Showing 45001 words to 48000 words out of 86085 words

Chapter 16 - FEERYAL Part 3 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt

irin wanan gud'a da kirari irin haka."
"Barni na fad'i da babban murya lokacin fad'ar ne yayi, kaga ikon Allah ba'ayi wa Allah dabara, shi ke tsara komai yadda yaso baya shawari da kowa."
Ammah tayi maganar tana zama da ci gaba da fad'in
"Amma ace cikin nan bai kai na haihuwa ba duk girmansa."
Aunty ta ce
"Ai kuwa dai kam da sauran wata d'aya nan gaba."
"To Allah ya bud'i ido lafiya."
Aunty ta amsa da "Amin ya rabbil alamina."

Tuni labari ya karad'e gidan Feeryal ta dawo da ciki rukuku.
hankalin Umma karima ya tashi, yaran gidan kuwa sai zuwa suke kallonta 'ya'yan Umma karima suka kai mata rohoto ciki ne babba a jikin Feeryal, hankalin ta ya dad'a dugunzuma.
Ajmaal na dawo daga gurin aiki bai wuce sashin su ba ya shigo sashin Aunty.
baki ya bud'e yana kallon Feeryal da katon ciki.
cikin ya zauna d'as ya yi mata kyau duk da girman sa,
ta kara haske sosai.
murmushi ta yi masa ta ce
"Sannu Ya Ajmaal."
ya karaso yana fad'in
"Sannu Feeryal ke ce da gaisuwa ai,
muna godiya da maraba da zuwan babyn mu."
murmushi ta kuma tana sunkuyar da kanta kasa.
Shamsuddin da Faisal da suka biyo bayan sa, suma duk suka tsaya kallon ta.
duk ta gaishe su kanta a kasa, suna yimata barka da zuwa.
da nuna farincikin su da ganin cikin.
Aunty ta fito ta ce
"Ku zauna mana Shamsuddin."
Ajmaal ya ce
"Dawowan mu ke nan daga gun aiki, zamu shigo anjima."
suka fita.

"Fito muje Bishira kar a ajiye abun fad'a, tun da ya amsa cikin nashi ne, ai shike nan maje mu dubota kar ace dai babu je, har ta kwana, yaro da kalen fitina da son sa mutane wahala."
Hajiya dake tsaye tana jiran fitowar goggo Bishira tayi maganar.
goggo Bishira ta fito tana gyara mayafin ta suka nufi side d'in Aunty.
suna sallama Aunty ta tare su cike da karramawa suka zauna,
Aunty ta zamo bakin kujera tana gaida Hajiya.
ba yabo ba fallasa ta amsa.
suka gaisa da goggo Boshira,
Hajiya ta ce "Ina ita yarinyar take?."
Aunty ta mike ta ce "Yanzu ta shiga ciki bari a kira ta."
Goggo Bishira ta ce
"Aunty Faty in bacci take ki barta."
"Aa ba bacci take ba, yanzunnan ta shiga."
Aunty ta shige d'aki suka fito da Feeryal.
Hajiya ta bita da ido har ta zauna kasan carpet.
Hajiya data rike baki ta ce "To haka abun yayi, to sannu ya nauyin jiki."
Feeryal ta sunkuyar da kai tana cewa "Ina kwana."
Hajiya bata amsa ba sai kallon ta da take. tana cewa
"Da gaske dai cikin ne."
goggo Bishira ta dube ta ta ce
"Sannu Feeryal ya nauyin jikin."
kai takuma sunkuyar wa tana wasa da 'yan yatsunta.
sannan ta gaishe ta.
goggo Bishira ta amsa tana kuma tambayar ta ya nauyin jiki.
nan ma kai ta kuma sunkuyar wa.
Hajiya ta mike tana cewa
"To Allah ya bud'i ido lafiya."
goggo Bishira tayi wa Aunty sallama suka tafi.

Umma karima bata iya hakuri ba sai da tazo sashin Aunty ta gane wa idanunta zahiri.
Aunty na ganin ta tayi wani murmushi ta ce
"Ki karaso mana Hajiya Karima ya zaki tsaya daga bakin kofa,
ga gurin zama ki zauna."
Umma karima data dibirbirce da ganin Feeryal zaune da katon ciki a gaba.
ta juya har tana cin karo ta fita.
Aunty ta yi dariya tana girgiza kai.


Kwanan Feeryal biyar da zuwa, bata fita ko kofa daga parlour sai bedroom d'in kwanan ta.
suna zaune da Miemi suna hira, Miemie ta mike ta ce zata tafi, Feeryal ta rako ta har wajen get d'in Aunty wan da tun zuwanta bata fito nan ba.
suna tsaye a bakin get d'in ta waje Miemie ta ce
"Feeryal wannan katon ciki yaushe ne zaki haifo shi,
ni yau sai naga cikin ya karamin girma, ko zaki haihu ne? ni nayi zaton a ranar da kika zo ma Allah haihuwa zakiyi, sai numfashi kike da kyar."
Feeryal tayi murmushi.
"Miemie ni kam zan koma nagaji da tsayuwa."
"Ke ai yanzu ko abin gudu ya zo sai dai a gudu a barki."
"Kai Miemie me zai hana ni iya gudu."
ta juya tana dariya.
cak ta tsaida dariyar da take, hango shi yana tahowa da alama masallaci zai tafi, dan ana kokarin shiga sallar la'asar.
da sauri ta kawar da kanta ganin idanunsa a kanta,
tasa kai ta shige dad'an sauri...

Tun da Feeryal ta shiga watan haihuwan ta, bata bacci kullum ciwon baya ciwon mara,
yau kuwa ta tashi da ciwon dayafi na kullum.
hankalin Aunty ya bala'in tashi.
Daddy ya ce maza a wuce da ita asibiti.
asibitin Dr family'n su aka wuce da ita, dan Daddy ya ce baza'a kaita asibitin Abdulrahim ba.
yana dubata ya ce C'S za'ayi mata batare da b'ata lokaci ba aka shige da ita operation room.....!


Nan da nan aka soma shirya yi mata CS, in da likitan da wasu ma'aikatan sa suka soma gudanar da C'S d'in.
Aunty da Daddy suna tsaye a bakin kofar hankali tashe.
sai anbaton sunan Allah suke da nima mata sassauci daga Allah.
motarsa ne ya shigo asibitin a guje,bai tsaya wani dai-dai parking ba ya fito da sauri.
Daddy ya bishi da kallon me ya kawo ka, fuska a d'aure.
cikin tafiya mai kamada gudu ya shige cikin operation room theater theater d'in da sauri.
yana shiga

sauran ma'aikatan suka juyo, dan ganin wanda ya shigo musu kai tsaye,

shiko likitan bai d'ago ba yana ta kan tsaga ta.
da sauri ya isa gaban wani hanga ya janyo rigar da likitoti suke sakawa idan zasuyi
operation, ya d'aura kan kayan jikinsa. kana ya zaro hand glove da facemask ya nufi gadon ya na saka hand guluf da facemask.
da sauri ya shige gaban sauran ma'aikatan ya tsaya gefen likitan, dai-dai san da likitan yake tsaga fatar karshe.

yayi saurin kai hannunsa guda kan hannunsa ya ruko askar. yayin da
hannunsa guda ya kai fuskarsa ya ja facemask d'in kasa likitan ya juyo ya kalleshi, sanin ko waye shi
sai ya sakar masa ya d'an ja gefe. ya gyara zaman facemask d'in, cikin kwarewa da sanin aikin sa ya idda karasawa ya zaro babyn, wanda tuni ya calla kara yana wutsil-wutsil da kafafu da hannaye.
ya lumshe ido yana bud'e wa a kansa, kana
ya mikawa likitar bayan ya rabashi da cibiyar,
shiko likitan ya mikawa sauran ma'aikatan, suka kai shi gadon da aka tanada domin gyara jarirai.
ya gyara tsayuwarsa da kyau yana bud'a hanyar tare da kuma zaro wani d'an.
ya sauke wani ajiyam zuciya a fili, yayin da idanunsa ke kan d'an.
bayan ya kuma mi ka musu, nan da nan ya soma d'in ke ta
in da likitan ya cigaba da taimaka masa da karb'ar kayan aikin da miko masa abun da yake bukata.
nurse biyu mata suna tsaye daga kanta suna ta janta da hira,
jifa-jifa take amsasu cikin tsiririyar muryarta.
cikin kankanin lokaci ya gama, ya matso ta kanta idanunta a lumshe take basu amsar magar da suka matsa mata da yin sa.
hannunta ya kama ya had'e hannayen nasu kana ya sake a hankali ya juya.
a sannu ta bud'e idanunta tabi bayan sa da kallo, bawai ko dan ta gane ko waye bane sakamakon shigar dake jikinsa irin na sauran likitotin.
ya taka gaban gadon da jariran suke, wanda tuni an kimsasu cikin kaya masu kyau da tsada wan da Aunty ta taho da shi.
ido ya kura musu suna ta shure kafafu da kokarin tura hannu a baki.
a sannu ya mika hannayen sa ya ruko hannayen su.
ya kura musu ido sosai yana d'an jijjiga hannun nasu, fuskarsa a yalwace da annuri yana ta sakin tsiririn murmushi wa yaran.
wasu nurse mata biyu suka karaso gurin cikin girmamawa suka ce
"Sir bari mu d'auke su iyayen patent d'in suna waje, tun d'azu suke cewa a fito musu da su, anyi musu albishir twins aka ciro."
baiyi magana ba bai kuma fasa wasan da yake da hannayen su ba.
yakai 10second kafin ya zame hannun sa daga nasu, yad'an matsa gefe.
suka d'auke su suka fito sa su.
Daddy da Aunty har suna rige-rigen karb'ar su.
Aunty ta rungume wanda aka mika mata tana fad'in
"Alhamdulillah!."
Daddy ma haka bakinsa ya kasa rufuwa.
bayan ya yi wa nurse's d'in tukuici da kud'i masu yawa.
Abdulrahim ya fito yana warware hannun rigarsa.
Aunty ta bishi da murmushi da farincikin daya gaza b'oyuwa a fuskarta, tana fad'in
"Sannun ku da aiki Abdulrahim."
Daddy kuwa bai kalli in da yake ba, idanunsa akan jikarsa, daya gaza janye ido a kansa.
kai ya jinjina ya wuce ya tafi can gefe yana d'aga kiran yada shigo wayarsa.
aka fito da Feeryal a ture a kan gado aka wuce da ita wani room.
su Daddy suka bi bayan su da sauri, yana tsaye yana kallon wucewar su.
Ajmaal da Shamsuddin da Faisal ne su shigo da sauri suka karoso in da yake cike da matukar farinciki suke fad'in
"Ya Abdulrahim ina baby's d'in mu, ina twins d'in mu suke!."
sukayi maganar cike da matukar farinciki sosai.
dan tuni Daddy ya kira ya fad'a musu tun kafin a fito da ita.
murmushin gefen baki yayi ganin yadda suke maganar kamar kananun yara suna wani tsalle ya ce
"Suna can."
ya nuna musu kofar room d'in da aka shige da Feeryal.
ai ko da sauri suka juya suna rige-rigen shiga.
shiko ya fice ya shiga motarsa ya bar asibitin.
su Ajmaal
suka karb'e yaran a hannun su Aunty kamar zasu had'iye su dan farinciki.
sai yabawa da zuzuta kyan su suke.
Daddy yayi murmushi yana kallon yadda suke yi kamar zasu had'iye yaran.
ya ce "Iye anyi 'ya'ya sai murna ake."
sukayi dariya Shamsuddin ya ce
"Wayyo kalle su fa kyawawa wlh duk kama da Ya Abdulram suke, suka d'auko farin Feeryal."
"Asalin kama ma kuwa."
cewar Ajmaal da Faisal.
Aunty tayi murmushi dan ko ba karya 'ya'yan asalin kama da uban su suke.
sai sannan suka masa bakin gado in da Feeryal ke kwance suka gaisheta suna yi mata ya jiki.
murmushi tayi musu tana lumshe idanunta tare da juya fuskarta ta jikin garo.
Daddy ya ce
"To mu fitan ku waje likita ya ce a barta ta huta, ku bawa Aunty'n ku yaran ta kwantar da su suma suna bukatar hutu."
suna shirin fita Hajiya da Goggo Bishira Ammah Miemie Kulu mai aikin Hajiya da Sumayya suka shigo.
Miemie kamar zatayi tsalle dan murna Sumayya ma haka, dan ita halinta da sauki dan wani lokaci bata d'aukar zugar Ameerah.
ko da suka fito zata biyo su Hajiya Ameerah ce mata tayi wai zataje kallon 'ya'yan aljanu ita ba inda zata.
ita Sumayya na son yaran tun bata gansu ba, tana ji a ranta ko ba komai dai 'ya'yan yayansu ne, dan bata daga cikin 'yan'uwan ta masu cewa ba cikin yayan nasu bane.
Miemie da Sumayya suka riga kowa d'aukar yaran.
da kyar goggo Bishira ta karb'i na hannun Sumayya dan Miemie kam ta rike na hannunta gam.
Hajiya ta leko fuskar su ta tana fad'in
"Eh to ga kamar abokin turawa a jikin su, ah to yanzu kam hankali zai kwanta."
Ammah ta girgiza kai.
Aunty ko Murmushi kawai tayi.
sai da likita ya shigo ya ce su bata guri ta huta kafin kowa ya fita aka bar Aunty da ita.
da zasu tafi Sumayya da Miemie suka ce su bazasu tafi ba,
suna tare da Aunty a asibitin.
Sumayya tana like da yaran da har cikin ranta take jin kaunarsu.
Aunty ta kira su Hajja Umma ta video call.
Abba da Hajja Umma sunyi matukar farinciki Aunty ta hasko musu yaran sunata yabawa da fatan Allah ya raya.
lokacin bacci ya d'auki Feeryal suka ce idan ta tashi zasu kira.
Aunty na kashewa ta kira Maryam, Maryam kamar zata fasa wayar da ihu
"Wai da gaske Aunty Faty Feeryal twin's ta haifa?."
cewar Maryam cike da zallar farinciki.
Aunty tayi dariya tana fad'in
"Gasu kuwa kina gani."
ta ce "Jibi ina hanya inasha'allah."
Aunty ta kashe tana mata dariya.


Umma karima ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta shiga wani mummunar bala'in tashin hankalin da bata b'a shigan irin sa ba.
tayi sintiri ta zaga cikin parlour'n ta yafi a kirga.
Siyama ce ta shigo kamar an jefo ta tana haki da fad'in
"Aunty Karima ta haihu an cire 'ya'ya biyu duka maza, yanzun nan su Ajmaal suka shigo da idona na gana hoton yaran!."
Umma Karima ta buga kirji ta d'aura hannu a ka tana fad'in
"Nashiga uku!."
takuma dannan lambar da tun d'azu take ta gwada shi ya ki shiga.
jin wayar tashiga yanzu ta sauke numfashi sanda aka d'aga kiran.
"Dr ya zakayi min haka, ko nawa nagaya maka zan baka in har ka aiwatar da abun da na fad'a maka."
daga cikin wayar ya ce
"Hajiya matsala aka samu muna tsaka da aikin Dr AA FIYA ya shigo, karshe ma dai shi ya karasa aikin, abun da ya bani mamaki kuma, kince min bata gidan bai ma san da cikin ba, to ya akayi yasan biyu ne a cikin ta, bayan ya ciro d'ayan da mahaifarsa, a yadda ya koma domin ciro d'ayan yasan da akwai wani a cikin,
naso da ya kauce da ragowar d'ayan zansan yadda zanyi da shi, in yaso sai asan yadda za'ayi ma dai duka."
Umma Karima data cire d'ankwalinta tana fifita da shi ta ce
"Ya b'ata komai yama akayi yasan an kaita asibitin bayan baya gidan san da aka fita da ita!."
ta kashe wayar tayi zaman 'yan bori a kasa, tare da d'aura hannu akai ta kurma ihu tana fad'in
"Wallahi tallahi bazan barka haka ba Abdulrahim, Feeryal gidan nan ba naki bane,
dukiyar Alhaji Abubakar AA FIYA nawa ne, da na dad'e ina farautarsa yau zankarasa farautar dana d'au tsawon shekaru ina yin sa."
Siyama ma zubewa tayi kan kukera, tana jin kamar itama tayi ihun ko zata sami sassauci daga d'acin da take ji cikin zuciyarta.
burin ta dana Aunty'n nata da banbance ita burin ta ta aure shi su zauna inuwa d'aya ne,
duk wani abun da 'yar'uwan nata zata fad'a jinta kawai take,
ba so take a kashe shi ba ita so take ta aure shi ya zamo mallakinta.
Umma Karima ta mike da sauri ta fita ta nufi sashin Mommy.
tun kafin ta shigo parlour'n Mommy take jin yadda Mommy take cewa
"Wlh karya ne in har kuwa akace 'ya'yan nan nasa ne, to bazai rike 'ya'yan aljanu ba, ai dole ma su san yadda zasuyi yayan suyi kama da shi,
wani suffa ne aljanu bazasu iya juyawa ba, d'ana bazai zamo uban aljanu ba kuwa!."
ta wurgawa Ajmaal wayar sa kad'an ya rage ya fad'i yayi saurin cab'e wa, yana cewa
"Mommy ki bar wannan maganar tun da ta haihu ai ya kamata yanzu ko mai ya wuce, basai an fad'a ba ana ganin yarannan an san na Ya Abdulrahim ne, yara gwanin sha'awa ya kamata kiyi maraba da jikokinki."
"Dan uban ka bazan yi ba fita ka bani guri anan!."
Ajmaal ya juya ya fita.
Umma Karima ta karaso tana rike baki.
"Hajiya Halima mai jikoki an haifo miki manya-manyan sarakunan aljanu, sai ki cigaba da rainon su suzamo gamashekar da zasu girma su sare wuyarki."
"Haba Hajiya Karima wace irin fatar tsiya ce wannan, ai wlh 'ya'yan nan baza su kwana a duniyar mutane ba sai dai duniyar aljanu, can in da suka fito."
Mommy ta shige bedroom d'in ta tana zuba uban masifa.
Umma Karima ta juya ta fita tana zaman jiran sakamako idan baiyi mata ba ta d'au mataki da kanta a yau d'in nan ba sai goge ba.


Motarsa ne yakuma shigowa asibitin.
suka fito shi da Dr Imran suka nufi room d'in da Feeryal take yana rike da laidar magunguna,
Dr Imran kuma yana d'auke da wani katon laidar shopping .
Sumayya da Miemie suna ganin su suka mike suna musu sannu da zuwa,
Aunty ko shigarta toilet d'in room d'in ke nan zatayi al'walar sallar azahar sukayi sab'ani.
Dr Imran ya tsaya suna gaisawa da su Sumayya, shiko ya tako bakin gadon.
ya tsaya a kanta idonta a lumshe tana bacci yaran a jere a gefenta suma baccin suke.
sosai ya zuba musu ido ita da yaran, a fili ya sauke ajiyan zuciya.
a hankali yakai hannu ya shafi gefen fuskarta, ajiyan zuciya ta sauke tare da juya kai ta kwantar da fuskarta atafin hannunsa.
a hankali ya lumshe idanunsa tare da bud'e su a kanta.
ya zare hannun nasa a hankali ya kai fuskan yaran ya shafa zuwa kawunan su.
Dr Imran ya karaso yana fad'in
"Wow masha'Allah see beautiful baby's I congratulate you."
Dr Imran ya masa kusa da shi cikin yin kasa da murya sosai ya ce
"Gaskiya mutumi na kayi kokari fa ka zuba jarumta sai da ka samo masu kama da kai."
ya yi kamar baiji abun da Imran ya fad'a ba ya juya yafice.
har ya tada mota Dr Imran ya iso da sauri dan yasan halinsa sarai sai ya iya tafi ya barsa.
suna fita Aunty na fitowa daga toilet, Sumayya ta nuna mata kayan da suka kawo.
Aunty ta fita ta ce zataje masallacin cikin asibitin tayi sallah.


Mommy ta fito da sauri tana gyara mayafinta, ta shiga mota direbanta yaja suka nufi asibiti.
suna isa ta fito da sauri ta ce wa direban
"Jirani yanzu ina zuwa juya da motar ta hanyar fita."
ta nufi ciki tana tambayar wata nurse wanda akayiwa C'S da safen nan tana nuna mata d'akin da take,
Mommy ta tura kofar babu ko sallama.
lokacin Feeryal ta farka tana kallon su Miemie da suke ta zayyano sunayen da za'a rika kiran yaran da shi.
Aunty kuwa bata dawo daga sallah ba.
Mommy ta bugawa Sumayya harara tana cewa
"Uwar me kika tsaya d'auka anan?."
Sumayya ta turo baki.
Mommy ta karasa bakin gadon ta rike kugu tana kallon yaran,
tare da aikawa Feeryal da mugun kallon .
sai kuma ta jinjina kai kana ta sa hannu ta d'auki d'aya ta rike shi ta gefe, sannan ta kuma d'aukar d'aya ta juya ta fita, Feeryal tabi bayan ta da kallo.
su Miemie ma haka.
tana fita ta shiga mota ta ce direban yaja su tafi da sauri..
Mommy na fita ba da jimawa ba Aunty ta shigo.
da mamaki ta kalli kan gadon ta ce "Ina yaran."
Miemie ta ce "Mommy ce tazo ta d'auke su."
da sauri Aunty ta ce "Ta kai su ina?."
"Mu ma bamu sani ba."
cewar Sumayya.
Aunty zata kuma magana aka turo kofa Ajmaal ne ya shigo cike da d'okin ganin yaran.
Sumayya tayi saurin cewa
"Ya Ajmaal Mommy ta zo ta d'auki yaran ko kuna tare da ita ne?."
"Mommy'n ina ta kai su!?."
yayi maganar hankali tashe.
Sumayya tace
"Muma bamu sani ba kawai zuwa tayi ta d'auke su ta fita, kafin Aunty ta dawo daga sallah."
da sauri ya aje shopping bag d'in hannunsa yafita da sauri.
yana kiran Abdulrahim a waya.
"Ya Abdulrahim kana ina Mommy fa tazo ta d'ibi yaran nan, yanzu na shigo asibitin wai bata jima da fita ba ta d'ebe su."
d'ip ya katse kiran.
Ajmaal ya zaro wayar yana binsa da kallo.
sai kuma ya juya da sauri ya koma room d'in.
yana kuma tambayar su Miemie yadda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login