Showing 57001 words to 60000 words out of 86085 words

Chapter 20 - FEERYAL Part 3 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt

ya koyar ba, bare a zo fannin sura,
ita kanta sallar da al'walar bansan farillai da sunnoni da mustahabban ta ba,
a yanzu kuwa alhamdulillah kuma duk ta sanadiyyar sa ne,
Mom izu sittin ce yanzu a kaina godiya yakamata kije kiyi masa."
Mom ta tab'e baki tana zamewa gefe.
ta zauna kan kujera tana fad'in
"Kaje kayi wanka za'a kawo ma abinci."

Ya fita ya koma sashin su.
Ajmaal Shamsuddin Faisal sunyi farincikin ganin yadda d'an'uwan nasu ya kimtsu, har ya koma wani uztazu-uztazu.

Feeryal ce suka fito ita da Miemie da Ameerah, zasuje gurin gyaran gashi.
motar Aunty suka d'auka Feeryal ce tayi driving nasu.
suna isa samaruwa suka fara roshin a kansu, kuma yawancin duk wan da yazo Feeryal yake tinkara, da tayin soyayyar sa.
babu wanda ta kula cikin su har aka gama musu suka juyo gida.
wasu samari biyu suka biyo su har gida.
Feeryal na shiga da moto suma suka sako nasu.
a bakin get d'in side Mommy ta tsaya zata sauke Ameerah, nan suka sami damar fita a mota suka tako jikin motar.
"Haba 'yamma ta wulakanci ba bu kyau, ku bazaku gaya mata ba, idan bata jin hausa ku gaya mata da yaren da ta sani mana."
ya juya da harshen turanci yana gaya mata son ta yake, dan zaton sa hausar ce bata ji.
da sauri Miemie ta ce
"Dan Allah kuyi hakuri ku tafi ga yayan mu can zuwa."
d'ayan ya ce "To ai dai-dai ke nan bari muje mu gaya masa mu surukansa ne."
Feeryal taja motar tabi ta gefen sa tawuce sashin Aunty.

Fuskarsa a murtuke suka karaso kusa da shi, suna mika masa gaisuwa, bai amsa ba sai dad'a gimtse fuskar da yayi,
samarin ya sosa bayan keya yana fad'in
"Yaya da ma waccan kanwar taka da take jan motar can ne muka gani muke so,
to ba da wasa muke ba shi yasa ma muka taho gida, bamu tare su a hanya ba."
fuska ya dad'a gimtsewa sannan ya ce
"Ku fita ku bar gidan nan yanzun nan!."
yadda yayi maganar yasasu shiga taitayin su,
suka juya suna cewa
"Muje ina ga sai an sako manya cikin lamarin.....!



Rasheedat S Director
Mommyn Twins ce🤙🏻

My number 08034690723


Suka shige motarsu suka bar gidan da sauri.
tsaki ya ja ya nufi masallaci.
bayan an idar da sallah ya fito zai shiga gida, yaji wani saurayi yana fad'awa Ajmaal wai yazo gurin 'yammatan da suka shigo a mota ba da jimawa ba.
bai tsaya jin wacce amsa Ajmaal ya basa ba, ya nufi gurin security ya ce kada su kara barin wani ya shigo gidan nan, in har ce musu yayi gurin wata yarinya yazo agidan nan, har sai an basu sanarwar ansan da zuwan sa..


Hajiya ta nimi Daddy da Dad akan maganar auren,
Zaraddin da Saddiqa.
Hajiya ta ce
"Naji shiru kan maganar auren Zaraddin da wannan yarinya Saddiqa, tun da Allah yasa ya dawo, to ai gara ayi-ayi auren,
babu amfanin zaman su duka babu aure,
in ba so ake su tsufa a gida ba,
Bilkisu da Rahma ma ya kamata ku tsawatar musu su fitar da jikin aure,
yara duk sun zamo gandan-gandan a gida ba aure."
Daddy ya ce
"Ai ina ga nin ba wani abun da za'a jira ma, kawai wata mai kamawa da sati za'a d'aura auren zan sanarwa Bappa Salihu,
ko ya kagani Tukur?."
Daddy ya karasa maganar da son jin ta bakin Dad.
Dad ya ce
"Yaya ai duk abun da ka yanke shine dai-dai Allah ya kaimu lokacin."
Hajiya da Daddy suka amsa da amin.

Daddy da kansa ya kira Zaraddin bayan barin su gurin Hajiya.
koda Daddy ya sanar masa da hukuncin da suka yanke,
Zaraddin yayi shiru sannan kuma ya ce
"Ba damuwa Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi."
Daddy yaji dad'in ganin shiriya sosai tare da shi.
yayi ta sa masa albarka.

Ko da Dad ya sanar wa Mom hukuncin da Daddy ya yanke, ta tuma tsalle ta ce bata yadda ba, itafa bata yadda a had'a d'anta da wacce aka zubarwa ciki ba.
cikin masifa Mom tacigaba da fad'in
"Yarinyar da uwarta shahararriyar matsafiya ce, a wani dalilin za'a had'a d'ana da ita,
taga bayan d'ana ake so ke nan ko, to wlh ban aminta da wannan had'in ba,
idan ma ana yi masa kallon d'an iska da ai yanzu ya shiryu,
ita fa babu wanda bai san me uwarta ta aikata ba, wanda tsabar zunubin ta akayi sama da ita, ba'a sake jin d'uriyarta ba,
shine ake so a had'a Zaraddin da ita, to ban yadda ba."
Dad ya ce
"Ni dad'i na da ke bakya tsayuwa kiyi lissafi da tunani kike yanke hukunci,
tun da kikaji nayi shiru ban ce komai ba ai yakamata kisan akwata a kasa,
yanzu idan mukace bamu yarda da auren nan ba, shirinmu bazai tafi yadda muke so ba,
ki bari kiga yadda zata kasance, ba za'a yi auren ba kuma shiri na zai kammala, ke dai kiyi shiru ki barsu suyi ta shiri."



Major Sadam har yanzu yana kan bakarsa.
tun ranar da akayi wa Feeryal C'S ya sami labari, sai dai ya ce ba zai tinkare ta da wuri ba har sai ta sami sauki sosai.
watanni uku ke nan da yi mata C'S, yanzu yake jin ya dace ya tinkare ta.
wayan abokinsa Inspector Nasir ya kira yanzu yake can Ogun state, bayan gaisu da tambayar lafiyar junan su, Major Sadam ya kara da tambayar sa lafiyar matarsa da d'ansa sannan ya d'aura da fad'in
"Nasir yanzu 3 month ke nan da yiwa Feeryar C'S,
yanzu ne ya kamata na tinkare ta, ko da ace 'ya'yan sunan nan zan iya rike ta ita dasu dan bazan iya jiran har sai ta yaye ba, tun kafin lokaci ya kara kure min,
ina jin zan shiga Legos jibi."
Inspector Nasir ya ce
"Eh tabbas yanzu ne ya kamata kam tun da har ta kai watanni uku ta warke, a kai tafiyar ranar Saturday zanbi jirgi Friday na shigo Abuja sai mu wuce ranar Saturday."
ya ce "To Allah ya kaimu."

Kamar yadda Inspector Nasir ya fad'a ranar juma'a ya shigo Abuja, washegari asabar suka bi jirgi zuwa Legos.
sai da suka duro garin Legos kafin Inspector Nasir ya sanawar Aunty da zuwan nasu.
Aunty bata d'auki zuwan nasu da wata manufa ba, dan a zaton ta wani aiki ne ya kawo su zo.
sai da suka iso gidan yakuma kiran ta ta bawa security izinin bud'e musu get su shigo.
zuwan Inspector Nasir gidan sau biyu ke nan,
yazo yi wa Aunty gaisuwa lokacin auren su da Maryam sai kuma yau.
Feeryal da tafito daga sashin su Miemie zata koma sashin Aunty,
ta hango su suna fitowa daga motar da suka zo cikinta,
wan da mota ce na abokinsu daya taro su a airport.
tayi mamakin ganin su Nasir a farfajiyar gidan.
Inspector Nasir ya bita da murmushi, kamar bazata taho inda suke ba nauyin Nasir d'in ya sata tako wa in da suke.
Major Sadam ya kafe ta da ido,
sai gani yayi ta kara masa wani kyau da cikar girma, komai na jikinta sun kara girma.
kai a kasa take yi musu sannu da zuwa.
Inspector Nasir ya ce
"Aunty ki ta ce na gaishe ki, Aiman ma yace yana gaida Mommy'n sa."
murmushi tayi daya bayyana
jerararrun fararen hakoranta, masu d'auke da tsiririn wushirya a tsakiyar su, ya yin da kyakwawan dimple d'in ta suka lotsa.
cikin siririyar muryarta mai sanyi gami da fidda salon sauti mai kamada shagwab'a tad'an waro manyan idanunta tana cewa
"Aiman d'in har ya iya magana?."
Nasir yayi dariya ya ce
"Ya kusan iyawa dai amma yana kwab'a wa."
kai ta jinjina tana kuma murmushi.
Major Sadam ya tafi gaba d'aya a kallonta, ko kiftawa baya yi.
Inspector Nasir ya gyara tsayuwar sa yana cewa
"Feeryal gurin ki mukazo fa, amma kafin nan zamu fara tinkara Aunty Faty da Alhaji,
yau bazamu bar gidan nan ba sai da sa rana,
amma kafin nan kiyi mana jagora zuwa ciki ki shaidawa Aunty Faty zamu shigo."
batace komai ba ta juya a hankali ta nufi side d'in Aunty.
daga saman benen sashin sa yake hango komai a kan idanunsa,
rai b'ace ya sauko yayi waje,
kasancewar sakanin side nasa da inda suke da rata kuma a kafa yake takowa, har ta shige sashin Aunty kafin ya karaso inda su Nasir suke.

Ya gane su dukan su su biyun,
a daren da suka kaita asibitin sa da ke Abuja, a lokacin da mai tawagar d'aukar amarya ya d'auke ta suka sami nasarar kwatota, suka garzaya da ita asibitin sa tana a sume.
Wani kallo ya wurgawa Major Sadam sannan ya ce

"Me ya kawo ka?."
Major Sadam ya ce
"Gurin ta nazo."
gimtse fuska ya kuma yana cewa
"Kar ka kara zuwa gurin ta, idan bakaji ba kuma zan d'au mataki a kan ka."
Major Sadam ya ce
"Akan wani dalili zaka hanani zuwa gurin ta, a da take matar ka yanzu kuma ta mai rabo ce,
ka shiga sawun manema mu fafata wanda Allah ya bashi sa'a ya aureta,
babu dalilin da zai ka ka hanani zuwa inda take, dan ni na fara sonta, kuma har gobe bazan daina son ta ba, kuma sai na aure ta."
wani irin shaka yayi wa kwalar Major Sadam cikin fusatacciyar murya ya ce
"Zan iya kashe ka idan ka kara cewa zaka aureta,
sabo da ita d'in matata ce!."
Major Sadam shima ya shake kwalar sa.
da sauri
Inspector Nasir ya shiga kokawar rabasu yana fad'in
"Haba ku kuwa meye haka sai kace wasu kananun yara,
Major sake shi tun da ya ce matar sa ce,
zamu so sanin dalilin sa na fad'in haka."
"Karya ne so yake na hakura na bar masa ita, a da take matarsa ba yanzu ba, ni zan auri Feeryal ni zan aure ta yanzu, na bata kulawar da ya kasa iya bata, cikin wata biyu ya mai da ita karamar bazawa."
ran Abdulrahim ya matur b'aci yanayin da yake shiga idan ransa ya b'aci suka soma bayyana.
damasun sa suna bud'awa yayin da jijiyo yin hannunsa suka mike rad'a-rad'a, zufa yana sassafuwa ta cikin sumar kansa.
wani irin had'a Sadam ya yi da jikin motar da suka zo cikin sa, ya shake wuyansa, idanunsa suka firfito, tamkar zasu zazzago kasa.
Major Sadam ya shiga kokarin kwatar kansa, Inspector Nasir yayi-yayi ya iya b'anb'are hannunsa a wuyan Major Sadam ya kasa.
da karfi ya shiga kiran security ganin numfashin abokin nasa yana kokarin barin jikin sa.
Daddy da ya fito daga side d'in sa zai tafi masallaci ya yi saurin isa inda suke yana fad'in
"Kai Abdulrahim wani irin shashanci ne wannan, sake shi sake shi na ce."
yayi maganar yana jan bayan rigarsa.
ganin baya da niyyar sake shi, baya ma jin me yake fad'a.
Daddy ya kai masa mari yana fad'in
"Kashe shi zakayi? sake shi nace!."
kan sa ya gara da jikin gilashin motar da sai da glass d'in tayi sara ta tsage, sannan ya saki wuyar sa ya juya yana taka kasa da karfi ya nufi side nashi.
Sadam ya durkushe kasa yana dafe wuyansa gami da yin tari.
Daddy ya shi yi masa sannu da bashi hakuri yana tambayar me ya had'a su.
Inspector Nasir ne ya sanar masa abun da ke faruwa.
Daddy ya ce
"Kaji shashanci da shirmen banza, kayi hakuri ku je idan da bukatar na ne me ku zan neme ku, in banda shiririta mace ai allurar cikin ruwa ce,
tashi sannu kaje yi hakuri."
Daddy ya d'ago kafad'ar sa ya mike yana gyara zaman kwalar rigar sa.
ya kad'a yatsun sa yana fad'in
"Bazan kyale shi ba."
ya shiga mota suka bar gidan.
Daddy ya juya yana fad'in
"In banda Abdulrahim ina kai ina fad'a da hukuma,
ai baka isa ka hana wani zuwa gurin ta ba tun da ba auren ka a kanta."

Yau bai tafi asibiti ba sai bayan sallar azahar, sakamakon b'acin ran da yake ciki yau,
ana yin sallar la'asar kuma ya dawo.
sashin Hajiya ya wuce fuska ba annuri.
Hajiya na ganin sa ta ce
"Wai kai abokin turawa yaushe ne fuskarka zata canza?
kullum ya kullum fuska a turnike babu annuri,
da na d'auka had'aka da wancan 'yar da akeyiwa tunanin aljana ce yasa kake b'ata rai,
na mance da dama haka kake,
haba kasaki rai kullum mutum babu walwala, ko akwai wani abun da yake damun ka ne?."

Zama ya yi yana kuma gimtse fuska
"D'anki yasan bazai iya da Mommy ba ya had'a ni da ita, ansan aljanar ce aka bani ita gashi ai tana kan addabata, idan nasa kafa na bar kasar nan bazaku sake gani na ba."
ya yi maganar yana mikewa tsaye ya nufi kofar fita.
Hajiya ta rike hab'a tana fad'in
"To kaji min d'a,
aljanun nata ne suka shige jikin ka suke addabar ka,
to ai gara da ka fad'a da wuri a nemo masu rokiyya, ai da ne muka d'auka aljanar ce ita, yanzu kam mun gano kyawunta ne yasa aljanu shafarta,
dama ba kai kad'ai kake iya tarar su ba, ai dole su shige jikinka,
ashe dai yarinyar kirki ce,
tun da ta hana wancan munafukar Karima'r kashe babanka."

Dadday da ke shigowa ta d'aya kofar parlour'n Hajiya yajiyo hirar tasu, ya jinjina kai tare da yin murmushi irin nasu na manya......!

Mommyn Twins ce


Aunty na tsaye suna waya da Maryam
"Eh Feeryal fa tun d'azu da safe ta shigo tace min gasu Nasir sun zo, sun ce a gaya min zasu shigo amma shiru ban gansu ba,

ashe komawa sukayi to me yasa suka koma kuma, basu shugo ba?."
Shigowar Daddy yana fad'in
"Abdulrahim ne ya kora su."
Aunty ta zaro wayar a kunnen ta tana cewa
"Ina zuwa Maryam zan kira ki."
kallon Daddy ta yi ta ce
"Ya kore su kuma akan me?."
"Sabo da har da manemin Feeryal a cikin su."
shiru Aunty ta yi tana juya batun, Daddy ya ce
"Bansan meye nufin sa na yin hakan ba, bayan babu auren sa a kanta, in ba na ja masa layi ba bazai dai na kora mata mane ma ba."
kai Aunty ta jinjina ta zauna suka kama wani hirar da Daddy.

Shirye-shiryen bikin Zaraddin da Saddiqa yana dad'a kankama, duba da lokaci nata karatowa.
sosai Aunty ta bada himma wajen ganin komai ya tafi yadda ake bukata, dan itace uwar tasu yanzu.
kamar yanda Daddy ya saba a duk sanda za'ayi biki a gidan, kaf 'yan gidan shi yake musu ashobe, adadin yadda suka tsara yin ashoben su ko da yakai kala goma-goma ne. ko yanzu ma hakan ta kasance,
teloli suna ta zuwa karb'ar d'inkin 'yan gidan.
dan bikin saura sati guda ke nan.

Mom da ke tsaye tana kaiwa da kawo wa cikin parlour, waya na rike a hannunta tana ta kiran number Dad.
Dad ya shigo yana fad'in
"Haba kina ta kira tun da nace miki gani zuwa ai zanzo."
"Gara dai na d'aga ma hankali kazo, ni ban gane al'walan kifi a ruwa ba, yau fa saura sati d'aya auren nan, banga wani matakin da kace zaka d'auka ba, in kasan bazaka d'auki wani mataki ba, gara na fita nayi hauka a fasa auren nan, dan na rantse bazan bari a had'a d'ana da karuwa ba, zan d'aga hauka da bori na d'agawa kowa hankali,
tun da kai ka zama matsoraci sai yadda akayi da kai, kazamo kamar rakumi da akala,
sai yadda akayi da kai."
"Matsala ta dake gajen hakuri, ki saurara ki zuba ido kiji."
Dad ya juya ya fita Mom ta d'aga murya tana fad'in
"Idan baka san yadda zakayi ba ni nasan yadda zanyi,
gara ma kasan in da dare ya maka."


"Feeryal fito mutafi mana ke fa shirin ki sai a hankali ni nama fi son ke ki fara shiri sabo da shirin ki sai an jiraki,
kin san halin telan nan idan bamu je ba bazai yi da wuri ba."
"Kai Miemie ai na gama muje."
Feeryal tayi maganar tana gyara zaman gyalen abayar jikinta.
suka fito.
direban Mommy ne zai kaisu Ameerah na zaune a motar tana jiran su, suka karaso.
duka baya suka shiga direba na kokarin tada mota, aka bud'e murfin gefen da Feeryal take.
duk suka juyo da sauri dan ganin wanda ya bud'en.
fuska a gimtse babu wasa yayi wa Feeryal alama da hannu ta fito.
yi tayi kamar bata fahimci a bun da yake nufi ba.
Miemie da Ameerah kuwa kowa ya shiga taitayin sa.
"Fito na ce."
ya fad'a idanunsa a kanta yana kuma gimtse fuska.
kallon motar tayi ta tuna da motar Mommy'n sa ce,
a ranta take fad'in
sabo da motar mamarsa ce ya ce ta fita musu a mota, da sauri ta zura kafarta waje ta sako kafar daf da nashi, soba da yana tsaye daf bakin kofar sosai, ta rab'a gefe ta tafi da sauri ta nufi side d'in Aunty.
ya rufa kofar yayi wa direban alama da su tafi.
ya juya ya na kalmashe hannunsa a kirji idanunsa a kanta harta shige.

Da sauri ta fad'o cikin parlour'n.
Aunty na ganin ta ta ce "Baku tafi ba har yanzu Feeryal?."
baki ta kuma cunowa tana fad'in
"Ammie bani key'n motar ki, Sahab d'in nan dan yaga na shiga motar Mommy'n sa ne zai ce na fita, bazan kara shiga motar bama dama Miemie ce ta ce muje a ciki."
Aunty ta zuba mata ido kamar mai nazarin wani abu sannan ta ce
"Yana d'aki je ki d'auka."
ta wuce da sauri tana kunkuni itafa ya b'ata mata rai abunda ya mata, sabo su kannen sa ne kuma motar mamarsa ne shi yasa ya fito da ita.
ta d'au makullin tayi waje.
Aunty ta ce
"Kije a hankali banda gudu."

Parking lot ta isa ta shiga d'aya motar data d'auko key'n sa.
ta ja motar mai ganin side d'in ya bud'e ta fita.
tana kokarin juya motar ta saita hanyar nufa babban get,
taji anyi knocking glass d'in motar.
da sauri ta d'ago shi ta gani, tana shirin zuge glass shi ya rigata bud'e murfin.
ido cikin ido suka kalli juna.
"Koma ciki."
ya fad'a idanunsa cikin nata.
saurin janye idanunta tayi, ta cuno lips d'in ta ta ce
"Wannan motar Ammie'na ne."
gira ya d'a alamun ya fahimci in da maganar nata ya dosa, wato tunanin ta wancan motar Mommy'n sa ce.
hannu ya mika ya zare key'n motar ya ce
"Wannan motar Daddy ne ya siya ba ita ta siya ba, dan haka fita, kaf parking lot d'in ta duk motocin ciki Daddy ne ya siya kar kiyi gigin d'auko wata."
da sauri ta talle shi taji haushin maganar nasa, nan da nan idanunta suka ciko da kwalla.
wato gori ya yi mata ita bata da ikon d'aukar wani mota cikin gidan nan, tun da ita ba 'yar gidan bace.
duk yadda taso danne kukan kar tayi a gabansa, ina sai da kukan ya kwace mata, ta fita da gudu tayi ciki tana toshe bakinta.

Ta wuce Aunty a parlour da gudu tayi cikin bedroom nata.
ta zube kan gado tare da fashewa da kuka.
karo na farko data ji gorin wani ya mata zafi.
tun tashin ta da ta fahimci wace ce ita, duk gorace-goracen da ake mata kazamin gori mai muni. bata tab'a jin zafin gori irin wanda ya mata yau ba, sai taji nashi ya fi na kowa mata zafi.
ta sha kukan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login