Showing 6001 words to 9000 words out of 86085 words
Chapter 3 - FEERYAL Part 3 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt
sai ta d'agawa Daddy hankali."
ya yi kwafa yana taune lips.
"Be careful ana wasa da mutuwa ne."
ya fad'a yana wurga masa kallo mai kama da hararar, yana nade hannun rigarsa.
kwafa Ajmal ya kuma tare da taune lips gami da girgiza kai.
Nutsuwa da jin dad'i ya ziyarci Aunty sai godiya da tasbihi ta ke wa Allah subhanahu wata'ala.
Mommy ta matso in da Hajiya take tana cewa
"Hajiya cewa fa kikayi kin amince da auren, Hajiya ko kin mance wa aka aura masa ne."
Hajiya da hankalin ta yafara kwanciya ganin Daddy na da rai bai mutuba ta ce
"Ke da'alla Halima rabani koma wa ya aura masa in dai har bazai mutu ba."
Umma Karima da maganganun Hajiya ya shanye mata ruwan kai,
da sauri ta zame jiki tabar asibitin, dan tana jin idan tacigaba da zama zuciyarta zata tarwatse a yadda take jin kanta..
Sai daf magriba Daddy ya farka, har yanzu su Aunty basu gusa ba, saima kara tuttud'o wa dangi suke,
sai dai da sun zo za'a dakatar da su awani keb'ab'b'en parlour, dan ba'a so a dami shi da surutu.
Daddy na farkawa ana sanar da farkawar nasa, Hajiya ta suri kafa tayi room d'in da yake.
Abdulrahim na tsaye yana cire masa ruwan da yaka re yanzu.
Hajiya ta karaso bakin gadon tana cewa
"Abubakar ka tashi? sannu kaji kayi hakuri ka gafarce ni, in Allah ya yarda bazan sake wata magana ba,
rayuwar ka da lafiyar ka yafi min ko mai, ya jikin naka Abubakar?."
Daddy ya yi murmushin jin dad'i ya ce
"Jiki da sauki sosai Hajiya."
"To madalla zamu tafi gida ba anjima ko."
Daddy ya kalli Abdulrahim yana cewa
"Zan iya tafiya gida anjima ko?."
"After 7 days kafin mu gani ko zaka iya koma wa a kwanakin."
ya fad'a yana gyara rukon ruwan allurar daya zuko cikin Syringe ya kamo hannunsa yana masa ta cikin cannula.
Daddy ya ce
"Hajiya kinji sai nayi kwana bakwai kafin a sallame ni na koma gida."
Hajiya ta ce
"To-to ai shike nan in dai zaka sami lafiya ko wata guda ne ai za'a zauna,
kai abokin turawa zai warke dai babu abun da zai same shi ko?."
baki ya tab'e ba tare da ya yi magana ba ya zare syringe'n.
Aunty ta turo kofar da sallah Ajmal da Shamsuddin su na biye da ita.
wani murmushin farin cikin gani Daddy zaune Aunty ta sake.
daga in da Daddy ke zaune shima ya maida mata murmushin.
Mommy ta turo kofa ta shigo tana wani shashshan kamshi tana cika tana batsewa.
Abdulrahim ya dubi Aunty yana cewa
"A sama masa wani abun ya ce yanzu."
kana ya maida dubansa ga Daddy ya ce
"Daddy zaka iya yin sallah bayan ka d'an tab'a wani abin."
kai Daddy ya jinjina, da sauri Aunty ta fita.
Mommy tabi bayanta da harara, Aunty ta isa in da ta aje basket d'in abincin data koma ta girka masa, dan tasan dama idan ya farka dole zai bukaci abinci.
ta d'auko ta koma d'akin ta soma had'a masa abunda tasan yafi bukata.
bayan Ajmal ya taimaka masa yaje ya wanko bakinsa ta aje masa saman gadon ya soma ci.
"Kai dun gidan ku ina tambayar ka yaushe zaiji sauki kayi burus da ni."
Abdulrahim ya tarkasa 'yan kayakin sa yana cewe
"Ki jira lokacin mana."
ya sa kai ya fice.
Daddy ya ce "Hajiya zanji sauki ai in Allah ya yarda."
Hajiya ta ce "To Allah ya kawo manzon sauki da gaggawa."
Kwanan Daddy uku a asibiti kullum a can su Aunty suke wuni, kwana kuma Ajmal da Shamsuddin ne suke kwana a kanshi.
Umma Karima kam tun da tazo ranar farko bata kara zuwa ba, sai ta fake da wai itama bata jin dad'i ne.
sai yau Feeryal itama ta sami zuwa duba Daddy, dan kullum in tace zataje ta gaishe shi, Aunty takan ce tabari tukunna.
yau Aunty da kanta tace ta shirya suke.
Feeryal bata sake ba dan su Farida da su Ameerah Nabila Sahla yau duk suna gurin, gashi Miemie bata zo ba,
sukayi ta mata habaici tana gefe.
dataga zaman shirun ya dame ta sai ta d'au wayarta tasoma sana'ar ta wato buga game.
magana taji a kanta tayi saurin d'ago wa.
wani saurayi ne yana tsaye a kanta ya kurawa kyakkyawan surar ta ido yana fad'in
"Sarki ya tabbata ga ubangijin daya halicci wannan sura."
"Feeryal zo ki rike min wannan."
ta jiyo maganar Aunty daga bayan su.
ta mike da sauri tana d'agowa suka had'a ido da Abdulrahim.
da sauri ta bi hanyar da Aunty take.
Da daddare kamar yadda suka saba, direba ya kwashi su Hajiya da Mommy da wasu daga cikin 'yan gidan.
Aunty ta d'au jakar ta tana kokarin fita taje ta same su su koma gida.
Daddy ya ce
"Fad'imatu yau banda ke a tafiyar ki zauna ki taya ni zama kad'aici na dami na."
"Daddy naga gasu Ajmal da Shamsuddin, basu wadatar ba."
"Su ba sa'an hirata bane basusan wace irin hira nafi so ba, ke kad'ai kika sani dan haka ki zauna ko kuma mutafi gidan tare."
"Aa Daddy baka gama warkewa ba, ai da Abdulrahim ya sallame ka, to Daddy Feeryal fa da wa zataje gida, kasan bazai yuwu ta bisu ba."
Daddy ya ce
"Baga mijin ta ba in zai tafi sai ya d'auki matarsa su koma gida tare."
Daddy na rufa baki Abdulrahim na shigowa yana rataye da jakan kayan system nasa da wasu 'yan tarkacen sa.
ya karaso yana fad'in
"Daddy ya jikin akwai wata matsala ne?."
Daddy ya ce
"Babu komai jiki da sauki sosai Abdulrahim zaka iya tafiyarka, amma ka d'auki matarka tana waje ku koma gida tare."
bai yi magana ba ya sa kai yana fad'in
"Sai da safe.........!
Yana fita Dr Imran ya taho inda yake.
"AA na kiraka baka d'aga ba ashe kana gurin Daddy."
tafiya ya soma yana dad'in
"Ya akayi?."
Dr Imran ya ce
"Dr Daniel ne ya kirani yace ya kiraka baka d'aga ba."
"Kace masa Daddy na is seriously ill, next week zan shigo."
Dr Imran ya ce "Okay zan sanarasa."
Nurse Samira ke takowa tana nufo in da suke.
Dr Imran ya ce "Oh yau tana night ashe, anya bazakayi na uku da ita ba kuwa?."
Dr Imran ya yi maganar cikin zolaya.
bai kulashi ba ya ci gaba da tafiyarsa.
Samira ta karaso da sauri tana narke murya
"Sir the patient of that room his BP is higher."
"Je ka duba shi."
ya ce wa Dr Imran, fuska tad'an kwab'e bata so haka ba ta so a ce shine zaije da kansa dan ta samu damar tsayuwa kusa da shi, ta shaki kamshinsa mai dad'i.
Dr Imran ya yi hanyar room d'in tabi bayan sa.
Feeryal na zaune ta nad'e hannayen ta cikin mayafin ta, da alama sanyi take ji dan gurin akwai sanyi sosai kanta a sunkuye.
"Let's go."
da sauri ta d'ago jin maganar daf da ita.
shi ta gani yasa kai ya wuce tabi bayansa da kallo.
sai kuma ta waiga gefe da gefen ta zaton ta da wani yake.
har yafita harabar asibitin bata motsa ba.
yakai 10mit da fita Aunty ta fito, baki ta rike ganin ta zaune, sai mammatse ido take da bacci ke cike tap cikin su.
ta karaso in da take tana fad'in
"Ke Feeryal baku tafi ba ashe ko Abdulrahim d'in bai gama abin da yake bane?."
baki ta turo
"Ammie ni bacci nake ji."
"Daddy ya ce kutafi da Abdulrahim wata kila bai gama abun da yake bane, munyi waya da Ammah'n Miemie tana jiran ki idan kun isa, can zakije ki kwana sashin ta."
"Ammie kwana zakiyi a nan?."
"Eh Feeryal sai gobe zan dawo."
Feeryal zata kuma magana Dr Imran daya fito daga duba Patient, ya karaso yana gaida Aunty ta amsa tana tambayar sa.
"Abdulrahim fa ko wani aikin yake?."
ya ce
"AA ya fita fa bai jima da fita ba bari muga ko ya tafi."
ya leka ta waje ya juyo yana fad'in
"Ga motar sa can bai tafi ba."
Aunty ta ce
"Jiranki yake kije ku tafi taso maza, ga Daddy na kirana bari naje sai da safe ko 'yanmatan Ammie."
Aunty ta juya tana d'aga kiran Daddy da ya shigo wayarta.
"Gani zuwa Daddy."
tayi maganar tana nufar room d'in da yake da sauri.
A hankali tasoma takawa tana wasa da bakin mgyalen ta.
ta sako kafarta a step d'in karshe na sauka daga kofar da zata sadaka da farfajiyar asibitin,
idan kunnen ta ya jiyar mata dai-dai tabbas taji maganar sa amma batayi zaton da ita yake ba.
yanda ta ke sauka gaba d'aya ilahirin jikin ta motsawa yake, musamman kirjinta da nonuwanta da bata sa musu bra ba suke rawa cikin rigarta.
a hankali take takowa cikin yanayin ta mai sanyi.
"Wow kai kaga wata halitta kuwa."
cewar d'ya daga cikin wasu maza uku da ke tsaye a farfajiyar asibitin.
duk suka maida dubansu gare ta kowa na fad'in albarkacin bakin sa.
d'aya daga cikin su ya ce
"Kai gaskiya bari naje na tsala wannan."
ya soma takowa gareta ya sha gabanta yana fad'in
"Hi 'yammata ga mota can ko zaki shiga murage miki hanya, kema dubiyan kika zo ne?."
ido ta bisa da shi tare da girgiza kai, ta kauce tabi gefe ta karasa jikin motan.
taja ta tsaya jiki a sanyaye.
yana zaune cikin motan waya a hannunsa yana daddannawa. aje wayar yayi tare da yiwa motar key batare da ya kalli inda take ba ya ce
"You are waisting my time! ."
a hankali ta saka hannu zata bud'e gidan baya, tajisa a rufe ta matso ta bud'e
gaba ta shiga tana rufe murfin ya fige motar yayi hon masu gadi suka bud'e masa get ya fita.
a hankali ta gyara zamanta tare da jan numfashi ta sauke.
wani sassanyan kamshi na bugar hancin ta,
a hankali ta juyar da fuskanta ta jikin glass tana kallon gefe.
Sunyi tafiyar da yakai na 20min babu wanda ya yi tari cikin su.
a sannu bacci ke fizgarta ta d'an lumshe ido bacci nason d'aukarta.
da sauri ta ware idanunta afirgice jin yadda ya taka burgi zaton ta karo sukayi, jikin ta ya kama cirawa, ta d'ago a zabure tana ware ido kan titi.
ganin ba karo ba ne ta juyo da sauri ta kalle sa.
ganin idanunsa a kanta a hankali ta sunkuyar da kai tana wasa da 'yan yatsunta.
ji tayi ya fisge mayafinta a razane ta waro ido.
tana binsa da kallon tsoro.
ido ya kura mata fuskarsa babu wasa, ya mika hanu ya fisgota ta matso daf da shi.
dibirbircewa tayi nan da nan idanunta suka kawo kwalla.
ya saka hannu saman kafad'arta yad'an ja rigarta. ya tura yatsa yana zaga gurin kamar mai niman wani abu,
da d'an sauri ya ciro hannun sa ya sauke shi kan kirjinta ta saman rigarta ya laluma shi.
wani irin waro ido tayi jin hannunsa saman nonuwanta, kamar dai yadda yayi a kafad'arta, kamar mai niman wani abu.
sake ta ya yi yana fad'in
"Stupid Be careful!."
saurin matsawa tayi tana binsa da kallon tsoro.
ya bud'e mota ya fita.
tabi bayansa da kallo wani katon Mll da suke tsaye daf da shi ya shiga.
sai sannan ta sauke numfashi ta kai hannu ta tab'a kafad'ar ta zuwa saman kirjinta,
ko me yake nima oho.
ta kwab'e fuska hawaye na shirin zuba, gaba d'aya a mugun tsorace take.
bai wani jima ba ta hango sa ya fito daga ciki yana tahowa hannunsa rike da bakar laida mai girma.
ya karaso ya bud'e gidan baya ya saka laidar ciki, kana ya dawo mazaunin direba ya shiga yaja motar.
kankame jikinta tayi har suka isa gida.
yana gyara parking tayi saurin kai hannu zata bud'e gefen da take, taji sa gam.
ta d'an juyo ta dube shi jiki a sanyaye.
hannu ya saka ta baya ya d'auko laidar ya saka mata shi kan cinyar ta, sannan ya bud'e motar.
bin laidar tayi da ido kana ta kai hannu ta bud'e ta fita rike da laidar.
Miemie dake tsaye tana zaman jiran isowarsu dan Aunty ta kira Ammah ta sanar mata sun taso, ta turo Miemie tazo ta jira isowarta.
Miemie ta nufo ta da sauri tana binta da da dariya, ta karaso ta karb'i laidar hannunta tana fad'in
"Kawo na karb'e ki Aunty Feeryal."
hararar ta Feeryal tayi.
Miemie ta saki dariya tana cewa
"To ya zanyi tun da kin aure min Yaya dole na kiraki Aunty, dama wayon na kiraki Aunty ce yasa kikace sai Yaya na."
baki Feeryal ta bud'e Miemie ta ce
"Karya na fad'a ne? muje gashi can tahowa kada ya ce na tsaida mishi mata tana shan wuya."
Feeryal ta kwab'e fuska kamar zatayi kuka.
da sauri ta sa kai dan alla-alla take ta ganta cikin d'aki ko zata ji nutsuwa ya zo mata.
Ammah na parlour tana ganin su ta mike tana cewa
"Yauwa kun iso Feeryal? to bari naje na kwanta, kuyi bacci da wuri dai kar ku zauna hirar shiririta ku kasa tashi da asuba."
sukace to.
Ammah ta shige d'aki suma suka shige bedroom d'in Miemie.
Feeryal ta zube bakin gado tare da sauke numfashi.
ta zame gyalen kanta ta jefashi gefe.
Miemie ta zauna gefen ta tare da aje laidar a tsakiyar su, tana fad'in
"Wai tsarabar me aka kawo mana ne, najisa da nauyi da alamar munyi babban kamuwa."
Feeryal batayi magana ba sai zubawa laidar ido da tayi, tunanin abin da yamata a mota ne yake ta mata yawo cikin kwakwalwa, tsoro mai had'e da fargaba suka sami nasarar lullub'e ta.
ta gaza fahimtar me hakan yake nufi.
Miemie ta soma cicciro kayan da suke cikin laidar.
da mamaki duk suka waro ido kan kayan.
manyan hijabai ne kala gomo duk a cikin laidodinsu.
sai bra dozin uku mai guda shabibbiyu.
Miemie ta kalli Feeryal Feeryal ta kalleta.
dariya ta kwashe da shi cikin muryar dariya take fad'in
"Yafi so ya ganki cikin hijabi, gaskiyar sa ya yi kishin kayan sa kar wani d'an hau ya gane masa kayansa,
ikon Allah har shima ya gane bakya son sa bra ke bakisan idan kina tafiya kirjinki matsawa suke ba, ko a cikin gyale ne kuwa."
Feeryal tayi rau-rau da ido sai ga hawaye.
wato hakan ne yasashi lalub'arta ya tabbatar wa kansa babu bra'n a jikin ta.
hawaye suka dad'a zubo mata.
Miemie ta kuma kwashewa da dariya ta ce
"To meye na kukan ya gwada miki baya son ki rika yawo haka sai ki kiyaye."
ture kayan tayi ta mike ta shige bathroom, Miemie ta bita da dariya.
tayi wanka tafito d'aure da towel, ta saka kayan baccin Miemie,ta haye gado ta kwanta gefen ta
Miemie dake rungume da pillow tana waya Murad d'in ta.
Washegari sai dare Aunty ta dawo shima dakyar Daddy ya barta.
a daren ta shigo sashin Ammah ta d'auki d'iyarta suka koma sashin su.
washegari da safe Miemie ta biyo ta da laidar kayan ta.
Aunty tabi kayan da kallo sai kuma ta girgiza kai tayi murmushi.
kwanan Daddy 8 sai sannan Abdulrahim ya sallame shi.
tun zuwan Feeryal sau d'ayan nan kuwa bata kara zuwa ba.
satin Daddy guda da dawowa yasa aka akayi odar kayan d'akin Feeryal daga waje, dan yace a satin zata tare.
sai da kayan ya iso Nigeria sannan ya sanarwa Abdulrahim za'a zo a shirya mata kayanta a d'aya gefen b'angaren sa.....!
Kaya na isowa Daddy yasa aka wuce dashi direct b'angaen Abdulrahim.
a d'aya plat d'in da ke gefen nashi aka zuba kayan.
wanda sashi uku ne cikin side d'in nasa, nashi upstairs a tsakiya sai na Kuraiba a gefe ta hagu sai wanda aka zubawa Feeryal kayanta a ciki ta b'angaren dama,
in da ko wannen su da kofa sakanin su da b'angaren nasa.
ma'aikatan da aka taho dasu daga kasar da aka siyo kayan suka soma Arrangement d'in kayan yadda ya kamata, abunka da aikin mutum basu d'au wani lokacin kirkiba suka gama shirya komai a inda ya kamata.
kama daga babban parlour bedroom's guda hud'u zuwa bathroom's babban kitchen da sauransu.
nan da nan guri ya d'auki kyalkyali tamkar a turai.
Kuraiba tun da taji shigowar mota tafito ta leka.
ganin kaya cikin babbar mota hankalin ta ya dugunzuma.
ganin goggo Bishira kanwar su Daddy da Ammah sun shigo suna nunawa wad'anda suka kawo kayan in da zasu shiga da shi.
da tabbata da gaske ne jita-jitan da take ji game da tarewan Feeryal d'in.
da sauri ta juya ta koma ciki, ta zari makullin motarta, da mayafi ta fito ta shiga motar ta bar gidan.
A b'angaren Umma Karima da Siyama kuwa.
damuwa yataru ya dame su, Siyama ta dubi Aunty'n nata da duk nutsuwa ya kaurace musu ta ce
"Aunty Karima yanzu shike nan komai yatashi a banza shi ke nan, na kara narasa Abdulrahim a karo na biyu, na shiga uku ina zan sa kaina, ji nake kamar naje na kashe Feeryal sannan na kashe kaina kwa ya rasa gabad'an mu."
"Uhum nafiki shiga tashin hankali Siyama,
tashin hankalin da nake jina ciki yanzu yafi na lokacin aurenshi da Kuraiba,
sannan babban bakincikina ma boka ya gaza ganin su cikin kwaryar tsafinsa, bare yasan matakin da ya kamata ya d'auka a kansu,
wanan sinanniyar yarinyar wlh sai naga karshenki a duniyar nan!
yadda kike ta b'ata min shiri sai kin biduniya ba takalmi in zanyi yawo tsirara wlh sai na sa kin tsani kanki."
Hajiya na samin labarin shigowar kayan gidan tasa a kirawo mata Daddy.
Daddy ya shigo ya sameta a parlour'n ta.
bayan ya gaishe ta tayi masa ya jiki ya ce da sauki.
Hajiya ta gyara zama tana fad'in
"Naji labarin wai an kawo kayan d'akin da yarinyar nan, ashe kasan turawa ka aika aka siyo,
to ni dai damuwa ta karka mance da ko waye ita, kar ka zauna kayita wahalar banza a kanta, 'yar da ba wani asali take da shi ba,
tun da ka nace kace sai ka had'a ta da abokin turawa to shi ke nan ni dai ina gudun wani abun da zaizo ya biyo baya."
"Hajiya insha'allahu babu abin da zai faru sai alhaki, Allah dai ya wuce mana gaba."
Hajiya ta kawar da kai tana fad'in
amin.
Daddy ya yi saurin mikewa dan ya gano so take takuma b'aud'e hanya gara ya yi azama tun kan, ta karkace hanya...
Kiran wayar Mom d'in Kuraiba ce yashigo wayar Mommy.
Mommy ta d'aga da sallama gami da fara'a tana fad'in
"Hajiya Luba an wuni lafiya ya gidan."
daga cikin wayar Hajiya Luba ta ce
"Ina ko lafiya tun daga gidan ki rashin lafiya ya soma har zuwa gida na,
yanzu fisabilillahi Hajiya Halima irin sakayyar da d'anki zai mana ke nan,
a tun tarihin kawayen mu babu wata wanda aka tab'a mata haka, ace aure ko shekara baiyi ba d'anki ya kuma karo aure,
haba wace irin rayuwa ce wannan; ga shi tashin hankali ya haifar mata zuban jini tana da ciki, gata a kwance ta shigo min a firgice, haba Hajiya Halima taya za'ayi mana haka gaskiya baku kyauta mana ba."
Mommy ta ce
"Allah ya baku hakuri Hajiya Luba wlh wannan auren ba da son raina aka d'aura shi ba, nayi duk iya bakin kokari na ganin hakan baifaruba amma an nuna min fin karfi,
amma ina mai tabbatar miki auren nan babu