Showing 36001 words to 39000 words out of 86085 words
Chapter 13 - FEERYAL Part 3 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt
yawa basai ta kofar can ba."
ta yi wani mikewa da karfi cikin b'acin rai ya sa mata kafa ta zube kasa.
wani irin ihu gami da hargagi tayi, ta d'ago tana binsa da wani irin kallo da kwayar idanunta suka sauya isuwa wani kala na ban tsoro.
mari ya d'auke ta da shi cikin fusatacciyar murya ya ce
"D'auke idanun ku a kai na!."
kururuwa ta sayi tare da birgima a kasa tamkar wacce aka zubawa ruwan zafi a jiki.
tana fad'in
"Kai bil'adama karka sake dukan mu da wannan hanun naka,
mai kamada garwashi, idan ba haka ba zamuga bayan ka."
bata rufa baki ba yakuma d'auketa da mari,
ihu ta kuma tana birgima da maganganu barkatai da muryoyi daban-daban.
ayoyin alkur'ani ya soma karantawa yana tufa mata, tuni jikin ta ya d'auki rawa tana.
tana fad'in
"Ka dai na kona mu ka daina kona mu, bazamu fita a jikinta ba har sai mun kaita ga sarkin bakaken aljanu,
bazamuyi asarar shekara da shekaru muna neman ta mu same ta yanzu mu kasa tafiya da ita baaaa, ka dai na kona muuuuu!
bazamu janye baaaaa sai mun tafi da itaaaaa!."
ta zabura zata mike ya shako wuyanta tare da taka kafafunta da nashi kafan.
sannan yaci gaba da tofa mata ayoyin Alkur'ani.
wan da tuni jikin ta ya shiga kakkarwa, tana kokarin janye hannunsa a wuyanta ta kasa.
nan da nan zufa ya shiga tsastsafo mata.
ko wani hudan gashi na jikin ta, fita yake da zufa hatta daga cikin gashin kanta kuwa zufa ne ke gangarowa zuwa fuskarta.
Da kyar ta iya bud'e baki cikin muryar jin azaba suke fad'in
"Zamu fita zamu tafi ka dakata kada ka kashe mu, mun rantse maka zamu kauce a jikin ta."
a fusace ya ce
"Fita zukuyi duka a jikinta ba kaucewa ba! idan kuka sake muka kara karo da ku to na rantse muku da girman zatin Allah sai na kashe ku! kada ku sake tunanin dawowa jikin ta, idan kuka kuma sai na kashe kuuuu!!."
yayi maganar cikin karaji sosai mai firgita kunnuwan duk mai saurara.
kai take gyad'awa ba kakkautawa tana fad'in
"Mun rantse munyi alkawari duk randa muka kara dawowa ka kashe mu, sakar mana manumfasa zamu tafi, zamu fita a jikin ta bazamu sake dawowa ba mun d'au alkawari, hannunka akwai garwashi ka sake mu zaka kashe mu, zamu fita zamu fita."
ya sake mata wuya yana binta da mugun kallo, da karfi ta saki tawayen atishawa sau uku a jere jikinta ya sake ta sulale kasa.
Ya mike tsaye yana jan dogon tsaki, ya gyara zaman rigarsa.
ya sunkuya ya d'ago ta cak ya nufi cikin bathroom da ita.
cikin bathtub ya direta,
a sannu yashiga zare kayan jikinta,
ya tub'e ta tsaf batare da ya cire bra da pant d'in jikin ta ba.
yana tallafe da ita, yana daga wajen bathtub d'in.
kana ya soma tara ruwan d'umi cikin bathtub d'in.
nannauyan numfashi ta sauke jin d'umin ruwan na rasa ta, ta juya kai ta dad'a manna kanta jikin hannunsa kamar jaririya a hannun uwanta.
a hankali take sauke numfashi.
ido ya kurawa fuskarta bacci tayi a hannunsa.
d'aya hannun nasa ya saka cikin ruwan ya d'iba ya wanke mata fuska yayi hakan har sau uku.
kana a hankali yakai hannunsa zuwa bayan ta, ya b'alle mab'allin bra'n jikinta ya zare shi yana kauda kai da ganin ta.
sannan ya cirota ya had'eta da kirjinsa ido ya rumtse jin zuciyar sa ya buga.
a sannu ya ware idon akan ta, da sauri ya d'auke kai daga kallonta.
ya zaro towel ya nad'eta da shi,
yafice a bayin da d'an sauri ya karasa bakin gado ya kwantar da ita.
ya janyo blanket ya rufeta yasa hannu ta cikin bargon ya zaro pant d'in jikinta, da yake a jike.
ya ajiye shi nan bakin gadon kana ya juya ya nufi kofa ya zaro key cikin aljuhun sa ya bud'e kofar ya fita.
A b'angaren Maryam ko da ta ketaro titin bata ganta ba.
tashi waige-waige tana tambayar mutanen gurin.
tanayi musu kwatancen ta, wasu suka ce mata sunga san da wani ya d'auke ta ya sa a mota.
kuka maryam ta fashe da shi tana fad'in ta shiga uku.
ta koma in da motar su yake cikin kuka take fad'a wa direban su abunda ke faruwa.
direban ma yashiga tashin hankali.
ta shiga motar ta ce suyi sauri su tafi gida su sanar.
suna isa gida Maryam ta shigo da kukan ta.
hankali tashe Hajja Umma take tambayar ta meke faruwa ina Feeryal.
cikin muryar kuka take sanar mata abun da ya faru.
Hajja Umma tayi salati tana kwad'awa Abba kira.
Abba ya sauko hankali tashe, jin abunda ke faruwa hankalin sa yayi bala'in tashi.
nan da nan yayi report, wa jami'an da kes d'in ta na wancan karon yake hannun su.
nan da nan aka baza jami'ai da tuanin mutanen mai tawargar d'aukar amarya ne,
suka d'auke ta.
dan har yanzu yana tsare ana ta kan kama mutanen sa...
Sai wajen kare 4 na yamma ta farka daga nannauyan baccin da take.
a hankali ta mike tana ma mammatse ido jin jikin ta ya bala'in mata tsami.
mika tayi gami da salati tana jin kamar an mata duka duk jikinta yayi laushi.
a hankali ta ware idanunta a cikin d'akin, da mamaki take dad'a ware idanunta, ganin d'akin ya sauya mata.
hannu ta kai ta mussuke idanunta, takuma ware shi da kyau cikin d'aki.
sai kuma da sauri ta janye bargon dake rufe a jikinta,
ta kai duban ta jikinta tana mamakin ganin ta babu kaya sai towel shima towel d'in ba'a d'aure yake ajikin nata ba.
da sauri ta ja towel d'in ta d'aura a kirjin ta,
da sauri ta zamo bakin gadon ta sako kafafunta kasa, tana kokarin mikewa tsaye.
ta hango pant d'in ta a gefe.
mamaki yakuma kamata.
kafafunta ta ta aje kasa tana kokarin mikewa ba shiri ta koma ta zauna tana fad'in
"Wash."
jin yadda kafar tayi tsami tana yi mata zafi sosai.
kallon kafar tayi taga kafar tayi ja.
a hankali takai hannu ta shafo wuyanta da take jikin sa kamar ba nata ba.
karar bud'e kofar da taji ne yasata d'agowa da sauri.
wani irin zabura tayi da ganin shi. kwakwalwarta ya tsaya ya daina aiki, me yakawo ta nan, ko shine zatace me yakawo shi.
to ma wai a ina take ne?.
ganin ya na takowa cikin d'akin gaba d'aya ta kid'ime tashiga ja da baya ta haye sakiyar gadon.
tana nuna shi da hanu murya na rawa take fad'in
"Ina ne nan me yakawo ni nan? kar ka matso ni."
ganin yana kuma nufo ta ta zamo ta d'aya gefen ta duro a gadon,
ta yarfe hannu tana fad'in
"Wayyo kafata."
ta d'aga kafar da kyar ta nufi kofa.
ganin kokarin fita take ya daka mata tsawa.
"Ke kar ki sake ki fita a haka."
bata tsaya ba ta mika hannu zata bud'e kofar,
ya yi taku biyu zuwa uku ya damko hannunta ya dawo da ita ciki.
kuka ta saka tana fad'in
"Ni dai tafiya zanyi wayyo Ammie na."
gaba d'aya ta birkice tana son kwatar hannunta da ko kyakkyawar motsi hannun baiyi ba a cikin nasa.
ido ya zuba mata kamar mai son karantar wani abu.
da sauri ya d'aga ta cak ya direta kan gado,
sai kuma da sauri ya kai hannu ya ja towel d'in jikinta kasa nonuwanta suka bayyana.
wani irin b'ari jikinta yakara,
ta saki kara wani irin masifaffen tsoro yakuma lullub'e ta.
kai tashiga juyawa tana fad'in
"Sahaaab kar kayi min dan Allah."
da sauri ya kuma rirriketa yana cewa
"Tsaya mugani."
yayi maganar idanun sa a kan ababen kirjinta......!
Ya kurawa nonuwan ta ido dai-dai kan nipples d'in,
sai kuma da d'an sauri ya kai hannu ya cafko d'aya yana dad'a kurawa nipple d'in ido.
zabura tayi jin yadda ya cafko breast nata, ta ja numfashi mai cike da mashahuriyar tsoro cak numfashin ya tsaya.
kallon sa ya maida kan fuskarta kana ya saki nonon nata ya kai yatsarsa hancinta, ido ya d'an waro jin bata numfashi.
ya mike yana mamakin yadda take babu wuyan tsoro yasakata suma.
ya sauko a gadon yaje ya d'au ko kayan ta daya cire mata, d'azu yanzu a bushe suke,
ya saka mata underwear da doguwar rigar ban da bra da pant.
ya sunkuce ta yayi waje da ita, yana kallon fuskarta da idanunta ke a lumshe.
cikin mota ya sakata gidan baya ya dawo mazaunen direba ya ja motar mai gadi ya bud'e masa ya fita.
yana fita daga gidan titi ya ketare ya isa bakin get d'in
AA FIYA HOSPITAL, asibitin sa da ke cikin garin Abuja.
wan da yake kusa da gidan sa titi ce ta rabasu.
duk weekend yana Abuja ranar juma'a yake zuwa da yamma yaga patients asabar da lahadi, ranar Monday kuma yabi jirgi ya koma Lagos da safe.
cikin hanzari security'n dake bakin get d'in asibitin suka wangale masa get, yasako hancin motar duk suka rusuna suna miko masa gaisuwa.
ya gyara pakin a farfajiyar asibitin, yafito da sauri ya bud'e gefen da take ya cirota ya rungumo ta a jikin sa da sauri yayi cikin asibitin da ita.
yana shiga hankalin jama'a da ma'aikatan dake cikin asibitin yadawo kansa.
da sauri wata Nurse ta turo welcher, in da wasu Nurse's maza uku suka nufo sa suka mika hannu zasu karb'e ta.
hannu ya d'aga musu tare da furta
"It's okay."
ya sakai da sauri ya shige office d'insa.
a kan gadon dake cikin office d'in ya shinfid'a ta, kana cikin hanzari ya shiga bata taimakon gaggawa ya d'aura mata drip mai d'auke da allurai cikin sa.
cikin hanzari ya kunna na'uwar Scanning.
ya matso ya ja rigarta sama yana kallon shafaffen cikin ta fari tass.
a sannu ya d'aura scanner kasan mararta.
yayin da ya maida idanunsa kan computer, yana d'an yawo da shi kasan mararta.
ido ya waro sosai kan computer yana mai dad'a d'an danna scanner a marar nata.
da sauri ya kalli fuskarta kana ya maida dubansa ga computer, yana sauke ajiyan zuciya a fili.
knocking akayi batare da ya janye idanunsa daga kallon na'urar ba ya ce
"Who is at the door?."
daga bakin kofar akace
"Im Dr Khadija Barau Can I come in?."
tsayuwarsa ya gyara ya dad'a jan underwear jikin ta ya rufe cinyoyin ta zuwa gwuiwarta,
sannan ya ce
"Yes, come in."
ta turo kofar da sallama ta shigo, babbar mace ce da shekarun ta zai iya kaiwa 40 tana sanye da medical glass.
ita d'in d'aya daga cikin likitotin da suke aiki da shi ne, Dr Khadija Barau tana da zama da iyalanta a nan cikin garin Abuja,
a matsayin kani ta d'auke shi tana bashi kulawa irin na yaya da kani,
a duk san da yake Abuja d'awainiyar abincin sa a wuyanta ya ke sanin baya cin abincin masu aiki.
kullum direban ta yana hanyar kawo masa abincin safe da rana da dare, a gidan sa dake nan.
Ta karaso ciki tana fad'in
"Doctor naga shigowarka lokacin ina duba wani mara lafiya ne, ba dai bigeta kayi da mota ba, subhanallah buguwar a ciki ke nan, Allah yasa babu wata matsala sosai? ."
ya ce
"No, she is my wife."
zaman gilashin idanunta ta gyara da kyau, kana ta kalli Feeryal dake kwance sannan ta maida idanunta kan computer ta waro ido tana cewa
"Wow! I congratulate you."
kai ya jinjina yana kokarin numfashin ta ya dawo.
Dr Khadija ta masa ta gurin kafafunta ta saka tafin hannunta tana gogo tafin kafanta.
ta ce
"Doctor, hurry up and get her breath back, don't take too long."
bata rufa baki ba ta ja numfashi, ta zabura tana kokarin mikewa.
Dr Khadija ta bita da murmushi tana fad'in
"Sannu kinji."
ido ta kura mata ta lumshe idanunta ta bud'e su a kanta.
firgigit tayi ta mike zaune tana kokarin durowa a gadon.
tayi saurin ce mata
"Bi a hankali, a kwai drip a hannunki."
da sauri ta kalli hannun nata kana ta kalle shi.
Dr Khadija ta ce
"Dr Allah ya sawaka bari naje akwai patients a layi."
ta fita tana mata Allah ya sawaka.
tana ganin fitarta ta kuma yunkurin sauka, hannun ta da ruwa ke shiga ya rike.
kuma yunkurin sauka tayi ya ce
"Ki jira ya karasa shiga."
kallon ruwan tayi saura kiris, ta kalle shi tana kwab'e fuska zatayi kuka.
cikin muryar da ke kunshe da son yin kuka ta ce
"Ni gida zan tafi."
tayi maganar tana kokarin kwatar hannunta ta kasa.
ido ya zuba mata hawaye ya fara gangara fuskarta.
bai sake ta ba yana rike da hannun nata bai kuma yi magana ba.
yana kallon yadda hawaye ke bin fuskarta.
yana tsaye rike da hannun nata har ruwan ya karasa shiga,
ya cire mata.
ai ko da sauri ta dire a gadon tana yarfe hannu.
key ya d'auka ya bud'e d'ya kofar wan da kofar fita ce ta baya.
alama ya yi mata ta zo ta wuce.
a hankali ta tako ta wuce yabi bayanta.
ke b'abb'en hanya ce wan da shi kad'ai yake bi, idan zai shigo asibitin ko zai fita, a kwai motar hawan sa a d'an ma dai-dai cin parking lot a gurin.
motar ya bud'e ya shiga san nan yayi mata alama da ta shigo.
jikinta na d'ari-d'ari ta shiga yaja motar mai gadin dake bakin get d'in wannan hanyar ya bud'e suka fita.
tana ta raba ido wai ya akayi ne ta ke ta ganin ta a wurare daban-daban, wan da ba ita take kawo kanta ba.
tunanin ta ne ya tsaya ganin iya titi ya ketare yayi not a bakin wani katon get.
ganin yana kokarin shiga gidan tayi saurin kallon shi murya a sanyaye ta ce
"Sahab nan ba gidan bane."
kallon ta yi sannan ya kuma mai idanunsa ga hanya, ya karasa ciki ya gyara parking sannan ya bud'e ya fita.
ya zaga gefen da take ya bud'e yayi mata alama data sauka.
jiki a sanyaye ta zuro fararen kafafun ta da babu takalmi kasa.
ya juya ya samo tafiya tabi bayansa bayan ta rufe motar.
tana tafe tana waige-waige wai shin a Nigeria take ko a wani kasar dan gidan bai yi mata kamada a Nigeria take ba.
a bun da ya kuma bata mamaki yana isowa jikin kofar wanda yake na glass ne gaba d'aya glass d'in ya kawo haske da kaloli masu kyau, sauti kuma ya biyo baya
"You are welcome sir."
ido ta ware sosai tabbas daga jikin gilashin sautin ke tashi.
sannan ya zuge da kansa, ya sa kai ya shi tabi bayansa a hankali.
ganin ta bayyana cikin wani hamshakin parlour taja ta tsaya.
Wani kofa ya bud'e ya shiga jim kad'an ya fito har lokacin tana tsaye.
ya tako cikin parlour'n ya zauna kan d'aya daga cikin kujeru na alfarma dake cikin parlour'n, ya d'au rimut ya kunna tv batare da ya kalli in da take ba ya ce
"Kije kiyi sallah."
da sauri ta kalle shi ta ce
"Ni gida zan tafi."
d'agowa ya yi ya wurga mata wani kallo mai shiga jiki
"Ba zakiyi sallar ba?."
ya fad'a yana tsare ta da ido.
baki ta cuno ta tare da yin kasa da kanta.
sanna ta soma d'aga kafarta ta nufi kofar da taga ya shiga.
tabi d'akin da kallo lallai in ba ta mance ba wannan d'akin ta bud'e ido ta ganta a ciki kafin yanzu.
a hankali ta taka ta nufi kofar da tafi yakinin nan ne bathroom ta bud'e ta shiga.
a sannu
ta tub'e kayan jikinta tayi wanka tare da yin al'wala ta d'auro towel da tagani a bayin, tad'anyi jim bata iya wanka ta maida kayan da ta cire.
a hankali ta bud'o kofar ta leko babu kowa da sauri ta fito.
rike da kayan tana tunanin taya zatayi sallar ba hijab kayan kuma bazata iya mayarwa jikin ta ba.
tana saka da tunanin aka turo kofar, da sauri ta kalli kofar tana kare jikinta da gyalen ta.
ya karaso cikin d'akin ya aje laidar hannunsa bakin gado ya juya ya fita batare da yace ko mai ba.
yana fita tayi sauri ta matso ta bud'e laidar.
abaya ce a laidar sa da hijab shima a cikin laidar sa, da pant da bra.
da sauri ta saka kayan tazura hijab dai-dai lokacin da ake kwad'a Kiran sallar magriba.
ta haye sallayar da ta gani cikin d'akin, ta fuskanci ta in da sallayar ke kallo ta tada sallah.
tana idarwa ta mike da sauri ta fito parlour.
ganin baya nan ta nufi kofar sai dai ta rasa ta yadda ake bud'e kofar,
ta koma d'akin da tunanin masallaci ya tafi.
tana zaune tajiyo kiran sallar isha
bayan ta gabatar ta zauna zaman jiran shigowar sa ya bud'e mata ta tafi.
ta gumi ta buga tana tunanin ta yadda akayi ma tazo nan.
tabbas tasan kasuwa sukaje taga wasu suna kallonta sannan suka biyo ta daga nan bata kuma iya tuna ko mai ba.
akasan ranta take fad'in
"To ina Aunty Maryam kar dai ace itama sun bita,
to ya akayi kuma na ganni a nan tare da Sahab??."
haka ta rika tambayar kanta da kanta da bata da amsar da zata baiwa kanta.
gashi bata ga wayarta ba ba bare ta kira Maryam d'in ko Hajja Umma.
bata ankara ba taga 8 ta gota, ta mike da sauri ta isa bakin kofa, sai jin kofar tayi a rufe.
da mamaki ta koma ta zauna bakin gado, ta kuma buga tagumi.
sai wajen takwas da rabi taji alamar ana bud'e kofar.
yana shiga ta mike da sauri.
ya karaso ya aje mata basket d'in abincin da Dr Khadija ta aiko masa da shi, sanin su biyu ne abincin yafi na inda da take aiko masa.
tun kafin yayi magana
ta shiga girgiza kai tana fad'in
"Na koshi na koshi bana jin yunwa, dan Allah Sahab gida zan tafi."
tayi maganar da sauri kamar zatayi kuka.
kallon ta yayi ta marairaice fuska hawaye ya cika kyakyawan idanunta.
ya juya tabi bayan sa da sauri har tana had'a wa da sassarfa.
ganin ya shige wani bedroom taja ta tsaya jim kad'an ya fito da makullin moto tabi shi da sauri.
tun kafin yace ta shiga mota ta bud'e ta shige.
sai da taga sun haura titi kafin tasoma jin nutsuwa.
ta rungume hannayenta ta cikin hijab dan sabo da sanyin EC dake tashi cikin motar.
idanunta akan hanya tana alla-alla su isa.
tafi mai nisa sukayi gidan Alhaji Tahir Abbas da gidan sa da rata sosai.
suna haurawa titin da zai sada su da gidan Alhaji Tahir Abbas ta kuma jin dad'i.
suna isa dai-dai get d'in gidan yayi parking a bakin get.
da sauri ta kai hannu zata bud'e kofar taji sa a rufe,
ta juyo a d'an sanyaye ta kalle shi.
da sauri ta janye idanunta sakamakon had'uwar da idanunsu ya yi.
'yar karamar laida mai d'auke da tambarin pharmacy a jiki ya mika mata, a hankali tasa hannu ta karb'a.
"Kullum kisha har ya kare."
ya fad'a yana janye idanunsa daga kallonta.
a hankali ta gyad'a kai ya bud'e motar da sauri ta fita.
yabi bayanta da kallo har ta karasa get ta bubbo mai gadi ya bud'e ya leko,
ganin ita ce ya bata hanya ta shige gidan da sauri har tana had'awa da sassarfa.
sai da yaga shigarta kafin