Showing 60001 words to 63000 words out of 86085 words
Chapter 21 - FEERYAL Part 3 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt
ta tayi shiru dan kanta, tamike tana share hawaye da turo baki, ganin Ammie'n ta bata biyota ba bare ta zo ta rarrashe ta kamar yadda ta saba.
ta fito parlour tana kumbura a dole tayi fushi ba'a zo an rarrasheta ba.
Aunty ta bi da ido har ta karaso ta zauna can gefe tana kuma kumbura baki tana jan hanci.
"Je ki sako abinci ki ci."
cewar Aunty tana duban ta.
"Na koshi."
ta fad'a a shagwab'e.
tana kuma tura baki ganin har ta fito Aunty bata tambaye ta me ya same ta ba.
Aunty ta girgiza kai tana mai da idanunta kan TV.
Feeryal ta cika fam Aunty tana kallon ta da witsiyar ido.
wayan ta ne yayi ring ganin Miemie ce,
kamar bazata d'aga ba har ya kusa yankewa kafin ta d'aga.
Miemie ta ce
"Feeryal bai barki ba ko? gashi TJ ya ce sai kin zo da kanki kafin ya bada d'inkin ki,
kin san halin sa sai yace wai so yake ya ganki bazai bawa kowa ba."
"Zan zo ina ruwan shi da ni da zai hanani zuwa."
ta kashe wayar.
Aunty ta mike tashige kitchen tana girgiza kai da yin murmushin da ita tasan manufarsa.
Aunty na shiga kitchen ta mike ta nufi kofa ta fita.
Tana fita tanufi babban get masu gadi suka bud'e mata karamar kofa ta fita.
a hankali take takawa eriyan shiru babu kowa.
wani ta hango yana tsaye da waya a kunnen sa, yana ganin ta ya soma tako wa in da take.
"Sannu 'yammata."
ya fad'a san da ya iso in da take.
ta kalle shi tana kawar da kanta ita ma tace masa sannu.
"Am na ce ba ko taxi kike nima ne?."
kamar bazata amsashi ba sai kuma ta ce
"Eh."
ya ce "Okay ni ma taxi nake jira amma kinsan unguwa kamar wannan taxi basu fiye shigowa ba, kowa zaki ganshi a motar gida ne ya ke zuwa, ni ma na kawo ziyara ne so motata kuma ta d'an sami matsala, dole a taxi zan koma,
amma yanzu nayi waya da wani direban taxi ya ce min yana kusa da nan zai iso yanzu, mu d'an jira ya karaso, amma ina zaki je ne ke?."
ta ce
"TJ plaza kan titin gaba in zaka shigowa wannan titin."
ya ce
"Okay nan kusa ma zakije, yanzu taxi zai iso,
am na ce amma ke ba 'yar Alhaji Abubakar AA FIYA ba ne."
juyowa tayi ta kalle shi sai kuma ta kuma kawar da kanta."
"Yi hakuri fa na fiya dambaya ko, naga bakiyi kama da 'yan gidan bane, ko ke 'yar matar sa da akace ya auro ta daga wata kasace, dan kin fi kama da 'yan ta can kasashen labarabawan nan."
batayi magana ba tana jinsa.
ya danna waya ya kai kunnen sa yana cewa
"Kayi sauri mana dan Allah muna jiranka, gashi ka sami karin fasinja."
yana sauke wayar taxi tana shigowa titin, koda motar ya karaso mutane biyu ta gani cikin motar,
d'aya a baya sai direba a gaba.
mutumin da suke tare da shi ya zaga ya shiga gaba yana fad'in, "Shiga da sauri muje kinga ya d'auko fasinja."
ta bud'e gidan baya ta shiga a hankali tana rufa kofar yaja motar da gudu.
shiru tayi a hankali zuciyarta yana d'an harbawa.
sosai motan ke sharara gudu, ganin sun kusa da plazan da zata sauka ta ce
"A TJ plaza zan sauka."
suna zuwa dai-dai gurin ganin bai sa alamun tsayuwa ba tayi saurin cewa
"A nan zan sauka."
babu wan da ya kula ta sai kara gudun motar da akayi.
da karfi ta ce
"Direba na ce ma can zan sauka, ka tsaya na sauka ana."
da sauri ta had'e maganar ganin na gefen ta ya ciro bindiga ya nuna mata.
zabura tayi ta matsa gefe tare da fasa kara tana toshe bakin ta.
tsawa ya buga mata ya ce
"Idan kika mana ihu sai na fasa kanki anan rufa baki!."
zabura ta kuma tana dad'a toshe bakinta da tafin hannunta jikin ta na rawa.
"Yi sauri muje kara gudu."
cewar na gaban wanda suka shiga mota tare da ita.
shi kuma d'aya na bayan wanda suke tare da ita ya d'aure mata fuska da bakin kyalle.
sannan ya kwace wayar hannunta ya kashe ya tura a aljuhun sa.
Feeryal jikinta na kakkarwa sosai, sabar yanda ta firgita ruwan hawaye ya d'auke a idanunta.
sosai suka tafi suka fita wajen gari sosai.
kafin taji alamun motar ta tsaya, suka sauko suka fito da ita.
suka jata zuwa bayan wani katon dutse da ciyayi sosai a gurin.
sai da suka shige da ita mab'oyar, kafin suka bud'e mata fuska.
Feeryal ta razana da inda ta ganta, gaban wani katon mutum mai katon tumbi, yana zaune a kasa kafadunsa a mike ya aje katon ciki gaba.
wasu kattin biyu na tsaye a kansa,
dukansu da shi suna hura sigari.
ga kuma mutane ukun da suka taho da ita suma suna tsaye.
ogon nasu dake tule a kasa ya ce
"Kai wannan zazzafar fa ita kuka samo, gaskiya wanan mutumin ya iya haihuwa ga dukiya ga kyakyawan 'ya'ya gaskiya nera tayi,
wannan ba karamin hutawa zakayi da ita ba, matso nan yarinya matso."
ta kuma zabura tayi baya tana girgiza masa kai, cike da mugun tsoro.
"Ke ba ance ki matso nan ba!."
d'aya daga cikin munen ya fad'a yana kokarin cafkota.
"Aa rabu da ita yau ai muna tare."
"Gaskiya oga zazzafa ce idan ka more, ni zan biyo baya kai gaskiya wannan taji kayan had'i."
cewar d'aya daga cikin wanda suke tsaye suna ta bushe bushen hayaki.
suna ta binta da mayataccen kallo.
A b'angaren su Miemie kuwa har suka gama zaman su basuga ta zo ba, TJ ya basu d'inkin su har da nata suka juyo gida.
sashin Aunty suka shige suna kiran Feeryal, Aunty ta fito tana fad'in
."Ku duba ta a d'aki tana ciki."
suka shiga bata nan, har bayi Miemie ta leka bata nan.
suka fito suna gayawa Aunty bata ciki.
Aunty ta ce
"To ina tayi."
kamar da wasa ta gwada number taji shi a kashe......!
Kamar da wasa fa aka nimi Feeryal aka rasa,
hankalin Aunty ya yi masifar ta shi,
Daddy ma haka.
da karfe 5 Abdulrahim ya dawo daga asibiti.
yana shiga yako kowa a tsaye a kan kafarsa, Daddy yanq rike da waya yana ta kai kawo.
ya kashe mota ya fito tun kafin ya karaso in da suke Hajiya take fad'in
"Gara da Allah yasa ka dawo Abokinn turawa, wasu maysiyata sun sace wannan yarin ya Feeryal, tun safe ake niman ta ashe d'auke ta sukayi sai yanzu suka kira Abubakar suke gaya masa, sunyi garkuwa da ita."
wani irin bugawa kirjinsa yayi da karfi,
har sai da yakai hannu ya dafe dai-dai saitin zuciyar sa, a hankali ya furta "Beuaty!."
Hajiya ta ce
"Eh ita bity sun sace ta."
Daddy ya dube sa yana fad'in
"Sun kirani sanar wa kawai sukayi min na san da sun d'auke ta, amma basu fad'i bukatar su ba,
ina shirin tambayar su suka kashe wayar, da sun fad'a ko nawa ne sai a basu yanzu a karb'o ta."
Daddy bai rufa baki ba wayar Abdulrahim yayi ring ya d'ago wayar b'oyayyiyar number ce,
da sauri yayi picking call d'in ya kai kunnen nan sa.
"Dr AA FIYA maraba da dawowa muna shirin sanar maka, sai tsofin ka suka riga mu, kasami labarin yadda ya dace ko mu kara yi ma bayani."
rike wayar yayi da karfi zuciyar sa yana tafarfasa.
cikin fusatacciyar murya ya ce
"Nawa kuke bukata? ku sako ta kada wani abu ya same ta!."
dariya aka kece da shi
"Hahaha tun da wuri haka yau dai da ita zamu kwana, wannan laushin jikin da kyan sura ai dole mu d'ana,
to meye na fusatar kai da ba matar ka bace yanzu,
amma fa kayi asarar had'ad'd'iyar mace, tun da bakayi mu bari mu d'an more,
ka saurare mu gobe zamu sanar maka."
da karfi cikin hargagi ya ce
"Wallahi! idan kuka tab'a ta sai na kashe ku zan yi muku kisan wulakanci!."
kashe wayar akayi muryoyi da yawa suna dariya.
Ya ciro wayar ya buga shi da kasa, yana wani irin huci.
Mommy ta ce
"Abdulrahim ka nutsu dan Allah, kana yi musu irin wanan barazanar ai sai suki fad'in nawa suke bukata, suyi ta jan rai suki sakin ta,
a bisu a hankali yadda zasu fad'a da wuri a kai musu a karb'o ta."
ya juya a fusace yana taka kasa da karfi, ya shige mota.
Daddy ya biyo shi da sauri yana cewa
"Kar kaje kace zaka sanar wa hukuma, sai da sukayi min gargad'i a barsu a gani daga nan zuwa gobe."
ina kunnuwan sa sun toshe baya ma jin Daddy ya fige motar a guje kamar zai tashi sama.
a d'ari security suka bud'e mata get suka dare dan kad'an ya rage yayi ciki da su.
Ajmaal ya tatta wayar da tayi fisis.
Jikin kowa yayi sanyi Aunty kam sai hawaye, da ambaton sunan Allah.
wani kira ne ya shigo wayar Daddy, Ajmaal Zaraddin Shamsuddin Faisal suka dad'a matsowa kusa da shi duk zukatan su na d'ar-d'ar.
Daddy ya d'aga kiran yasa a handsfree daga cikin wayar aka ce.
"Ka gaya wa d'an ka gada yayi gigin sanarwa hukuma, ko ya ce zai ne mo mu, idan yayi d'aya cikin biyun nan zamu kasheta bayan mun gama abun da zamuyi da ita."
d'ip aka kashe kiran.
Mommy da Hajiya da Ammah sukayi salati.
Hajiya ta ce "Amma wad'an nan ba imani, Abubakar maza ka kirawo Abokin turawa ya dawo kada ya aikata abun da zai sa su kashe ta."
Abbieh da Dad suka d'aga waya suna rige-rigen kiran shi.
Ameerah Miemie Sumayya sai kuka.
Bilkisu Saddiqa Rahma Sahla ma sunyi jigum cike da jimami.
Abbieh da nashi wayar ya fara shiga ya yi ta ring bai d'aga ba.
ya kira yakai sau goma baya d'aga wa.
Ganin magriba ya karato Daddy ya ce kowa yaje ya yi sallah, a roki Allah.
Aunty tana sallah tana kuka, bayan tayi addu'a ta mike tsaye da kafafunta tana jiran shigowar Daddy.
Aunty ta kira Abba'n Abuja ta sanar masa,
hankalin su ya tashi matuka,
Abba ya ce
"Ko nawa suke bukata su fad'a za'a basu, zan bi jirgin karfe 6 na safe insha'allah zan shigo gobe."
jiki a sanyaye Aunty ta ce "To Allah ya kaimu."
har sai da akayi isha tana kan sallaya Daddy ya shigo.
tana ganin shi ta mike tana fad'in
"Daddy sun kuma kira sun fad'i nawa suke so? Abba ma ya ce zai zo gobe."
ya ce "Munyi waya da shi yanzu yace min zai gobe,
har yanzu basu kara kira ba amma Abdulrahim ya dawo yanzu, ya ce bai sanar wa hukuma ba,
dole yanzu mu jira su sake kira su fad'i in da za'a kai musu kud'in, da adadin kud'in da suke bukata."
Aunty ta zauna bakin gado jiki ba kwari tana fad'in
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un, ya Allah ka tsare ta kar ya barsu su cutar da ita."
hawaye ya zubo mata ta share.
Daddy ya fita yana amsa waya.
Yana tsaye a can saman upstairs yana rike da mug, dare ya tsala gidan yayi shiru amma hasken wuta ta ko ina tamkar rana.
kallo d'aya zakayi masa ka fahimci tsagwaran b'acin rai mai garwaye da damuwa.
a hankali yakai mug d'in bakin sa ya kurb'i sudan tea d'in ciki, kana ya saki mug d'in ya fad'o kasa ya tarwatse.
mai gadin dide d'in sa ya zabura daga gyangyad'in da yake kan kujera, jin karar fashewar abu.
ya d'aga kai da sauri ya hango sa tsaye daga can sama.
ogansa bai kwanta bacci lallai wad'an da sukayi garkuwa da ita basa da imani.
abun da mai gadin yayi ta fad'a cikin ransa ke nan.
Washegari da asuba bayan an idar da sallah.
duk mazan gidan suna masallaci.
malamai da yawa cikin masallacin Daddy yasa anata karatun kur'ani.
karfe 6 da 'yan mintuna Abban'an Abuja ya iso aka yi masa jagora cikin masallaci.
ana cikin gaisawa wayan Abdulrahim yayi kara, duk aka juyo gare sa.
Daddy ya ce
"Sune ko?."
"Su ne." ya fad'a yana d'aga kiran ya kai wayar kunnensa ba tare da yayi magana ba.
daga cikin wayar muryar da jiya ya masa magana shi ya sinkoayo shi yana fad'in
"Kamar fa tsoron barazanar da ka mana naji, yara sun so more kayan alatun nan na hana su, nima kuma ban tab'a ba,
amma mun barta tasha sanyi dan a tantagaryar kasa ta kwana sanyi na bugata."
ido ya rumtse ya bud'e sanda yaci gaba da fad'in
"Kasa a handsfree dan nasan tsoffin attajiran nan suna gurin."
a hankali ya zaro wayar yayi kamar yadda suka bukata.
"Idan kun shirya karb'arta ga abun da muke bukata,
muna bukatar billion d'ari biyar, daga nan zuwa yammacin rana, idan ba'a kawo mana ba zamu kashe ta bayan ko wannen mu ya mata fyad'a."
da sauri Abbieh ya ce
"Haba ku d'an rage mana billion d'ari biyar ai yayi yawa, kuyi hakuri ku dai fad'i dai-dai kima."
"Lale marhabin da zuwa Alhaji Tahir Abbas, lallai kuna ji da yarinyar nan tun da takanas babban bako ya taso daga Abuja ya zo Legos akan b'atar ta,
baza mu rage ko sisiba,
acikin ku waye bashi da fin kud'un da muka ambata,
Alhaji Tahir Abbas Alhaji Abubakar AA FIYA, Dr AA FIYA idan kun shirya zamu gaya muku inda zaku kawo kud'in ku karb'e ta,
idan ya wuce yammacin yau to tabbas zamu aikata abun da muka fad'a."
"Ina za'a kai muku!."
ya fad'a zuciya na tafarfasa.
"Da kyau mana Dr AA FIYA ka dakace mu zamu fad'a ma in da zaka kai, ka shirya kud'in."
suna kaiwa nan suka kashe wayar.
ya yi wani irin mikewa zuciya na tafarfasa.
Abba'n Abuja ya ce
"Ka dakata kafin banki su fito sai muje a cire musu kud'in."
Daddy ya ce
"Aa Alhaji ni zan bada kud'in, bari na rubuta check sai yaje ya karb'arba a banki."
"No akwai kud'i a kasa."
ya fad'a yana fita daga masallacin da sauri, suka bi bayan sa da kallo.
Da misalin karfe 2 na rana yana zaune cikin mota kirar Jeep Wrangler mai bakar gilashi, waya a rike a hannunsa yana sauraran kiran su, dan sun tabbatar masa da karfe 2 zasu kirashi ya kawo musu.
biyu da minni 3 kiransu ya shigo wayar sa, suka kwatanta masa in da zai je sannan suka ce kada ya sake ya zo da hukuma, sun rantse idan ya sab'a musu sai sun kashe ta.
"Ina mai tabbatar maka zamu kasheta bayan mun mata fyad'e kaca-kaca mun more wannan kyakkyawan surar, sai mun kasheta! idan kace zakayi mana wata dabarar."
ya d'auke ta da mari Feeryal ta fasa kara.
da karfi ya rumtse idanunsa karar marin da ihun ta yaki gushewa cikin kwakwalwa da kunnuwan sa.
ya bud'e rinannun idanuwan sa san da aka ci gaba da fad'in
"Fuska mai laushi kamar auduga wannan jiki a kwai dad'in tab'awa, idan ka b'ata lokaci komai zai iya faruwa dan ba karya wannan halitta na fisgata,
wata kila idan ka jinkirta ka samu na kwakule ta, idan ka dad'a b'ata lokaci yara su kwakule suma."
"Kaiii! ga kud'i na shirya maka cikin mota narantse idan kuka tab'a ta dukkanin ku bazan kyale ku ba, sai kun d'and'ani mutuwa!."
"Hahaha da kyau mana nafahimci tafasar zuciyar ka a kanta,
idan ka canza shirin abun da zai faru ke nan."
d'ip aka kashe wayar.
wani irin figar motar ya yi tamkar zai lula sararin samani ya.
Cikin kankanin lokaci ya kawo shi in da suka kwatan ta masa.
yana tsayuwa kira ya shigo wayarsa.
suka kuma fad'a masa ta in da zai bi, yakuma jan motar zuwa gurin.
sau uku suna fad'a masa ta in da zai bi, bayan ya iso in da suke bukata suka ce ya dakata a gurin.
"Ka fita a motar ta koma mashigar ka ta biyu ka jira a gurin za'a kawo maka ita,
dan har da motar muke bukata."
d'an jim yayi yana latsa computer motar, ya d'au wayoyin sa ya fita kamar yadda suka bukata, ya taka har mashigar da ya shigo na biyu ya tsaya a gurin.
suka ce ya baiwa in da yake kalla baya, ba musu ya juya bayan sa.
yana juyawa wayar hannunsa tayi dirrr yad'an matse wayar, yana daidaita tsayuwar sa.
Biyu daga cikin su suka fito daga mab'oyar su, d'aya na rike da bindiga,
suka zo gurin motar suna waige waige, mai bindigar ya bud'e motar yana saita bindigar cikin motar.
d'ayan da ba bingida a hannunsa ya shiga motar yana bud'e kwalayen da ya shirya kud'ad'en ciki, ya cika motar da su.
duk ya bubbud'e su yana zuba su har kasa.
kud'ad'e ne har kasa suka jinjinawa junan su, sannan suka koma mab'uyar su suka fito su da sauran 'yan uwan nasu da ita.
daga can mab'uyar su suka turo ta, suka ce ta mike nan.
kanta ba d'an kwali kafa ba takalmi tasa gudu tana waigen ganin ko zasu biyo ta.
gudu sosai ta ke tana haki, har ta b'ullo in da yake tsaye.
baya tayi da sauri tare da dafe kirji ta fasa kara tana toshe bakin ta, zaton ta su ne dan bayan sa ta gani.
da sauri ya juyo yana binta da kallo tare da mata alama da hannu tazo.
ta taho da gudu ta rungune shi, tare da fashewa da kuka.
hannun sa ya saka ya zagaye ta da shi yana dad'a matseta a jikinsa.
a hankali yayi sama da d'aya hannunsa,
yana shafa gashin kanta da yake baje a bayan ta.
yayin da idanunsa ke dad'a canza kala b'acin rai karar a kan fuskarsa, yana dad'a mannata da kijinsa, ya yin da zuciyar sa ke harbawa.
Da sauri da gudu-gudu suka karasa gurin motar,
in da direban taxi ya fito da taxi a inda suka b'oye sa, mutum hud'u suka shiga taxi mutum biyu kuma suka shiga mator da yazo da shi.
suna shirin barin gurin suka jiyo karar helicopter daga sama yana yin kasa-kasa aka fara bud'e musu wuta.
karar harbin ya sata birkicewa a kid'ime ta kankame shi, tana b'oye fuskarta a jikinsa.
ya dad'a rungume ta sosai.
Basuyi sammanin zuwan hukuma ba, a d'ari kowa ya fara niman mafaka,
wanda tuni hukuma suka cim musu, sojoji suka bi igiya suka duro kasa, ganin zasu halaka sukayi saranda duka miko kai aka kamasu da hannu.
sai da harbin ya lafa kafin ya curota a kirjinsa sai san nan ya fahimci ta suma bata numfashi.
cak ya d'agota kamar jaririya, ya nufi in da motar sa yake.
wanda tuni jami'an tsoron sun tura marayin cikin jirgin helicopter wasu jami'an kuma suka shiga taxi.
a gaba gefen mai zaman banza ya ajiye ta saboda bayan aciki yake tun daga but har bar tsakiyar da kud'i.
ya shiga ya mazaunin direba da sauri ya kwanto ta a jikinsa.
a kusan tare suka bar gurin da hukumar.
Ba AA FIYA STREET yayi da ita ko asibiti ba, wani gidan sa dake wata unguwa ya tafi da ita.
yana isa mai gadi ya bud'e masa,
babban gida ne mai kyau da tsari.
a farfajiyar gidan ya kashe motar ya ciccib'o ta yayi ciki da ita,
bai dire ta ko ina ba sai wani kayataccen bedroom na musamman.
ya wuce bathroom kai tsaye, a kyakkyawan bathtub mai kyau da tsari ya dire ta ciki,
ya kunna ruwa mai