Showing 18001 words to 21000 words out of 86085 words

Chapter 7 - FEERYAL Part 3 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt

da ita, duk ku taru kuyita kumburi kuna cika kuna batsewa kamar kububuwa." Jamal
"Idan ba a suffar aljanun zasu zo ba me zai hana mu iya zama da su, biyayya ga iyaye kuma ai wajibine, haba ki barmu haka mu huta ko mu tafi mu fasa gaisuwar."
"Yo ku tafin mana mai mugun baki, ana fad'i tashi a kanku idan aka barku da aljanun zaku iya ne."
"Me zai hanamu iyawa da su, a barmu da su d'in kawai."
Hajiya ta harare shi tana kai loman nama bakin ta.
Ajmaal ya ce "Ke dai kici namar ki, bama Ya Abdulrahim ya ce ba kowani irin nama zaki rika ci ba, kuma ba kullum zaki rika ci ba, amma kullum duk sanda za'a ganki da kwanon nama a gaban ki."
"Yo in ban da abokin turawa ma ai nama kara lafiya yake."
cewar Hajiya tana kai loman nama bakin ta.
"In ji wa? shi likita ya gaya miki kice ba haka ba."
Ajmaal yayi maganar yana rike hab'a.
Hajiya tace
"Ko d'azu ma sai da nasa Kulu ta kamo min tashar da ake saka shirin, haka matar take cin nama kuma da bakin ta tace nama lafiya yake karawa,
itama likita ne yagaya mata."
"Hajiya in ban da abun ki shirin film gaskiya ne, ai ba komai ne ake fad'ar sa kuma ka samu da gaske ne hakan ba, shirin film ne kawai, gara dai ki kiyaye, kafin ki kasa iya tafiya."
da sauri ta ware ido ta dubi Abdulrahim ta ce
"Abokin turawa ba wani da yawa nake ci ba, sai nafi sati banci ba, ai bazai zamo illa ba ko."
Ajmaal ya yi dariya
"Hajiya anji batu kan lafiyar jiki, ba'a kaunar lafiya ta tab'o, to ai sai ki rika kiyaye wa."
mikewa Abdulrahim yayi cike da kosawa da surutun nasu, yanufi kofar fita.
Hajiya ta bud'e murya tana fad'in
"Kai abokin turawa tafiya ma zakayi, ina tambayar ka bazaka bani amsa ba."
bai ko juyo ba yayi gaba abinsa.
ta kalli Ajmaal tana fad'in
"Kaga wannan d'an'uwan naka ban tab'a ganin mara alkibla irin sa ba, bazaka tab'a gane me ya dosa ba,
dan Allah kaje ka tambaya min shi ka gano min bazan kasa iya tafiya nan gaba bako."
Ajmaal ya mike yana dariya gaba d'aya Hajiya ta rud'e, in dai lafiya ce ba'a kaunar ya tab'o..

Bayan sallan la'asar Feeryal ta foto zata shiga kitchen.
Kuraiba ta shigo tana yi mata kallon sama da kasa.
Feeryal taja ta tsaya a kofar kitchen.
Kuraiba tashiga karewa parlour'n kallo tana takowa gami da wasa mata harara.
tana kuma fad'in
"Sati guda dama na d'iba naga wani irin shiri kika shigo da shi, sai kuma naga akasin haka ashe ma fanko ne."
ta sheke da dariya ta tafa hannu kana ta ci gaba da fad'in
"Sai gashi har kwanin ki goma yau da tare wa, ban tab'a ganin yakai minti 10 da ke ba,
kash ayya ashe dai duk buge ne sorry fa."
d'akunan cikin parlour'n tashiga bud'e wa tana lekawa sai da ta leka duka d'akunan hud'u, ko ina har kitchen da store kana ta fito tana tafa hannu da fad'in
"Da kyau mana ko ni da akasan waye ubana kayan d'aki na bai kai wannan ba, sai ke da ba'a san asalinki ba, wai wannan shine duka kayanki,
saboda karya, ko da shike aiki da asiri meye baza'a iya ba."

Feeryal na tsaye tana kallon ta bata tanka mata ba.
ta tako gabanta ta dafa kafad'arta, tayi mata wani kallo tare da yamutsa fuska sannan ta saki dariyar makirci ta ce
"Laa karki damu da wannan fa ai ke kanwata ta ce tun da muna auren miji d'aya ai munza 'yan uwa, duk mun zamo abu guda, naga cucumber a cikin d'in nan naki bari na d'auka amma fa babba zan d'auka,
kin san laulayin ciki tun da yayi min cikin nan bani da abincin ci sai cucumber."
ta shiga kitchen d'in ta zab'o babba ta fito ta d'aga mata hannu ta ce
"Bye."
Feeryal na tsaye har sai da taga ficewar ta kafin ta shige kitchen.

Dad ne ya shigo side d'in sa yana kwalawa Mom kira.
da sauri ta fito jin kiran da
yake kwad'a mata.
ya dube ta yana fad'in
"Kin gani yaron nan Zaraddin
bai kwana a gida ba, yana so ya jamin abun magana, gashi Yaya Abubakar ya tare ni yana
tambaya ta ina yaje bai kwana a gida ba?."
Mom ta yamutsa fuska ta ce
"Sai kace an mai da Zaraddin d'in d'an tayi da beyi kwana
d'aya a gida ba, a taru ayi ta magana, ansan matasa da wannan
yanzu haka suna tare da
abokansa ne, zaka samu gidan
wani abokin sa yaje ya kwana,
wannan ai ba sabon abu bane a gun matasa, aje gidan aboki a
kwana, haba dan Allah duk kabi ka tada hankalin ka kawai daga
ya yi magana."
Dad ya zauna yana fad'in
"Wannan yaro duk abun da zan
fad'a masa bazai ji ba,
ya natsu yajira lokacin da
komai zai dawo karkashin ikon
mu in yaso duk abunda zaiyi ya yi amma ya tsaya dole sai ya b'ata min shiri, zamu gamu da shi bazai dawo ba duk in da
yaje ai zai dawo ai,
wai yaron nan shaye-shayen
nasa yakai har da giya yake
shigowa gidan nan."
Mom ta ce
"Narasa me Zaraddin ya tsare
wa mutane ayi ta maganar shi
kamar shine kad'ai mai abun
fad'a, ni dai kar a tambad'a
min yaro da mugun baki."
Mom tayi ta surutai da
zage-zage.


Feeryal ne tsaye cikin
parlour'n ta tana gyara shi.
da sauri ta waigo jin an turo
kofa.
Kuraiba ce ta shigo tana wani taku ta iso cikin parlour'n.
ta zube kan kujera tare da fad'i
"Wash Allah wlh na gaji."
sai kuma ta kalli Feeryal ta ce
"Barka dai amarya ana ta gyara ne haka, wlh duk a gajiye nake daren jiya ko rumtswa Mijin
Kuraiba bai barni nayi ba, oh
sorry Abdulrahim mai gidan namu, tun d'azu naso shigowa
mud'an yi hira baccin gajiya
ya kamani dole na kwanta,
to ykk."
tageren murmushi tayi sannan
ta ce
"Lafiya lau."
Kuraiba ta mike tana cewa
"Um bari na barki kiyi aikin
ki zan shigo muyi hira sanda
bakya komai."
a bakin kofa sukayi kiliya da
Miemie zata shigo.
kallon banza Miemie tayi mata
kamar yadda itama Kuraiba tayi
mata.
Miemie ta karaso ciki da sauri, ta harari Feeryal ta
ce
"Me wannan tazo yi a nan?."
Feeryal ta ce "Nima ban sani
ba yanzu shigowar ta kuma ta
fita, amma dai ce min tayi hira taso muyi bacci ya kamata
bata zo ba sai yanzu, amma gobe zata zo."
a hatsale Miemie ta ce
"Wannan ba karamar munafuka
bace, ni haka kawai bana son
ta, idan kika sake mata sai
tayi shanya a kanki."
Feeryal ta ce "Ni ina ruwana ma da ita, Ammie na ta ce kar
na sake nashiga sabgarta,
zauna Miemie dan Allah kar ki tafi yanzu."
"Ke ni yanzu zan tafi dama nazo nuna miki ashoben Yaya Yusuf ne,
Daddy ya
bada kud'i a yi mana odan kayan, dukan mu har da ke."
baki Feeryal ta washe tana kallon kayan a wayar Miemie ta ce
"Ai kuwa sunyi kyau."
"Idan ya iso zan kai mana
gurin d'inki, yanzu zanje wa Ammah aika ne direban ta na
jirana."
tayi waje da sauri..

Yusuf d'an yayan Mommy ne da suke ciki d'aya, wanda suke kira da Kawu Sani.
Kawu Sani shine babban d'an Bappa Salihu, yana zaune da iyalansa a Yelwa.
Yusuf shine babban d'an Kawu Sani, shi yana da zama a cikin garin Jos in da gidan sa da gun aikin sa yake can cikin garin Jos.
Daddy ne zai karb'a masa aure a nan Lagos za'ayi bikin.
matar anan cikin Lagos take,
bayan an gama biki zasu koma Jos.
biki na saura sati jama'an Yelwan Shendam suka taho.
in da shima tuni ango Yusuf yana nan.

Ana saura kwana uku bikin Miemie ta karb'o musu d'inkin su. a parlour suka baje kayan Feeryal tana ta yaba kyan d'inkin.
bayan fitar Miemie Feeryal ta mike zata koma d'aki, ya shigo
rike da waya a kunnen sa, sai da ya wuce dinning kafin ta shige d'aki. wayan sa data gani ranar a d'akinta ta d'auko ta fito,
dai-dai lokacin da yazo zai wuce rike da karamar flask mai d'auke da Sudan tea a ciki.
ta moko masa wayar
a hankali cikin muryarta mai sanyi ta ce "Ga wayar ka......!



Kallon kyakkyawan hannunta fari tass mai dauke da zara-zaran yatsu da tayi musu kwalliya da jan lalle ya yi, gami da wayar da take miko masa.
sannan ya mai sa idanunsa kan fuskarta.
da sauri ta yi kasa da kanta jin yadda idanunsa ya yi mata mugun kaifi da ganin ta.
lips d'in ta ta turo gaba ganin bai karb'i wayarba sai idon da ya tsare ta da shi.
ta kuma miko masa wayar, tana kuma cuno lips d'in ta.
ya miko hannunsa ya karb'i wayar kana ya sa kai ya shige.

Tana ganin shigewar sa ta kofar dake sakanin parlor'n ta da nasa, ta gyara mayafin kanta tawuce ta fita ta ainahin kofar fita daga gefen nata zuwa farfajiyar side d'in.
ta nufo get mai gadi ya gaisheta tare da bud'e mata kofa, ta fice.
sashin Aunty ta nufa tana ta kiliya da 'yan biki da gidan ya fara d'aukar jama'a.
wad'an da suka santa suka san da auren ta da Abdulrahim suka rika nuna ta, wasu su yaba wasu su kushe suce 'yar tsuntuwa ce ba'a san asalinta bama.
wad'an da basu santaba kuwa ta zame musu abin kallo da burgewa.
tana daf da isa side d'in Aunty suka had'u da Ajmaal.
murmushi tayi masa tun kafin suyi kusa da juna.
shima murmushin ya yi mata.
"Feeryal an fito ne."
"Ina kwana Ya Ajmaal."
"Lafiya lau Feeryal antashi lafiya."
murmushi ta kuma tana fad'in
"Lafiya lau."
da sauri yasa kai yawuce yana jin zuciya na kokarin kawo masa abin da bai dace ba a kan ta, da sauri ya kwab'i zuciyarsa da take bijiro masa da yanzu ita ce mallakinsa.
ya sanarwa zuciyar
ita d'in haramiya ce a gare sa mallaki ga d'an'uwan sa.

Da sauri ta shige parlour'n Aunty cike da son ganin ta, tun daga bakin kofa take kwad'a mata kira
"Ammie Ammie Ammie."
Aunty ta fito daga cikin bedroom da sauri jiyo muryar ta.
da sassarfa Feeryal ta tafi ta rungume ta tana dariyar murnar ganin ta.
Aunty ta rike baki fuska d'auke da fara'a ta ce
"Ke Feeryal waya ce ki fito?."
baki ta cuno cikin muryarta mai sanyi gami da shagwab'a ganin ta gaban Ammie'n ta ta ce
"Ammie ai ina so na ganki ne, idan nazo sai kiyi ta ce na koma, ni dai kwana zanyi yau, kullum ni kad'ai zanyi ta zama, danma Chuchu da Chulu suna zuwa, Miemie ma tana zuwa amma bata jimawa, ni kawai na dawo zan zauna a nan tare da ke."
Aunty tayi dariya ta ce
"To ke da kike da 'yan taya hira ma, kawayen ki suna zuwa kullum suna tayaki hira, bakiga ni kad'ai nake rayuwa ta ba, sai in Daddy ya zo ni nake samin mai taya hirar,
sai kuma idan kin haifo 'ya'ya dozen duk zan kwashe su na rike, kinga na sami 'yan hira ke nan ni ma."
kafad'a Feeryal ta make tana b'oye fuskarta jikin Aunty.
Aunty ta kuma yin dariya ta ruko hannunta tana cewa
"Zauna dai ki ci cake da yogurt yau bazan mai da ke a kan kafarki ba."
ta zauna kan kujera Aunty ta shige kitchen tana jin kewa gami da kaunar d'iyar tata,
bataki ace ta zauna sucigaba da rayuwar su ba, amma ina sawun giwa ya kere na rakumi.
ta fito mata da Cake da yogurt mai sanyi dai-dai misali, ta aje a gabanta kana ta zauna gefenta aiko da sauri ta gyara zaman ta ta soma ci, suna d'an tab'a hira irin na d'a da uwa.
a hankali take ci dan bata so taci da sauri Aunty tace ta tafi.
ai ko Aunty ta gane wayon ta ta tasan cikin ta duk son cin cake d'in nata bata ci yawuce yanka uku zuwa hud'u.
Aunty tana ganin ta ci yanka uku
koma kitchen ta d'ebo da yawa ta kawo mata tace.
"Tashi muje na rakaki ga wannan sai kije ki aje ki wuni kina ci."
kamar zatayi kuka tashiga bubbuga kafa kasa tana fad'in
"Ammie ni dai zan zauna."
Aunty ta ce
"Aa Feeryal ki koma d'akin ki, ta so maza."
ta ruko hannunta ta mike suka nufi kofa tana bubbuga kafa a kasa.
a bakin get na side d'in Aunty ta tsaya ta ce
"Maza ki koma d'akin ki karki kuma fito wa sai kinyi fin wata kafin ki to."
ido ta waro ta ce
"Ammie har wata to ai jibi ma zamuje dinner."
"Aa Feeryal ki zauna a d'akin ki a bin ki me zai kai ki wani gurin dinner."
"Ammie Daddy ne fa da kansa yamana ashobe."
"Ke dai jeki maza kar ki tsaya ko ina."
ta fita badan ta so ba.
a b'angaren Aunty itama ji take kamar karsu rabu, sai dai ta b'oye gudun kada Feeryal d'in tasami mafakar tuburewa..

"Ke Feeryal."
taji an ambata a bayan ta, da sauri ta waigo, Nabila ta gani.
Nabila ta wurga mata kallon banza sannan ta ce
"Kije ana kiran ki a can."
Feeryal takalli in da Nabila take nuna mata, mutane da yawa a gurin wanda ta gane cikin su Umma Karima da Siyama ce kad'ai.
Nabila ta juya a hankali tabi bayanta.
tun kafin ta karaso Siyama da Umma Karima suke aika mata kallon tsana.
har ta karaso gurin Umma Karima takuma wasa mata kallon banza tana fad'in
"Kunganta nan wannan kyawun duk na gaibu ne,
in banda aikin asiri me Abdulrahim zaiyi da tsintacciya, wacce tagama bin maza har cikin gidan nan an kamata da wani, wai ita ce surukar Hajiya Halima, ai Hajiya Halima ta bada mata wlh datayi sake aka mallake mata d'an da ta haifa a cikin ta,
in nice tuni ban shafe babin su ba, mujen ku dan Allah."
Umma Karima tayi gaba bayan ta kuma wasa mata kollon wulakanci.
Siyama ma haka harda jan dogon tsaki.

Feeryal tabi bayan su da kallo kana ta juya.

Umma Karima tun kafin su shige sashin Mommy take yab'a magana mai nuni da kaskanci gami da wulakanci, kan Feeryal har suka shige sashin nata.
Mommy ta tare su tana fad'in
"Meke faruwa ne Hajiya Karima?."
Umma Karima ta yamutsa fuska tana cewa
"Saken da kikayi ne ya bani mamaki, har yaushe zaki bar nagartaccen d'anki ya cigaba da zama da wancan kaskantacciyar yarinyar data gama tambad'e wa a waje, wlh Hajiya Halima kina bani mamaki."
Mommy ta ce
"Hmmm Hajiya Karima kibar wannan maganar tukun a gama bikin nan, ni nafi kowa son ganin naraba yaron nan da yarinyar nan, dan wlh ni banyi na'am da ita a matsayin sirikata ba, dole zai saketa dan ban shirya had'a jini da aljanu ba,
shiyasa ma na gargad'e sa kada ya sake yace zaije gareta da wata bukata ta aure, bari jama'a su watse daga gobe zuwa jibi gata zakiga hukuncin da zan yanke."
Umma Karima ta ce " Da dai ya fi gara ki farka daga baccin da kike."
kawayen nasu kuwa kowa ya cigaba da tofa albarkacin bakin sa wasu na fad'in
gara ta farka gida kamar wannan ace sirikar gidan ta kasance haka, wasu ko cewa suke tun da har an bari ta aure shi to a hakura kawai a barsu,
masu fad'ar haka kuwa Umma Karima ji take kamar ta nitsa musu mashi a zuci.

In da sabo ta saba tana shiga gefen ta takama wasu tsabgogin ta mance da duk tozarcin da Umma Karima tayi mata.

Bayan kwana uku ta kasance ranar d'aurin auren Yusuf da amaryar sa.
anata shagalin biki Feeryal tana gefen ta ko sha'awar fita bataji.
magana tajiyo a parlour tana kwance a bedroom,
ta mike tafito, ta tsaya daga bakin kofar bedroom.
su Ameerah ta gani da wasu 'yan'uwan su da sukazo daga Yelwa, 'ya'yan Kawu Sani ne kannen angon Yusuf.
duk 'yammata ne kansu d'aya, su uku sai ita na hud'u.
"To gata nan da kuke ta dami na nazo na kai ku ku ganta, ni fa kar kusa yarinya ta rainani."
cewar Ameerah tana yamutsa fuska.
tare da ci gaba da fad'in
"Idan kun gama kallon ta kamar TV sai ku fito."
ta juya tayi waje.
Feeryal tabi bayan ta da kallo tana mamakin yanzu Ameerah bata cika tsayuwa a gaban ta tana mata rashin mutuncinta data saba ba, sai dai ta tsaya daga nesa, tana mata kuma zata juya, ta kauce daga in da take.
hankalin ta ta mayar kan 'yammantan da taji suna cewa
"Ai kuwa da gaske ne kamar balarabiyar."
murmushi tayi musu ta ce
"Kuzauna nakawo muku ruwa."
ai ko suka zauna, ta shiga kitchen ta ta d'ebo musu drink's da donut da nama ta kawo musu.
suka karb'a suka kuma yi mata godiya.
tayi murmushi tare da zama a gefe.
suka kusa cinyewa kuwa kafin suka mike sukayi mata sallama.
tun kafin su fice daga side d'in suke maganar ta,
d'aya daga cikin su ta ce
"Ni kam banga aibunta ba da su Ameerah suke kushita ba, gata kyakkyawa kamar ita tayi kanta."
sauran suka ce ai kuwa kam suma basuga makusa a tare da ita ba.
suna koma sashin Mommy Ameerah ta harare su tana fad'in
"Ku har wani iya zama kukayi a gurin ta."
"Wlh tana da kirki har abinci ta bamu, ta zauna mukayi hira, ita wacce kike yabon nata ma ko kallo bamu isheta ba."
suka had'a baki wajen fad'a.
hararsu tayi ta ce
"Kwad'ayayyu sai kun ci abincin aljanu ai."


Ana sallar magriba Miemie ta shigo side d'in Feeryal da sauri.
tana zaune a kan sallaya ta idar da sallah ke nan.
Miemie ta rike hab'a tana fad'in
"Wai ke Feeryal ko da yaushe in dai za'aje wani guri kullum ke ce karshen shiri, dan Allah ki tashi ki shirya kafin ayi isha, 12 fa za'a tashi dan yau zasu wuce Jos."
"To yanzu zan shirya."
Miemie tafi tana fad'in
"Kiyi sauri zan kira ki idan muka fito."
ta ce tom.

A hankali take shirin dan har cikin ranta bata jin zataje gurin dinner, dan tasan zata fuskanci kalubale a gun Mommy da Umma Karima da wasu daga cikin danginsu.
kiran Miemie ne ya shigo wayarta, Miemie ce ta
"Kiyi sauri ki fito Feeryal gamu mun fito."
ta ce "Tom."
ta sauke wayar, tayi ta lalawai, Miemie tayi ta kiranta a waya tayi ta ce mata gatanan fitowa, daga bisani ta ce mata itafa su Mommy take tsoron abun da zasuje su mata.
Miemie ta ce
"Ina ruwanki da su muna gefe suna gefe."
kai ta girgiza kana ta ce
"Gani fitowa."
sai sannan ta d'auko ashoben nasu tasaka pant da underwear batare da ta sa bra ba, tayi tayi ta tasaka doguwar rigar tasama takasa, dole sai ta kasa ta saka ta janyo sama ya wuce da kyar.
d'inkin ya kamata sam bataji dad'i ba, dan bata saba sa kayan daya matse ta ba.
ta d'au gyale ta saka akan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login