Showing 51001 words to 54000 words out of 86085 words

Chapter 18 - FEERYAL Part 3 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt

kashe su,
Mommy da baki kashe su ba,
me yanzu mutane da kawayen mu zasu rika fad'a Mommy'n mu tayi kisa."
Sumayya ta kuma rushewa da kuka.
Ajmaal yayi waje yana share kwalla.
Ameerah da hawaye ya ciko idanunta ta zube jikin Mommy tana share mata hawayen da ke gangara kan fuskarta.
yayin da itama jikinta yayi sanyi..

Bappa Salihu ya shiga gurin Daddy.
anan ya tadda su Dad da Abbieh.
sunyi mamakin ganin sa suka mike suna yi masa sannu da zuwa.
Daddy da har yanzu jikin sa da saura ya ce
"Bappa baka sanar mana zaka zo ba bamu tura mota domin taron ka ba a gafarce mu."
Bappa Salihu ya ce
"Zauna Abubakar."
ya dubi Dad da Abbieh yana cewa "Tukur Sulaiman ku kirawo hukuma azo a tafi da Halima."
Abbieh yayi saurin cewa
"Allah ya huci zuciyan ka Bappa da dai anyi maganar a cikin gida daya fi."
"Hakane kuwa kayi hakuri Bappa kuskure kam anyi sai dai fatan a gyara nan gaba."
cewar Dad.
Bappa Salihu ya ce
"Babu maganr gyara kuskure, baza'a rufe maganar a gida ba dan suma raine da su, hukun cin kisa kuma kisa ne, dole kuma a hukuntata,
Abubakar ka sake ta kafin a tafi da ita."
Daddy ya gyara zaman sa yana cewa
"Bappa na saki Halima amma na maida ita, abisa umurnin Hajiya,
da fari nima hukuncin dana so zartarwa ke nan, kiran hukuma azo a tafi da ita,
sai dai yin hakan bashi ne zai sa, yaran su dawo ba."
Bappa Salihu ya ce
"Ko da bazasu dawo ba hukunci ya rayata a kanta, kuma dole a zartar da hukunci."
Abbieh ya ce
"Bappa a bar maganar zuwa yarinyar ta sami sauki, a halin da ake ciki yanzu shima kansa Yaya Abubakar ba balafiyar ne da shi ba, kayi hakuri a aje maganr tukun."
Daddy da Dad duk suka sa baki akan bar kiran hukuma tukun.
Bappa Salihu badun ya so ba ya
hakura amma da tabbatar musu da cewa, zai zauna tare da su a nan har lokacin da za'a yanke wa Mommy hukunci.
ya fita yana tambayar Ajmaal ina Abdulrahim yake?.
ya ce tun jiya daya shige side d'in sa bai ga fitarsa ba har yau.
Bappa Salihu ya nufi sashin nasa Ajmaal na biye da shi.
mai gadin side d'in a ya shaida musu yana ciki.
suka karasa kofar parlour'n sa Ajmaal ya ya babbuga.
ya d'au tsawon ninuna 5 kafin yazo ya bud'e.
yana sanye da gajeren wanda da singilet.
fuskarsa babu annuri.
Bappa Salihu ya bubbaga kafad'ar sa yana cewa
"Sannu kaji najimin duniya, Allah ya huci zuciyar ka."
baiyi magana ba har Bappa Salihu ya juya daga bakin kofar suka fice daga side d'in yana tsaye.
kana a sannu ya taka ya koma ciki.
A b'angaren Bappa Salihu kuwa suna fita
Ajmaal ya d'auke sa, zuwa asibiti in da Feeryal take.
sosai Bappa Salihu ya bawa su Aunty hakuri ya koma ga Feeryal itama yakuma bata tabbacin za'a bi mata kadinta.
Aunty dai har yanzu hawaye bai bar zuba a idanunta ba, sai dai tace masa ba komai, dan Abba'n Abuja ya gargad'e ta da d'aukar mataki a hannunta, shima kuma baiyi magana ba har lokacin duk da sunji matukar zafin abun da ya faru..

A b'angaren Mommy kuwa jikinta ya sanyaya matuka zafi biyu ta ko ina, gana Daddy gana mahaifinta.
tana zaune tayi jigum a d'aki kiran Hajiya Luba ya shigo wayarta.
kamar bazata d'aga ba harya kusa yankewa kafin ta d'aga.
"Hajiya Halima ikon Allah ashe haka kika kware a iya kisan kai,
amma anji kunya atarihin mu mu kawaye babu wacce ta tab'a aikata irin abunda kika aikata yanzu, to ina laifin ki had'a da babban d'an naki duk ki kashe sakarai mara lissafi."
Hajiya Luba tana kaiwa nan ta kashe wayar.
Mommy tabi wayar da kallo jikinta na dad'a jin sanyi, wanda har ya kai da jin kamar abun kunya ta aikata,
dan tun da abun ya faru take amsa kira daga kawayen ta suna masu mamakin abun da ya faru.

Kwanan Feeryal biyu ita ma aka sallame ta.
tun da suka dawo gida Aunty a zubda kwalla take, ta kasa iya daure zuciyarta.
a yammacin ranar da suka dawo Aunty na zaune a gefen Feeryal tana had'a mata ruwan zafi da milo, jifa-jifa tana share hawaye.
ganin hawayen nata yake sa Feeryal d'in yin hawaye.
a hankali Feeryal ta kwantar da kanta jikin kafad'ar Aunty,
takai bayan hannunta ta goge hawayen da suka zubo mata.
cikin muryarta mai sanyi ta ce
"Ammie to wai mu meye damuwar mu ma, ba kin ce idan na haihu za'a basu d'ansu ba,
to ai 'ya'yan su suka kashe mu babu ruwan mu, Ammie ki daina kuka ni ma kina sani kuka, daga yau kar mu sake damuwa tun da dama nasu ne."
Aunty ta matse ido da karfi tana son had'iye kukan da ya taso mata.
da sauri ta mika mata cup d'in ta mike ta fice ta shige d'akin ta, dan bata son yin kukan agaban ta.
bin bayan Aunty tayi da kallo har ta fice.
a hankali ta kai cup d'in bakin ta ta kurb'i yea d'in.
Aunty tayi kuka sosai kafin ta fito bayan ta wanke fuskarta ta share kamar batayi ba.
tana fitowa Abdulramin ya shigo d'auke da sallama mara sauti a bakin sa.
Aunty ta amsa ya karaso ciki ya gaisheta batare da ya had'a ido da ita ba.
Aunty ta amsa gaisuwar tasa gami da d'an yin murmushi ta ce
"Tana ciki."
ta juya ta koma d'akin ta.
a sannu ya tako ya tura kofar, da sauri ta d'ago zaton ta Aunty ce.
ganin shine ta sauke idanunta kasa.
ido ya kura mata tare da soma takowa cikin d'akin, ya iso bakin gadon.
tana jin yadda idanunsa yake kafe a kanta.
sinkayo muryarsa tayi
"Ina mai baki hakuri na rasa 'ya'yan ki da kikayi."
ta jiyo maganar sa daga in da yake tsaye a kanta.
da sauri ta d'ago ta kalle sa sai kuma ta cuno lips tare da sauke idanunta kasa ta ce
"Ya'yan ku dai ai dama naku ne, ba haka kuka zab'ar musu ba, ni babu ruwana."
tayi maganar tana dad'a cuno baki cikin yanayin ta mai sanyi da fita da yanayin shagwab'a.
cike da jin haushin yadda Mommy'n sa tasa Ammie'n ta tashiga damuwa take ta kuka akan yaran.
ta juya kai ta d'aya gefen tana mai dad'a cuno baki gaba.
bataji takun tafiyarsa ba sai karar bud'e kofa taji, ta juyo ta hangi bayan sa yana fita daga d'akin.
kai ta kuma juyawa tana mai dad'a b'ata fuska da gaske wai haushi take ji dan ansa Ammie'n ta kuka..

"Feeryal."
taji an fad'a ta juyo da sauri jin muryar Chuchu da Chulu.
yunkurin mikewa tayi da sauri, suka rike gefe da gefen kafad'un ta suna cewa
"Yi a hankali Feeryal."
ta zauna suka zauna a gefen ta suna fad'in
"Ki gafarce mu san da abunnan ya faru bama kusa, munyi bakincikin da muka gaza taimakon 'ya'yan ki har suka salwanta, muna niman afuwarki ki gafarce mu."
hannaye bibbiyu suke rokonta.
ganin yadda suma suka nuna damuwa sosai ta ce "Ni fa yanzu na daina damuwa tun da dama nasu ne, ko ma me sukayi da su oho ni ban damu ba."
Chuchu da Chulu sun dad'e a gurun ta kafin suka tafi...



Zaune yake a office d'insa, idanunsa a lumshe ya jingina bayan sa jikin kujera yana d'an jujjuyawa.
Dr Imran ne ya shigo ya karaso yana yi masa kallon tausayawa,
tabbas uwansa ta kasance mai son kai,
ko bai fad'i damuwar sa ba bayau ya saba zama da shi ba,
duk da halayen sa masu wuyar gane wa ne, amma tabbas ya lura da shiga kunci tare da shi tun ranar da uwassa tayi sananiyyar mutuwar 'ya'yan sa.
table d'in gaban sa ya bubbuga, a hankali ya bud'e lumsassun idanuwan sa.
Dr Imran ya ce
"AA akwai C'S da kasa time 1 30 an shirya ko mai saura 20 seconds yanzu."
mikewa yayi tare da d'aukar makullin motar ya nufi kofa yana cewa
"Kayiwa Dr John magana bazan yi C'S ba."
Dr Imran yabi bayan sa da kallo har ya fice.
ire-iren wad'an nan halayen nasa duk wan da yake tare da shi yakan sha wuya wajen gano inda lamuran sa suka dosa, baka b'a gane albiblarsa.

Ya shige mota ya bar asibitin.
ko da ya koma gida wanka yayi ya sauko parlour, da gajeren wando kad'ai babu riga a jikinsa.
ya kure gudun AC yana zama kan kujera.
system nasa dake kan table d'in gaban kujerar daya zauna, ya kunna,
sosai ya mai da hankalin sa ga system d'in.
yana dada ware idanunsa cikin system d'in, yayin da damatsan hannunsa suke bud'awa.
sai kuma ya mike zumbur ya nufi stairs, cikin zafin nama ya yake had'a stairs bibbiyu ya shige bedroom dakika uku yafito yana gyara zaman riga da wandon jikinsa.
ya sauko ya d'au makillin mota yayi waje da sauri.
ganin yadda ya figi motar da sauri cikin azama mai ganin side d'in ya wangale masa get.
ganin yadda ya dumfaro babban get da gudu security suka bud'e masa get ya fice kamar zai tashi sama.
sosai yake sharara gudu kamar ba'a cikin gari yake tafiyar ba a wajen gari yake.
mintuna kalinan suka kawo shi asibitin da akayiwa Feeryal C'S.
bai ko dai-dai ta parking ba ya duro a motar da bai tsaya rufe kofar motar ba.
wata doguwar igiya mai karfi yana rike a hannunsa.
da karfi ya naushi kofar office d'in Dr ya bud'e yasa kai ya shige ciki.
da sauri Dr ya mike yana fad'in
"Lafiya Dr AA FIYA! zaka shigo ta irin wannan yanayin?."
hannunsa yakai kan belt d'in kugunsa yana gyara zamansa, yashiga d'aga kafarsa yana takowa cikin office d'in tamkar na mijikin zaki!.
Dr ya mike zumbur yana kuma fad'in
"Ya zaka shigo min kai tsaye irin haka, kamar baka san aikin ka ba."
a gabansa ya tsaya yana binsa da wani irin kallon da ya kusa sashi ya saki fitsari a wando, murya a gautsatse ya ce
"Ina file d'in da ke d'auke da rcd d'in bazata iya haihuwa ba dole sai an mata C'S!?."
da sauri Dr ya ce
"Ya zaka zo kana challenge d'ina, I'm Dr ka sani yadda kake likita haka nima likita ne,
so baka da hurumin shigo min kana yi min irin wannan tambayar kamar ka mai da ni bansan aiki na ba,
kasan na fika a shekaru tun kafin ka zamo likita nake aikin likitanci,
so ba bu wani abun da zaka nuna min, in zaman duniyar ce nariga ka sanin ta,
haka ma hai kin."
wani irin wawan mari ya d'auke shi da shi, da sai da bakin sa ya fashi jini ya fita daga gefen bakin,
ya shako makokwaronsa
cikin kakkausar murya ya ce
"Waya saka!."
numfashi na sama-sama idanunsa suka firfito da kyar ya iya fad'in.
"Ka sake ni zan gaya maka."
gara shi ya yi da jikin bango da karfi sai da kansa yayi jini,
kana ya saki wuyan nasa yana kuma d'auke shi da marin daya fi na farko.
a gigice ya ke fad'in
"Babu wan da ya sani, ba zata iya haihuwa ba ne dole sai an mata C'S."
igiyar daya shigo da shi ya janyo yana ware shi,
yayin da suffarsa ya dad'a rikid'ewa ya canza izuwa na ban tsoro.
da sauri likitan yashiga ja da baya fitsari ya kwace masa, murya na gargada ya ke fad'en
"Ka dakata na gaya maka da gaske babu wan da ya sani."
wani irin naushi ya kai masa ya zube kasa ya d'ad'd'aure shi da igiyar ya ciccib'o shi ya yi waje da shi, ya bud'e bayan bot ya jefa shi ciki, ya shige motar da mugun gudu yabar asibitin.

A wani b'ari na gidan gona ya shiga da shi,
wani katon d'aki ne mai d'auke da na'urori ya yi masa kyakkyawan d'auri jikin kujerar karfe.
bayan ya masa duka bugun girma, ya farfasa masa jiki ya yi masa jina jina sannan
ya kunna shocking jikin kujerar."
ya soma jijjiga gami da ihun azaba.
sai da ya tabbatar da shocking ya shige sa sannan ya kashe.
numfashin azaba yake saukewa,
yana fad'in
"Zan gaya maka kada ka kashe ni, matar baban ka ce ta sani."
ya kunnan na'uwar d'auka gani kai tsaye yayi connecting da satellite
d'in in house nasu AA FIYA STREET.
gaba d'aya TV gidan ya d'auke duk wanda yake zaune gaban TV gyara zama ya kuma yana kallon TV da mamaki ganin sa a wani guri shi da Family Dr su,
dayake d'aure jini na fita aduk in da yamasa rauni.
Bappa Salihu Daddy Dad Abbieh Ajmaal Shamsuddin Faisal.
duk suna parlour'n Daddy.
in da kowa ya mai da hankalin kan TV.
dai-dai in da Abdulrahim yake d'auke sa da mari ya shako wuyansa.
likitan ya tuntsire da dariya jini na sauka a bakin sa,
"Idan ka kashe ni a ina zaka sami sauran labarin, akanta ita da ban ma aikata mata komai ba, ina daf da aikatawan ka shigo."

Aunty na d'aki ita da Feeryal kiran Ammah ya shigo wayarta.
tana d'agawa Ammah ta ce
"Ammien Feeryal kina gaban TV kuwa?."
Aunty ta ce "Aa Ammah'n Miemie me ya faru."
da sauri ta ce
"Kunna TV ki gani ko ni kad'ai nake gani."
da sauri Aunty ta d'au rimut ta kunna TV d'akin Feeryal.
tayi arba da abun da kowa yake gani a cikin gidan.
Sumayya ta shigo bedroom d'in Mommy da gudu tana fad'in
"Mommy Mommy kunna TV ki gani."
Sumayya ta d'au rimut ta kunna TV.
Hajiya ta gyara zama tana fad'in
"Bishira Kulu wa nake gani ne nan kamar abokin turawa,
shirin fim ya koma ko kisan kai shima ya soma."
Hajiya tayi d'ip da maganar jin yana fad'in
"To bari na aika ka lahira tun da can kake son zuwa."
ya mika hannu zai kunna shocking d'in da sauri likitan ya ce
"Aa a'a zan gaya maka Hajiya Karima ce ta sani na ciro mata mahaifan ta tare da 'ya'yan a cikin mahaifan,
kafin kuma na cire kazo, hahahaha ka girgiza ne to ai bakaji komai ba, dan wannan ba shine karo na farko ba,
mamarka da amaryar baban ka yanzu haka babu mahaifa a jikin su........!

Mommyn twins ce



"Dukansu tasa na cire mata mahaifar su,
lokacin da baban ka ya auri Hajiya Fatima da wata uku ta sami ciki, ta kwanta tana laulayin cikin, ni ya kirani nazo naja jinin ta, dan naje nayi gwaji dan an d'auka malaria ce, bayan na je na gwada naga ciki take da shi,
na dawo gidan ku domin na yiwa Alhaji albishir da cikin nata,
Hajiya Karima ta tare ni kafin na isa sashin Hajiya Fatima,
ban kawo komai ba nafara yi mata albishir da cikin amaryarta.
a take ta yi min tayin kud'i masu soka kan tana son na ciro mata mahaifar da cikin ke ciki na kawo mata,
kuma zatasa a gina min sabon asibiti.
yawan kud'in da kwad'ayin sabon asibitin yasa banyi tantama wajen aminta ba, dan ba kud'in wasa tace zata bani ba, a take na canza result d'in na sanar wa Alhaji akwai wani ciwon da nagani cikin jinin ta, ina so a kawota asibiti dan a bincika da kyau.
a ranar Alhaji ya d'auke ta ya kai ta asibitin nayi scanning naga twins ne a cikin nata na tsawon 2mon.
na samarwa Hajiya karima tace fad'uwa yazo dai-dai da zama dama mahaifa mai d'auke da twins take so, ta kuma karamin kud'i a kan wanda tace zata bani,
a take na sanarwa Alhaji akwai wani ciwo a cikin ta wanda idan har ba'a yi gaggawan cirewa ba zata iya rasa ranta.
nan take ya sa hannu ya ce a cire mata.
a ranar ba'a kwana ba nayi mata
operation naciro mahaifar mai d'auke da cikin 'yan biyu, na bawa Hajiya Karima nan take ta tura min kud'in da tace zata bani,
a cikin watan tasa aka fara gina min sabon asibiti.
na gina sabuwar rayuwa nasoma fantamawa da kud'in da ta bani ga sabuwar ginanniyar asibitina."

Yaja numfashi yana fad'in
"Zan sha ruwa ka bani ruwa na sha."
wani gigitaccen mari ya d'auke sa da shi, zuciyarsa na tafarfasa, ya shiga naushin bakinsa sai da ya zubda masa hakoram gaba.
Daddy ya yi wani irin mikewa hannu na rawa yake nuna Dr ta cikin TV yana fad'in
"Dama a ranar mahaifan Fad'imatu ka cire da 'ya'ya na aciki, kayi min karyar cewa ciwo ne a cikin ta!?."
Bappa Salihu ya roko Daddy ya zaunar da shi yana cewa,
"Zauna Abubakar Allah baya zalunci sannan karya bata d'aurewa raminta kurarriya ce."
Abbie da Dad Ajmaal Shamsuddin Faisal, duk sun cika da d'inbin mamakin daya sasu bud'e baki suna kallon abun da ke faruwa kamar a shirin film.

a b'angaren Hajiya kuwa wani uban salati ta sake tana fad'in
"Laaaha'ilaaha'illaaa, amma Karima anyi shegiyar bakar makira, a she dama Fatima ba juya ba ce ta sani kullum da kalar gorin da nake mata kan ta kasa haihuwa, ashe-ashe ita ce tayi sanadin rashin haihuwar nata,
amma dai Allah ya d'ebe miki albarka Karima."
goggo Bishira da kulu sai tafa hannu suke.
"Allah ya toni asirinki Hajiya Karima, Yaya Abubakar ya haifo zaki mai share masa hawaye,
munafuka algunguma, ka kashe shi Abdulrahim sannan kazo ka had'a da ita."
cewar goggo Bishira tana gyara zaman ta idanunta akan TV.

Ammah ta fito da sauri ta nufi sashin Aunty Miemie na biye da ita.
tayi mamakin ganin Aunty zaune tana kallon TV tana sakin murmushi, Feeryal na gefe tana sharar kwalla.
Ammah ta karaso ciki jiki a asanyaye.
Aunty ta d'ago ta kalle ta tana murmushi ta ce
"Ammah'n Miemie ashe dai ni ba juya ba ce."
Ammah ta zauna jiki ba kwari ta na cewa
"Hajiya Karima idan batayi wasa ba bazata sami rahamar Allah ba."


Ihun azaba ya yi yana fad'in
"Ka taimaka ka bani ruwa na sha zan gaya maka sauran."
gorar ruwa ya d'auka da sauri ya bud'e baki dan ba hanun karb'a duk a d'aure hannayen suke.
ya tsiyaya masa ruwan cikin baki ya kama sha kot-kot, baiyi fin kurb'a uku ba, ya sheka masa sauran a fuska kana yayi wurgi da gorar.
Dr ya ja numfashi yana latse ruwan dake bin bakin sa sannan ya cigaba da fad'in


"Bayan wani lokaci a ranar da mamarka zata haifi Ameerah, tare da ita akaje asibiti bayan tayi min tayin kud'i mai tsoka ta waya, ganin yawan kud'in yasani amincewa suna kawo ta asibitin ita da baban ku da kakarku, nayi rubutu na ce C'S za'a mata, kamar yadda Hajiya Karima ta bukata, bayan da kanta ma zata iya haihuwa na ce dole sai an mata C'S,
kamar yadda Hajiya Karima ta shirya.
babu b'ata lokaci mahaifin ka ya sa hannu aka shiga da ita.
bayan na ciro Ameerah sannan na cire mahaifar na damkawa Hajiya Karima, ta biyani kud'in da tayi min tayinsa.
ganin yawan kud'in yasa naji dad'i, har na kara ginin asibiti na da kud'in,
a cikin 'yan shekarun nan ma ta kuma nima na tana niman mahaifa yazo a sa'an zanyi wa wata C'S na cire na kai mata ta biyani.
shi ne da aka kai matarka haihuwa ta ce na cire mahaifar da yaran a ciki gaba d'aya,
kuma ai kazo kafin na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login