Showing 21001 words to 24000 words out of 86085 words

Chapter 8 - FEERYAL Part 3 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt

ta,
ta zura takalmi mara tudu sosai.
ta d'an feshe jikin ta da turare ba masu karfi ba.
kana ta d'au handbag da wayan ta fita..

Tana fita ta hangoshi yana fito daga gefen sa,
tana kokarin wucewa yayi mata alama da hannu ta koma ciki.
tsayuwa tayi kamar zatayi kuka, takuma duban shi ya tsare ta da ido, fuskarsa bawasa.
kasa tayi da kanta tana jin hawaye na taruwa mata, sai dai ta kasa iya kuma kallon sa.
a hankali ta juya ta koma ciki ta fad'a saman bed.

Sai da yaga shigewar ta kafin ya fita.
motoci nata fita da mutane yawanci a daren zasu wuce, dan daga gurin dinner ango da amarya zasu wuce Jos da wasu daga cikin 'yan biki da yawa.
dan akwai wani gaggarumin shagalin da za'a gudanar a washegari a can Jos d'in.
tuni anyi bukin jiri na jiran su 11:30 zasu tashi, shi yasa 11 za'a tashi a gun dinner.
Daddy da ya fito daga side d'in Aunty ya tsaya suna sallama da wasu 'yan'uwan shi.
Abdulrahim ya karaso gurin san da motar ba'in ya tashi.
Daddy ya dube shi tare da amsa gaisuwar da yake masa,
ya ce
"Ina Feeryal ga 'yan'uwan ta nan duk kowa yafita za'a tafi."
shiru ya yi baiyi magana ba
Daddy yakuma duban sa tare da karantar sa kana ya ce
"Idan kai bazakaje ba, to ita kabarta taje, akan me yasa zaka hanata, wata kila tasa ranta tana son zuwa."
nan ma baiyi magana ba sai nad'e hannayensa da yayi a kirji.

A b'angeren Feeryal wayanta tajanyo tana share d'an guntun kwallan da suka zubo mata.
ta danna numman Aunty, tana d'agawa cikin muryar shagwab'a ta ce
"Ammie Sahab ya hanani zuwa."
da sauri Aunty ta ce
"Ban amince kiyi gardama ba ki zauna, ban sanki da kafiya ba kar naji kinyi masa gardama"
baki ta cuno ta sauke wayar.
itafa ba gun biki take son zuwa ba so take tasamu ta fita taje b'angaren Ammien nata..
da sauri ta kalli kofa jin an turo kofar.
daga bakin kofar ya tsaya ya ce
"Ki tashi ki sa hijab kije."
aiko bai rufa baki ba ta mike.
ya tab'e baki yajuya.
babban hijabin sallar ta ta zura tayi waje.

Yana tsaye daga sama yana hango cikin gidan.
motoci duk sun gama tafiya.
akan idon sa ta shige sashin Aunty.


Aunty ta bud'e baki cike da mamakin ganin ta ta ce
"Ke Feeryal bana ce kar ki fito ba."
"Ammie shi yace naje."
"Feeryal yaushe kika koyi karya?."
"Allah Ammie da gaske Sahab shi ya ce nasa hijab naje."
Aunty tayi shiru tana nazartar ta kana ta ce
"To me ya hanaki binsu Miemie ku tafi kika zo nan?."
zama tayi kan kujera tana cewa
"Nifa dama Ammie ba zuwa zanyi ba ni bazan je gurin dinner ba."
"Ai ko sai ki tashi ki koma d'akin ki, tun da ba tafiya zakiyi ba."
"Ayya Ammie kibari sai anjima, idan suka dawo sai na koma, nima nayi dinner na anan."
tayi maganar tana cire hijab d'in.
Aunty tayi murmushi tana girgiza kai....karfe goma nayi tace ta tashi ta tafi dare ya yi.
Feeryal ta shagwab'e fuska,
"Ammie kaina ciwo yake min kuma ina jin yunwa."
Aunty ta ce
"To tashi maza mijin ki likita, shi yasan maganin da ya dace ya baki,
fad'a min dai yanzu me kike son ci, sai na dafa na baiwa Baba Rabi ta kawo miki yanzu,
gobe idan Allah ya kaimu ma ki huta na d'auke miki girkin gobe duka, ni zan dafa nabayar a kawo miki, kinji ko 'yammatan Ammie."
takuma shagwab'ewa tana fad'in
"Faten dankali da kifi kuma zan jira kiyi."
dakyar talallab'ata tace yanzu zatayi tabada akawo mata.
suka fito ta yi mata rakiya har bakin side d'in su sai da taga shigarta kafin ta juyo.

Feeryal na shiga d'aki ta kwab'e hijab tashiga kokarin cire kayan jikinta, dan ba karamin damunta yake ba.
tayi-tayi ta cire ta gagara,
tarika kokawa da rigar kamar zatayi kuka.
da sauri ta shige bathroom jin fitsarin da take ji yana kokarin fitowa, tayi ta fito tacigaba da kokarin cire rigar ga zip d'in rigar can sama kuma yayi tauri sosai.
zama tayi bakin gado tana maida numfashi kamar wacce tayi wani aikin.
ta janyo waya ta dannan number Aunty tana d'agawa ta ce
"Ammie na kasa cire rigar, zanzo ki jamin zip d'in."
Aunty ta ce
"Me ya kaiku yin matsastsen d'in ki, karki fito ai ba ke kad'ai bace a side d'in mijinki na nan sai kije yaja miki, haka kawai kamatse kanka da kanka kahana kanka jan numfashi da kyau."
Aunty ta kashe wayar Feeryal ta kwab'e fuska kamar zatayi kuka.
taya za'ayi ma taje tace yaja mata zip ai gara ta kwanta haka.
ta gyara ta kwanta.
tana sa kafad'arta akan gado taji rigar yana cizon ta, gashi ko numfashi mai dad'i bata iya ja dan bata sama ba sa irin matsastsun kayan nan ba, uwa uba kuma bata iya bacci da kaya masu nauyi ba, in ba sleeping dress ba.
ta mike da sauri ta d'au hijap ta fito.
tana sa kafarta a farfajiyar gidan tajiyo kukan kule, ai da gudu ta koma ciki..
ta haye gado ta kwanta.
ta matse ido tana fatan bacci ya d'auke ta.
amma ina tamkar mistsinin ta ake tacikin kayan,
idan ya manne da jikinta har wani radad'i take ji.
zunbur ta mike tana sosa jikinta idonta sun cika da kwalla.
tana son tafita taje Ammien ta ta taimaka mata tacire rigar, amma tana tunanin mage a waje.
kwalla ta share in har ba kwana zaune take son yi ba to tana bukatar rigar nan yabar jikin ta.
ke nan bata da zab'in da ya wuce taje ya taimaka yazuge mara zip d'in.
kwalla ta share ta d'auki hijab ta saka kana ta fito a hankali tana waige-waige, dan a tsoro take sai gani take kamar zata gamu da magen..

Kofar da ke sakanin gefen ta da nashi, wanda take ganin duk san da zai shigo tanan yake shigowa.
a hankali ta isa jikin kofar ta bud'e jiki a sanyaye.
ido ta zubawa corridor daya bayyana a gana ta, bata tab'a kawo kanta nan ba.
a hankali tabi cikinsa ta taka har zuwa wata kofar da ta gani a can gaba, nan ma ta bud'e a hankali sai da ta d'anyi jim kafin tazura kafafunta ta shige ciki.
wani sassanyan kamshi ne gami da sanyi ya bugeta, har sai da ta d'an kame jikinta ta nad'e hannunta cikin hijab, dan ba kad'an ba sanyin ya rasa fatarta ya zarce har cikin jikinta.
gani tayi ta bayyana cikin wata duniya.
katon parlour mai d'auke da kayan alatu na musamman.
ido ta shiga bazawa cikin katafaren parlour'n.
can ta hango sa zaune saman kujera idanunsa akan system d'in da ke gabansa.
takai 10snd tsaye
kana a hankali tashi d'aga kafarta tana takowa cikin parlour'n.
yayin da take dad'a jin sanyin na kuma shi garta.
tun shigan ta idanunsa a kan abun da yake bai d'ago ba.
a d'an nesa da shi ta tsaya d'an kallon shi tayi kana ta sunkiyar da kanta tana wasa da bakin hijabin ta.
a hankali cikin muryarta mai sanyi ta ce
"Um dan Allah Sahab dama..dama..dama umm."
sai kuma tayi shiru.
a sannu ya d'ago idanunsa ya sauka cikin nata, da sauri ta janye nata idanun takuma yin kasa da kanta.
mai da idanunsa yayi kan laptop d'in.
hannu ta yarfe kana ta ce
"Dama.um dan Allah dama so nake kad'an taimaka kajamin zip..zip d'in riga ta, nakasa cirewa ne, kuma bazan iya bacci da shi ba."
tsai da abun da yake yayi kana ya d'ago, kasa takuma yi da kanta.
5 second idanunsa a kanta, sai kuma ya gyara zamansa ya yi mata alama da hannu ta zo......!



A hankali tashiga d'aga kafarta, ta maso in da yake.
sai kuma taja ta tsaya
kanta a kasa tana wasa da 'yan yatsun ta ta cikin hijab.
"You are waisting my time."
ya fad'a yana gimtse fuska.
a hankali ta juya bayan ta a sannu tad'an ja hijab d'in tayi sama da shi.
ratan da ke sakanin su yakai taku uku, sai noke-noke take takasa jan hijab d'in duka.
gajeren tsaki yaja, yana daga zaune ya mika hannu ya fisgota, razana tayi har sai da wayar ta yafad'i kasa.
ido ta waro jin ta a kan cinyarsa.
gaba d'aya ta firgita tarasa ina zatasa kanta.
shiko ko a jikin ta,
ya tura hannunsa tacikin hijab d'in ta, yana lalub'o ta inda zip d'in yake.
d'aya hannunsa kuma yaja hijab d'in ya haura da shi sama har zuwa kafad'ar ta.
kana ya zuge mata zip d'in.
da sauri ta mike tasaki hijab d'in ya rufe ta, kana ta taka da sauri tabi ta kofar da ta shigo ta fice daga parlour'n nasa.
baki ya tab'e ganin yadda ta wani birkice, ya gyara zamansa ya cigaba da abun da yake.

Tana shiga bedroom d'in ta tasauke numfashi.
sai kuma ta turo baki gaba, ta cire hijab ta shige bathroom.
tana shiga ta cire rigarar tayi wurgi da shi, dan yabata haushi, ta cire underwear da pant ta tara ruwan d'umi cikin bathtub ta shige ciki tasoma wanka.

Ring d'in da ya ji ne yasa shi d'agowa ya kalli in da sautin ke tashi.
wayarta data yasar bata ma san san da ta yasarba shi ke kara a kasa.
mai da hankalin sa ya kuma yi kan system nasa, kiran na yankewa wani kiran yakuma shigowa,
tsaki yaja ya mika hanu a hatsale da zummar d'aukar wayar ya kashe dan nacika masa kunne.
ganin sunan da ke bayyane kan screen d'in wayar, yasashi hakura da abun da yayi niyya.
Ammie'na. sunan dake bayyane kan fuskar wayar ke nan.
kiran ya yanke a take wani yakuma shigowa.
a hankali yakai hannunsa zaiyi picking call d'in sai kuma ya fasa.
ya aje wayar a gefe, kiran na daf da yanke wa ko tunanin me yayi, ya mika hannu ya d'au wayar tare da d'aga kiran,
muryar Aunty ya jiyo tana fad'in
"Ke Feeryal kar ki kuskura ki ce zaki fito a cikin daren nan, ki bari yanzu nakusa gama faten dankalin da kikace kina so, Baba Rabi zata kawo miki sai ta ja miki zip d'in, kin ji abun da na gaya miki ko ki dai na fita bada izinin mijinki ba, ki bar tunanin duk cikin gida ne,
wata kila shi baya so karki rika yin abun da mijin ki baya so, wani irin kifi kike so a sa busasshe ko d'anye?."
a hankali ya zaro wayar ya kashe kana ya mike tsaye, tare da rufe system d'in ya zura takalman sa yanufi gefen ta rike da wayar.

Feeryal ta gogo sabulu a fuskarta tana kokarin wankewa tajiyo kukan mage.
abun da bata sani ba tun fitarta na farko da tajiyo kukan sa, ta gudo ta dawo bata rufe kofar ba ta nan yasami damar shigo wa.
wani irin zabura tayi ta mike tsaye tashiga wanke kumfar sabulun da sauri-sauri jikin ta na b'ari.
a razane ta waro idanunta jin kukan kyanwan nadad'a mosota. ta fita daga cikin bathtub d'in da sauri kad'an yarage ta fad'i, tana kokarin janyo towel kawai taga magen Hajiya yashigo bayin dan data shiga bata rufe glass d'in bathroom d'in bama garin saurin taje tacire rigar, tayi wanka dan ta daina jin kaikayin da take ji.
wani irin ihu ta sake tayi baya batare da ta janyo towel d'in ba, jikin ta na kyarma.
magen kuwa ruwan da ya zuba a kasa yabi yake sha, yana gama sha yaje daf da bakin kofa ta gefe ya kwanta.
Feeryal da gaba d'aya ta firgice tafita hayyacin ta, ihu take sosai tana yarfe hannu da bubbuga kafa a kasa tana fad'in
"Kafita kafita kafita!."

Kalmar daya doki kunnen Abdulrahim ke nan dai-dai sanda yasako kafarsa cikin parlour'n nata.
da sauri ya d'aga kafa yatura kofar bedroom d'in ta da karfi.
jiyo sautin maganar daga cikin bathroom ne, yawani irin d'aga kafa ya iso bakin kofar bathroom d'in da karfi ya tura ya shige ciki.
cikin tafasar jini.
cak yaja yatsaya ganin babu kowa cikin bathroom d'in sai ita kad'ai, sai kuma mage a kwance a gefe.
da sauri yayi kokarin juyawa jin idanunsa ya yi wani irin fizga.
da karfi cikin kid'ima gami da mugun tsoro ta ce
"Sahab dan Allah ka ce yafita bana son shi kafita min da shi."
gaba d'aya ta birkice ta mance a wani irin yanayi take.
sai tsalle take tana nuna masa magen dake kwance a bakin kofar.
ya yin da ilahirin jikinta ke motsawa gami da girgiza ga yanda take tsallen.
nonuwanta da mazaunan ta gaba d'aya motsawa suke, irin motsin da duk wanda ya yi arba da shi, sai yaji kamar zaiyi karamar hauka.
da karfi ya rumtse idanunsa ya yi baya da kafarsa, yana kokarin niman hanyar fita.
dai-dai nan magen ya yi motsi tare da gyara kwanciyar sa, yin kahan da yayi kuwa yad'a firgitata ta tafi ta dugu ta rungume shi tare da sakin kara, ta kankame shi tana fad'in
"Sahaaab kace ya fita."
idanunta ya yi sama
gaba d'aya jikinta yasake tana kokarin sulalewa kasa ya yi saurin tarota ya ruko ta.
yana kallon fuskarta bata cikin hayyacin ta.
ya d'agota cak ya had'e ta da jikin sa.
yana jin kansa kamar zai bud'e.
ya ilahi wlh jin kansa yake kamar bashi ba.
da kyar yashiga fafutukan son dai-dai ta nutsuwar sa, ya shiga jan kafafun sa da suka masa mugun nauyi.
yafito rungume da ita a kirjinsa.
ya isa bakin gado, idanunsa ya rumtse da karfi san da yake kokarin shinfid'a ta akan gadon.
ji yayi ta rirrike rigarsa cikin harhad'a kalmomi murya can kasan makoshi ta ce
"Sahab..karr...kr.. kar ka tafi fi zai..zai zo."
ido ya kurawa lips d'in ta da take motsasu wani irin muguwar kasala ya dad'a ziyartar sa.
ido ya rumtse tare da kokarin janye hannayenta dake rirrike da rigarsa.
sai ji ya yi takuma kankame shi.
da kyar ya iya bud'e idanunsa da suka fara sauya kala a kanta.
ya yi saurin janyo blanket ya rufe mata jiki, yana jin kirjin sa na bugawa da sauri-sauri tamkar zuciyar sa zai faso kirjinsa ya fito.
da sauri ya juya ya d'aga kafa zai bar gurin yaji taruko rigarsa ta baya.
"Sahab kafita da shi bana son mage."
da sauri ya juyo idanunta a lumshe lips d'in ta take motsawa a hankali.
"Sahaaaab! kar ka tafi."
ta kuma fad'i cikin wani irin selling voice.
tana dad'a kankame rigarsa.
numfashi ya sauke gami da furzar da huci, yana jin bugun zuciyar sa na dad'a karuwa.
idanunsa ya maida kan kofar bayin ganin magen nafitowa, sai da yazo tsakiyar dakin ya yi kuka.
wani irin zabura tayi wanda hakan ya yi sana diyyar dawo da ita hayyacin ta dake kokarin barin jikin ta.
ta junkura ta mike ta kuma cakumo shi tarirrike shi da karfi tana b'oye fuskarta cikin kirjin shi.
sam bata ma san awani yanayi take ba, tsoro ya shafe mata iya tuna komai, mafaka kawai ta ke bukata, dan tana ji idan magen ya matso gareta zata iya mutuwa dan tsoro.
a kid'ime take fad'in
"Sahab kar ka barshi yazo ya tab'a min jiki, ka kore shi!."
takuma kankame shi tana danna fuskarta cikin kirjin shi.
yakai 10 seconds kafin ya iya dai-dai ta numfashin sa.
yayin da bugun zuciyar sa ya karu, jin ababen kirjin ta cikin nashi kirjin suna yawo.
ba shiri yayi baya ya jingina da jikin garu..
"Oh My God!."
ya furta a kasan ransa, wan da har sai da lab'b'ansa suka motsa.
tsikar jikin sa ya tashi.
ya yi shiru yana sauraran bugun zuciyar sa.
ita kuwa dad'a shigewa jikin sa take tana b'oye fuskarta cike da zallar tsoron kyanwa, jikin ta na kyarma.
har lokacin bai iya kyakkyawar motsi ba, yana jingine yana sauraran zuciyarsa da bugun sa ke kunkuwa a duk motsawar da zatayi a jikinsa.

A hankali ya d'ago hannayensa ya sauke su a bayan ta ya zagaye ta dasu.
sai da ya lumshe ido jin laushi da taushin jikinta.
a sannu ya ya bud'e idanunsa daya lumshe kan magen da ya ke fita daga d'akin.
yana mai dad'a manna ta da jikinsa.
jin kyanwar ta kuma yin kuka sai dai wannan karon a hankali tayi kukan, amma bai hanata kuma zabura ba.

A hankali ya yi sama da hannunsa ya sauke shi kan sumar kanta mai tsamtsi dake fidda daddad'an kamshi,
yashafo sa a hankali.
kana ya ciro kanta dake cikin kirjinsa ya tallafo kanta yana kallon fuskarta, da idanunta ke a lumshe, a sannu a sanu yake matso da fuskarsa kusa da nata, har ya kawo shi daf da nata.
idanunsa ya lumshe a hankali ya tafi da bakin sa zuwa kan lips d'in ta, ya d'aura lips d'in sa kan nata, kana ya sumbaci lips d'in, tare da cafko nata ya tsotsa ya zarce da harshensa zuwa cikin bakinta.
a tare suka sauke numfashi mai sauti.

Wani irin waro ido Feeryal tayi a kan fuskar shi, jin d'umin bakin sa ya gauraye ilahirin cikin bakinta.
idanunta ta rufe sannan takuma bud'ewa tana son sanin shin bacci take ko ko idanun ta biyu.
ido takuma warewa jin ya dad'a tallafo kanta da kyau yana kissing nata.
ya tafi da hannunsa d'aya a bayan ta yana dad'a mannata a jikinsa.

Tsoro gami da mamaki suka lullub'e ta, juya kanta tayi ta kwace bakinta.
tare da zamewa a jikinsa tayi baya da sauri.
tana binsa da kallon dayafi kama da tuhuma.
a hankali ya bud'e lumsassun idanunsa ya zuba mata.
da sauri ta kalli kanta tayi wani irin zabura tare da calla kara tayi baya da sauri tajanyo bargo ta kare jikinta.
ta durkusa a kasa tana kankame jikinta, tare da rufe idanunta ta kankame shi gam-gam.
wani irin yanayi yake ji yana dad'a shigarsa mara misaltuwa, da kyar ya iya dai-dai tsayuwar sa yana jin wani irin tashin sikar jiki.
a hankali yaja kafasra ya yi waje..
tana jin fitarsa ta zabura ta mike da sauri, ta d'auki towel dake bakin gado ta d'aura a kirjin ta da sauri, gaba d'aya ta kid'ime tama rasa me zatayi.
da sauri ta isa gaban wardrobe ta bud'e ta d'auko sleeping dress.
tana kokarin sawa taji an bud'o kofa.
da sauri ta waigo shi tagani ya mai da kofar ya rufe.
nutsuwa yakau a jikinsa kana iya hango yanayin dake tare da shi, wanda ya sauyashi izuwa wani daban.
saurin sunkuyar da kanta tayi, tana jin wani matsanan ciyar kunya na lullub'e ta.
a hankali yashiga takowa cikin d'akin yakuma kafe ta da ido, duk da kanta na kasa jikin ta na shaida mata tana jin yadda idanun sa yake yawo cikin jikinta, wani sanyi take ji na shigarta tamkar iskar damina ne ke buso ta,
har sai da ta saki kayan baccin kasa ta rungume hannayenta a kirji,
sabar sanyi da taji yawani buso ta.

A hankali ya karaso in da take ya yi daf da ita sosai, wanda hakan yasata jin wani d'umi na shigarta.
a sannu ya mika hannu ya ruko hannayen ta, data rungume su a kirjin.
ya had'e hannayen yarike su duka da hannunsa guda,
kana ya kai d'aya hannunsa ya d'ago

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login