Showing 42001 words to 45000 words out of 86085 words

Chapter 15 - FEERYAL Part 3 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt

kad'ai.
"Kai taso muje."
Tag ya fad'a yana janyo shi daga kwancen, ya mike tsaye ya tura shi waje.
suna isa gaban sa ya durkusar da shi kasa ya zube gaban sa.
ya mika hannu yana fad'in
"Miko min bulala."
da sauri Zaraddin ya mike yasa gwuiwowin sa a kasa yana fad'in
"Dan Allah Ya Abdulrahim kayi hakuri Wallahi na shiryu kar ka duke ni yau, d'azu ma sai da suke ni, kuma duk ayyuka na na gama akan lokaci,
ka tambaye su ko minti 20 banyi ba na share gidan gonan nan tas na nome in da ciyawa suka fito,
na canza ruwan kifi na wanke dem, na kwashe kashin kaji na zuba musu abinci da ruwa da magani, na share kashen shanu da raguna na zuba musu abinci da ruwan sha, zabbi da d'awesu da jimina Wallahi suma sai da na share gefen su na zuba musu abinci, kuma gasu nan ka tambaye su, kuma ka tambaye sauran ma'aikatan ma, daga nan kuma malam yazo ya koya min karatu, muna gamawa aka mai da ni d'akin nan ko minti 30 banyi da komawa ba yanzu haka."
ido ya zuba masa fuskarsa a mirtuke.
Zaraddin ya juyo ya kalli su Jaq yana cewa
"Ku gaya masa da gaske duk abun da na lissafa nayi, dan Allah Ya Abdulrahim ka taimaka ka mai dani gida, na rantse maka bazan sake aikata ko mai ba wlh na daina,
Wallahi tallahi ka tambaye su gaba d'aya na gama shiryuwa, ni nake fara fad'a musu lokacin sallah ya yi, ka tambaye su kafin su tashi suyi sallah na riga su,
ni nake buga kofar nan idan naji malam ya tada sallah sai su zo su bud'e min,
lokaci biyar akan lokaci baya wuce ni, ka taimaka ka mai da ni gida idan na sake aikata wani abun na yarda ka yi min hukuncin da yafi wannan, ni da shaye-shaye da 'yammata munyi hanun riga, har da abokan banzan ma har abada bazan sake ba, wlh na dai na kayi hakuri."
"Kira min malam."
Abdulrahim ya fad'a yana duban Tag.
da sauri Tag ya fita ya nufi gefen da sauran ma'aikatan gonar suke, batare da b'ata lokaci ba suka dawo da wani dattijo.
malamin ya mikawa masa hannu suka gaisa kana ya dubi malamin yana cewa
"Ya kai izu nawa yanzu."
da sauri Zaraddin ya ce
"Wallahi nafi ashirin saura kad'an na haura izu talatin."
"Ban tambaye ka ba."
ya fad'a fuska ba wasa.
Zaraddin
yayi saurin kunshe bakinsa yana tsilli-tsilli da ido, ya kwantar da kai kamar maraya.
malamin ya ce
"Eh yana daf da kaiwa izu talatin, kuma yana ganewa sosai yanzu."
kai ya jinjina sannan ya ce wa malamin
"Zaka iya tafiya."
malamin na tafiya ya mai da dubansa ga Zaraddin ya ce
"Idan ka kai izu sittin ka shirya zaka ko ma gida."
yana gama fad'in haka ya jefar da bulalan hannunaa ya mike ya fita.
Zaraddin kamar ya fasa ihu yana ji yana gani suka jashi suka maida shi d'akin duhu suka kulle shi......!



"Feeryal yi sauri ki fito ki shirya mana mu tafi, sai juya jiki kike duba kiga 11 har ta gota, sai azahar kike so mu tafi."
cewar Hajja Umma data ke ciro mata kayan da zata saka, su tafi asibiti don yin awu.

Feeryal ta fito daga bathroom d'aure da towel, tana gyara zaman towel d'in da yaso kasa mata sakamakon cikin ta daya tosa, watannin cikin biyar ke nan.
Hajja Umma ta ciro mata doguwar riga tana d'ago rigar, magani ya zube kasa.
Hajja Umma ta aje rigar bakin gado ta sunkuya ta tattaro maganin tana fad'in
"Me kuma ya kawo magani nan."
ta kwaso magungunan tana kallon su
"Wannan ai maganin da masu ciki suke sha ne,
wannan ne ma ban san amfanin sa ba, Feeryal maganin ne bakya sha kike tarasu anan, ko ba su bane?."
Feeryal ta zauna kan kujerar Morro tana fad'in
"Ina sha fa Hajja Umma ba ke kike bani na sha ba."
"To ai shine nima nagani to ya akayi wad'an nan suka zo nan."
mai ta d'auka ta soma shafawa tana cewa
"Wannan maganin fa Sahab ne ya bani ranar daya dawo da ni d'in nan, wai narika sha kullum ni kuma nasan lafiya ta kalau shine na ajiye."
Hajja Umma tayi shiru a ranta take fad'in
"Yama san da cikin, kafin mu mu sani ke nan ma."
a fili kuwa cewa tayi
"To yi sauri ki shirya, mu tafi bari na zo."
tayi waje...


Lagos...

"Boka wai har sai yaushe bakin aljanin nan zai isa inda take ne,
dan Allah boka kayi duk yadda zakayi ka katura akashe abun da ke cikin ta lokaci nata tafi, a lissafi na yanzu watannin cikinnan biyar ke nan, saura wata hud'u ya zo duniya, boka idan yazo kwai matsala fa a kashe shi tun kafin yazo, sannan a shirya auren Siyama da shi."
Boka Mali ya d'ago daga bugo kasan da yake ya ce
"Ai kin ki bazai karasa ciwuwa ba har sai kin karasa jefa cikon na uku cikin kaskon can, ki tashi kije ki nemo cikon aikin ki,
ki tabbatar da biyu ne cikin sa ba d'aya ba, dan a wannan karon idan kika kuma kuskure to aikin ki ya rushe duka,
bazai tab'a gyaruwa ba, kin kuma tabba babban kuskure zaki fuskanci kalubale, mai girma."
kirji ta dafe ta ce
"Boka yanzu a ina zan samu kasan irin kasadar da nayi a wancan lokacin kafin na samo,
na karshen dana zo da shi sai da na narka kud'i kafin na samo, cutana yayi ce min yayi biyu ne a ciki, amma Boka babu yadda za'ayi aljanu su samo min, ni ko mawa ne zan iya badawa in har zan sami biyan bukata."
Boka Mali ya kece da kazamin dariya yana cewa
"Babu halin yin haka in har kina son cimma burin ki to dole ke zaki samo da kanki."
shiru tayi sannan ta gyara zama ta ce
"Boka zan samo kota halin yaya."
"Tashi kije ki taho da shi aikin ki ya gamu daga ranar duniyar ki tana hannunki."
Umma karima ta mike da sauri zuciyar ta abushe ta dasawa ranta ko ta halin yaya zata samo.



Yau Farida sanmakon zuwa AA FIYA STREET tayi kamar yadda halinta yake bata zuwa sashin kowa daga na Daddy sai na uwar ta da kakarta.
daga sashin Daddy ta tafi side d'in Hajiya.
tana zaune suna hira da Hajiya, 'yarta data yaye ta da d'an jimawa nata tsalle-tsalle cikin parlour'n.
Hajiya tabi yarinyar da kallo tana fad'in
"Har yanzu uwarki ta kasa yin ciki ta kuma haihuwa kun zauna irin abun 'ya'yan zamani, wai baza'ayi ciki ba sai yaro ya shekara biyar."
Farida ta ce
"Wai Hajiya yanzu an karb'i cikin aljanar yarinyar nan a matsayin na Ya Abdulrahim ke nan?
taya ma hakan zata yuwu a ce mu had'a jini da kaskantacciyar da ba'a san daga ina ta fito ba, ba'a san su saye dan gin ta ba, ta yuwuma 'yar wani kaskantacce talaka ne, taya za'ayi mu had'a jini da ita, wlh idan ta haihu ma ba'a isa a danganta mu da d'an da ta haifa ba,
dan cikin nan na tabbata bana Ya Abdulrahim bane."
Hajiya ta ce
"Um ni ma dai haka nagani, Abubakar ya tattare maganar ya hana yin sa, ba muna nan ba zamuga yadda d'an zai fito idan baiyi kama da Abokin turawa ba, to bazai karb'e shi a d'a ba, suje can su nima masa uba."
"Hajiya maganar kama ma bata taso ba, kawai ciki ba nashi bane dan wlh baza a kawo mana shege cikin gida ba."
Farida ta had'eye ragowar maganar nata sakamakon shigowar da yayi parlour'n.

Wani kallo ya wurga mata ta shiga taitayin ta.
ta mike da sauri tana gaishe shi bai amsa ba ya zauna.
ita ko ta ja 'yarta da sauri sukayi waje.
Hajiya ta dube shi tana cewa
"Abokin tuwa an shigo, dama ina ni man ka, cikin nan fa ni ina ganin ba naka bane,
kawai so ake ayi ma rufa-rufa a baka cikin da ba naka ba."
"Ni zan fad'i hakan ba ku ba."
ya yi maganar yana murtuke fuska.
da sauri Hajiya ta ce
"Yauwa ba naka bane ai dama nasan za'a rina, su rike kayan su a can, bari ma na kira Abubakar ya kira su tun da wuri, bazamu karb'i cikin ba gara tun da wuri su sani, tun kafin ta haihu."

Fuska ya dad'a sukewa ya ce
"Cikina ne mana ba ku kukaje kukayi jinyarta a daren mu na farko ba."
"To fisararre zama da wancan shegiyar aljanar yarinyar ya saka zama mara kunya, sau nawa ake kamata da maza a cikin gidan nan Karima tasha zuwa ta fad'a min."
ya dago ya dube ta sannan ya ce
"Yanzu idan aka ta da ke kina da hujjar da zaki kawo akan ta tab'a zina."
Hajiya ta ce
"Zancen banza yarinyar da a cikin gidan nan ta kawo wani, ga shaida an ganta da ido."
"Ni ne shaidar da yakamata a ji daga baki na, ba kurika yanke hukunci kaitsaye ba, Beauty bata tab'a sanin wani namiji ba, ni na fara sanin ta mace,
kada wani ya sake sheganta min d'a idan kuma ba haka ba zan d'auki mataki a kan kowa!."
yana gama fad'in haka ya mike yanufi kofar fita.
Hajiya ta saki uban salati
"Laha'ilaha'illallah Abokin turawa, Eh ba shakka anyi ma turen aljanu, dole na sa a nemo mai rokiyya."
Goggo Bishira data fito daga d'aki ta sinkayo zancen a sama ta saki murmushi tana karasowa cikin parlour'n.
"Zo Bishira kirawo min Abubakar ina ga fa yaron nan ya sami matsala, Eh an masa turen aljanu."
Goggo Bishira ta zauna tana cigaba da murmushi ta ce
"Hajiya wani turen aljanu gaskiya ya fad'a, duk da shiru irin nasa sai da aka sa shi ya maganu, tabbas shine babban shaidar matarsa gaskiya ya fad'a, a budurwa ya sami matarsa dan haka babu wata hujjar da za'a ce ciki ba nashi bane, kuma dai na wannan maganar, yafi kowa sanin cikin nashi ne ko akasin haka."
"To ai shike nan mu namu ido idan aka haifi aljani muna daga gege."
"Allah ma ya tsare."
cewar Gogga Bishira.



Umma karima ce da Mommy zauna anata kuskus, Umma karima ta kawo musu magani su sakawa Daddy a abinci wanda bokan ta ya bata.
sun rasa hanyar da zasu bi su saka masa dan ba cin abincin su yake ba.
Umma karima ta gyara zama cikin yin kasa da murya ta ce
"Yanzu ya zamuyi gashi malam ya ce, mu tabbata yaci maganin nan, yana ci duk asirin da Hajiya Fatima ta masa zai karye, sannan ya sake ta tabar gidan nan, kin ga babu labarin zuwan d'an shege cikin gidan nan, tun da ita uwar gayyar tabar gidan,
amma Hajiya Halima wani hanzari ba gudu ba, ga wani shawari mana, wata kila idan muka bi ta hanyar zamu sami kofar b'ullewa."
Mommy ta ce
"Yauwa fad'i muji Allah yasa ta b'ulle, ayita ta kare."
Umma karima ta ce
"Na ce me zai hana a had'a Siyama aure da Abdulrahim, bayan aure da kwana biyu ta dafo abinci ta zuba maganin ciki ta kawo mishi, irin dai ace girkin amarya, amarya tayi girki ta kawo wa uban miji,
amma yanzu mu idan muka ce zamuyi kinsan halin Alhaji ba lallai ne ma yaci ba, sai ya iya zargin wani abun ma,
amma idan ita tayi masa kuma yasan amarya ce zai iya ganin hakan a tsigar kyautatawa irin ta suruka, bazai kawo komai a ransa ba zai ci, amma me kika gani in kina gani da wata dabarar sai a sauya, ni dai ina ga ita ce kad'ai hanya mai sauki, amma ya kika ce?."
Mommy ta d'anyi jimm sanna ta ce
"Eh to wannan hanyar da aka biyu tayi, amma kina ganin su yaran zasu amince, kinsan fa taurin kan Abdulrahim."
da sauri Umma karima ta ce
"Haba haba Hajiya Halima kina uwar tasa bazaki iya juyasa yadda kike so ba, ai Abdulrahim yana jin maganar ki, kina bashi umurni zaiji,
nima zanje na tirsasa Siyama dolen ta ta amince dan bukatar mu yabiya,
idan ba haka ba fa wlh zamu zamo 'yan kallo, muna ji muna gani mu da gidan 'ya'yan mu zaifi karfin zaman mu,
karshe ita da bata saka ko d'aya ba ita zata mallake gidan."
Mommy ta ce
"To shike nan inaga hakan kawai za'ayi."
Umma karima ta ce
"Yauwa shine magana Hajia Fatima tana son ganin bayan mu, idan bamuyi da gaske ba kuwa sai ta kora mu da kafafunmu, dan malam ya tabbatar min da kalan asirin da take wa Alhaji, ya ce gurin manya manyan bokaye yake zuwa, tana yawo da sunan Alhaji da namu dan a farrakamu a kan 'ya'yan mu, gara mu tashi mu tsaya tun kafin dare ya yi mana."
Mommy ta jinjina kai tana fad'in
"Ai kuwa ta sha karya."


Umma karima na fita Mommy ta kira shi, ta ce idan ya dawo tana niman sa.
har dare bai shigo ba takuma kiransa,
ko da yazo ta ce ya zauna tana da magana da shi.
bayan ya zauna Mommy ta ce
"Abdulrahim yakamata kayi aure fa zaman ka haka ba mata, bai kyautu ba,
ga Siyama kanwar Hajiya Karima na yaba da hankalin yarinyar, me zai hana ka aureta tun da 'yar gida ce ansan halinta, Kuraiba dai tsautsayi ce yasa na ce ka aure ta, amma ita wannan ai an san komai nata."
da sauri ya d'ago ya dube ta sannan ya ce
"Shi ke nan ni rayuwata a haka zata kare, ko wace kare da doki ita za'a bani na aura,
ai ni nagama aure Mommy ko da ina da burin na sake aure bazan auri wama kika ce Siyama take ko wa? bazan aure ta ba,
idan zamata a gida ne bakwa so zantafi na baku guri."
yana kaiwa nan ya mike tsaya ya fice......!



Kuyi hakuri wlh nafi kowa son nagama littafin nan na huta wanna littafi ya katse min abubuwa da dama amma insha'allah mun kusa mu karkare


Mommy ta bud'e baki tana kallon sa har ya fice.
a fili ta ke fad'in
"Ai dole na lallab'a ka a wannan karon dan burin mu ya cika, idan na ce zan d'aga jijiyar wuya hakar mu bazata cimma ruwa ba."

Wata mota ce ta sauke Kuraiba ta shigo gidan su, a parlour ta tadda Hajiya Luba.
Hajiya Luba ta bita da kallon bakinciki.
ta kasara ta zube kan kujera tana fad'in
"Wai dan Allah Momma yau she ne zaki je ki sami Mommy ki bata hakuri na koma d'aki na,
wlh ni nagaji da zaman gidan nan, ko ba komai a can ina ganin Abdulrahim naji dad'i,
haba dan Allah ni wlh nagaji ina son Abdulrahim shi d'in had'ad'd'en gaye ne,
ganin sa ma kawai yakan iya gusar da karamin kishi,
kar iddata ta cika azo kuma dole sai an sake d'aura aure."
wani uban harara uwar tata ta doka masa tare da jan dogon tsaki ta ce
"Ai kin banza wai ke a hakan har kina tuanin Abdulrahim zai maida ki,
tun da kika dawo gidan nan fa kullum a kan hanyar fita kike,
kullum mai d'aukar ki daban mai dawowa da ke daban,
a hakan zaki koma ki cigaba da kasancewa a matsayin surukar gidan AA FIYA,
ai tun da kika rushe min shirina ke ma bazaki sami abun da kike so ba,
sai ki mike kafa mucigana da zama dake a cikin gidan nan,
ke da Abdulrahim kuwa har a bada."
Kuraiba ta mike tana cewa
"To ai shi ke nan ni nasan yadda zanyi na koma."
ta wuce d'akin ta....


A hankali cikin Feeryal ke dad'a wayo, kusan kullum tana tare da Ammie'n suna waya video call tana ganin lafiyar.
Maryam ta koma gun mijin ta can Ogun State bayan tayi wata biyu da haihuwa. yanzu ita d'aya ce tare suke kwana da Hajja Umma, ita ke kula da ita sosai, wata nayi zata kaita gun awu a duba cikin aga lafiyar sa.
san da Major Sadam yasan da cikin yaji ba dad'i dan yasan dole yanzu sai ta hife cikin kafin ya samu damar aurenta.
ya kudara wa ransa zai jira ta haihu amma ba zai jira har sai ta yaye ba, zai aure ta tazo da abun da ta haifa gidan sa.
san da cikin ya kai watanni 8 Daddy ya yi tattaki yazo garin Abuja.
ya ce yazo tafiya da ita yana so ta haihu a can Lagos.
Abba ya ce sam bazai tafi da itaba, a nan zata haihu su da suka kasa iya rike ta.
da kyar Daddy ya shawo kan Abba ya aminta su tafi da ita.
karfe 8 na safiya jirginsu ya tashi zuwa Logos.
karfe goma saura suka iso Lagos, wanda tuni mota ya iso airport yana zaman jiran saukowar su.
direban Daddy ya kwashe su suka nufi AA FIYA STREET.
Aunty na tsaye a farfajiyar side d'in ta tana zaman jiran isowarsu.
tun kafin motar ya gyara parking ta taho da sauri mai had'e da gudu ta taho jikin motar.
motar na tsayuwa ta bud'e da sauri tana fad'in
"Oyoyo 'Yammatan Ammie."
Feeryal da farincikin ganin Ammien ta ya lullub'e ta tafi to da sauri, zata rungume ta Aunty ta ce
"Tsaya tsaya bi a hankali."
tayi maganar tana kallon katon cikin ta.
kallonta bai isheta ba wai Feeryal d'in ta ce haka Allah buwayi.
Daddy ko Dariya ya yi ganin yadda gaba d'aya ta tsaya kallon ta.
cikin tsigar zolaya ya ce
"To kaka Fad'imatu a kaita ciki ta huta mana."
Aunty ta yi murmushi tare da janyo hannunta suka shige ciki.. Daddy ko ya koma motar direba ya kaishi side d'in sa.
a parlour Aunty tasa ta zauna kasan carpet ta mike kafafunta, da suka d'an kumbura.
ta je dinning ta kwaso mata lafiyayyun cake data shirya mana na musamman, gami da yogurt na musamman ta dire shi a gabanta.
kana ta zauna gefen ta tana ta yi mata sannu, kallon Feeryal baya isar ta wai 'yar ita ce da katon ciki irin wannan."
ta kuma fad'in
"Sannu kinji Feeryal Allah ya sauke ki lafiya, ga ababen kaunar ki na musamman na shirya miki."
murmushi ta yi ta ce
"Ammie yanzun fa ina cin abinci musamman tuwo sosai nake ci."
"Ai dole kici abinci Feeryal wannan ciki, dole ya saki cin abinci."
sunkuyar da kamta tayi tana kai loman cake bakin ta.
Aunty ta d'au waya ta kira Ammah ta shaida mata isowar Feeryal d'in.
kan kace me Miemie ta shigo.
ta bud'e baki da hanci tana kallon ta.
"Kai Miemie babu oyoyo."
Feeryal ta fad'a tana mata murmushi.
"Hum Feeryal ke ce haka?."
Miemie ta fad'a tana rike hab'a tare da zama kusa da ita, cike da farinciki mai had'e da mamakin ganin ciki ya bayyana sosai a jikin ta.
Ammah data shigo yamzu itama tsayuwa kallon Feeryal d'in tayi da mamaki.
kana ta rangad'a gud'a tana fad'in
"Kaga d'an duma ko a fad'e ka ko ayi shiru zaka bayyana kanka,
anyi sake d'an zaki ya girma,
Allah sarki Feeryal sannu da kokari Allah ya kauda idon makiya."
Aunty ta yi dariya tana fad'in
"Kai Ammah'n Miemie

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login