Showing 1 words to 3000 words out of 86085 words

Chapter 1 - FEERYAL Part 3 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt

Da sauri Aunty ta waro ido ta ce
"An d'aura fa kace Daddy!."
"Kwarai kuwa an d'aura yanzu, cikin yardar Allah Fad'imatu,
Bappa Salihu ne ya ce a d'aura yanzu dan wani jinkirin ba alhaki bane, musamman a gab'ar da ake yanzu."
jiki a sanyaye Aunty ta ce
"Daddy ni dai ina fargabar abin da zaije ya dawo."
Daddy ya katseta
"Kiyi fatan alkhairi Allah zai wuce gaba,
yanzu abin da nake so dake je ki kira min Feeryal d'in."
Aunty ta mike jiki ba kwari ta nufi d'akin Feeryal ta tarar da ita tana bacci, ta dawo ta sanar masa ya ce a barta sai ta tashi.

Kaf matasan gidan suka fito daga masallacin, dake kofar gidan jiki a sanyaye.
dan lamarin d'aurin auren ya zo wa kowa a matukar bazata, shi kansa Daddy bai san a take Bappa Salihu zai ce a d'aura ba.
Zaraddin ne yabiyo Dad d'insa da sauri kamar wani zararre yana cewa
"Yanzu kana ji kayi shiru aka d'aura auren yarinyar da nake so, na rantse bazan yadda ba,
wannan munafurci ne kawai ai an sanni ni nake son ta saboda shi yana da kud'i shine za'a bashi ita, to wlh bazan yadda ba sai an juya aurennan yadawo kaina."
Dad ya harareshi ya ce "Shashashan banza matsa kabani guri, wanda baisan abin da yake yi ba, anata kokari a kanku bakwa gani,
ina ruwanka idan an bashi ita,
kar ka sake naji wani magana ka yadda ka b'ata min shiri kagani,
shashasha kawai."
Zaraddin ya tsaya daga hanya, Dad ya shige sashin sa bai fasa surutu ba.
Mom ta ce
"Kai da waye kuma kake fad'a?."
ya ce "Ni da wancan shashashan d'an naki mana, wai dan an d'aura wa Abdulrahim aure da wancan yarinyar da suka so kashe kansu a kanta, shine yake hauka wai sai an maida auren ya dawo kansa,
jimin shashanci fa auren da babu wanda yasani kamar auren munafurci ana idar da salla Bappa Salihu ya miko goro da minti ya ce a d'aura yanzu."
Mom ta rike baki ta ce
"Feeryal d'in aka d'aurawa Abdulrahim aure da ita?."
sai kuma ta shiga tafa hannu tana fad'in
"Tabd'i jam lallai akwai babbar matsala,
yanzu shi Yaya Abubakar d'in har ya lamunce ya d'aurawa d'ansa aure da 'yar da ba'asan asalinta bama,
'yar da aka tsinta cikin ruwa, yarinya mara daraja ya yadda ya amince ya had'ata aure da mutum kamar Abdulrahim,
ai ko shi Zaraddin d'in da akewa kallon mai rawar kai bazan yadda na lamunce a had'a shi aure da ita ba,
kuma Hajiya Halima tana gidan ta zuba ido akayi wannan aure."
"Can musu suje can su karata, ni yanzu hidimar dana sa agabana kad'ai nake kwarara."
Mom ta zauna tana ta jinjina lamarin...

Can bakin masallaci kuwa.
Ajmal yayi kokarin dai-dai nutsuwarsa,
yana ta kokarin yaki da zuciyar sa.
ya iso in da Abdulrahim ke sunkuye gaban Bappa Salihu da ke zaune kan dakalin masallaci,
yana masa magana kasa-kasa.
murmushi Ajmal ya yi yana fad'in
"Congratulations bro."
Faisal da Shamsuddin ma suka karaso gurin suna fad'in
"Muna tayaka murna Ya Abdulrahim."
bai yi magana ba sai fuska daya dad'a murtukewa.
Bappa Salihu ya ce "Shiga ciki Abdulrahim Allah dai yamaka albarka yasa 'ya'yanka suyi maka biyayya fiye da yadda kakeyiwa iyayen ka."
ya mike ya nad'e hannunsa a kirji ya soma takawa zuwa ciki.

Daga masallaci in da aka gama d'aurin auren, Bappa Salihu ya tafi sashin Hajiya.
ya kai mata goro da minti yakuma shaida mata an d'aura auren Abdulrahim da Feeryal, shi yabada umurnin a d'aura nan take bayan an idar da sallar asuba.
Hajiya dake kan kujera ta zamo kasa tayi zaman dirshem, ta kwalalo ido tare da buga kirji ta ce
"Auren ka d'aura masa da yarinyar da rabin ta mutum rabin ta aljana, kasan waye wannan yarinyar kuwa,
to wlh ni dai ban amince ba,
ta in da aka hau tanan za'a sauka yadda kuka d'aura haka zaku kunce, dan kunyi aikin banza ne,
dan billahillazi, abokin turawa bazai zauna da yarinyar nan ba."
Bappa Salihu ya mike yana fad'in
"Idan ke baki aminta ba ni da 'yan'uwa na Jibir da Ali duk mun amince,
kuma mun yanke hukunci akan d'anmu Abubakar da jikan mu Abdulrahim, dan baki fimu karfi da iko a kansu ba."
Bappa Salihu ya juya ya fita.
Hajiya da harbakin ta na kumfa ta ke fad'in
"Zancen banza kai wlh bazata sab'u ba, yadda kuka d'aura haka zaku kunce."

Bappa Salihu na fita sashin Mommy ya tafi.
Mommy ta tarbi mahaifin nata, bayan ta cika shi da kayan karin kumallo ta zauna suka shiga gaisawa, kasancewar daren jiya da ya iso bata samu sun gaisa ba.
Bappa Salihu bai tab'a komai daga cikin abincin ba.
gani bai ci komai ba Mommy ta ce
"Baba ga abinci fa an kawo maka."
ya ce
"Aa bar wannan yanzu haka nasan Abubakar ya kai min abinci can d'aki na, idan naje zanci acan."
Mommy ta d'anyi dariyar yake a kasan ranta kuwa haushi ne tam dan tasan abincin daga gun Aunty zai fito.
dan duk iyayen nasu idan suka zo Daddy ke d'awainiya da su da kansa,
daga sashin Aunty kuma yake fita da abincinsu.
tayi kwafa a kasan ranta ita da take 'yar su wai sai wata ce can za'a rika d'aukar abinci daga gurin ta ana kai musu.
ta wani jijjiga kai tana kuma jan kwafa a kasan ranta
Mommy ta d'an muskuta tare da kwakulo murmushi ta ce
"Baba ko kazo yin wani abu ne, naga baka shigo da wuri ba jiya sai dare,
ko jirgi ne aka rasa sai na dare?."
ya ce
"Tafiyar ce dai da ba'ayi masa shiri ba, shi yasa ban sami jirgi mai tasowa da rana ba,
lokacin da na iso Jos jirgi har ya tashi,
na bari sai gari yawaye kuma ina ganin b'ata lokaci ne, shiyasa nabi jirgin da zai taso da daddare,
dan nazo na aiwatar da abin da ya kamata da wuri."
Mommy tayi murmushi ta ce
"Ai kuwa kasha hanya mutan gidan kowa lafiya."
ya ce "Lafiya lau suke."
ya saka hannu a aljuhu yana cigaba da fad'in
"Yauwa ga goron auren d'anki da aka d'aura d'azu da asuba d'in nan."
wani irin mike wa a haukace Mommy tayi ta buga kirji
"Aure Baba! wai dama abun da ya kawo ka garinnan ke nan? wlh Baba bazai yuwuba yazama dole a wargaza auren nan!."
Mommy tana maganar a haukace tana jin kamar kanta zai bud'e.
Bappa Salihu ya ce
"Ke Halima zauna wani haukar banza ce wannan,kamar wanda aka fad'a miki mutuwar d'an naki,
abun da Allah ya hukunta kin isa kice ba haka ba, shirmen banza kawai."
Mommy ta zauna tana fad'in
"Baba a gaskiya ni ban yadda da wannan auren ba, ni kwata-kwata yarinyar ce bana kaunar ta."
"Au haka ne shine ke kika iya nemo masa mata ya aura, dan mahaifin sa ya bashi zab'in sa, sai ya zamo abin tada hankali,
shi yasa nace a d'aura auren nan take sabo da irin wannan shiriritar taku,
ke zaki zauna masa da matar,
shi Abdulrahim d'in da akayiwa dirar mikiya cikin rayuwar sa, ba'a jira jin ta bakinsa ba, ba'a jira jin ko da wacce yake so ba, aka zab'ar masa bai yi irin wannan haukar ba,
to ki maida hankalin ki baki isa ki hana abin da Allah ya hukunta ba."
Mommy da gaba d'aya kwakwalwarta ya cakud'e ta ce
"Baba wannan abun fa makirci ne kawai, duk shirin Hajiya Fatima ce, so take ta juya shi ta juya ubansa,
ban san me yasa ake son lallai sai ya aure ta ba, in dai auren ake son a kara yi masa a nima masa wata amma ba ita ba."
"Kaji shirmen banza kawai ita mahaifinsa yaso ya aura masa, karki kuskura kice zaki d'agawa mutane hankali kinji nagaya miki,
shirmen banza kawai shi yasa na d'aura auren d'iyanin sabo da gudun irin wannan shirmen,
zaku hana abin da Allah ya hukunta ne."
Bappa Salihu ya mike yana cigaba da fad'a.

Kuraiba ta fad'o parlour Mommy a hargitse tana fad'in
"Mommy wata magana nake jihaka, wai da gaske Abdulrahim aure yayi?
yaushe ne mukayi auren ko shekara bamu rufa ba shine zai kuma aure, wai kuma wannan yarinyar mai kama da aljanun,
Mommy kice min karya ne bama auren ya yi ba bare ace ita yarinyar ce ya aura."
Bappa Salihu ya daka masa tsawa
"Wace irin shashanci ne wannan zaki fad'o guri babu sallama, haukar banza kawai shine me idan ya yi aure matan ubansa nawa ne gasu nan kina ganin su rai uku,
kuma har yanzu yana da ikon karo d'aya bare shi mai mata d'aya,
haukar banza kawai."
Bappa Salihu ya fita yana cigaba da fad'a.

Bappa Salihu na fita Mommy ta kamo Kuraiba tana fad'in
"Zo nan aikin banza sukayi dan wlh ba abun da zai sa Abdulrahim ya zauna da yarinyar nan,
kwantar da hankalin ki kar ki wani tada hankalin ki ki sawa ranki damuwa,
muga yadda za'ayi su kai masa ita, yadda aka d'aurashi a titi haka zai watse a titi,
koma b'angaren ki kije ki kwanta ki huta kibarmin komai a hannuna."
"Mommy kin tabbata?."
"Aa ba ni na gaya miki ba ai ni yarinyar ce sam-sam bani kaunar ta, dan me zaisa na zuba ido a had'a ta da d'ana,
kije nagaya miki ke dai."
Kuraiba ta juya ta fita
gefen Abdulrahim ta nufa, tana shiga ta ganshi ya fito cikin shirin tafiya asibiti.
tasha gabansa tana taunar cingam tana yi masa wani kallon sama da kasa sannan ta ce
"Abdulrahim auren mu baiyi shekara ba aka kuma yi maka aure, baka gaya musu cewa ba wani isasshen lafiya ce gareka ba,
kai kana likita ma baka fahimta ba,
in ba haka ba zuwana gidan nan zan iya kirga sau nawa ka kusanceni, shima sai nayi tattaki nazo gare ka,
saboda ina maka kallon namiji mai lafiya da bazai iya rike kansa batare da mace kusa da shi ba, baka tab'a yin awa 3 a kaina ba,
a hakanne za'a kuma baka mata, wannan yarinyar da tasan mazama ina zata iya zama da kai."
"Bani hanya na wuce!."
yafad'a cikin tsawa fuska babu wasa.
duk da rashin mutunci na gaban goshin ta sai da ta girgiza da tsawan daya buga mata.
ta matsa gefe tare da sakin kukan makirci sannan ta rungume shi ta baya tana fad'in
"Ban tab'a ganin haka ba aure bai shekaraba ace za'a kara aure, me kawaye na zasu d'auke ni, please mijin Kuraiba kace baka son auren nan."
fezge jikin sa ya yi yasa kai yafice a a parlour.
yashiga motarsa yabar gidan.

Umma Karima da labari ya isar mata ta garzaya sashin Mommy a bujajan.
ko zama batayi ba, ta soma fad'in
"Amma kin bani mamaki Hajiya Halima, kina da ranki a cikin gidannan ki zuba ido a aurawa d'anki aure da wannan annobar yarinyar da take son ganin bayan mu,
kuma kina zaune kin rungumi hannu kin yi shiru,
shikenan burin Hajiya Fatima ya cika, ta mallaki mijin ki ta mallaki d'anki,
to me yayi saura baki da wani amfani kin zamo 'yar kallo."
Mommy ta ce
"Zauna Hajiya Karima, wlh na rasa yadda zanyi ne sun d'aure ni da jijiyata, Baba ya tsaya tsayin daka cikin lamarin, jira nake ya tafi wlh bazan tab'a zuba ido na bar auren nan ya yuwuba tun da aka d'aura wlh sai ya sake ta,
zan nunawa Hajiya Fatima ni na haifi Abdulrahim."
Umma Karima da gaba d'aya hankalin ta ya kai kololuwa wajen tashi ji take tamkar zatayi hauka.
ta zauna tana fad'in
"Uhm yanzu naji batu, idan baki sa auren nan ya watse ba, ina mai tabbatar miki ke zaki watse, dan wlh Hajiya Fatima da wannan mayyar aljanar ruwan sai sun kora mu a gidan nan mun zama 'yan kallo daga can bakin get."
Mommy ta buga kirji ta ce
"Ai insha'allahu sai dai su subar gidan nan ba dai mu ba,
yau Baba zai bar garinnan ai wlh bazan kyale ba bazan tab'a bari d'ana ya zauna da yarinyar nan ba."
Umma Karima ta jijjiga kai tana jan kwafa zuciyarta na wani irin tukuki abin mamaki wai Feeryal ce aka aurawa Abdulrahim.
idan ta tuna haka sai taji tamkar tayi ta kururuwa ko zataji saukin lamarin, bata tab'a sammani ko hasashen hakan zai iya kasancewa ba,
da tuntuni tayiwa tufkar hanci.
ji tayi zaman parlour'n Mommyn yamata kad'an ta koma sashinta tasa direbanta ya kai ta gurin bokanta.

Umma Karima na zube gaban boka Mali tana haki, cikin matukar tashin hankali.
baka Mali nata zane-zane da buga kasansa,
idonsa na kan katon kwaryar tsafin dake gabansa.
ya d'ago yana cewa
"Mun kira su daga shi har ita basu bayyano ba, meke faruwa ne a duk sanda muka kirasu bama ganin su, duk iya makircinmu mun gaza ganin su da ido,
idan muka gwada wannan sa'ar ta gagara to tabbas sai anyi babban gaggarumin shiri a kan su."
"Boka koma meye a yi kai nifa in da halima a kawar da yarinyar tabar duniya ko zan huta, wlh boka ji nake kamar nayi hauka wannan shegiya tambad'ad'd'iyar yarinyar, bana kaunar bud'e ido na ganta daga ita har uwar goyon nata,
boka dan Allah ka taimaka min kamar yadda kasaba taimako na,
wlh bansan ina zan sa rayuwata ba idan auren nan ya zaunu, duk yadda za'ayi a wargazara auren asa ya yi mata saki uku basai an kai ga tarewa ba, ka fi kowa sanin matsala ta."
wani kazamin dariya ya sheke da shi.
kana ya d'au wani bakin ruwa ya na zirarawa cikin kwaryar tsafin nan, yana yi yana kiran sunan Feeryal da Abdulrahim.
har ya juye ruwan duka.
ya d'ago a daburce yana fad'in
"Basu amsa kiranye ba me suka takaaaa!
dole sai munyi aiki cikin duhu da bakaken aljanu."
Umma Karima ta ce
"To boka ni dai ko ma meye ayi bukatata kada auren nan yayi tasiri ya wargaje cikin gaggawa."
"Tashi kije cikin duhuwar dare zamu soma aikin ki."
ta mike tana fad'in
"Nagode boka dan Allah a wargaza auren na, wlh ban san ina zan sa rayuwa ta ba idan auren ya zaunu."

A hanyar komawar ta gida Umma Karima sai fifita take da d'ankwalinta, duk AC da ke motar ita gumi take.
ta gyara zama tare da jan tsaki gami da kwafa a karo na sau ba adadi, tana fad'in
"Tsintacciya tambad'ad'd'iya da ni Karima kike narantse in zanyi yawo tsirara sai na wargaza auren nan, bake ba zama a matsayin matar Abdulrahim baki isa ki kuma b'ata min shirina a wannan karon ba."
direbanta ya juya ya kalleta yana cewa
"Ayi hakuri dai abi a hankali Hajiya, kar ki kwashi kud'i kiyi ta dankarawa mutumin nan mu tashi a tutar babu."
wani uban harara ta dankara masa tare da jan dogon tsaki
"Mtttsss in kud'ina gaba d'aya zai kare wlh sai na hana Feeryal zama da Abdulrahim, yi sauri muje gida da'alla."

Tun a daren ranar Bappa Salihu ya yi shirin tafiya,
Daddy yayi-yayi ya bari ya yi ko da kwana uku ne,
ya ce ina aje kawai a shirya masa tafiya, da safe zai tafi.
akwai abin da zaije ya yi a gida.
washegari
Daddy Dad da Abbie suka fito rako shi zuwa sashim Hajiya dan yaje ya mata sallama.
a waje suka had'u da Abdulrahim zai shiga gaida Bappa Salihu.
cikin girmamawa duk ya haishe su.
Bappa Salihu ya dafa kafad'arsa tare da bubbugawa ya na fad'in
"Babban mutum Allah ya maka albarka."
"Amin."
ya furta a kan lab'b'ansa idan ba idon ka na kallonsa ba bazaka san ya amsa ba.
ya nad'e hannayensa a kirji suka taka zuwa sashin Hajiya.
Hajiya ta karkata baki tana fad'in
"Um to Allah ya tsare hanya ina ka d'aura auren ya tamku gudun kada ya warware nan gaba."
Bappa Salihu ya ce
"Idan bazaki fad'i alkhairi ba kiyi shiru, babu ruwan ki kicire hannunki cikin lamarin."
"Na cire hanu na ai na cire hanuna kuje ku karata, ni ina ruwa na idan yaso kuje ku aura masa 'yar sarkin aljanu ma ni ina ruwa na."
Bappa Salihu ya ce
"Eh hakan ma yafi ki cire hannun naki, to ni natafi Allah ya sada mu da alkhairi."
Hajiya ta kawar da kai tana fad'in
"Allah ya tsare."
Bappa Salihu yayi gaba su Daddy suka bi bayansa.
a waje ya tsaya yayi ta sawa Abdulrahim albarka tare da nasihohi, da ban hakuri kan ya yi hakurin zama da zab'in iyayensa.
har airport Daddy ya rakashi sai da jirgin su ya tashi kafin ya juyo gida...

Mommy tana ganin dawowar Daddy tasan Bappa Salihu ya tafi.
ta kira Abdulrahim ta ce duk abin da yake yabari ya zo.
yana shirin fita office ya nufo sashin ta.
bedroom d'in ta ya wuce ya sami guri ya zauna saman kujerar da ke d'akin, yana duba agogon dake d'aure a hannunsa, da alama dai sauri yake.
Mommy dake zaune bakin gado ta gyara zama tana dad'a tamke fuska ta dube shi da kyau sannan ta ce
"Me kake jira da auren yarinyar can da aka kakaba maka,
baka guntule shi haryan zu ba, har kabari ya kwana a kanka."
ta jefo masa takarda da biro tana cigaba da fad'in
"D'auka yanzu ka rubuta mata saki uku nakaiwa uwar gayyarta da hannuna, na nuna mata na isa da kai."
kallon takarda da biron ya yi kana ya kalli Mommy sannan ya ce
"Mommy lokacin da kika nuna min Kuraiba a matsayin zab'in ki, ban bijere ba nayi miki biyayya,
to dan me zan bijire nakiyiwa Daddy biyayya tun da duk haka kuka zab'arwa rayuwa ta, shike nan sai na kare rayuwar tawa a haka,
bani da ikon aiwatar da hakan sai idan Daddy ko Bappa Salihu sun umurce ni,
ko yanzu suka umurceni zan aiwatar."
ya mike tsaye yana cigaba da fad'in
"Mommy ina da CS 11."
Mommy data daskare a gurin ta waro ido had'i da buga kirji ta ce
"Abdulrahim ni kake gayawa haka, au wanda ya aurama shi zai baka izinin sakin,
tun da bani na aurama wannan ba ban kai na baka izinin sakin ta ba,
Eh lallai ba'a barka banza ba, yazama dole na warware barbad'en da akayi maka."
baiyi magana ba yayi waje da sauri dan saurin yake,
aka tsare shi da wani batun da aka dame shi da shi tun jiya.


Da gudu Miemie ta shigo sashin Aunty ta wuce dakin Feeryal.
Feeryal tana kwance a bakin gado tana buga game, Miemie tayi tsalle ta haye gado tana tsallen murna had'i da rangad'a gud'a.
cikin muryar dariya da farinciki sosai take fad'in
"Kai gaskiya wannan had'i ba karamar dacewa tayi ba, wlh na jima banyi farinciki irin na yau ba,
ayyiririii Feeryal amaryar Ya Abdulrahim."
da sauri Feeryal dake binta da dariya ta waro ido tare da fad'in
"Ke Miemie rufamin asiri babu ruwa na, ko me irin sunan Sahab ma babu ruwa na dashi bare wannan Sahab mugun, ki raba sunan mu kar ki sake had'awa."
tayi maganar tana turo kyakkyawan bakin ta.
Miemie ta zauna ta kalmashe kafa tana cewa
"Ke dalla matsa can, kuma shi Ya Abdurrahim da kike ganin shi babu ruwan shi yana da saukin kai sosai idan ba wai laifi kayi ba babu ruwan shi da kai."
"To ni ina ruwana ma da shi, yayanku ne ai ba Yaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login