Showing 33001 words to 36000 words out of 86085 words
Chapter 12 - FEERYAL Part 3 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt
da kalmar.
da karfi ya bud'e idanunsa da suka rine sukayi jajir nan take.
jakar ya sauke daga bayan sa jininsa na wani irin tafarfasa,
jijiyoyin kansa zuwa na hanayensa suka mike sukayi rad'a-rad'a.
ya bud'e jakar ya ciro takarda da biro hannunsa na kakkarwa ya d'aura biron kan takardan ya rubuta ya d'ago, yayi taku biyu yazo gaban Feeryal dake tsaye ta toshe bakinta da tafin hannunta,
jikin ta na kyarma hawaye na zuba a idon ta,
lamarin ya bala'in tsorata ta.
jajayen idanunsa ya zuba mata tare da mika mata takardan.
ta ciro hannunta dake toshe da bakin ta ta karb'a.
da sauri ya juya yana gyara rukon jakansa ya fice daga parlour'n.
Mommy ta ce "Tom kama hanya kiyi gaba bake ba d'ana yanzu, mayya aljanar banza, burinku bazai cika ba."
Mommy ta sata gaba ta kad'ata tayi sashin Aunty.......!
Aunty dake zaune a parlour ta mike zumbur ta taro Feeryal da ta shigo da gudu tana waigen bayan ta.
hankali tashe Aunty take fad'in
"Ke Feeryal mene ne kina lafiyar ki kuwa?."
rirrike Aunty tayi gam tana fad'in
"Ammie Mommy ce."
sai kuma ta sake ta tana kuma juyawa ta kalli kofa, ganin bata biyo ta nan ba ta sauke numfashi.
Aunty tace
"Mommy kuma Hajiya Halima ce ta biyo ki to a dalilin me?."
ta kardan ta mika mata ta ce
"Ammie ya sake ni ita ta ce Sahab ya sake ni."
wani irin girgiza Aunty tayi da jin abun da Feeryal d'in ke fad'a, hannu na rawa ta karb'i takardan tana cewa
"Innalillahi wa innailaihirraji'un saki kuma!."
Feeryal ta gyad'a kai.
Aunty gaba d'aya ta rud'e takasa ko da iya bud'e takardan sai rikeshi da tayi gam cikin hannunta hannun na rawa.
sai ambaton sunan Allah take.
Feeryal ko wucewa cikin bedroom d'in ta na side d'in tayi, tana mamakin ganin yadda Aunty ta rud'e gaba d'aya ita fa dama ba sakin bane ya razanata,
ganin yadda Mommy take masifa ce ya razana ta tana tsoron kada ta bigeta.
ta shige d'aki tayi kwanciyar ta hankali kwance.
Kan kace me gidan ya d'auki zancen sakin Feeryal.
Umma karima tayi tsalle tayi murna tashigo sashin Mommy da farincikin ta tana fad'in
"Yau kin nunawa Hajiya Fatima iyakar ta, yau kinyi abun da ya dace, har yaushe dama zaki cigaba da zuba ido d'anki ya salwanta, gara da kika nuna mata ke kika haifi Abdulrahim kuma kina da ikon sashi duk abun da kika so da hanashi,
an yadda kwallon mangwaro an huta da kuda, sai susan in da dare ya yi musu,
ana ji ana gani a zalinci yaro a had'a shi da aljanar ruwa masu tsafe-tsafe haba dan Allah."
Mommy ta ce "Ai yanzu kam ya kare har naji hankali na ya kwanta, kai Hajiya Karima nagode miki, wlh badun taimako da sani a hanya da kike ba da ban san ya zan yi ba, yan zu badun kin je kin jiyo wannan labarin ba, da sai dai aji mutuwarsa ace haka Allah ya hukunta, daga nan nima na bakwanci lahira."
Umma karima tayi wani dariyar makirci tana cewa
"Kai haba Hajiya Halima ai babu godiya sakanin mu, ni masoyiyar ki ce ta hakika shekara nawa muna tare mun zamo abu guda, bazan so ganin abun da zai cutar dake ko yayan mu ba, shi yasa tun farko banso had'ata aure da nagartaccen yaro irin Abdulrahim ba."
"Yanzu kam ai zance ya kare suje can su karaci tsiyar su, badai da jinina ba wlh."
cewar Mommy tana buga cinya..
Umma karima ta mike tana fad'in
"Ah to ai gara da kika ankare tun kafin lokaci ya kure miki, ni bari na je dan dole na kaiwa malamin nan labari, nayi masa tukuici na musamman,
dan ya taimake mu ya ankarar da mu tun kafin lokaci ya kure."
Mommy ta ce
"D'an jirani ina zuwa."
ta shige d'aki ta fito da d'aurin kud'i 'yan dubu-dubu da suka kai guda d'ari ta damka mata ta ce
"Ga wannan ki basa kiyi masa godiya dan Allah."
Umma karima ta karb'a tana cewa "Ai ni ma ko dole na kara masa bari naje yanzu."
Tana fita sashin Aunty ta zarce.
Aunty na zaune a parlour tana sauraran karatun alkur'ani dake tashi a tv.
Umma karima ta shigo babu ko sallama ta nimi guri ta hakimce kan kujerar da yake fuskantar ta,
ta d'aga kafa ta d'aura d'aya kan d'aya, tana girgizashi tare da bin Aunty da wani kallon wulakanci.
sannan ta ce
"Hajiya Fatima ya gajiya ya fargaba, tun yanzu naga kinyi kwalas har kin tsare ne haka da wuri, tun bakiga karshen wasan ba,
bakiga ko mai ba muzuba mugani, ki dakance ni ina kan zuwa ta kanki."
tana kaiwa nan ta mike ta nufi kofar fita daga parlour'n.
Aunty tabi bayanta da kallo tana shirin fita daga parlour'n Aunty ta ce
"Shi aure da kike gani iko ne na Allah dan abune mai rai,
da rayuwar sa da mutuwar sa duk daga Allah suke,
Allah ne kad'ai keyin yadda yaso da shi ba d'an mutum ba, ina sauraran ki Hajiya Karima!."
Umma karima tayi wani dariyar rashin mutunci, kana ta kad'a kai tayi waje.
Daddy na Saudi ya sami labarin,
Aunty kam taki gaya masa da ma ta ce sai ya dawo, Ajmaal ne ya sanar masa da abunda ke faruwa,
Daddy yayi masifa fari yayi baki, ya kira Abdulrahim ya yi masa kaca-kaca ya nuna masa b'acin ransa da bai tab'a gani ba.
shi dai bai ce masa kala ba har ya kashe wayar.
ko da Daddy ya kira Mommy kalmar da ya iya fad'a mata ke nan
"Kin kyauta Hajiya Halima."
daga nan bai kara cewa komai ba ya kashe wayarsa.
Kwana uku da faruwar lamarin, kafin 'yan Abuja suka sami labarin.
Abba ransa ya b'aci matuka ya kira Daddy ya ce zai tura a d'auko Feeryal bazataci gaba da zama a gidan ba, tun da suka kasa iya riketa suka maida ta karamar bazawara.
Daddy ya yi ta bashi hakuri,
ya ce idan ya dawo gida ko mai zai dai-dai ta.
Abba ya tire yace sam yau za'a sata a jirgi a kawo ta Abuja shi zai nima mata mijin da zai iya riketa.
Daddy bazai ja da Abba ba a matsayin sa na sirikinsa haka yabar zancen akan sai ya dawo.
a ranar kuwa Abba ya sa aka shirya mata tafiya Abuja.
Feeryal tana ta murna zataje taga Hajja Umma da Maryam da suke ta waya da ita tun da safe,
dan Maryam d'in tana gida, anyi posting d'in inspector Nasir ogun State kuma tana da tsohon ciki, shi ne ta dawo gida sai ta haihu kafin ta koma.
Sai da a kazo d'aukar ta kafin jikin ta yayi sanyi ganin zata rabu da Ammie'n ta, har da kukan ta.
duk da Aunty taji ba dad'i rabuwar su amma tasan zata sami saukin maganganun da ke kai kawo a cikin gidan.
Karfe 12 na rana motan gidan Alhaji Tahir Abbas ya isa airport d'aukar Feeryal.
Hajja Umma da Maryam suna tsaye a farfajiyar gidan suna jiran isowar ta.
suna isowa tun kan motar ta paka suka yiyo gurin motar suna fad'in
"Oyoyo Feeryal."
Feeryal ta fito cikin farinciki suka rungume juna.
ta bud'e baki tana kallon Maryam da katon cikin ta,
"Laa Aunty Maryam dama kin kusa haihuwa ne?."
ta fad'a da mamaki tana rike hab'a da waro ido kan cikin tana dariya.
Maryam tayi dariya taja hannunta, sukayi ciki Hajja Umma tana ta zolayar ta...
Ranar har dare suka kai suna hirar yaushe gamo.
da daddare suna kwance a dakin su na da, Maryam tana manne da waya tana waya da Inspector Nasir.
ta mikawa Feeryal wayar da Nasir ya ce a bata su gaisa, dan tun tasowarta ya sami labari daga matar tasa.
Feeryal takarb'a ta gaishe shi a takaice ta mika wa Maryam wayar.
Inspector Nasir yayi dariya jin tayi saurin mikawa Maryam wayar, ya ce
"Wai har yanzu mutumiyar a haka take dai bata sauya ba, kamar mai jin tsoron magana,
ni dai daga yau kullum zanrika tuni kada wani yazo ya kuma mana shigar sauri, dan har gobe Major Sadam yana son ta,
bazai zo ba har sai tayi idda, in Allah ya yarda bayan idda da sati za'a d'aura auren nan, ke dai kiyi ta mana fadanci."
Maryam ta ce
"Tom Allah ya nuna mana, amma ai za'a barta ta huta tukun, daga yin idda sai aure kuma ai yayi wuri da yawa."
da sauri Nasir ya ce
"Aa wife kar muyi haka dan Allah wannan karon ki mara mana baya kin fi kowa sanin halin da Major Sadam ya shiga a lokacin da ya rasa ta,
dan Allah ki taimaka mana."
numfashi ta sauke ta kalli Feeryal dake kwance tana buga game a wayarta ta ce
"Duk da yarinya ce har yanzu amma addini ya bata dama a wannan karon ta yi zab'i da kanta, sannan iyaye su taimaka mata wajen duba ingancin zab'in nata,
idan har Sadam yana cikin kundin kaddarar ta zai aure ta."
"Wife auren Feeryal fa duka-duka wata biyu da kwanaki ne, har yanzu iyaye suna da damar kuma zab'ar mata miji, na tabbata idan Abba ya kawo mata Sadam a matsayin miji bazata ki ba, dan haka da wuri zamuzo mu sami Abba Major Sadam zai rike Feeryal ruko bana wasa ba dan yana sonta."
"Uhum a dai bari lokacin yayi ni dai nafi son a barta, tazab'i wanda ranta ya kwanta da shi kar a dawo gidan jiya."
ya ce "Hmmm Wife ke dai ki bamu gudumawa wajen fahimtar da ita irin son da Sadam ya ke mata, yanzu ya baby na yake."
shafa cikin tayi ta ce
"Gashinan sai motsi yake."
"Had'a ni da shi naji motsin sa."
ta zaro wayar ta d'aura kan cikinta, kiss yayi wa cikin ta waya yana fad'in
"Muna maraba da zuwan ka abar kauna."
ta zaro wayar ta kai kunnenta tana fad'in
"Ni na matsu ya fito na huta."
"Saura kad'an ai EDD ya cika, insha'allah bazaki wuce EDD ki ba sai kiga ma a daren nan in Allah ya yi ikon sa,
ki haihu, in kin wuce ma bazaki kai kwana goma nan gaba ba, saura 6 days fa."
ta ce
"Ni dai kayi min addu'a Allah ya kawo min da sauki."
sun jima sosai suna waya Feeryal kam tuni tayi bacci.
Washegari Abba Hajja Umma Maryam da Feeryal duk suna kan dinning, suna breakfast.
Hajja Umma ta rike baki ganin abun da Feeryal ta maida hankali kan cinsa, ta ce
"Wato dai har yanzu hali na nan, shi yasa baki karu ba jikinnan nanan kamar tumatur."
murmushi tayi tana kai loman cake bakinta.
Abba ya yi dariya ya ce
"Ta karu mana ke bakiga takara girma ba, ai dole ma na kara sadaki, tun da shi wancan ya kasa iya rikewa."
dariya tayi tana d'agawa Hajja Umma gira.
Hajja Umma ta yamutsa fuska tana fad'in
"Ahaf ni na dad'e ina cin moriyar."
da wasa da dariya suka watse a kan dinning d'in...
Bayan kwana biyar Maryam ta tashi da nakuda,
nan da nan aka garzaya da ita asibiti.
cikin ikon Allah ta suntulo d'anta na miji.
zo kaga murna gurin su Hajja Umma, Feeryal baki yakasa rufuwa, ana fitowa da baby'n ita tariga kowa karb'a.
tana kallon yaron da ya mugun burge ta, sai hotuna take musu.
takira Aunty video call, Aunty tayi murnar ganin sabon baby.
Inspector Nasir da ya kira wayar Maryam video call yana hannunta ta d'aga.
ta nuna masa d'ansa kamar yasa hannu ta cikin wayar ya d'auke shi,
yayi ta murna yana kissing d'in sa ta waya.
da kyar ta baiwa Hajja Umma shi.
ko minti goma bata bari yayi ba ta kuma karb'ar sa.
tuni asibitin ya soma cika da 'yan'uwan Inspection Nasir dana su Abba, da yamma aka sallame su dan lafiya lau ta sauka, ita lafiya jaririn ma lafiya.
sun fito daga cikin asibitin ana kokarin shiga mota Major Sadam ya iso asibitin.
ya paka motarsa ya fito.
cikin girmamawa yake gaida Hajja Umma da sauran mutanen, kana ya juya ga mai jego cike da farin ciki yake fad'in
"Sannu da kokari muna godiya da samar mana baby."
Maryam tayi murmushi.
Hajja Umma ta dunguri Feeryal dake rumgume da yaron ta ce
"Mika masa d'an nasu ya gani."
a hankali ta taka zuwa in da yake ta mika masa yaron, ya mika hannu ya karb'e shi idanunsa a kan ta.
kaucewa tayi gefe ta tsaya dan kallon da yake mata yayi mata yawa.
motoci biyu ne a gurin ga mutane kuma da yawa, ya ce wa Hajja Umma su shigo motarsa ya karasa da su gida.
mejego Maryam da Hajja Umma suka shiga gidan baya,
ya tako gaban Feeryal ya mika mata yaron yana fad'in
"Muje Madam."
tana tsaye har ya shige mator sai da Hajja Umma ta leko ta ce
"Shigo mu tafi mana Feeryal."
ta tako a hankali tana kokarin wucewa in da su Hajja Umma suke ya bud'e mata gefen gaba, ya ce
"Shigo nan."
a sannu taja kafarta ta shige motar ta zauna, tana gyara rukon jaririn.
ya fita daga mazaunin sa ya zaga ya rufe mata kofar, kana ya dawo mazaunin sa ya ja motar suka nufi gida...
suna isa tayi saurin fita ta nufi ciki..
Da Feeryal ake jegon dan kullum tana like da jariri, ana gobe suna Aunty ta zo.
Feeryal tayi ta murna.
ranar suna akayi suna nagani na fad'a, iyayen Inspector Nasir sun nuna bajin ta kwarai da gaske, dan ba karamin kaya sukayiwa mai jego da d'an ta ba.
bayan suna da kwana biyu Aunty ta koma...
haka rayuwa yaci gana da tafi, jego dai da Feeryal akeyi..
Ranar da Maryam tayi arba'in,
da kwana biyu suka shirya da Feeryal zuwa kasuwa.
direba ne zai kaisu suka fito, Feeryal na rike da jaririn daya ciki sunan baban Nasir ana ce masa Aiman.
direba yajasu zuwa kasuwa.
suna tsakiya da yin sayayya Feeryal ta rumtse idanunta da karfi jin yadda kanta yayi wani irin masifaffen tsarawa.
sigar jikinta ya tashi.
da sauri ta bud'e idanunta jin wani irin sauti mai gauraye da maganganu na tashi a can cikin kunnuwan ta.
ta ware idanun nata kan wasu samaruka uku dake tsaye gefe suna duba kaya,
da karfi ta kankame Aiman dake rike a hannunta duk suka juyo suna kallon ta,
sikar jikinta yakuma tashi tana jin sautin na dad'a karuwa cikin kunnuwanta,
jikinta ya d'auki b'ari gaba ki d'aya jikin ta kyarma yake.
dafa Maryam tayi cikin mashahuriyar tsoro ta ce
"Aunty Maryam kiga wad'an can suna kallo na, zo mu tafi gida."
Maryam ta juyo ta ce
"Ina suke Feeryal."
da hannu tayi mata nuni ta ce
"Gasu can Aunty Maryam zo mu tafi!."
tayi maganar cikin matukar tashin hankali, jikin ta na kyarma.
Maryam ta yi saurin karb'ar Aiman dake shirin fad'uwa a hannunta ta ce
"Ni ban ga kowa ba ai babu mai kallonki kowa harkar gaban sa ya ke, ki natsu mana Feeryal."
baya tashiga ja idonta a kansu,
dai-dai kafad'un su take ganin wani jan haske kamar wutan kendir ke ci a gurin.
kamar yadda suma kuke kallon dai-dai saitin goshin ta da wani haske ke fita da kad'an kad'an yana zagaye tsakiyar goshin nata kamar nannad'in mantega.
da gudu ta juya ganin suna dumfaro in da take,
tana sa gudu suka biyo ta a guje......!
Babu editing
Da iya karfinta take gudu bata ko kallon in da take jefa kafarta,
tana waigen su tsoro tashin hankali su suka bayyana a gareta.
tamkar hankalin ta zai bar jikin ta sabar tashin hankilin da take ciki.
Maryam da ta biyo ta tana kiran sunanta hankali tashi, Maryam ta saka ihu ganin tasa kai zata sallaka titi, batare da tsayuwa duba titin ko jiran ababen hawa su wuce ba.
karan ababen hawa kake ji suna taka burgi.
jama'a sai d'aura hannu suke a kai suna salati.
wani irin burki wata moyar da tayi daf da ita tayi,
duk da haka sai da gaban motar ya tureta ta zube kasa.
da sauri ta mike a zabure ganin sun dumfaro titin, ta karasa sallake titin da gudu a kid'ime ta yi bayan wata mota dake pake gefen titi.
tab'oye jikin ta na kakkarwa.
tarika rab'ewa jikin motar tana tafiya da gefe da gefe.
yana zaune cikin motar gaban wani shago yana jiran Dr Imran daya shiga shopping cikin shagon.
tun ihu da salatin mutane ya maida hankalin sa kan titin, sai dai sam bai lura ya gane ko wace ce ba, sai yanzu da yake kallon ta ta cijin
glass d'in motar.
kamar gilmawar walkiya suka ketaro titin wani igigitaccen kara ta sake ganin sun bayyana a gaban ta.
da karfi cikin zafin nama ya bud'e motar,
dai-dai sanda tayi baya luuu zata zube kasa ya yi saurin rukota ya janyo ta jikinsa.
da karfi, hannu ta shiga nunawa tana fad'in
"Gasu nan sun biyo ni, bana son ganin su ina jin tsoron su!."
hannunta ya sake jikin ta ya sake gaba d'aya,
idanunta ya rufe.
da sauri ya d'ago yana duban in da take nuna masa, bai ga kowa ba.
da sauri ya ciccib'e ta ganin hankalin mutane yafa dawowa kansu.
ya bud'e mota ya shinfid'a ta a sit d'in baya, kana ya dawo mazaunin direba da karfi ya figi motar.
Dr Imran daya fito da kaya niki niki a hannunsa ya bud'e baki yana kallon yadda ya figi motar.
A bakin wani katafaren had'ed'd'en gida yayi hon,
aka wangale mata get.
yasa kai ya shige ciki, a farfajiyar gidan ya yi parking, ya bud'e ya fito da sauri kana ya bud'e gefen da take ya ciccib'o ta ya yi ciki da sauri da ita.
kai tsaye bedroom ya wuce da ita ya shinfid'a ta a kan gado.
kugu ya rike yana kallon fuskarta da idanunta suke a lumshe.
numfashi ya fesar kana ya juya har yakai kofa zai fita, yaji ta yi wani irin gurnani.
da sauri ya juyo, tayi wani irin mikewa ta fincike d'ankwalin kanta ta yamutsa gashin ta dayake a tsefe ta kuma yamutsa shi tare da girgiza kan.
ta duru a gadon tana kokarin rufawa a guje.
da karfi ya tako ya dawo da baya, ya damko hannunta.
ihu ta kuma yi ta fizge hannunta ta d'aga kafa zata kuma sa gudu.
ya kuma damko ta ya d'au ke ta da wani irin gigitaccen mari da sai da ta kife kasa.
har sai da gefen bakin ta ya fidda jini.
Ta d'ago tana wani irin kecewa da dariya, da wani irin murya mai fidda amon sautin muryoyi daban daban har kala uku.
"Hahahahaha yau ba makawa sai mun tafi da ita, tun da muka samo ta."
ta mike yayi saurin rigata isa jikin kofar,
ya rufe tare da murza key ya zare key'n ya jefa cikin aljuhun wandon sa.
da wata irin murya take fad'in
"Tun da muka samo ta dole zamu tafi da ita, shekaru masu tarin yawa muke jiran zuwan wannan rana,
tun ranar da muka sami tabbacin zuwanta duniya muka d'aura d'amarar samo ta,
mun zaga duniyar nan muna niman ta,
an baza mu ta ko ina dan nemo ta, tun da muka samo ta dole mu tafi da ita, mu karb'o kambun karramawa, dan mu mukayi nasarar samo ta,
muna da hanyoyin fita da