Showing 39001 words to 42000 words out of 86085 words
Chapter 14 - FEERYAL Part 3 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt
ya ja motar ya tafi.
Su Abba suna zaune suna alhenin lamarin da tuni hukuma suka sunduma ciki.
suna ganin ta suka mike duk suka mike cike da mamaki.
Maryam ta tafi da gudu ta rungume ta na fad'in
"Feeryal ke ce ina kika shiga."
Hajja Umma ma ta rungumo ta.
Abba ko sai fad'in alhamdulillah ya ke.
ya ce "Dama hukuma sunce insha'allah zuwa dare za'a gano in da kike,
bari na kira wannan yaro Sadam dan yanzun nan yasake komawa, kasuwar dan yakuma bincikan lamarin, ku sake ta ta karaso zo zauna nan Feeryal hukuman suna waje ne shi ne basu shigo ba ai da sun shigo."
suka sake ta ta karo suka zazzauna Abba ya mike yana fad'in bari yaje ya sami jami'an tsaron da suka samo ta.
ta ce "Abba ba da kowa muka zo ba fa, Sahab ne ya kawo ni."
Abba ya zauna yana dubanta ya ce
"Sahab wane ne Sahab kuma?."
da sauri Maryam ta ce
"Wai Abdulrahim kike nufi?."
Abba ya mai da hankalin sa ga Maryam ya ce
"Wane ne shi d'in?."
"Abba Abdulrahim dai AA FIYA tsohon mijin ta."
Abba ya ce "Wane shi ne ya dawo da ke da ma shi ya d'au ke ki?."
da sauri Maryam ta ce
"Abba ni fa da take nuna min wai wasu suna kallon, ni fa babu wan da na gani, ko da take gudun ma babu me binta ita kad'ai take gudun ta."
baki ta cuno ta ce
"Allah na gansu kuma sun bini, ni dai ban san ya akayi na ganni tare da shi ba,
amma shi ya dawo da ni."
abun da ta sani ta basu labari.
a take suka fahimci ciwonta ya tashi kuma taga halittun da ita kad'ai ke iya ganin su.
Hajja Umma ta ce
"Ai mun godewa Allah ma da ya takaita iya haka, Allah ya dad'a rufa asiri."
a take Abba ya sanarwa hukumar cewa an same ta.
Tun daga ranar ba'a sake barin ta ta fita ko nan da can ba,
gudun abun da zai je ya dawo....
Lagos...
"Kuraiba ke ma lokacin barinki gidan nan ya yi."
Umma karima ta fad'a
tana wani shekewa da dariya tana kallon video da aka turo mata yanzu.
ta taka ta isa ta hakimce kan kujera tana kad'a kafa,
"Ni ce mamallakiyar komai na Alhaji Abubakar AA FIYA, kar ki ji dad'i ki baje kafa hatta uwar mazan gidan ita kanta sai ta bar min gidan, yanzu ta kan ki zan waiwayo Kuraiba."
ta danna wani lamba ta kai wayar kunne.
"Ai kin ka yana kyau Jaguu yanzu zakaji sakon ka, idan ka samo sauran zan turamaka tukuici mai tsoka."
ya ce "Angama Hajiya."
ta kashe wayar tana dad'a girgiza kafa...
Abuja....
Feeryal ce ta fito daga bayi da sauri tana fad'in
"Aunty Maryam ki kalli ni fa ashe da gaske ne kika ce narika cin abinci zan kara kiba, nakusa kai ki yau ma tuwa zanci da yawa na kara kiba."
Maryam dake zaune tana shayar da d'anta ta ce
"Kaji ta kamar wani abincin kirki ta ke ci, ke da shinkafarma bai fi kiyi cokali biyar ba kice kin koshi, sai dai in cake da yogurt ne ke hura ki."
"Allah Aunty Maryam yanzu ina ci fa, ai kin ga banjima da cin abinci bama, yanzu zansa kaya naje na sake ci dan na fara jin yunwa."
Maryam tayi dariya tana fad'in
"Yarinya tana so tayi kiba ta dawo cin abinci."
gaban mirror ta zauna tana murmushi tana shafa mai suna hira da Maryam, tana gamawa ta saka kaya ta tsaya gaban mirror tana kallon kanta.
"Aunty Maryam."
ta kira sunan tana tana kallon ta ta cikin mirror.
Maryam ta d'ago tana duban ta, ta ce
"Ba ki gani ba Allah har tunbi nayi, nayi kiba fa da gaske kuwa."
tayi maganar tana d'ame rigarta ta cikinta tana shafa shi.
Maryam ta girgiza kai tana mata dariya.
itama dariyar tayi.
ta zo ta d'auki Aiman tana fad'in
"Taho muje ka rakani muci tuwa, zan bawa Aunty Maryam mamaki idan naci na koshi nazamo katuwa kamar ta."
tayi waje Maryam ta biyo ta tana cewa
"Kamar da gaske wani cin abincin arziki zakiyi, muje naga yawan abincin."
Hajja Umma suka karasa dinning tana fad'in
"Ai zaki gani Hajja Umma zubo min tuwo cikin plt."
Hajja Umma ta yi mata hararar wasa tana fad'in
"Ni na isa na zuba duk masu aiki sun koshi karshe na zubar, kwatan malmala zan saka miki."
"Ah to wai ita gani take wani abincin kirki take ci, kullum sai ta ce min wai ta kara jiki, har da wani wai yau har tunbi tayi dan ta ci abinci d'azu."
Hajja Umma ta kalle ta tana zama kan kujeran dinning.
da sauri ta ce
"Ke Feeryal mike tsaye."
Hajja Umma tayi maganar tana dad'aatsowa kusa da ita.
ta mike tana cewa
"Allah Hajja Umma ke bakiga tunbin ba, ai kin san ina cin abiinci sosai."
"Bani d'an nan, ke Maryam karb'e shi."
Hajja Umma
ta karb'i d'an ta mikawa Maryam.
tana bin Feeryal da kallo daga sama har kasa.
da sauri ta ce
"Ke rabon da kiyi al'ada tun yaushe?."
shiru tayi tana son tuna tun yaushe ne rabon ta da yi.
Maryam ta ce
"Ai kuwa dai kamar tun da tazo fa banga tayi ba."
Hajja Umma ta ce
"Amma Maryam baki da hankali amma kuma shine baki fad'a ba, ni ina zan sani tun da dake kuke rayuwa cikin d'aki, sai dai in kun fito mu had'u,
kullum kuna tare da ita, amma ki kasa gane sauyi tare da ita, ni sam ban tab'a luraba in ba yau da aka kawo wanna zancen ba,
sabo da kullum babban riga abaya take fitowa da shi,
kina kallon ciki har yayi wayo a jikin yarinya ku kwana tare ku tashi tare ki kasa ganewa, duk da jikin ta d'anye ne dama ai ko gashi nan ya kara d'anyace wa in ba ka lura ba bazaka gane ba dan jikin nata d'anye ne dama,
d'auko mayafin ki maza muje nan asibitin bayan."
Feeryal tabi jikinta da kallo tana mamakin maganar Hajja Umma.
sai da Hajja Umma ta fad'a kafin
Maryam take ganin alamun ciki karara a jikin ta.
nan da nan Hajja Umma ta d'auketa sukayi asibiti, kwajin farko aka tabbatar mata tana da ciki, bayan anyi scanning aka tabbatar musu da wata uku da sati biyu ke nan cikin a jikinta...
ko da Abba ya sami labarin
Nan da nan ya kira Daddy ya sanar masa.
zo kaga farinciki gun Daddy d'iyanin ya kira Abdulrahim, ya ce yazo yana niman sa.
batare da b'ata lokaci ba ya amsa kiran.
ya nimi guri ya zauna a kasan carpet.
Daddy ya dube sa da kyau sannan ya ce
"Yanzun nan na sami labarin Feeryal tana da ciki, kimanin watanni uku da sati biyu, shi yasa na kiraka na sanar maka da wuri dan ka shaida."
shiru yayi kansa a kasa bai yi magana ba, Daddy ya ce
"Ka tashi ka je dama na shaida maka ne tun da wuri."
ya mike ya fice batare da ya ce kala ba.......!
Babu editing sai a karanta da hakuri
Yana fita sukayi kiliya da Ajmaal zai shigo gurin Daddy.
Ajmaal ya yi masa gaisuwa na girmamawa kamar yadda ya saba, sannan ya wuce parlour'n Daddy.
a tsaye ya iske Daddy da alamar fita zaiyi,
ya karaso yana fad'in
"Barka da warhaka Daddy."
"Yauwa Ajmaal ya aikin kun dawo?."
Ajmaal ya ce
"Eh mun dawo Daddy ai ki Alhamdulillah, dama document d'in nan ne na kawo ma ka sa hanu."
"Shi ne kabar yayan ku ya wuce ai da shi ka bawa yasa hannun kawai, ka bisa ka kai masa ya sa hanu."
Ajmaal ya ce to, har ya kai bakin kofa Daddy ya ce
"Ajmaal kana da labarin kun sami d'a ko 'ya kuwa?."
da sauri ya juyo ya ce
"Aa Daddy haihuwa akayi ne wa ta haihu?."
"Ba haihuwa akayi ba tukun Feeryal ce ke da juna biyu, zaku sami d'a bada jimawa ba, in Allah ya yarda."
Ajmaal da farinciki ya lullub'e shi ya wani tuma tsalle yana fad'in
"Yes! masha'allah im very happy."
Daddy ya bishi da dariya ganin ya juya da gudu ya yi waje..
Ajmaal bai tsaya ko ina ba sai sashin Mommy.
yana shiga da d'in bin farinci ya ce
"Mommy albishirinki Feeryal na da ciki."
Mommy Umma karima Siyama Sumayya Ameerah duk suna zaune cikin parlour'n.
dukkanin su zabura sukayi tare da had'a baki wajen fad'in
"Ciki!."
"Wallahi da gaske ciki take da shi."
ya yi maganar da farincikin daya gaza b'oyuwa tare da shi.
Umma karima da maganar ya nasheta yakusa kashe ta a zaune.
ta kasa iya furta komai.
sai zazzare ido take kamar tsohuwar mayya.
Mommy ko zama ta gyara
tana murtuke fuska "To sai me zaka zo kana fad'a min, ai dama karshen alewa kasa an turata yawon bariki kam ta ya bazatayi ciki ba."
"Mommy yawon bariki kuma? ciki kam ai na Ya Abdulrahim ne."
da sauri ta ce
"Kai kutumar ubanka, idan na sake jin maganar nan a bakin ka sai na ci maka mutunci,
au tanan aka b'ullo taje tayi ciki za'a lankayawa Abdulrahim, shi da yake nan ita tana can wata duniyar, sabo da a b'ata masa suna to duk wanda ya fad'i maganar nan wlh bazan kyale ba."
"Allah ya baki hakuri Mommy amma ciki kam na sa ne, dan watannin cikin sun nuna nasa ne."
Sumayya dake ta washe baki tun san da ya fad'a
ta ce "Alhamdulillah zamuyi baby, Ya Ajmaal Feeryal d'in ta zo ne?."
"Tazo gidan uban ki wa ai wlh ba a isa a yi min wanna sakar zaren ba, zancen banza fita ka bani guri, naga uban da ya isa ya ce cikin nasa ne, dan uwar ki ke Sumayya da kike cewa zakuyi baby, d'an shegen ne abun alfahari,
tukunna ma yaushe Feeryal d'in tazamo dangin ki, ko kalen dangi kika soma, na sake jin maganar nan a bakin ku sai na ci ubanku dukan ku, shegu marasa mutunci da rashin sanin ciwon kai."
Ajmaal kam tuni yayi waje abinsa bai ma tsaya jin abun da take kuma fad'i ba.
sai yanzu Umma karima ta sauke numfashi had'a da mulmulo wani uban ashar ta d'auna.
"Tamd'ijam! wata sabuwa wallahi karya ne!."
ta fad'i tana buga kafa a kasa.
Mommy ta ce
"Zancen banza ne ma kawai."
Umma karima ta mike zumbur ta yi waje.
Hajiya ta rike hab'a bayan da Ajmaal ya gama fad'a mata zancen.
ta ce
"To ikon Allah yanzu ita yarinyar ciki gare ta, kuma na Abokin turawa ke nan, to ai shi ke nan Allah ya raba lafiya, amma wannan d'a ko ya zaizo haka zai fito irin uwarsa mutum-mutum aljani-aljani."
Ajmaal na fita Umma karima na shigowa.
ta nimi guri ta zauna tana fad'in
"Hajiya kin ji wani sabon labarin da ya fito a gidan nan kuma ko, wai Feeryal na da ciki ana son juya lamarin ya dawo kan Abdulrahim."
Hajiya ta ce
"Yanzu wannan yaro Ajimi ya zo min da batun, na ce ko wani irin d'a za'a haifo, jinsin aljanu da mutane."
"Hajiya cikin nan fa bana Abdulrahim bane, ko kin mace yarinyar nan a cikin gidan nan na kamata da wani kato ta sakashi cikin hijabi suna iskanci, sannan tun yaushe Abdulrahim ya sake ta, ba'a ce tana da cikin ba sai yanzu,
haba ai wannan zance hankali bama zai d'au ka ba,
duk shiri ne da son a b'atawa gida kamar wannan suna,
wlh idan aka bari akan cikin Abdulrahim ne aka karb'i d'an shege a gidan nan, daga lokacin mutuncin gidan nan ya zube, ta ya ma yariya tana wata duniya a lankaya masa ciki, baya tare da itan ma sai an bida da sharri, in dai cikin nasa ne da gaske me yasa ba'a gansa tun a nan ba sai da ta sa kafa ta tatafi dadironta tayiyo cikin sannan dan ana so ayi rufa-rufa kada duniya susan halin da ake ciki, ace wai cikin sa ne."
Hajiya ta ce "To nima dai shi ne na gani wanna zance babu lauje cikin nad'i kuwa, amma bari na nimi Abubakar dan ni bai zo min da zancen ba har yanzu."
"Hajiya idan kika bari aka karb'i cikin nan, wlh ke ce na gaba da za'a fara kwatancen ki dan ke ce gidan gaba d'aya, gara ki kwab'i zancen tun da wuri, suje can su nimi wan da ya mata ciki badai jikan ki ba."
Umma karima tayi ta iza Hajiya tana karawa wuta fetur nan da nan Hajiya ta d'au zugarta har tana fad'in
Ba'a isa a lakawa jikanta d'an shege ba, suje can su karata da tsiyarsu.
sai da taga ta gina Hajiya ta zauna daram kan maganar ta kafin ta koma sashinta.
in da ta tadda kanwar tata Siyama hankali duk a jagule, da bakin cikin lamarin.
A b'angaren Daddy ya shigo side d'in Aunty dan ya sanar mata, ya isketa tana waya da su Hajja Umma.
tana ganin shi ta rungume shi tana dariyar farinciki.
Daddy yaja kumatun ta yana dariya da fad'in
"Um musu an girma za'ayi jika."
dariyar farinciki Aunty ta kuma ta ce
"Jika kafi d'a wuya hausawa sun fad'i gaskiya, ban samu ba gashi d'iyata ta samar mana, Allah ubangiji ya kawo jika lafiya."
"Oh Fad'imatu ba bu kunya ana murnar an sami jika."
Daddy ya yi maganar cikin zolaya.
Aunty ta zame jikin ta tana fad'in
"Tare dai muke murnar kai ma ga murnar a fuskar ka."
ya yi murmushi mai nuni da zallar farinci.
D'iyanin Hajiya ta sa aka kira mata Daddy a waya.
yana shigowa tun kan ya zauna, ta ke fad'in
"Wai wace magana ce nake ji ne ha, wanna yarinyar tayi ciki ake son d'angwalawa Abokin turawa, to wlh tun wuri ka kwab'i maganar nan, dan basu isa su miko mana d'an da ba namu ba, su nimi uban cikin tun kan dare ya yi musu."
Daddy ya zauna yana fad'in
"Dama Hajiya ina da shirin zuwa gaya miki,
ai Hajiya bamu isa muce cikin nan ba nashi bane, dan likita ya tabbatar da cikin wata uku da sati biyu ke nan,
kin ga kuma yanzu wata d'aya ne da sati biyu da karewar auren su, sauran watanni biyun a gidan nan tayi, basai an tsauwala bincike ba ciki ya tabbata nashi ne,
mu dai kawai muyi fatan Allah ya raba lafiya, kar muyi wata maganar da zai zubda mana kima a d'auke mu kananun mutane."
Hajiya tayi shiruuu sannan ta ce
"To me yasa basu fad'a ba sai yanzu, ni fa kar aje a d'auki d'an wani a bashi, dan irin wad'an nan yayan su ke kashe iyaye ayi ta cewa d'a ya kashe ubansa alhalin dama ba uban sa bane."
"Babu ko mai Hajiya insha'allah hakan ma bazata faruba ciki kam nashi ne."
"Eh ai dama haka zakace in dai magana akan abun da ya shafi Fatima ce, duk in da aka bi da kai zaka b'ulle."
Daddy dai bai kuma cewa ko mai ba dan yasan yana kuma cewa wani abu Hajiya zata b'alle.
Kuraiba kuwa hauka ne kawai batayi ba, data sami labarin.
ta shiga mota tayi gidan su,
hankalin mamarta ma ya bala'in tashi, Hajiya Luba ta dubi d'iyar tata ta ce
"Wai ina cikin da kika ce min a kwai? shi wata nawa bai nuno kansa ba."
Kuraiba ta turo baki ta ce
"Ai zuban jini nake kullum dana je naga likita ya ce min wai zuban jinin da nake ne yasa cikin yake komawa baya, amma yana nan ina jin motsin shi."
"To tashi maza muje asibiti, na kai musu shaidar kina da ciki, taya zakiyi sake har wata tazo ta riga ki yin ciki,
kullum ina ta zuba idon jin kyakkyawan labari, sai kuma naji shiru, ai yanzu ya ci a ce cikin nan ya baiyana kansa,
Kuraiba kar kiyi wasa kar ki bari cikin nan ya fita, akwai babbar matsala fa, ta shi maza mu tafi."
"Mom ni gaskiya bazan je wani asibiti ba, ai ba a b'oye bane kowa yasan ina da ciki,
ki kira Mommy ki ce mata bazan zauna nan gaba akawo d'an shege gidan ace d'an Abdulrahim bane, tama san yadda zatayi tun da wuri."
"Ke dalla tafi can tashi muje na karb'o shaidar cikin ki, ba kiranta a waya zanyi ba, da kaina zanje na tabbatar mata nan gaba bazai yuwu a had'a sunan d'aki da d'an shege a matsayin d'an uwa ba, gara tun wuri ta sani."
ta zari mayafi ta ce
"Muje maza."
da fari Kuraiba taso bijerewa tafi asibin, Hajiya Luba tace fa sai sun tafi.
suna zuwa asibiti,
ana gwada ta aka ce bata da komai.
Hajiya Luba dake tsaye cikin d'akin gwajin ta ce
"Sake gwajin nan likita ciki fa a kwai shi tun ba yau ba."
"Hajiya ki kalla scanning dai baya karya, hasali ma mahaifanta bai tab'a d'aukar ciki ba, sannan akwai matsala ma a mahaifar nata, wanda bincike ya nuna yawan shashayen maganin hana d'aukar ciki barkatai ba'a kan ka'ida ba, shi ya kawo wannan matsalar, da kamar wuya ta iya d'aukar ciki."
Hajiya Luba ta shiga fifita da bakin mayafinta.
Likitan ya sallame su, suna fita Hajiya Luba ta ce
"Amma kin cuceni Kuraiba, kin ruguza min mafarkin dana jima nake yin sa,
wanda shi yasa nayi ruwa nayi saki wajen ganin kin zamo surukar Hajiya Halima sabo da na nuna mata iyakarta,
naci alwashin sai na mallaki dukiya dan na kuntata mata kamar yadda a duk san da na ganta nake shiga kunci,
sabo da tana auren mijin daya ninka mazajen mu dukiya shi yasa take fankama a cikin mu kawayenta, tana nuna ita mijinta mai dukiya ne,
shi yasa naci alwashin sai na mallaki dukiyar da take takama da shi, ni zan zamo mai dukiya ba nama son na kasance a karkashi wani,
shi yasa na zab'i had'a ki da d'anta dan na cimma burina, sai gashi kin ruguje min duk wani abin da na dade nake buri."
fuska Kuraiba ta yamutsa ta ce
"Lallai ma Mom wani irin tunani ne wannan da ke, to ni na auri Abdulrahim ne dan shine irin mijin da nake buri, bawai dan wani dukiya ba, duk da ban samu abun da nayi sammani tare da shi, ban damu ba dan gari da fad'i,
idan kayi ihu wani baiji ba wani zai jika,
ni kam dai nayi gidan mijina, ni nasan yadda zanyi na kwato 'yanci na, Mom ki aje wannan tunanin ma."
Hajiya Luba ta bud'e baki da hanci tana kallon d'iyar tata data wuce bakin get ta tari abun hawa ta hau ta tafi...
A cikin gidan gona ya gyara parking, kamar ko da yaushe Jaq da Tag suka iso gurin shi, bayan sun bud'e masa mota ya yo gaba suka biyo bayan shi.
suna shiga ciki yaja kujera ya zauna ya ce
"Ku fito da shi."
da sauri suka bud'e d'akin da Zaraddin ya ke ciki.
da sauri ya kare fuskarsa da tafin hannunsa, sakamakon hanken da ya zoyarcin cikin d'akin, wan da ya ke duhu babu ko kyallin haske, yana kwance a kasan turb'aya babu riga a jikin sa sa, sai gajeren wando