Showing 27001 words to 30000 words out of 86085 words

Chapter 10 - FEERYAL Part 3 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt

masifa aka had'a ka da shi, yanzu zanje nasami uban naka, shi da yaji ya gani sai yazo yatare ta tun kafin ta b'alle, kai da kake shan gaban aljanun ma yau baka iya ba sai uban wa zai iya, zancen banza kai wlh bazai yuwuba tun wuri ya sama ma lafiya ya rabaka da damuwa."
Hajiya ta shige d'akin ganin su Mommy ciki ta karaso tana fad'in
"Abun ya gawurta ke nan, to mu ina zamu iya muna mata, wanda maza masu gadi hukuma masu rike da bindiga da suke bakin get ma basu iya da ita ba,
ina yake shi iliya d'an mai karfin ba shi yake iyawa da ita ba, aje a had'a mutum da masifa, kai abokin turawa wazai iya maka da ita kai zakazo ka tare ta."
Hajiya ta karashe maganar tana waige-waige ko yana d'akin.

Kuraiba data shigo da sauri jin hayaniya yaki karewa, itama taja ta tsaya.
bata bukatar samun amsar meke faruwa dan tashin farko ta fahimci, abun da ke faruwa,
ranta ya jagule a yadda ta ganta tasan taji ta maza,
to yaushe ne Abdulrahim d'in yazamo haka ko jinya yake a b'oye yasa mi sauki,
bakinciki ya lullub'eta,
dama b'oye mata kansa yake,
ko kuma da gasken saukin ya samu.
taji wani kololon bakinciki ya kuma tokare mata zuciya.


da karfi Aunty takuma kiran sunan ta cikin tashin hankali.
"Feeryal! innalillahi wa innailaihirraji'un!."
takuma fad'i a cikin kunnenta.
fizgo numfashi tayi tare da kankame Aunty cikin muryar tsoro gami da galabaita ta ce
"Wayyo wayyooo Allah
Kayi hakuri Sahaaab zan mutu akwai zafi wayyoooo Ammie na."
jikinta yana kokarin kuma sakewa.
da sauri Ammah ta bud'e fridge ta d'au ruwa mai sanyi ta wasa mata a fuska.
Hajiya ta rike baki ta gwalalo ido.
"Yoo wannan yaro hauka yayi ne zaiyi irin wannan aikin, ke Safiyya juye ruwan a tsakiyar kanta, duka zata kuma komawa suman."
Ammah tayi saurin ta yuye ragowar a tsakiyar kanta.
wani nannauyan numfashi ta sauke tare da sakin kuka, ta kankame idanunta da karfi, tana dad'a rirrike Aunty,
cikin muryar kuka take fad'in
"Dan Allah kayi hakuri na tuba."
jikin Aunty yayi sanyi, murya a sanyaye ta ce.
"Feeryal bud'e idanunki."
da sauri ta ware idanunta jin muryar Ammie'n ta.
takuma sakin kuka ta rungume ta tana cewa
"Ammie ki tafi da ni."
da sauri Mommy ta juya zata fice a d'akin.

Ammah ta ce
"Allah sarki sannu 'yar halak yau kin goge wa kowa tantamar sa."
da sauri Mommy tayi waje Kuraiba da bakinciki ke kokarin hallaka zuciyarta ta bi bayanta.
Umma Karima ko kallon banza ta wurgawa Ammah sannan ta juya tayi waje, suna joyota tana fad'in
"Karyan banza duk wannan shiri ne."
Hajiya ta dubi Aunty tana fad'in
"To kin sata gaba tana kuka, tashi zakiyi kije ki kinyata ta, bari na aiko muku da gabaruwa da lalle da gishiri."
tayi waje tana cibaga da fad'in
"In banda jaraba irin na 'ya'yan yau, me zai kaika had'a shinfid'a da yarinyar da take aljana-aljana mutum-mutum."
Kuraiba na tsaye parlour'n tana ta cika tana batsewa, wani dogon tsaki taja ta ce
"Wani shegen rakin karya da son a sani, aikin banza kawai mutane sun taru kamar wani abu."
taja dogon tsaki.
Hajiya tabita da kallon shekeke ta ce
"Zancen banza kai ke meyasa baki tara mutanen ba lokacin naki, ko tarin ki bamuji ba, babu wanda ya shaida ranar farkon ki, ko banza ita yanzu taci tukuici."
Hajiya tayi gaba tana bombomi.
bakinciki ya dad'a turnike Kuraiba tabi bayan Hajiya da kallon banza tana fad'in
"Tsohuwar nan baki sanni nane."
ta koma gefen tanajin bakinciki na dad'a shigarta.

Siyama takasa zaune ta kasa tsaye, tana zaman jiran Umma Karima ta dawo taji me yake wakana.
tana ganin tanin yadda Umma Karima ta shigo a hargitse, ta tare ta tana fad'in.
"Aunty Karima lafiya? Allah yasa aljanun sun jata sun tafi da ita."
Umma Karima ta ce
"Ina an kuma samun gaggarumar matsala, Abdulrahim ya kusance ta, banci ta zama ba yanzu zanje na sanarwa boka, ya duba yaga me zai faru nan gaba, kar aiki ya kara wargaje wa,
na barta can tana ta narkewa sai kace a kanta aka fara kai budurci gidan miji."
Siyama ta dafe kirji
"Ya kusance ta!?."
fifita ta soma da hannunta jin wani zafi ya shige ta.

A can gefen Feeryal kuwa, tana rirtike da Aunty, taki sakin ta sai kuka take.
hankalin Aunty duk gaba d'aya ya tashi.
Feeryal sai fad'i take
"Ammie mu tafi Ammie kar ki barni."
sosai ta dage tana kukan da fad'in ita dai su tafi.
wayar Aunty ya yi kara ganin Daddy ke kiran nata tayi saurin d'agawa.
Daddy ya ce Fad'imatu ina kika shiga ne na shigo ban ganki ba?."
Aunty ta ce
"Daddy gani a side d'in Abdulrahim."
kafin ta rufa baki yajiyo kukan Feeryal da sauri ya ce
"Me yasami Feeryal d'in?."
Aunty tad'an yi jim.
Daddy yakuma fad'in
"Fad'imatu me ke damin ta?."
ta ce
"Am bata da lafiya ne kuma wai sai lallai mun taho da ita."
d'an shiru Daddy ya yi yana son nazartar shirun da Aunty tayi,
da sauri ya ce
"Ku taho da ita bari na kira Abdulrahim d'in."
Daddy na kashe wayar yakira sa.
baya gidan tun shigowar su Mommy ya fice a mota.
yana ganin kiran Daddy ya d'aga da sallama, Daddy amsa gaisuwar da yake masa sannan ya ce
"Nasa Aunty'n ku ta d'auko Feeryal ta maido ta side d'inta, idan ta sami sauki za'a mai da ita."
shiru ya yi baiyi magana ba, Daddy ya kashe wayar.

Aunty ta dubi Ammah dake kokarin shiga bayi ta had'a musu ruwan zafi, ta ce
"Ammah'n Miemie Daddy ya ce mu tafi da ita."
Ammah tace
"Yauwa hankalin ta zaifi kwanciya ma, bari a wanke bedsheet d'in."
Aunty tad'an d'agata aka zare zanin gadon Ammah ta shiga dashi bathroom ta wanke kana tayi amfani da Wishing machine wajen busar da shi.
a d'akin kuma Aunty ta d'auko mata doguwar riga tasaka mata, tana ta mata sannu da sanya mata albarka.
Feeryal ko kuka har yanzu yaki karewa sai masar kwalla take tana yayyarfe hannu.
Ammah ta fito da bedsheet d'in a goge kamar ba shi ba.
wajen tafiya Feeryal ta gagara, Aunty ta ruko hannunta ta tashi su tafi tana mikewa ta koma ta zauna da sauri, hawaye na zuba.
Ammah ta ce
"Ammie'n Feeryal kamar fa bazata iya tafiyar nan ba, a kira direba kawai yazo."
Aunty ta ce to, ta kira direban ta batare da b'ata lokaci ba ya iso.
suka tallafe ta da kyar ta iya takowa farfajiyar gidan, tana matsar kwalla da yarfe hannu.
a tsakiya suka sata direba yaja.
har kusa da kofar parlour Aunty direban ya kaisu kamar yadda Aunty'n ta umurce sa.
suka tallafe gefe da gefen kafad'ar ta suka shiga da ita.
d'akin ta dake side d'in suka shige da ita.
a gyare yake tsaf kamar da mai kwana cikin sa, dan kullum sai Aunty ta gyara shi.
suna zaunar da ita bakin gado.
Ammah ta ce
bari taje side d'in ta ta dawo.
Ammah nana fita,
Aunty ta shige bayi ta had'a mata ruwa mai zafi sosai cikin Bathtub ta fito.
ta dube ta tana kwance a bakin gado ta ce
"Taso muje d'iyar kirki ga ruwa na had'a a gasa jikin zakiji dad'in jikin."
fuska ta kwab'e zatayi kuka, Aunty ta ruko hannunta ta mikar da ita zaune.
rau-rau tayi da ido sai ga hawaye sharr.
wayar ta yayi haske alamun shigowar sako, Aunty ta mika hannu ta janyo watar.
number ne babu suna ta bud'e message mai kunshe da sako kamar haka
("Karkiyi amfani da ruwan zafi mai zafi sosai a kwai d'in ki a jikin ki, magani zakisha.")
Aunty tarika juya maganar a ranta, ta kalli da tausayin ta ya kamata, sai kuma ta yi saurin kawar da komai cikin ranta ta aje wayar tana binta da murmushi gami da lallab'i.
"Taso muje 'yammatan Ammie kiyi wanka."
tayi ta lallab'a ta taimaka mata ta mike suka shiga bayi.
batayi mata amfani da ruwan zafi sosai ba kamar yadda ya fad'a.
tasa tayi wankan sarki suka fito. tana sa kaya ta kwanta dan jikin ta yayi zafi sosai.
Aunty ta shiga kitchen dan sama mata abun da zata d'an tab'a.

A b'angaren Hajiya kuwa tasa aka yanko mata zabbi guda uku, aka gyara tasa goggo Bishira tayi perpesin su da kayan yaji sosai da daddawa.
aka juye a kular da zai d'auka, aka fito da shi parlour'n Hajiya aka had'a da gishiri mudu uku da lalle mudu uku da gabaruwa,
ana had'a kayan guri guda Hajiya tana mita
"Dole sai an fita hakkin ta tun da ya janyo wa mutane wahala, kiramin Abubakar yazo ya kawo tukuici."
Hajiya tayi maganar tana duban goggo Bishira.
Goggo Bishira ta kirawo mata Daddy kana ta mika mata wayar ganin ya d'auka.
ta kai wayar kunne tana amsa sallamar da Daddy yake mata sannan ta ce
"To sai kazo ka kawo tukuici a kai musu, gashi nayi kayan jinya."
Daddy ya ce to.
bai jima ba ya shigo.
ya zauna Hajiya ta nuna masa kayan.
makullin sabuwar mota mai tsadar gaske ya d'aura kan kayan, sannan goggo Bishira ta d'au kulan naman, kulu mai aikin Hajiya ta d'au tray'n su gishirin Hajiya ta bi bayansu suka nufi sashin Aunty.
suna sallama Aunty ta tare su tana fad'in
"Sannunku da shigowa."
goggo Bishira tace "Yauwa sannu Aunty Fatima, ya me jikin."
Aunty ta ce "Da sauki."
suka sauke kayan a sakiyar parlour'n
Hajiya ta ce
"To ga kayan jinya gakuma tukuici."
Aunty ta ce
"An gode Allah ya saka da alkhairi."
gaggo Bishira ta dubi Aunty tana fad'in "Ina Feeryal d'in?."
"Tana ciki bacci ne ya d'auke ta."
cewar Aunty Hajiya ta ce
"To a ajiye mata gaisuwar mu."
Aunty ta ce
"To zataji."
suka mike Hajiya ta shiga surutu
"Tun da yaja wa mutane magana ya huta, ko banza yasa yau kafata jigile."

Fitar su bada jimawa ba motar sa tayi parking a bakin get d'in Aunty.
Miemie tazo zata shiga side d'in ya kirata.
laida ya mika mata ya ce "Ki kai mata."
ta amsa tayi ciki.
shiko yaja motar ya karasa side d'in sa........!



Kuraiba na jin shigowar sa ta nufi gefen sa.
yana tsaye cikin bedroom d'in sa yana rage kayan jikin sa.
ta turo kofar wani kallo ta bisa da shi tana takowa cikin d'akin, tun kafin ta karaso take fad'in
"Baka gaya musu kai ba cikakken mai lafiya bane, lokacin da aka kawo ni gidan nan,
shine har za'ayi min gori dan kaje ka gwada lafiyar ka akan wancan yarinyar da bata cika budurwa ba,
in ban da abin kunya ma me zai kai ka zuwa jikin yara, da basu san kansu ba,
tabbacin rashin sanin kai kowa sai da yasan kaje ka danne ta,
duk hakurin da nayita yi da kai sakayyar da zaka yi min ke nan,
me wancan yarinnyar ta iya me zaka sama jikin ta 'yar da bata gama kosawa ba,
ka kalleni
da kyau ni ce dai-dai kai,
zan iya daukar ko wacce bukatar ka, zan iya awa biyar a kankan har fin haka ina sex da kai,
kaki kabani dama na nuna maka yadda nake sonka,
kabani wunin yau na nuna maka, banbanci na da ita, zaka fahimci ita ba komai bace,
You will be happy to haveg sex with me.
zaka banbance karamar mace da babbar mace, ka kuntata zuciyata
haka nake hakuri nake maneji da kai,I think you are not completely healthy..
shiyasa baka yarda ka kusance ni, ban damu ba sabo da I choose you as my husband.
kuma ina son ka."
ta karaso tana kokarin rungume shi, ya yi saurin d'aga mata hanu.
kana ya sakai yashige bathroom batare da ya ce da ita ko mai ba.
da sauri tabi bayan sa ta rungume shi ta baya tare da tura hannunta cikin wandonsa ta kamo dick d'in sa,
wani irin lumshe ido tayi, a maitance ta manna nonuwanta da bayan shi.
tana fad'in
"Mijin Kuraiba ka bani dama na nuna maka banbanci na da ita."
da karfi ya juyo ta ya janye ta da jikinsa, ya turata waje ya rufe kofar.
Kuraiba ji tayi kamar tayi hauka, ta fice a d'akin fuu tayi sashin Mommy...


Harwajen karfe 2 Feeryal na bacci, zuwa lokacin kuwa jikin ta ya dad'a yin zafi sosai.
Aunty ta taimaka mata taje tayi al'wala, tazo tayi sallah a daddafe.
ta had'o mata tea mai kauri, kad'an ta sha, tana matse ido dan sosai take jin zazzab'in.
laidar da d'azu ya baiwa Miemie ta shigo da shi, Aunty ta d'auko magani ne ciki da allurai, ta bud'e ta bata maganin kamar yadda tagani arubuce.
da kyar ta sha tana sha kuwa ta soma yunkurin amai, d'an tea d'in da ta sha kaf ta amaye shi a gurin.
hankalin Aunty ya tashi.
ta tallafe ta suka shiga bayi ta wanko bakin ta suka fito, ta kwanta bakin gado tana rawar sanyi tana jin kanta kamar zai fashe.
Aunty ta gyara gurin tsaf tana ta mata sannu.
Feeryal sai matse ido take tana hawaye.
ganin yadda jikin nata ke dad'a gaba-gaba Aunty ta d'au waya ta fito parkour ta kira lambar Abdulrahim.
fitowarsa daga wanka ke nan kiran nata ya shigo, ya kara in da wayar take ya d'auka yana duba mai kiran nasa, a hankali yayi picking call d'in ganin kiran na daf da yankewa, ya kara wayar a kunnen sa.
jin ya d'aga da sauri Aunty cikin tashin hankalin ganin halin da d'iyarta take ciki ta ce
"Abdulrahim kazo kayi mata allurar jikin ta yayi zafi sosai, tasha maganin ma amansa tayi."
jin yayi shiru baiyi magana ba Aunty ta kashe wayar, a hankali ya zaro wayar a kunnensa ya aje kana ya isa gaban wardrobe ya ciro kaya.

Aunty ta koma d'aki in da Feeryal take da sauri.
ta jika towel tarika share mata jiki dan zafin ya ragu.
ya d'au tsawon minti 20 kafin ya shigo, kansa a kasa.
Aunty na ganin sa ta mike tana fad'in
"Bacci ya d'auke ta amma jikin har yanzu da zafi, inaga ko sai anyi allurar zaiyi sanyi."
kai kawai ya jinjina batare da ya bari sun had'a ido da Aunty ba.
lura da yadda yake ta sunkuyar da kai Aunty ta fita a d'akin ta janyo kofar.
a fili yaja numfashi tare da furzar da huci cikin bakin sa, kana a hankali ya tako bakin gadon idanunsa akanta.
tana kwance tad'an dunkule cikin bargo, idanunta da suke a lumshe duk a kukkumbure,
fuskarta ya kara haske alamun tana jin jiki da zazzab'in.
kuma duk ya d'an sussunduma na kukan da ta sha jiya da daddare.
janye idanunsa ya yi a kanta kana ya d'au laidar da magani da alluran suke ciki, ya had'a allura syringy biyu sanna ya janye bargon gefe,
tana sanye da riga mara nauyi iya guiwa.
ya d'an dad'a matsowa, yaja rigar sama wandon rigar mai kama da pant ya bayyana.
ba shiri ya rumtse idanunsa jin yadda kirjinsa ya yi wani irin bugawa.
sai kuma a hankali ya ware idanun a kanta da d'an sauri ya kai hannu ya d'an janye wandon kasa kana ya saita allurar ya nitsa mata.
zabura tayi tana kokarin mikewa yayi saurin masa ruwar allurar kana ya zare.
kara ta sake tana mike wa zaune.
tana yin ido biyu da shi tawani irin zabura dayafi wanda tayi san da ya saka mata allurar, tana binsa da kallon tsoro.
d'aya allurar ya d'auka, yayi mata alama da hannu ta matso, da sauri takuma yin baya tuni idanunta suka kawo kwalla,
murya na rawa ta ce
"Kayi hakuri Sahab dan Allah kar kayi min."
fuska ya gimtse tare da zama bakin gadon, ya fisgota jikinsa ya matseta, kara ta sake tana kokarin kwace jikinta ya dad'a rungume ta da kyau, sai da yayi mata ya mulmula gurin kafin ya saketa.
ta masa can kuryar gado tana toshe bakin ta da kuka ya kwace mata.
ido ya zuba mata itama shi take kallo da idanunta da suke tsiyayar da kwalla masu cike da tsoron sa.
ya mike yafice a d'akin yana fita Aunty ta shigo da sauri ta hayo gadon tayi mata pillow da cinyarta, ta shiga rarrashi.
"Yi hakuri Feeryal jikin ki yayi zafi dole sai allura ce zata sa jikin tayi sanyi, sannu kinji Allah dai ya baki lafiya yayi miki albarka."
ita dai sai masar kwalla take,
idanun ta a lumshe takasa iya bud'e su dan jiri take ji.
zuwa can kuma bacci ya yi gaba da ita..
bara farka ba sai daf magriba, zuwa lokacin kuwa jikin nata yayi sanyi zazzab'in ya sauka.
ko da Aunty ta riketa zasu shiga bathroom tafiyarta ba irin ta d'azu ba, dan kuwa hatta zafin da take ji a kasanta yarago sosai.
da kanta tayi wanka ta d'auro al'wala ta fito.
Aunty bata d'akin bayan ta gyara mata d'akin saf ta tafi kitchen dan sama mata abun da zata ci.
kayan da Aunty ta aje mata shi bakin gado ta d'auka ta saka, shima kamar irin na d'azu ne rigar iya guiwa da wandon sa mai kamar pant, kana ta saka babbun hijabi har kasa ta haye kan
sallaya ta tada sallar magriba da taji an shiga a masallaci.
tana idarwa Aunty na shigowa rike da tray ta dire shi gabanta.
plt biyu ne kan tray'n sai cup.
d'aya perpesun zabbin da hajiya ta kawo mata ne ta d'uma ta d'ibo mata, d'aya kuma mutumin ta ne cake, sai tea mai kauri a cikin cup d'in sai kuma gorar yogurt mai masakaicin sanyi.
Aunty ta ce
"Cire jibab d'in maza ki ci sai kisha magani, kinji 'yammatan Ammie."
batayi musu ba ta cire dan tana jin yunwa.
zatafa cin cake d'in Aunty ta ce aa tafara shan tea sai taci perpesun kafi cake d'in.
d'an kad'an tasha tea ta aje. tad'au cokali ta d'au d'an madaidai cin naman ta kai bakin ta.
ido ta waro cin yaji ya gauraye mata baki, tana kokarin fito da shi Aunty tace
"Maza ci kar ki fito da shi."
da kyar ta tauna ta had'iye da kyar tana yarfe hannu da kwab'e fuska
"Ammie yaji ni dai na ko shi."
"Aa Feeryal d'an kara ko kad'an ne."
"Ammie da yaji sosai fa."
"Eh nasani Feeryal kad'an zaki kara."
da kyar ta lallab'a ta taci yanka uku har tana hawaye, Aunty ta ce to ta bari taci cake d'in ta, ta barta nan tatafi domin yin sallah.
tana gamawa ta mike taje bayi ta wanko hannnu ta fito.
ido ta ware cike da murnar ganin su, sai kuma ta gwab'e fuska.
Chuchu da Chulu suka bita da murmushi.
ta karaso ta zauna bakin gado in da suke zaune tana cigaba da kwab'e fuska.
Chuchu ta dafa kafad'ar ta tana cewa
"Laifin me mukayi ake fushi da mu?."
baki ta cuno tayi raurau da ido sannan ta ce
"Ba kunce zaku taimake ni idan zaiyi min mugunta ba, amma ai baku zo ba."
Chulu ta dafa d'aya gefen kafad'ar ta tace
"Tuba muke a wannan lokaci bamu isa mu kawo kanmu gareki ba, ko da muka ganki cikin tashin hankali shugaba ya kwab'e mu da sake waiwayan ki, dan aiwatar da hakan zunubi ne a gare mu, har idan kina tare da Garkuwar."
raurau tayi da ido tuno da zillar data sha jiya a hannunsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login