin su, saidai shakuwar su tsakanin sa da Yusuf tafi yawa.


Katin gayyata ya mika musu cikin jin kunya ya ce ''kuyi ha?uri wallahi abun ne yazo a ?uraren lokaci shi yasa ban zo naka muku da wuri ba''.


Dayake takardar a hannun Abdallah take tuni Yusuf yayi fici-fici da ido zabar jaraba tana cinsa ya ce ''ai dai ba zakace aure za kayi ba shi ne ka kawo mana kafin gayyata ko? Wallahi hakan ta kasance ko kofar nan ba zani da sunan wai zani bikin auren kaba'' ya faWa tare da zuwa bakin ?ofar shagon nasa da kuma dawawwa ciki ya tsaya a gaban Ishaq yana jiran amsar da zai basa ya Wora daga inda ya tsaya a masifa.


Shataaa da baki Ishak ya yi yana kallon Yusuf da mamakin miye ya sameshi yau ya fiya jaraba haka oho, ''kai dan Allah! kace Umar ma aure zai yi muna nan zaune?'' Abdallah ya faWa da babbar murya lokacin da yake karanta katin gayyatar auran Umar ?anin Ishaq wanda yake bi masa daga Ishaq sai shi.


Sai a lokacin Yusuf ya saki Wan ?aramin nunfashi alamar ya sauka kaWan daga jarabar daya tanadar ya yi wa abokin nasa dazaran ya tabbata katin aurenshi ne.

Dariya Ishaq yayi kafin yace ''wallahi abun ne ya zo a bazata, kawai mahaifin yarinyar da suke soyayya da shi ne ya sami sauyin wajan aiki daga nan garin, to kuma inda aka maida san kamar lalacewar rayuwa tafi yawa a can, to da yake ita ce babba a gidan kuma duk ?annanta maza ne yasa ya yanke hukunci aurar da ita kafin ya bar gari, shine yarinyar ta tsayar da Umar Win a matsayin zaSinta.
Sai da aka kai ruwa rana kafin iyayenmu suka yarda da maganar auren nan, wai ina yayansa banyi aureba shi ba zai fara ba kawai yabar maganar.
Sai da naje har ofishin Abby na sameshi da maganar akan yaje yasami su Baffah suyi magana, cikin ikon Allah kuwa ya shawo kan su suka yarda, ai nayi tunanin kaji zancen a wajan Abby kafin nazo na sanar daku'' ya karasa maganar yana kallon Abdallah daya zauna akan kujerar da mamallakin shagon kaWai yake hawa lokacin aiki.

Doka ne ba wani yaran shagon da yake anfani da kujera, ma'aini, almakashi da duk wani abun anfani wajan dinki matukar na Oga Yusuf ne.


Kallon sa Abdallah yayi ya ce ''wai kana nufin Abby yazo gida da zancen ofishi komai, ai koda yake ofishin kasuwanci ne baya maganar sa a gida wallahi, maganar gida daban, kuma ta ofishi daban, kai koma a gida ka sameshi ku kayi magana matu?ar bai shafi mutun ba to ba lallai wani ya jita daga bakin Abby ba har abada wannan Wabi'ar sace'' ya faWa yana mai tabbatar wa.


Sunfi mintuna talatin suna fira a tsakanin su, nan Abdallah yake faWawa Ishaq maganar auren Yusuf da Baba ya fara hidima tun yanzu, ''ai kuwa dai kaga daga an gama bikin Umar ranar talata kaga alhamis sai mu wuce kawai, dan har dani za'aje'' cewar Ishaq cike da jin daWin abokin nasu zai shiga jerin manyan mutane kafin suma Allah yayi nasu lokacin .


Haka suka ajiye zance akan ana gama bikin Umar zasu Wunguma zuwa Matamai su duka uku dan ganawar da Yusuf zai yi da matar dazai aura, kafin daga bisani Ishaq yayi musu sallama akan sai ya gansu ya wuce.


Bai jima da fita ba shima Abdallah ya mike ya ce ya tafi yau duka yayi missing Ummy da Abbyn shi na kusan awannin biyar, dan tun takwas bata rufaba ya baro gidan bayan sun karya da daddaWan abincin Ummy da take kashe su da dadin sa, ta kuma rayasu da ?orewarta.


Har ya kusan isa ?ofar gidansu sai kuma ya juya akalan Motarsa zuwa wannan filin, filin daya kyankyamesa daga farko sai gashi ya sami umarni daga zuciyarsa akan ya koma ba tare da kowa ya aike shi.

Haka kawai yaji bari yazo wajan ko zai kuma ganin Malama Talatuwa mai sanyin hali na magana, bai san miye ya shiga kansa game da yarinyar ba, saidai kawai yanaso ya kuma ganinta azahiri ba'a videon da Wazu da safe ma saida ya kuma kalla kafin yabaro gida.


Yanzu ma da yake hanyarsa ta komawa gida saida ya kalla, wannan shine dalilinsa na zartowa nan kai tsaye wai ko Allah zai sa ya ganta.


Yafi minti goma a tsaye yana ta hange-hange amma sam ba wanda ya gani, sai wasu Awakai guda biyu suna bin shawara ko Allah zai sa su sami rabansu. komawa yayi cikin motarsa ransa duk babu daWi, yana tafiya yana dube-dube kamar wanda ya ajiye ta abakin hanya take jiran isowar sa ya rasa wajan da take a tsayan.


Daidai da wata kwana yaga taron jama'a alamar ana sabga, rumfar maza a gefe guda samari sai shewa suke ana shan shayi, wasu kuma suna shan shisha, wasun su taba sigari ce a hannunsu suna zu?a a bainar nasi.


Da yawan matan wajan bikin duka a wajen gidan suke a zazzaune ana ta shewa da guWa, fira suke suna maida yadda akayi.

Wannan wata Wabi'a ce data zowa matan hausawa ayau na zaman tsakiyar titi da zaran an tafi gidan biki, wata haka za kaga kamar tallen kanta ta keyi a zaune, zata yi wawan zaman da bai dace ba gashi dama ba suturar arziki ake sakawa ba, haka rayuwa ta zama sai dua'i matan aure kamar zawarawa, zawarawan ma marasa kamun kai da san??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????in muhimmancin ri?e tarbiyyar iyaye tun irin ta yarinta.

Dan an miki Aure bashi yake nufin ki watsar da duk wani kamun kan da aka sanki dashi a baya ba, kuma baya sa kiji ce wa wai kin wuce a saka miki ido wajan cigaba da kula da tarbiyyarki ba a'a.
Iyayye mu gane mu hankalta, yaran mu mata sun raina mazajan aurensu, to mu mai zai hana mu ci-gaba da Worasu kan hanya koda bayan mun aurar dasu? Komai girman da ?arki za tayi kece dai wacce kika haife ta, da sau Waya ?arki za tayi lalaci a gidan Aure kuma kiji labari ko ki gani da idanunki kina da dama! Eh na ce kina da damar da zaki je har gidan Auren ta kiyi mata faWa, idan ya kama ki zane ta wallahi ki nemi mabugi na kirki ki zane ta da shi, za ta daWe tana tunawa da kuma kiyaye makamancin irin wancan laifin da ta aikata, kuma kinga kin koya mata darasi akan nata yaran, tun suna yara zata nusar dasu cewa zata iya taka wuyan mutun a cikin su duk wanda ya kuskura yayi ba dai-dai ba, Allah yasa mu gyara ameen.


Har zai fice sai kuma yaja burki ya tsaya dai-dai da fitowar ta daga gidan bikin da kwanon abinci a hannun ta, hijabin jikinta kalar ruwan sama, saidai duk yaga ta kansa, yau ba laifi jikinta babu dauWa sosai ba kamar ranar ba, tunda yau har ya iya gane kalar hijabin ta, sabanin waccan lokacin da bazai iya tantace kalar kayan dake jikin taba.
Kasancewar tana cikin tunanin sa yasa ya gane ta ta gilashin motar sa.


Bai fito daga motar ba sai dai ya ?ureta da ido gudun kar ta Sacewa ganinsa, magana suke da wata yarinyar wacce ba ta ranar bace, dai-dai da kiran wayarsa da Ummy tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login