Showing 42001 words to 45000 words out of 78880 words

Chapter 15 - YAR KANCE free pages na Maman Abdallah.doc

''kamar ana kiranka ko?'' maganarta ta dawo dashi daga duniyar gajeran tunanin da ya shiga.


Dubawa ya yi sai yaga Yusuf ne, Wagawa ya yi yana mai kara wayar a kunnensa, da sallama Yusuf Win ya fara kafin ya ce ''to ya gajiyar hanya ne? Nasan yau dai su Ummy sun sha raki, tunda na sanka da Wankaran san jikin tsiya'', ya faWa ta sashen da yake.

''Kai ni wallahi tun dawowarmu ban samu hutun awa Waya ba duk yinin yau Win nan kaji in faWa maka, ina isowa gida wani abun ya Sollo kai, gashi Dady ya shigo gari kaga kuwa ba hutu'', faWin Abdallah yana magana yana karkaWa ?afarsa da ya Wora Waya bisa Waya.

Da wannan damar ta yi anfani wajen kare masa kallo, kyakkyawa fari sol mai matsakaicin tsawo da kuma madai-daicin faWin jiki, doguwar fuskarsa wacce take cike ga kuma ?yayataccen gemu da kewayeyyen sajen da ya ?ara ?awata fuskarsa dashi, yana da madai-daitan idanun da ba za'a kira su manya ba, ba kuma za'a ce yana da kananun idanuba, hanci ne dai kam kamar an tsaga kara an Wora, ma sha Allah idan aka zo maganar baki kuma shiru ake yi, dan har kullum ce wa za ka yi janbaki yake sakawa, laSSansa na sama dana ?asa duka kalar roze ne, abun sai dai ace fatabarakallahu ahsanul khali?een.


Waye Abdallah abdul-?adir Ousman?...........

Do Allah ku faWa mini waye Abdallah? Kuma suwaye iyayensa Dady, da kuma Abby?>?)?


*?AR KANCE*

Na
Maman Abdallah

_*?ar gatan (D.A.W.A)*_



_Bismillahir rahamanir rahim

Page 14

=?? Tuna baya

__________ Colonel Ousman Abdul-?adir Ousman shi ne asalin sunan kakansa wanda ya haifi babansa.
Tsayayye, gwarzo kuma za?wa?wuri sojan da yake da matsayin Colonel a zamanin mulkin mallakar turawan ?asar Faransa, su Colonel Ousman sun taka rawar gani sosai wajan ganin ?asar mu ta zama tamun da gasken gaske ba wai inkiyar tamu bace, kyaukyawan Balarabe da mahaifinsa abdul-?adir ya kasance Balarabe ne daga ?asar Algeriya, sai kuma Allah ya hukunta aurensa da wata tsaleliyar budurwar da har tsayin zamanin zamansu an kasa tamtance wai shin shi ne ya yi dacen samun mace tagari ga kyau ilimi nasaba ga kuma kuWi ko kuma ita ne ta yi sa'ar samun mijin kecewa tsara da nunawa sa'a, cikin ikon Allah zama ya zaune su a Agadez har ya zamana da yawan zamansa anan ne.

Shekararsu shida da aure kafin Allah ya nufa aka samu cikin Ousman, wanda Allah ya ?wata masa sunan kakansa wato Ousman kenan. Gaba shi basu kuma samun wani haihuwar ba.

Cike da tarbiyya fata da kuma tsayawa akan buri suka raini Ousman da ri?e??en burinsa nasan zama soja tun a shekarun yarintarsa.

Bayan kammala karatunsa ne kuma aka tantanceshi, in da ya fara aikin bautawa ?asar, duk da a lokacin dole ne bin duk wani umarnin turawan mulkin mallakar nan hakan bai hana shi jajircewa ba wajan ganin ya inganta rayuwar al'ummar dake a kewaye dashi.

A takaice dai Colonel Ousman shi ne farkon sojan Waya fara bijirewa turawan nan, wanda cikin ikon Allah bayan gwagwarmaya da fafutuka har muka sami yancin kan mu a shekarar alif dari tara da sittin dai-dai uku ga watan Ogusta.


Shekara biyar bayan samuwar ?ancin kai kuma mulkin demokradiyya ta kankama a lokacin ne aka yiwa Ousman aure da wata yarinyar da ta kasance ?ar danginsu ce Sangaren mahaifiyarsa, ba tare da ya ja da maganar ba kawai aka sha biki, in da suke zaune anan Agadez, sai dai idan ya Wan samu sarari sukan kai ziyara kasar Algeriya tare da iyayensa.

A wata ziyarar da suka je kawai sai iyayen nasa suka ce su su koma, su kam sai sun Wan ?ara hutawa, badan Colonel yaso ba haka ya baro Algeriya cike da faWuwar gaban daya kasa sanin ko na minene.

Ajali idan ya kira dole sai an tafi, babu babba kuma babu yaro, mutuwa ba ruwanta da mai kuWi ko talaka, Sarki ko talakan gari, Wan gari ko bafatake, mai hankali ko mara shi, na kwance a gadan asibiti ko mai zaman jinyarsa, mutuwa bata duba kusanci ko cancanta, sannan kuma bata duba soyayya ko ?an'uwantaka, aduk sanda ta shirya take zuwa dan bata sanarwa, bagtatan ba shiri kake ganinta ba kuma zancen a dakata in shirya babu.
Jama'a muji tsoron Allah, a kullum muna tuna ce wa zamu mutu nan kusa ba wai a nesa ba, muna tuna zafi da raWaWin mutuwa da kuma matsatsi da ?uncin dake cikin ?abari, ko kai waye ba mai ?ara maka faWin ?abari sama da yadda ake ginawa kowa, babu wanda soyayyashi gareka yakai ya ce ba zai iya barin ka/ki zauna kai/ke kaWai a ma?abarta ba bari ya zauna ya taya ka/ki zama babu shi, babu wanda zai iya kuSutar da kai/ke face ayyukan ka/ki na alkhairi irin su: Sallah; Azumi; Zakka; Hajji; imani da Allah; da kuma tsayawa akan sunnar ma'aikinsa; biyayya ga iyaye; biyayya ga miji; zumunta, ri?on ana dadai sauran su.
Allah yasa mu dace duniya da ?iyama, ya kuma arzutamu da maWaukakin arziki na rabuwa da duniya lafiya da kuma cikawa da imani, kalmarmu ta ?arshe ta kasance (Laa Ilaha Illallahu, Muhammadur Rasulullah) s.a.w.


Bayan samun labarin rasuwar iyayensa ansha fama sosai kafin ya dawo dai-dai, duk da sunyi mutuwar fuji'a ne, an kwanta dasu lafiya ?alau amma gari na wayewa sai gwawwakinsu aka tarda, kuma duk wani binciken da za'ayi an yi shi, amma babu wani abu da sakamako ya nuna face lafiya ?alau kawai ajali ne ya riskesu.


*******************

Duba ba tsawon shekarun da aka yi kafin samuwar cikin Ousman,?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? da kuma tsawon shekarun da Fatuma ta Wauka ba tare da tayi koda Satan wata bane yasa aka gano ce wa, irin zuri'arsu Ousman sunada dogon baya ne irin wannan da sukan jima basu samu haihuwa ba, duk da kuwa lafiyar su lau kuma za su iya samun haihuwar a kowane irin lokaci.


Shekaru goma cirr da samuwar ?ancin kan ?asar Nijar, a kuma dai-dai lokacin da ake tsaka da bikin nuna murnar shekaru sun kai daga Waya zuwa goma na samuwar ?ancin kan Fatuma ta yanki jiki ta faWi, a dubawar farko da likitan ya yi ya gano tana Wauke da Wan ?aramin cikin da bai gaza rufe makommi uku ba.

Kuzo kuga murna a gun Ousman da sauran dangi kamar an ce masu haihuwar ce aka yi masu bawai bayyanar ciki ba.


Watannin tara na rainon ciki a karshe su suka bada kyaukyawan fari kuma zankaWeWan yaron da ya ci sunan kakansa wato Abdul-?adir, a ?alla an Wauki shekara biyar kafin suka sake samun wata haihuwar, a wannan karon ma Wa namiji suka samu, in da ranar suna yaro ya ci sunan Muhammad.


FaWar irin gatan da Abdul-?adir da Muhammad suka samu a gurin iyayensu Sata lokaci ne, sai dai inda aka yi sa'a gata da kuWi basu hana an basu tarbiyyar daya dace ba, an gina su bisa soyayya da kuma ?aunar sashen su, akan Muhammad babu abinda Abdul-?adir ba zai iya ba.

Sun samu ilimi fiye da tunanin mai tunani, in da suka yi duka karatunsu a ?asashen duniya mabanbanta.

Shi Abdul-?adir a ?asar Belgeque ya yi karatunsa, a babban birnin su Bruxelle, acan yayi karatunsa na kimiyya tun bayan da ya gama secondary school Win shi, in da shi kuma Muhammad yake karatun likitanci a ?asar Burundi, a babban birnin ?asar Bujumbura, shi nan a Lahiya Afirika ya yi karatunsa, saSanin Yayansa da aka tsillashi Lahiyar Europe.


Shekara huWu ya Wauka tsakanin dawowar Abdul-?adir gida kafin Muhammad ya dawo.
Kuma a wannan lokacin mahaifinsu ya yi ritaya daga aikin soja, bayan samun nasarori da kyaututtukan ban girma daga ?asa da makwabtanta.

Bisa wani ibtila'in da ?asar Algeriya tasa ran shiga na yiyuwar kawo farmaki daga wata ?asar da suke takun sa?a da ita, a lokacin hankalin ?asar da manyan cikinta da suka gama sanin haWarin abokiyar gwabzawar tasu ya tashi ainun, ido rufe suka fara neman mafita, bincike da kuma za?ulo masana da masu ilimin kimiyya domin shiri, koda basu kai farmaki ba to su samu garkuwar kare kai wannan shi ne babban burinsu.


Ana cikin hakan ne kuma suka haWu da bayanan Abdul-?adir Ousman bayan sunyi kutse a na'urorin ?asashen da suka samu damar yin hakan.

Basu yi ?asa a gwuiwa ba suka yi dirar mikiya zuwa ?asarmu, in da kai tsaye suka kai bu?atarsa zuwa ga babbar fada, wacce daga ita babu sama da ita a duka Niamey dama Nijar baki Waya.


Yadda manyan ?asa jagorori da kuma shuwagabanni suke zarya a ?ofar gidan Colonel Ousman Abdul-?adir yasa ya aminta da zuwan Wan nasa Algeriya dan basu tallafi daga abinda Allah ya hore masa na fikira. Sai dai a lokacin lamani kawai ya basu, in da ya ce yaron zai biyo su daga baya.


Tun daga wannan lokacin aka zuba jami'ai dan tsaron lafiyarsa, dan irinsu ba'a wasa da duk wani motsi nasu, rashin sa'a Waya za'ayi a samu mai ?aramar zuciya da irin wannan baiwa tasu, tsaf zai iya tashin ?asa a Wan ?an?abin lokaci idan yaso.


*******************

Ba tare da neman yarda ko shawarsu ba, haka Colonel Ousman ya zaSarwa yaransa matayen aure a cikin dangin mahaifiyarsa.

Aka kuwa yi sa'a ?an gida Waya ne, kuma uwa Waya haka ma Baba Waya, bi ma'ana yaya da kuma ?anwa.


Mussa Maigas
Shi ne asalin sunan maifinsu, mahaifiyarsu kuma Jamila ne sunanta, su uku ne a wajen iyayensu, ?arsu ta farko ita ce Fatuma wacce ita ce aka bawa Abdul-?adir, sai kuma sunan ya yi dai-dai da sunan mahaifiyarsa, sai yaronsu na biyu wanda mahaifinsu ya maidawa yaron sunan sa wato Mussa, shi yanzun yana ?asar Amurika da iyalansa, daga zuwa karatu yana gamawa suka rikeshi suka bashi aiki mai tsokar gaske acan, ko aure ma zuwa kawai ya yi aka yi masa kamar yadda ake yi wa kowa a dangin, ana gamawa ya yi tafiyarsa da matarsa, in da yanzun sunada yara huWu kenan. Yarinyarsu ta uku ita ce Gaisha a yarensu kenan, a namu kuma yaren na hausa sak muce Aisha, wacce ita ce aka bawa Wan Autan Colonel wato Muhammad.


Biki aka yi na azo a gani, wanda aka haWa harda bikin buWewa Muhammad asibitin da aka gama tsantsara ginin da babu kamarta a Agadez rankatakaf na haWe.


Bayan gama biki Angwaye da Amare sun tare a ?erarrun makwatan gidajensu wanda mahaifinsu ya gina musu shi, yaya da ?anwa, da kuma yaya da ?anwa.

Bayan shan amarci na tsawon wata Waya Abdul-?adir ya fara tattare komatsansa zuwa ?asar Algeriya dan cika al?awarin Waya Wauka.



Kamar kar su rabu haka suka ji tsakanin ?an'uwa biyu-boyun nan, Abdul-?adir da Muhammad, da kuma Fatuma da Gaisha.


Bayan ganin jikansu na farko daga tsatsun babban Wansu a shekara uku da aurar dasu da suka ya shirya wata tafiya wakansa, in da zai je Saudi Arabia ya yi duka watan Ramadan a can, daga nan zai wuce ?asar Holand wani taron ?ara wa juna sani, game da yadda za'a bawa ?asa tsaro da dabarun da ba sai jami'ai ne kaWai za su iya yin hakan ba.

Allah sarki rayuwa da batada tabbas, yadai samu ya yi umara na tsawon wata guda, a hanyarsa ta zuwa wannan taron jirginsu ya yi haWari, inda sai kawai labarin haWari ne ya riski iyalansa.

A lokacin an haifi Abdallah yanada watanni biyu a duniya, dan ko komawa Algeriya uwar da yaronta basu yi ba daga wankan jegon da aka kawo su gida suyi a washe garin bikin sunan daya gabata, sai bayan zaman makokin daya gudana ne kafin suka koma tare da maigidanta.


Wata irin kulawa suke bawa mahaifiyarsu da ta kasa samun nutsuwa tun bayan sa?on rasuwar mijinta uban yaranta daya risketa, Mami suke kiranta da suna, haka Abdul-?adir yake sintiri tsakanin Alger da kuma Agadez, lokacin daya ga kamar ba zai samu nutsuwa ba matu?ar bata kusa dashi duba da yanayin da take ciki na shuru-shuru, kawai sai ya yanke hukuncin tafiya da ita kusa da shi, anan ne kuma Muhammad ya ce bai san wani abu wai shi zama a Agadez ba, tunda ya kasance yayansa da kuma mahaifiyarsa basa gari ba zai zauna ba, ganin da gaske yake bisa furucin da ya yi sai yayan nasa ya canja shawarar dawowo da duka iyalansa, in yaso shi sai yake can a zaune, nan kuma ga Muhammad da mai Wakinsa Gaisha, ga kuma Matarsa Fatuma da kuma Wan jinjirin yaronsu Abdallah.

Sai ya kasance ahalin guda sun kuma haWewa wuri Waya, inda suke kula da mahaifiyarsu.

Shekara biyu da rasuwar Colonel Ousman ita ma Mami Allah ya karSi abunsa, yadda fatuma da Gaisha suka Wimauta da rasuwar surukar tasu kai kace ita ce ta haife su bawai mazajensu ta haifa ba.

Kuma har zuwa wannan lokacin Gaisha bata samu rabon haihuwa ba, kuma babu wanda ya damu a cikinsu, tunda dama sun san tsatsonsu.


Bayan addu'ar arba'in Abdul-?adir ya tashi komawa Algeriya, anan ne kuma Gaisha ta nemi alfarma a wajan ?ar'uwarta data bar mata Abdallah a agurinta, tunda dama an daWe da yaye yaron tun yana da watanni goma sha biyar, kasancewar yana yawonsa ko'ina cikin kuzarinsa yasa Fatuma daya fara buWe baki da kiranta da sunan Mamma ta yaye shi.

Ba wani Sata lokaci jirgin su Injiniya Abdul-?adir da matarsa ya Waga zuwa babban birnin ?asar Algeriya wato Alger, in da aka bar Abdallah wajan ?anin mahaifinsa Muhammad, bisa neman alfarmar ?anwar mahaifiyarsa.


Abby da kuma Ummy wannan suna ne da yaronsu mafi soyuwa agaresu ya yi musu, yaron da suke ji da ?aunarsa fiye ma da asalin iyayensa, Ummy batada wani lokacin da ya wuce na miji da kuma yaronta, dai-dai gwargwadon tarbiyya ta yaro nagari tana ?o?arin bawa Abdallah ita.

A Sangaren zumunci a tsakankanin ?an'uwa guda huWun nan abun sai san barka, ko yaya suka wuni da tarin ayyuka basa yarda su kwana ba tare da sunji muryoyin junansu ba, inda suka wajabta wa kansu kiran junansu aduk bayan sallar magariba, in ma dai shi Dady ne zai kira, ko kuma shi Abby ya kira, wani sa'in a wayoyin matayensu ake saWa zumuntar.


Wata ranar Laraba Abby ya fice a gidan tun da asubahi, dan yana kwance a gadon kwanciyarsa aka doko masa kira daga asibiti, inda ake faWa masa akwai wasu mutane biyu da aka kawo ba jimawa, a matse suke sosai gashi sauran Likitocin da suke nan sun kasa shayo kan matsalar, sun dai basu agajin gaggawa kafin idowarsa. Babu wani Sata lokaci ya fice zuwa asibitin.


Yana bada baya Ummy ita ma ta fara mur?ususun a ?asan Waki, wani matsanancin ciwon ciki ne ya rufe ta ba sassauci, dawowar Abdallah daga masallacin sallar asuba kenan, sai ya zauna a falo yana mai duba littafin addani na husnul-muslim a hannunsa, a lokacin yana da shekara koma sha Waya, kuma a wannan shekarar ya zana jarabawar ?arshe a matakin farko na karatu wato primary, in da ana gama hutun ?arshen shekara zasu shiga secondary.

Anan yake zaune a falon har kusan bakwai na safe, ganin har wannan lokacin bai ga fitowar Abby ko Ummy'nsa ba, sai ya mi?e ya faWa kicthing, kamar yadda yake a mafiya yawon lokuta yakan taya Ummy haWa abun karin kumallo, in da suke dafa koma miye suka yi niyyar dafawa cikin sauri, shau?i da kuma fira mai ma'ana ta tsakanin uwa da yaronta.


Dankalin turawa ya soya musu da kwai, sai kuma kunun fulawa da ya haWa wanda yasha ?wa?wa da kuma cukiu ga madara, ba lallai ya iya ganewa Abby baya gida ba, amma ya yi mamakin rashin fitowar su su duka biyun har yanzu da takwas na safe ya haura da mintinan uku.

Wani tunani ne ya faWo masa arai lokacin daya gama jere kayan Waya haWa a ?asan carpet Win dake falon, bayan ya shinfiWa wani lallausan carpet Win daya kasance shi ne ake shinfiWawa ya yin da za'ayi zaman cin abinci. ''Ya aka yi bai ga Abby a masallaci ba?'' ya faWa a bayyane, tuna ce wa koda ya riga iyayen nasa tashi kuma ya tafi masallaci, sukan haWe a can ne da Abby, a wani sa'in harma Abby'n ya yi masa ?orafin ya tafi ya bar shi.

Da hanzari ya tashi ya nufi Wakin barcinsu, in da ya fara buga ?ofar da tunanin ko barci ne ya Waukesu dayawa.

Jin shiru ba'a amsa masa ba yasa ya murWa mari?in dake shi ne mabuWin shigar Wakin, da wani mahaukacin gudu ya ?arasa in da ya hango Ummy a yashe a ?asa babu nunfashi a tattare da ita, ga Wayan hannunta daya ke a saman cikinta irin ta dafe shi Win nan.


Tashin hankali, kiWima, gigicewa babu wanda Abdallah bai yi ba ganin ya yi ta girgiza Ummy amma kamar matatta ta?i ko motsi, da wani gudun yabar Wakin kamar yadda ya shigo, in da ya nufi sashen masu aiki ta ?ofar dake tsakaninsu da kicthing, a wancan lokacin ma ?an aiki guda biyu ne, Baba Balaraba da kuma ?arta Lamunde, cikin tashin hankali yake yiwa Baba Balaraba bayanin halin da Ummy'n take ciki, babu Sata lokaci kuwa ta biyo shi suka tafi har Wakin da Ummy'n take a yashe, hankali da tunani na babba da yaro ya bambanta, baba Balaraba ita tayi tunanin a yi kiran Abby a faWa masa, ba musu kuwa Abdallah ya Wauko wayar Ummy hannunsa na karkarwa ya tura kiran.

Hankalin Abby ya yi mugun tashi jin abinda Abdallah yake faWa masa cikin kuka, ba tare da ya iya ce wa komai ba ya katse kiran, dan a lokacin idan ya ce zai yi magana yaron zai iya gane shi ma ya karaya tunma kafin yasan miye ya sami Matar tasa.

Cikin mintinan goma sai gashi ya faka matarsa a ?ofar gida, dan a ganin shi ya shiga da ita ciki kamar ya kuma Sata lokaci ne.


Ya samu nutsuwar zuciya ?warai daya fuskanci suma tayi bawai mutuwa ba kamar yadda yaji tsoron kasantuwar hakan a hanyarsa ta zuwa gida daga asibiti, in da Allah ne kawai ya kare shi har ya iso gidan lafiya.


Ba tare da ya yi la'akari da wasu masu aiki, direba ko maigadi ba, haka ya fallafo matarsa kwance a ?irjinsa har zuwa ?ofar gida, Abdallah ya yun?ura da nufin ya bisu Baba Balaraba ta girgiza masa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login