Showing 9001 words to 12000 words out of 86085 words
Chapter 4 - FEERYAL Part 3 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt
in da zaije za'a watse dan wlh Abdulrahim bazai tab'a zama da yarinyar nan ba,
yanzu ina Kuraiba'n take Allah dai yasa cikin bai fita ba."
"Gata nan kwance tana numfarfashi a gaya masa yazo ya d'auke ta ya jinyata ciwon da ya sa mata,
kuma a gaskiya idan kika bar auren nan ya zaunu bakiyi mana adalci ba."
"Haba Hajiya Luba kar ki damu yarinyar nan bana kaunarta sam-sam a rayuwa ta, babu abun da zaisa na barta tayi zaman aure da d'ana, yanzu kuwa zaizo ya d'auko ta."
Mommy na kashe wayar ta lalub'o number Abdulrahim dan tasan yau weekend yana gida.
yana d'agawa ta ce yazo yanzu tana nimansa kada ya b'ata lokaci.
bai b'ata lokaci da yawa ba yashigo kiran Mommy.
tun kan ya zauna Mommy ta rufe shi da bala'i.
"Baku isa ku kunyatani kai da mahaifinka a cikin kawaye na ba, ga matarka can Kuraiba tana kokarin yin b'ari, ka fita kayi gaggawar zuwa gidan su kaje ka d'auko,
ka magance maysalar da ke kolarin aukuwa kada ka sake cikin nan ya b'are,
ina ga irin ta and'agawa yarinya hankali har ya kaiga tana kokarin yin b'ari, to wlh bazan yadda ba,
yazama dole a kiyaye cikin a hakura da abin da bata so,
akan karin banza auren aljana a halakamin jika wlh bazai sab'uba,
maza kaje ka d'auko ta yanzu."
kafad'a ya d'aga ya juya ya fita.
Hajiya Luba tayi ta zuba idon ganin sa shiru, takuma kiran Mommy,
Mommy tayi mamakin da taji ance bai je ba, duk da tasan hakan ba wani abun mamaki bane a halin sa.
tayi ta baiwa Hajiya Luba hakuri, daga karshe dai ita taje ta dawo da Kuraiba dan shi kam yaki zuwa.
Sashin Daddy Mommy ta wuce ta tarar da shiko zama bayiba ta ke fad'in
"Yanzu Alhaji kaji ka aminta auren nan sai an zauna sai Abdulrahim ya zauna da yarinyar nan,
mene ne ajikin auren wannan yarinya da kake so ka jonawa Abdulrahim ita,
yanzu gashi can damuwa nason sa cikin jikin Kuraiba zuba,
nifa ban aminta da auren nan ba z
bazai taba'a sab'uwa ba."
"Ke Hajiya Halima ki maida hankalin ki kada ki sake zuwa min da wannan shirmen,
d'ana ne ko naki? haka naga dama dashi,
idan baki dai-dai ta hankalin ki ba zaki iya kaucewa ki bamu guri a gudanar da komai lafiya, kar ki sake zuwa min da wannan zance."
"Au haka zakace ma Alhaji, to sai me ko mai ma kayi."
ta juya fuuu tayi waje.
Mommy tayi sashin Hajiya da kukan ta wai Daddy ya ce zai koreta ta akan auren, ga shi kuma
cikin Kuraiba na shirin fita sanadin damuwar auren.
Hajiya ta ce
"Ai ko bai isa ba sai dai in a fasa tarewar, dama Kuraiba'n tana da ciki ne, amma dai bai fita ba ko?
ikon Allah ashe dai tana kunshe da abun, ai yafi aure kusan shekara babu motsin ciki ai ba kanta,
jeki zan kira shi ai karma ya soma."
Kwana uku da shirya kayan Feeryal a side d'in Abdulrahim Daddy yasa su Ainty da goggo Bishira da Ammah suka shiga babban kasuwar su suka had'o wa Feeryal lefe.
kud'in da Daddy ya narka wajen had'o lefen Feeryal sai da ya baiwa Aunty tsoro.
kwana uku sukayi suna shiga kasuwa, inda gidan gaba d'aya ya d'auki zancen, masu habaici sunayi masu mugun fata sunayi.
Aunty zaune tana waya da Hajja Umma. Mommy ta b'ankad'o kofar parlour ta shigo.
tana bin Aunty da kallon banza tana fad'in
"Hajiya Fatima burinki ya cika kinyi kutun-kutun kin sa an jona d'ana da d'iyar tsintuwarki, tsintacciyar aljanar ruwa mara asali,
amma kisani har a gobe nice nan uwar da ta haifi Abdulrahim nayi nakudar sa nasan zafin sa, wanda har a gobe bakisan ya ake nakuda bare nishin haihuwa ba;
ina so na sanar miki cewa baki isa kisa ayi wani shagalin biki ba dan d'ana bazai jera da aljanar ruwa ba,
idan kuma kikace zakiyi to mu zuba mu gani, mttsss!."
taja dogon tsaki kana ta juya tafita tana banko kofa.
Aunty ta bi bayanta da kallo tare da sauke numfashi.
tana dad'a gyara rukon wayar da ke kunnen ta.
Hajja Umma dataji komai ta cikin waya itama ra sauke numfashi tare da fad'in
"Fatima Allah dai ya miki albarka da baki tanka mata ba, dama kin shirya wani shagalin biki ne a tarewan nata?."
"Aa wlh ban shirya komai ba Hajja Umma, ta daiyi tunanin ko hakan zai faru ne."
Hajja Umma ta ce
"Yauwa to kada ma ayi dan gujewa wani tashin tashina,
muma babu wanda zaizo daga nan idan Allah yasa ta tare Allah ya kawo rabo in da rai zamuzo suna, zamuyi musu fatan zaman lafiya daga nan, zamuyi ta tayaku addu'a Allah ya kad'e fitina."
Aunty ta ce "Amin ya Allah amma Hajja Umma ni dai zanfi jin dad'i idan na ganku kusa."
"Fatima kiyi hakuri bazai yuwu muzo a irin wannan halin da ake ciki ba, kar azo a b'ata goma d'aya bai gyaruba, 'yan'uwanki bazasu zuba ido ayi musu cinkashi su share ba, to maganin bari kar a soma, kiyi hakuri kawai zamu zo ai nan bada jimawaba idan Allah ya nufa."
Aunty ta girgiza kai kawai, sukayi sallama.
Da yamma Daddy ya shigo.
jikin Aunty ya yi sanyi san da Daddy ya sanar mata a karshen satin nan Feeryal zata tare.
Aunty ta dubeshi jiki a sanyaye ta ce
"Daddy beyi wuri ba baza'a bari a kara lokaci ba."
"Fad'imatu karki ce komai dan Allah kiyi musu addu'a da fatan alkhairi, bana so najinkirta, ina so nayi amfani da wannan damar ne kafin Hajiya takuma waiwayowa kan lamarin,
yadda taga naji saukin nan zata iya kuma tada bori ta ce bata amince ba."
Aunty ta girgiza kai
ta ce
"Allah yasa hakan shine mafi alkhairi."
"Yauwa ko ke fa amin ya rabbil izzati, shin kinshirya wani hidima ne Fad'imatu?."
"Aa babu abun da na shirya Daddy ayi addu'a a kaita Allah ya basu zaman lafiya."
kai Daddy ya jinjina tare da kuma amsawa da amin amin.
Miemie zaune da Feeryal a d'akin ta, Miemie ta b'ata rai tana fad'in
"Ni wlh naji haushin da akace babu wani shagali a auren nan ni da nagama hasasho yadda shagalin zai gudana,
Allah ban so ba."
Feeryal ta bita da ido dan ita da ido take kallon duk wani mai magana kan auren nata da har yau take ganin kamar karya ko mafarki.
Ranar da ya kasance rana ce da Feeryal zata tare a side d'ib Abdulrahim, ranar ta tsinci kanta cikin tashin hankali sosai. ranar wuni tayi sukuku daga bisani kuma tasoma kuka,
Aunty ta sunkuya rarrashi.
Abdulrahim ne zaune a parlour'n Mommy da tayi masa kiran gaggawa.
ta dube shi tana cewa
"To bawai kaga an kaima wancan kyalkyal banzan sashin ka, ka saki jiki da ita ba,
tun da ya matsa sai ka aure yarinyar nan, ka bud'e kunnen ka da kyau kajini,
kar ka soma gangancin kusantarta dan kyan d'an maciji ne gareta, kasan takunka idan ba haka ba wallahi sai ta fasa kai duk ta wasa mana dafin tsiya, kaji na gaya maka ke nan."
baki ya tab'e ya mike ganin ta gama maganar nata ya yi gaba.
Hankalin Feeryal bai kara tashi ba sai da dare yayi, Aunty Ammah suka sata a gaba suna mata nasiha.
kuka sosai take da gaske dai mafarkin nason zamowa gaskiya.
Aunty ta gaza daurewa itama ta fashe da kuka, ta rungume Feeryal suna kuka kamar wacce mutuwa zata rabasu da d'ayan su.
Ammah ta rika baiwa Aunty baki itama tana share hawaye dan duk wanda ya gansu sai sun bashi tausayi.
Daddy da kansa ya shigo ya kama hannun Feeryal tana tirjewa tana mikawa Aunty hannu.
da kyar ya lallab'a ta tasassauta kukan,
ya dubi goggo Bishira da Ammah ya damka musu ita a hannunsu ya ce
"Ku kaita d'akin ta."
Feeryal takuma fashewa da kuka.
wannan karon sai da Daddy shima ya share guntun kwalla.
goggo Bishira da Ammah suna rike da hannunta har sashin Abdulrahim suka shige da ita gefen ta.
nasiha suka kuma yi mata kana sukayi mata saida safe suka janyo mata kofa.
Feeryal ta fad'a kan lafiyayyen gadon ta ta kuma fashewa da kuka tana kankame pillow.........!
Allah ya bamu aron rai ya nuna mana bayan sallah da rai da lafiya.
Abun da take ganin sa kamar mafarki sai gashi ya zamo gaskiya, yau ta rabu da Ammien ta gata a side d'in Abdulrahim kuma wai a matsayin matarsa.
wani kukan takuma fashewa da shi, tana dad'a kankame jikin pillow gami da kiran sunan Ammie'n ta.
a haka bacci yasami nasar d'aukar ta,
sai dai tayi ta juyi dan sam bata saba bacci da kaya masu nauyi ba,
dole ta mike ta isa jikin wardrobe tashiga bubbud'ewa tana lalumo ta in da Sleeping dress yake.
bata sha wuya wajen nemaba kuwa ta gani sabbi cikin kwalaye da laidodinsu, a jere kamar za'a bud'e kanti.
ta d'au d'aya mai riga vest da wando har kasa.
a sannu ta nufi kofar da take hango shi na glass.
a hankali takai hannunta jikin kofar gilashin da take tunanin nan ne bathroom.
tana kai hannunta jikin gilashin ya zuge, tasa kai ta shige a hankali.
ta tub'e kayan jikinta ta wasa ruwa kana ta saka kayan baccin, ta fito.
a hankali ta kwanta gefen gado ta rakub'e.
takai zamani guda da tunani ire-ire kafin bacci ya sami nasarar d'aukar ta...
Ab'angaren Kuraiba kuwa, ta kasa zaune ta kasa tsaye.
tun da taji an kawo Feeryal hankalin ta yayi mugun tashi.
karfe 12 ta fito ta nufi bedroom d'in sa.
ganin sa kwance yana bacci bata san san da ta saki wani ajiyar zuciya ba, dan tayi zaton yana can gurin ta ko ita Feeryal d'in tazo d'akin nasa suna tare.
ta janyo masa kofar ta juya tana jin dad'i a ranta.
Feeryal ba ita ta farka ba sai asuba.
bayan ta idar da sallah a hankali ta kifa kanta jin gado tana azqar, takai awa guda zaune sai da ta fara gyangyad'i. kafin ta mike a hankali ta kwanta bakin gado batare da ta cire hijab d'in jikinta ba.
Sai wajen karfe 10 da rabi ta farka.
ta shige bayi tayi wanka tafito, ta shirya cikin doguwar rigar atamfa data d'auka cikin sabbin kayan da suke cike tam cikin wardrobe din d'akin.
rigar ya zauna sosai a jikin ta yamata kyau matuka.
turarukan dake gaban mirror ta shafa masu dad'i gami da sanyin kamshi.
daga su bata kara komai ba, abinka da me kyau tamkar ta zauna ta tsara wani rantsastsen kwalliya haka take kyalli.
karfe 11 dai-dai ta shafa cikin ta data fara jin yunwa, wanda rabon ta da tasa wani abu a cikin tun jiya da rana.
ta mike a hankali ta je ta d'au gyale ta yafa a kanta ta nufi kofa, da zumbar tafiya sashin Ammie'nta.
Tana fitowa Baba Rabi na shigowa niki-niki da kulolin abinci, gami da flax's.
tayi saurin isa ta taimaka mata da wasu.
tana fad'in
"Sannu Baba Rabi ina kwana."
"Lafiya lau 'yar nan ya kwanan bakunta?."
batayi magana ba suka karasa saman dinning suka jera kulolin.
Baba Rabi ta d'ago ta dube ta tana fad'in
"Ammie'n ki ta ce na gaida ki ga breakfast d'in ku."
kai tad'an langwab'ar
tayi rau-rau da ido cike da yanayin ta mai kama da shagwab'a kamar a gaban Ammie'n nata take.
Baba Rabi tayi murmushi ta juya tana fad'in
"Nabarki lafiya."
har Baba Rabi takai kofa tana tsaye jiki ba kwari, sai da taga ficewar ta kana
a hankali taja kujera ta zauna.
Kulolin tashiga bud'e wa had'ad'd'un abinci ne kala-kala d'aya daga cikin flax's d'in kuwa Sudan tea ne a ciki.
sai da takai kan abun da tafi bukata wato cake da Ammie'n ta ta shirya mata shi a mazubi na musamman.
tayi serving
tasoma ci da tea d'in da tad'an had'a rabin mug.
tana kammalawa ta mike ta gyara mayafin kanta ta fita, ta nufi sashin Aunty.
Aunty na zaune cike da kewar ta sai ganin ta tayi.
ta mike tsaye tare da rike baki tana binta da kallon mamaki.
itako kai ta langwab'e tare da cuno d'an karamin kyakkyawan bakin ta.
Aunty tayi saurin ruko hannunta tana fad'in
"Ke Feeryal me ya fito dake ke da jiya aka kaiki? maza koma d'akin ki, kar ki sake fitowa sai in shi yace ki fito."
baki takuma turowa cikin yanayin ta gami da shagwab'a ta ce
"Ammie ni dai so nake na ganki, ni dai zan zauna a nan kawai, ni kad'ai babu kowa tsoro nake ji."
Aunty ta d'anyi jim sai kuma ta saki murmushi tana cewa
"In banda abin ki Feeryal nima bakiga ni kad'ai ce a nan side d'ina ba, haka nayi ta rayuwa a lokacin da babu ke bakima zo duniyar ba, da haka zaki saba har ke ma ki haifo 'yar ki, ko 'yanmatan Ammie."
ta karasa maganar da jan kumatun ta.
baki ta kuma cunowa tana make kafad'a.
Aunty ta janyo hannunta
"Zo ki koma d'akin ki anjima Miemie zatazo ta tayaki hira,
basai kin fito ba ma, ke baki san kin girma ba yanzu,
yanzu duk abin da zaki aikata a d'akin ki na alkhairi ninkin lada za'a rubuta miki,
lallai zaki sami lada da yawa amma zamu raba ladan ne ko, ko rowa zakiyi min?."
ta gyad'a kai tana sakin kyakkyawar murmushin ta,
Aunty ta yi murmushi itama.
haka tayi ta lallab'in ta gami da 'yan dabaru, har ta rakata kusa da side d'in ta.
tana tsaye sai da taga shigarta kafin ta juya ta koma nata side d'in...
A hankali take takowa tana wasa da bakin mayafin ta.
kamar ance ta d'ago karaf suka had'a ido da shi yana tsaye cikin garden, rike da mug yayin da d'aya hannunsa ke zure cikin aljuhun sa.
da sauri ta janye idanunta takara sauri,
ta shige ciki.
a hankali yakai mug d'in bakin sa ya kurb'i Sudan tea d'in sa, kana ya soma takowa ya nufi gefen sa.
Tana shiga direct bedroom ta shige.
ido ta waro cike da murna take kallon wad'an da suke cikin d'akin, tayi ihun murna tare da rungume su tana tsallen murna.
Chuchu da Chulu suna tayi mata dariya.
fuska ta d'an kwab'e ta cuno baki tare da marairaice murya tana cewa
"Dama kunsan ina nan ne, ni dai bana son zaman nan nafi son zama gun Ammie na."
Chuchu ta ce
"Ai nan ma da dad'in zama gashi komai na gurin yana da kyau."
fuska ta kuma kwab'ewa ta ce
"Ni dai nafi son zama gun Ammie na,
bana son zama side d'in Sahab d'in nan, kawai bana son nakasa yiwa Daddy biyayya har ya yi fushi da ni ne."
Chulu ta ce
"Ai kuwa idan baki zauna ba bazai ji dad'i ba, ba gamu ba zamu rika zuwa muna tayaki hira anan d'in."
"Kun tabbata?."
ta fad'a tana d'aura yatsar ta kan bakin ta.
duk suka amsa da "Eh mun tabbata."
suka zauna suka soma hira, nan da nan taji kad'aici ya gusa a gareta...
wunin ranar da su Chuchu tayi,
abincin rana da dare duk Aunty ke turo Baba Rabi da su.
washegari kamar jiya yau ma Aunty takuma aiko mata da breakfast.
Baba Rabi ta shirya kulolin kan dinning, ta kwashi na jiya ta tafi da su.
Feeryal bata fito da wuri ba bayan ta tashi a bacci sai da ta gyara bedroom zuwa bathroom. kafin tayi wanka ta shirya ta fito.
tana isa cikin parlour da sauri ta waiga can saman dinnin jin karar fad'uwar abu daga gurin.
shi tagani sunkiye yana kokarin d'aukar plt d'in da ya fad'i kasa.
kai ta kawar da d'an sauri dan bata sammaci ganin sa a gunba.
tsayuwa ta d'an gyara jin takunsa yana matsowa cikin parlour'n.
tana d'agowa ta gansa rike da plt a hannunsa guda d'aya hannun nasa kuma yana rike da Mug.
kai ta sunkuyar tana wasa da 'yan yatsunta.
wuceta yayi ya nufi ta kofar da zai sadashi da gefen sa dake ta cikin parlour'n nata.
tabi bayansa da kallo har ya b'acewa ganin ta.
sai kuma ta cuno baki gaba sannan ta juya ta wuce dinning.
tana zama Miemie ta turo kofa ta shigo.
tun daga bakin kofa Miemie ta soma yi mata kirari.
"Kaga a marya a gidan AA FIYA, ke kad'an ki kin zame musu kashin kifi a wuya, kinyi gaba kin bar karnuka suna ta haushi a baya."
Feeryal ta rike hab'a tana cewa
"Oh ni Miemie Allah ki rabani, ai babu ruwana na da ke tun jiya baki nime ni ba."
tayi maganar tana cuno baki gaba.
Miemie ta karaso tana fad'in
"Ke yanzu waya gaya miki ana zuwa gidan amare a washegarin ranar da aka kaisu, ai sai kaje ka gane wa idanunka damuwa, gara dai ka bari ayi kwana biyu zuwa sati, yanzu ma kawai nayi missing naki ne da yawa yasa nazo, amma sati nayi niyyar kiyi kafin nazo."
takai hannu ta toshe bakin ta tana cigaba da fad'in
"Um Allah dai yasa ba Ya Abdulrahim ango, kar yajini yayi ball da ni waje."
"Ai kuwa yana nan."
Feeryal ta fad'a tana waro ido.
Miemie ta juya da sauri tana fad'in
"Nashiga uku bari na tsere kafin ya fito."
dariya tayi ta ce
"Ke karya ne me zai zaunar da shi a nan yanzu dai ya d'ibi abinci yafita."
Miemie ta dawo tana cewa
"Na isa yanzu na karbi dukan da ban shirya masa ba, Murad na zuwa anjima yazo ya same ni da kumburarren jiki."
taja kujerar dinnin ta zauna ta dubi Feeryal data soma cin cake d'in ta tana yiwa Miemie dariya ta ce
"Ban gane ba kamar naji kin ce ya d'ibi abinci ya fita,
yaje ina dan yau dai weekend ba aiki bare nace asibiti yaje."
Feeryal takai cake bakin ta na tauna ta ce
"Ina zan sani nima ganin sa nayi a dinning d'in dana fito parlour'n, yana d'iba kuma yayi tafiyarsa."
Miemie ta ce
"Ba dai anan ya kwana ba ke nan?."
Feeryal ta waro ido kad'an ta shake da cake tayi tagwayen tari tare da cewa
"Ya kwana anan kuma Miemie?."
"Dalla jita daga magana ta rud'e shine me, bazai kwana anan ba akan ke ba matarsa bace, ki zauna noke-noke karki san yadda zakiyi ki janyo mijin ki gareki ba,
waya gaya miki yanzu ana haka ai duk wani kunya da sauransu ya kare da zallar kirsa zaki janyo mijinki, ki zauna dai garin kallon ruwa waccan kwad'on matar tasa tayi miki kafa."
Miemie ta karasa maganar da yamutsa fuska.
Feeryal ta bita da kallon mamaki, sai kuma ta girgiza kai tare da yin murmushi ta ce
"Miemie Allah bazan tab'a iyawa ba Sahab ya zauna a inda yake nima na zauan a in da nake, nayiwa Ammie'na alkarin zan zauna dan na cikawa Daddy burinsa, amma bazan tab'a iya abun da kike nufi ba."
Miemie ta mara baki ta ce
"Ai sai kiyi ta rashin iyawa, zaki sha kallo idan akayi auren mu da Murad d'ina, kizo gidan mu kiga yadda ake soyayya."
dariya ita dai ta bita da shi...
Abdulrahim na shiga parlour'n sa, Kuraiba na shigowa daga kofar gefen ta da ke ta cikin parlor'n nasa.
ya nima guri ya zauna kan kujera, tare da d'aura plt da Mug