Showing 78001 words to 81000 words out of 86085 words
Chapter 27 - FEERYAL Part 3 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt
sa.
sai da ya shari sati guda a gida kafin ya fara fita asibiti.
a d'an wannan sai kon kuwa sai da ya tabbatar da ya sabar mata da shi, ta soma sakin jiki da shi.
sai dai fa har yau tana jin zafin lamarin.
Aunty ta daina kawo musu abinci ta ce ta shiga kitchen da kanta ta girka musu, a kitchen d'in gefen sa takeyi musu girki.
Yau da wuri tagama ai ki ta shirya shi kan dinning, ta haura bedroom d'in sa ta gyara ta fito ta sauko,
tabi ta hanyar da zai kaita gefenta ta shige bedroom d'in ta,
tana shiga bathroom taji shigowar motar sa,
tayi wanka ta fito,
tana zaune gaban mirror ya shigo.
yana sanye da wando 3qrt da singlet.
ya tako ya zo ya rungume ta ta baya, kiss ya manna mata a gefen wuya yana kallon fuskarta ta cikin mirror.
a hankali cikin siririyar muryarta mai sanyi ta ce
"Barka da dawowa."
ido ya lumshe yana bud'e su a kanta kana ya kama towel d'in jikin ta ya kunce,
ido ya tsurawa ababen kirjinta ta cikin mirror, ya kai hannunsa ya cafko su, yana matse su ya yin da yake hango su ta cikin mirror.
fuska ta kwab'e yanayin sa ya sansar mata da abun da yake bukata.
"Sahab barni sanyi nake ji zansa kaya."
tayi maganar tana kokarin janye hannunsa daga kan nonuwanta.
a hankali ya furta
"Okay muke na baki d'umi."
sai kawai ya d'aga ta cak ya kaita kan gado,
yabi jikinta.
"Sahab ka bari kaya zan saka kawai."
bakinsu ya had'e,
sosai yake totsar ta ta ko ina kamar zai cinyeta da baki, ya d'ago idanunsa sunyi ja.
tuni ya cire kayan jikin sa.
fuska ta kwab'e duk da ya kashe mata jiki.
ya kwanta gefen ta ya d'ago ta ya d'aura kansa zellewa take kokarin yi ya riketa da kyau.
"Stop Beauty ke zakiyi da kanki bazakiji zafi ba."
ya yi maganar yana had'e kugunsu.
"Oh yeah! kinji ba zafi ko, fad'a min kina jin dad'in hakan."
ido ta rumtse da karfi tana kunyar saka nata idon cikin nashi kamar yadda shi yake yi.
"Fad'a min Beauty kina jin dad'in haka."
ya yi maganar cikin wani irin voice, mai nuni da zallar jin dad'i da fita hayyaci.
ido ta kuma rumtsewa,
ta daure duk da tana jin zafi, sai dai ta gaji a yadda suke d'in.
ta sulale a kansa tana cewa
"Sahab na gaji."
tuni ya juya ta kasa ya ci gaba da bata wuta.
sai da ya koshi kafin ya kyale ta.
sun fito daga wanka tana ta mammatse ido, tana zillewa gefe.
rukota ya yi ta zille gefe, ido ya d'an tsura mata sai kuma da sauri ya d'ago ta cak ya d'aurata a kan gado.
da sauri ta yunkura zata ta shi, ya yi saurin mai da ita yaja towel d'in jikinta kasa yana kurewa nonuwan ta kallo.
"Allah Sahab na gaji ka barni, ni dai akwai zafi har yanzu."
tayi maganar tana yunkurin tashi.
da sauri ya ce
"Tsaya beauty babu abun da zan miki, tsaya mugani."
ya kamo nonon ta d'aya yana kallon nipple d'in sa.
sai kuma taga ya saki murmushi irin wan da da wuya ka gansa a kan fuskarsa.
ya rungume ta yana manna mata kiss a goshi.
a hanka ya furta mata a kunne
"Taso ki sa kaya muje asibiti."
ido ta waro da tsoro ta ce
"Me zamuyi?."
"Muga kwanakin baby'n."
ya yi maganar yana shafa cikin ta da yake a shafe.
da sauri ta kalle shi shima ita yake aikawa wa wata zazzafa kallo.
Shi ya saka mata kayan da kansa ya rukota suka je gefen sa yasaka nashi kayan, sannan ya d'au makullin mota suka fita.
janyo ta ya yi jikinsa yana driving tana kwance a gefen jikinsa.
a haka suka isa AA FIYA HOSPITAL.
suka fito a mota yana rike da hannunta suka shiga cikin asibitin.
da Nurse Samira suka fara had'u, dan da taga shigowar motarsa sai ta tafito daga office d'in su da sauri, tana karairaya.
ganin sa rike da Feeryal a gefen sa, sai tayi burki zuciya na suya.
ganin wanda ke gefen nasa kyakkyawa ajin karshe, har sai da ta rainawa kanta,
yana da wannan ina zai kula wata.
ta kakalo murmushin yake ta ce
"Good afternoon sir."
Dr Imran ne ya fito daga office nashi ya washe baki yana fad'in
"Barka dai Madam kin rike mana Dr a gida kin hanashi fita a kan lokaci, AA tom sai a shiga office dama akwai patient a kasa."
Abdulrahim ya harare shi,
ita dai murmushi tayi tana yin kasa da kanta.
ya ja ta suka shige office d'in sa.
suna shiga ya bud'e wani d'an ma dai-dai cin wardrobe dake cikin office d'in,
ya d'auko bedsheet mai kyau da tsafta ya shinfid'a kan zanin gadon da ke kan gadon office d'in,
sannan ya d'aga ta cak ya d'aura kan gadon, ya kwantar da ita.
fuska ra kwab'e ta ce
"Sahab kar kayi min allura fa."
kai ya jinjina yana jan rigarta sama ya ce
"No bazan miki allura ba, kisa idon ki a nan."
ya nuna mata cikin computer.
dayake saitawa ya d'aura scanner a kasan mararta yana d'an yawo da shi a kasan marar nata.
ajiyan zuciya ya sauke mai had'e da murmushi, ya nuna computer ya kawo bakin sa saitin kunnen ta ya rad'a mata.
"Kina kallon baby'n Sahab da Beauty 1mon 2 weeks, baby bai san zafi ba tun san da kike raki ya shige abinsa,
wayshh Sahab a kwai zafi."
ya karashe maganar da kwaikwayar muryar ta.
ido ta rufe da karfi wato Sahab haka ya iya zolaya shima, kamar ba shi ba idan ka ganshi zakace babu magana bakin wannan,
dan a fuskarsa kad'ai ka kalla zaka cire rai da samun magana cikin bakinsa.
idan yana mata wasu abubuwan takan sha mamakin sa,
a d'an zaman su ta fahimci mutum ne mai mugun saukin kai sam baya son hayaniya magana kuma bata dame sa ba,
baya dogon magana amma da ita yakan yi magana mai tsowo.
kafa ta shiga shurewa da shagwab'a.
ya d'agota ya rungume yana manna mata kiss, ya yin da yake dad'a jinta sosai cikin zuciyarta.
Dr Imran ya yi knocking sai da ya gyara mata jikinta ya rufa mata mayafi, kafin ya ce ya shigo.
Dr Imran na shiga idanunsa ya sauka kan computer.
baki ya washe yana cewa
"Wow! gaskiya mutumina kai d'in bana wasa bane, wani babyn ka samo mana, Allah ya raba lafiya, to bari nayi sauri na sanar a gida a bani tukuici."
Abdulrahim ya harare shi.
ya kamo hannunta ya saukar da ita.
suka nufi kofar fita.
shiko Dr Imran dariya ya yi yana dan na wa lambar Ajmaal kira.
"Gara dai na sanar musu da wuri dan nasan kai kam bazaka fad'a ba, sai dai in sun gani da idon su."
ya yi maganar yana kai wayar kunnensa.
Ajmaal na d'agawa Dr Imran ya sanar masa Feeryal na da ciki har da watan cikin.
Ajmaal da ke tare da su Mommy a parlour'n Hajiya ya yi ihun murna.
yana fad'in
"Yes yes yes masha'allah!."
da sauri Hajiya ta ce
"Kai Ajimi lafiyar ka ai sai kasa mu ruga da gudu."
cikin matukar farinciki ya ce
"Hajiya Feeryal na da ciki wata d'aya da sati biyu."
Hajiya ta ware ido ta ce
"Ya haka kuma bayan batayi ko wata da dawowa ba."
Goggo bishira ta ce
"Hajiya kin mance san da ya karb'ota daga hannun 'yan kidnapping, bafa gidan nan ya dawo da ita ba, sai da sukayi kwana uku kafin ya dawo da ita,
kuma kiyi lissafi wata biyu da sati biyu ke nan da faruwar hakan."
Hajiya ta rike hab'a
"Oh 'yan zamani zasu kasheka da sauran kwanan ka, wato can ya lallab'a ya kai ta ya yi mata cikin."
Mommy kam sai tsunkuyar da kai abun da ta aikata ya zo mata sabo,
bakin mayafin ta ta kai ta shere hawayen da suka zubo mata,
ta ce
"Allah sarki Allah ya sauke ki lafiya Feeryal, ashe ba karshen koyayen Albulrahim na kashe ba, ka gafarceni Abdulrahim Feeryal ki yafe ni, ya Allah na tuba."
ta fashe da kuka duk aka dawo bata hakuri.
Ajmaal ya yi waje da sauri yaje ya sanar wa Aunty.
Aunty kuwa bakinta yakasa rufuwa sai murmushi take.
itama Daddy na shigowa ta rungume shi da murna take shaida masa.
Daddy ya yi dariya da farinciki fal ransa ya ce
"Oh Fad'imatu babu kunya ana murnar anyi jika."
duk sukayi dariya zuciyoyi cike da farinciki.
Wannan ciki na Feeryal taga gata da tarairaya, agun Mommy Aunty da kuma Daddy Hajiya ma ba'a barta a baya ba,
haka Ajmaal kullum a lissafin kwanakin cikin yake, wai yana alla-alla abun cikin yazo duniya,
su Farida da sauran kannen sa da 'yan gidan kowa na mararin isowar baby duniya,
har da Mom da yanzu taga babu wani sarki sai Allah ta yada makamanta, ta rufawa kanta asiri ta zau na cip dan miji kam yana nan a rufe an yanke masa shekaru 10 a gidan yari.
sannan shi kansa mai cikin,
tamkar a goya ta motsi kad'an za'a waiwayeta.
labarin cikin ba iya Yelwan Shendam da Abuja ya tsaya ba har Beirut Lebanon.
kusan kullum sai sunyi video call da 'yan Abuja da Lebanon suna jin lafiyar cikin nata.
Goggo Bishira kullum tana gurin ta idan Abdulrahim yatafi asibiti ita zataje ta zauna da ita, ita da su Miemie da Ameerah.
baya kai awa uku zai dawo gida ya d'aura daga in da ya tsaya a rainon cikin nasa.
kayayyakin amfanin asibiti na kula da mai ciki musamman ya shirgesu a wani d'aki na gefen bedroom d'in sa, harda computer scanning,
duk bayan sati yake duba lafiyar ciki.
a sanu a sanu cikin Feeryal ke girma, haka ma kulawar da ake bata ke kara hab'aka.
dan kuwa yanzu Aunty bata iya hakuri duk bayan kwana biyu zataje ta gano ta.
Akwan a tashi babu wuya a gurin Allah yau Feeryal ta tashi da ciwon nakuda.
tun da ya gane nakuda ne bai matsa ko nan da can ba,
bai kuma sanar wa kowa ba, sukayi ta nakudar su su kad'ai,
abun tun azahar har dare Feeryal na abu guda.
ta bashi tausayi matuka yarasa ina zai sakata ina zai saka rayuwat sa,
ta kankame shi tana fad'in
"Wayyo Sahab zan mutu ka cire min cikin nan na huta, zai kashe ni."
ya rungume ta yana cewa
"Sorry Beauty kin kusa saura kad'an ki haihu."
ido ta matse da karfi ta ce
"Tun d'azu haka kake ta fad'a kuma haihuwar yaki, wayyo Allah Ammie na zan mutu."
da sauri ya dad'a rungumo ta yana shafa bayanta.
haka sukayi ta yi,
idan abun ya motsa ya rungume abarsa suyi ta salati da addu'o'i idan ya d'an lafa mata ya d'auke ta da cikin yayi mata rukon jarirai.
sai wajen karfe 12 na dare nakuda mai gaf-gaf ya zo a hanzarce ya shige da ita,
d'akin da ya mai dashi gurin kula da lafiyar ta dana cikin.
ai kuwa ko minti biyar basuyi da shiga ba ta suntulo katuwar jaririyarta.
zokaga murna gurin sa ya had'e ta da jaririyar ya rungume su.
dole sai da yayi mata d'in ki dan ta karu sabo da girmar 'yar.
ya gyara ta ya gyara jaririyar su, ya shiryata cikin kaya masu kyau da tsada.
ya gyara gurin sannan ya kamata ya kai ta bayi yana ta masa sannu cike da tausayawa dan ta galabaita, ya mata wanka da ruwa mai d'umi ba mai zafi sosai ba dai-dai kima.
a d'auke ta ya kai ta d'akinsa ya dawo ya d'au jaririyar, da take ta musu-musu tana niman tura hanu a baki.
yana ta kallon yarinyar cikin wani irin so da kauna.
Feeryal na kwance jiki ya yi laushi.
ya yi mata alluran da zasu taimakawa jikinta, da kuka akayi allurar ya bata tea mai kauri tad'an sha, ta koma ta kwanta ba jimawa bacci ya yi gaba da ita.
ranar Abdulrahim bai rumtsa ba ya saka Feeryal a gaba yana aikin kallonta, yana kuma runmuge da kyakkyawar katuwar 'yarsa girmar 'yar bazakace yau aka haife ta ba.
Washegari da asuba a gida ya yi sallah, bai fita masallaci ba yana idar da addu'o'in sa,
ya dawo bakin gadon da ita da 'yarta suna bacci cikin kwanciyar hankali.
ya kwanta a gefen su ya ya rungumo su duka a haka shima wani bacci mai matukar dad'i ya d'auke sa.
11 jaririyar ta farka tayi kuka ta farkar da su duka.
ya mike da sauri ya d'auke ta yana jijjigata.
Feeryal ta mike zaune tana kwab'e fuska.
wani kayataccen murmushi ya bita da shi yana fad'in
"Beauty akwai in da yake miki ciwo."
kai ta girgiza tana turo lips d'in ta gaba.
murmushin ya kuma ya matso kusa da ita sosai ya rungumeta ta gefe,
ya ce
"See Beauty kama da ni tayi, hasken kuma naki."
tsintar kanta tayi da sakin murmushi har hakoran ta suka bayyana ta kwantar da kanta jikin kafad'ar sa, idanunta akan yarinyar da take ta juya kai tana bud'e baki,
yatsarta ta d'aura kan kumatun 'yar ta ce
"Wannan fa?."
gira ya d'aga mata ya ce
"Oh dimple naki."
murmushi duk sukayi.
"Mu gani ko nonon ya kawo ruwa yunwa take ji."
dad'a shigewa jikin sa tayi tace
"A bata tea ta sha."
ido ya waro ya ce
"Tea ai ko ruwa bazata sha ba daga nan har 6mon bare tea."
ya janyo wayarsa ya kira lambar Hajiya, Hajiya ta d'aga da sallama.
tana cewa
"Abokin turawa kun tashi lafiya."
ya ce "Lafiya lau Beauty ta haihu."
Hajiya tayi kambara ta ce
"Yanzu haka to gani zuwa."
Goggo Bishira da ke kusa da ita ta ce
"Ikon Allah wlh yarinyar nan tana raina tun jiya nake ta ganin alamun haihuwa tare da ita."
Hajiya tayi waje da sauri tana fad'in
"Je ki gaya wa iyayen su."
Gefen sa Hajiya ta shiga tana kwad'a sallama.
ya fito ya tsaya daga can sama ya ce ta hauro.
Hajiya ta ce
"Yoo a sama ka barta take nakudar, ni ina zan iya sintiri a sama kamar tsuntsuwa,
gwuiwa na ciwo."
da kyar ta haura tabi bayan sa da sauri suka shige d'akin tana fad'in
"Ikon Allah madadin ka fad'a tun d'azu a nemo magani a tafa mata na nakuda."
shiru Hajiya tayi da maganar ganin Feeryal zaune cikin nutsuwarta,
jaririyar ta na kwance a gefen ta.
Hajiya ta rike baki tana fad'in
"Aa wai dama har anyi haihuwar ne, ni sai naji kamar kace zata haihu,
ikon Allah."
ya ce
"Tun jiya ta haihu mace da daddare."
Hajiya ta kuma rike baki
ta karaso bakin gadon tana fad'in
"Au haihuwar tun jiya har azahar ta kusa sai yanzu muke sani,
lallai an gaisheka Abokin turawa,
bazaka kira azo a taimaka maka maka da wani abun ba,
ai ko d'an itacen rage saukin nakudar nan za'a girko a bata, sannu kinji 'yar nan."
baki ya tab'e jin wai itacen nakuda.
Hajiya ta d'au yarinyar tana fad'in
"Masha'allah wannan katuwar haihuwar jiya, kai sannu kin ji Feeryal sannu da kokari duk wannan 'yar ke kika iya haifa
ikon Allah ga yarrinya tubar kallah,
yoo taso muje d'akin ki ka barta anan, in ba rowar ganin su zakayi wa mutane ba,
wannan hawa da saukar ai sai kai."
Hajiya ta gyara rukon yarinyar tayi waje.
ya kamo ta suka bi bayan Hajiya yana rungume da ita ta gefe.
suna shiga gefen ta suka tadda Mommy da Aunty Ammah Mom da kannen sa duka a cikin parlour'n.
bai sake ta ba yana tallafe da ita har suka shige bedroom d'in ta.
su Ameerah suka rufu a kan Hajiya suna rige gigen karb'ar 'yar.
Hajiya ta ce
"Duk ki tsaya bari tayi wanka tukun."
yana fita su Aunty suka shige d'akin nata.
har ya kai bakin kofa ya dawo ya leko d'akin yana fad'in
"Hajiya kar a bata ruwa ko wani iri ne."
Hajiya ta rike hab'a ta ce
"Yoo jimin d'a, nifa banson wannan karyan turawan nan, da kai da kasha ruwan me ya kashe ka, ba gaka nan digirgir da lafiyar ka ba, a rika zaluntar yara suna jin kishi a hanasu ruwa."
"Please Hajiya kar a bata."
ya fad'a tare da juyawa.
Goggo Bishira tayi murmushi ta ce
"Baza'a bata ba Abdulrahim."
Aunty ma murmushin tayi tana girgiza kai.......!
Duk suka cika da mamakin jin tun jiya da 12 na dare ta haihu.
ya karb'i haihuwar ya yi komai da kansa.
bai sanar ba kuma har sai da rana tayi.
suka rika yi masa sannu suna yaba mata da kokarin haifo katuwar 'ya haka.
Hajiya tasa Goggo Bishira taje ta d'auko gabaruwa da lalle, tazo ta saka cikin babban tukunya ta zuba ruwa ta d'aura kan gas.
ana ta hira
Mommy tayi shiru tana ta sakar zuci
"Ina zai gayawa wani tana nakuda yana gudun kada wannan karon ma na kuma kashe masa 'ya, kauco na hakika ni Halima nayi asara, na kashe jikokina maza biyu da hannunan."
lura da halin da Mommy ta shiga Aunty ta miko mata jaririyar tana cewa
"Karb'e ta Mommy'n Ameerah wannan zata karya min hannu."
murmushi Mommy ta yi tana b'oye yanayin da ta shiga ta karb'e ta tana fad'in
"Ai Feeryal ta sha fama wajen d'aukarta a cikin ta, gashi sai karkata baki take wannan za'ayi acici a nan."
Ammah ta ce
"Ai kuwa dai ga baban ta ya hana a bata ruwa, idan maman tayi wanka tasha tea mai zafi, zata sami ruwan nono akan kari."
Hajiya ta fito daga bayi rike da bawun da ruwan wankan jaririyar ciki tana fad'in
"To taso Fatima kije ki wa mai jegon wanka, ga ruwa na had'a a bayi,
Bishira je ki juyo gabaruwan ya rika shan iska kafin a gama mata wankan, sai ki sa ta shiga."
Aunty ta dubi Feeryal tun d'azu take like a jikinta ta ce
"Taso muje kiyi wanka."
Aunty na mikewa kiran Abdulrahim na shigowa wayar Hajiya,
Hajiya ta d'aga tana kwad'a masa sallama, daga cikin wayar ya ce
"Yau wa Hajiya na mance ban gaya miki ba, karfa kuyi wa Beauty wanka da ruwan zafi sosai."
Hajiya ta ce
"Yoo ai ba ni zaka gaya min ba sai ka gayawa iyayen ka, kai tun kan a haifi uwan ka da ubanka nake karb'ar haihuwa,
kai zaka gwada min yadda ake wankan jego, yanzu zan tura Ajimi ma yaje ya ballo min dalbejiya, in dai so ake tayi kwari kuwa dole sai an bigi jikinta da ruwan zafi."
Hajiya ta kashe wayar tana cewa
"Jimin d'an nan ka rika sakowa mutane bidi'a cikin lamari."
Ammah ta yi dariya ta ce
"Hajiya kin san fa yanzu sai a hankali cututtuka sunyi yawa,
shi likita ne yafi mu sanin me yasa ya ce hakan,
a dai bi abun da ya ce d'in."
Hajiya ta soma mita
"Mu da da akayi mana mun mutu ne, yara da kalen fitina."
Aunty dai batayi magana ba taja Feeryal sukayi cikin bayi,
ta kara ruwan sanyi cikin ruwan zafin da Hajiya ta tara cikin bathtub.
tayi mata wanka sosai sannan ta sata ta shiga ruwan gabaruwa da lallen da Goggo Bishira ta dafa.
koda suka fito daga bayin
Mommy bata d'akin,
dan tun shigar su bayi ta fita a d'akin a matsayin ta na suruka.
Ammah ce ta shirya jaririyar bayan Hajiya ta mata wanka.
Feeryal na gama shiri, Aunty ta had'a mata tea mai kauri ta sha.
sai a lokacin Hajiya tabar su Ameerah suka shigo, dan ta koresu duka ta ce suyi waje sai an gama kafin su