Showing 54001 words to 57000 words out of 86085 words
Chapter 19 - FEERYAL Part 3 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt
cire ka sani dai ba ni na kashe maka yara ba mamarka ce ta kashesu,
kar ka kashe ni kayi hakuri dan Allah kar ka kashe ni."
d'ip TV ya d'auke ya dawo tashar da kowa ke kallo..
Mommy da ta mike tsaye jikinta na tsuma, tun san da Sumayya ta kunna mata TV har yanzu da TV ya d'auke.
wani irin suya gami da girgiza zuciyarta yake, lallai mutum a bin tsoro ne, wacce ta yarda da ita tabata dukkan yarda, ashe ita ce makashin ta.
lallai hausawa sunyi gaskiya makashin ka na tare da kai.
nannauyar numfashi Mommy ta sauke a fili ta furta
"Lallai Hajiya Karima kin jima kina zurma ni a rami, ban ankara ba har sai da kika ruftamin kasa a ka."
Wani irin zufa ne yake sassafowa Umma Karima, ta cire d'ankwalin kanta tana fifita.
"Bazan kyale ka ba Abdulrahim tun da ka tono asirin da ya dad'e a bisne."
Bilkisu Rahma Nabila duk suka juyo ga mahaifiyar tasu, ya yin da jikinsu ya yi matukar sanyi, gami da matukar jin mamakin abun da mamar tasu ta aikata.
Siyama ko hannu ta nad'e duk da tasan Aunty'n nata ma'abociyar ta'ammali da bokaye ne, amma batayi zaton abun nata yakai nan ba.
Bilkisu ta ce
"Umma me yasa zakiyi haka."
duk sauran 'yan'uwan nata ma kalar tambayar da sukayiwa uwar tasu ke nan.
Saddiqa data shigo da sauri ta ce
"Umma kowa a gidan nan ya kalli abun da ya faru, Umma ya zakiyi haka."
Nabila ta d'aura hannu a kai tana fad'in
"Mun shiga uku mu da gidan uban mu za'a rika mana gori da hantara, wanna tsintacciya Feeryal d'in shike nan ta sami abun mana gori itama,
shike nan muda gidan mu zata rika yimana kallon banza."
Rahama ta ce
"Wacce irin magana ce wannan Nabila ai abun da Umma ta aikata, shine abu mafi muni ba kallon da Feeryal ko mutane zasuyi mana ba,
idan Feeryal tayi mana kallon banza batayi laifi ba, dan mun aikata mata fiye da yadda zata mana."
Nabila ta yamutsa fuska tana fad'in
"Ko ma me Umma tayi wlh ni da gidan ubana bata isa tayi min kallon banza banci ubanta ba."
Bilkisu ta ce "Ki rufa mana baki Nabila, abun da Umma ta aikata abun kunya ne agare mu,
Umma baki kyauta ba."
Bilkisu bata rufa baki ba
Umma Karima ta juya ta shige d'aki tana fad'in
"Dole naje gurin boka yanzu yarufa min bakin kowa."
ta shiga tana kokarin d'aukar mayafinta
taji wani irin karar durowar abu da saida ilahirin side d'in ya girgiza, tamkar sama zai rusho ya afko kasa.
girgiza mai matukara ban tsoro da firgitarwa.
kafin ta dawo hayyacin ta daga sananin firgitan data shiga taji anyi sama da ita an buga da kasa.
wasu halittu masu ban tsoro suka bayyana wa ganin ta,
ya yin da
muryoyin su masu matukar bantsoro da firgitarwa suka karad'e jinta tamkar dodon kunnen ta zasu zazzago kasa.
idan kaji ana kuka ko ihu samin dama ce ga tashin hankalin da ka shiga,
idan tashin hankali yakai tashin hankali ihu ko kuka basa tab'a maraftarka.
yanayin ne ya kasance da Umma Karima wanda take fatan dama tayi ihun ko wani zai jita ya kawo mata d'auki,
dan tasan kiyamar ta ce ta tsaya.
saukar bulalu ta soma ji ta ko ina a jikinta, tamkar aska mai tsananin kaifi a ke tsastsaga jikinta da shi.
aka shiga tabaibayeta da sarkokin sarfe.
ya yin da muryoyin suka soma amsa kuwa cikin kunnuwanta.
"Yau sa'ar ki ta kare zaki karb'i hukunci mai tsanani daga fadar sarkin Aljanu,
ire-iren ki azzalumai sarkin aljanu ne yake yanke muku hukunci da kansa, a duk sanda kuka had'a kai da azzaluman jinnu kuna zaluntar bil'adama, ko jinnun da basu ci muku ba basu taka muku ba,
jeki ki bayyana kanki wa duk wanda kikayi wa zalunci,
kafin karb'ar hukuncin ki!!."
idanun Umma Karima suka firfito kamar zasu zazzago kasa.
ta yunkura da gudu tayi waje a gigice tana fad'uwa tana tashi cikin mawuyacin hali.
'ya'yan ta da suke tsaye cirko-cirko wan da firgicin girgizan da sukaji side d'in ya yi, kowa ya shiga niman hanyar guduwa waje.
ganin uwar tasu ta fito kamar an d'agota an jefo ta cikin parlour'n ta bugu da kasa.
ta kuma mikewa
ya yin da take jin saukar bulalun ta ko ina a jikinta.
'ya'ya nata sukayi kururuwa ganin halin da uwar tasu take ciki,
wan da basa iya ganin halittun,
sai dai azabar da take sha kad'ai ke bayyana a jikinta.
ta na tabaibaye da sarka
a haka ta nufi waje
idan ta fad'i sai tayi birgima a kasa ta gogo fuskarta da kasa jini ya fito kafin ta mike ta kuma fad'i a haka ta isa farfajiyar gidan.
inda 'ya'yan ta suka biyo ta a baya suna ihu.
Firgicin afkuwar lamarin ya sanya kowa na gidan fitowa farfajiyar gidan, har da Feeryal, da ta soma samin lafiya.
aka jefo Umma Karima tsakiyar mutanen gidan ta fad'i timm a kasa,
ta goga fuskarta da kasa ta d'ago baki na fita da jini, ta ke fad'in
"Ni karima ni na sa aka cire min mahaifar Hajiya Halima da Hajiya Fatima na kaiwa boka yayi min asiri da shi, dan na mallaki Alhaji,
da dukiyarsa baki d'aya, bayan na mallake shi nasa a kashe shi,
mahaifa uku boka ya ce na kawo, domin a kashe Alhaji,
mahaifa uku ya ce na saka cikin kaskon tsafi, na farko mahaifa mai d'auke da yara 'yan biyu da basu wuce wata uku cikin mahaifar ba,
na biyu mahaifar da babu komai cikin sa, na uku mahaifa masu d'auke da 'ya'yan da suka kai watanni tara,
a ranar farko dana saka mahaifar farko cikin kaskon tsafi,
a ranar ce Alhaji ya soma gamuwa da mugayen mafarkan da yasa masa ciwon zuciya,
bakaken aljanu suka soma bibiyarsa a mafarki domin hallakashi dan na mallaki dukiyarsa.
a ranar dana saka mahaifa na uku ana daf da kashe Alhaji na kirawo boka na a matsayin mai magani,
domin yazo ya karasa aikinsa, da ya shiga d'akin Alhaji, da ranar Alhaji bazai kwana a duniya ba,
Feeryal ta tare shi harta fasa kwaryar tsafin,
sanadin da aiki ya dawo baya,
boka ya ce sai na sake kawo wani mahaifar mai d'auke da yara biyu a cikin sa, kafin a karasa min aikin,
shine sanadin da nasa a ciro min 'ya'yan cikin Feeryal a cikin mahaifarsu, da likita ya tabbatar min da ya duba yaga biyu ne a cikin ta.
da ban yi sa'a ba nazuga Hajiya Halima ta je ta kashesu.
sanadin da yasa na aikata haka, ina bakin cikin da ni ban sami 'ya'ya maza ba, naso bayan na kashe Alhaji zan hallaka yaya mazan Hajiya Halima, sannan na mallake dukiyar Alhaji, tun da nasan idan ya mutu bani da gadon sa da yawa,
tun da a baya nayi ta kokarin ganin na sami d'a na miji ban
samu ba, har na ja direba na
muka soma had'a shinfid'a ko dan zan sami d'a na miji tare da shi, ina bashi kud'i domin
ya biya min bukata ko zan sami
cikin d'a na miji tare da shi,
amma akayi rashin sa'a na sami
cikin sai dai ba na mijin na haifa ba,
Nabila wannan ba 'yar Alhaji bane cikin da Sule direba ya yi min ne, a wani lokacin da Alhaji baya ma kasarnan,
nasan yadda nayi babu wanda ya gane bare a zarge ni,
har na haifi Nabila a matsayin 'yar Alhaji,
ban hakura ba bayan haihuwarta nayi ta kokarin ganin ko zan sami d'a na miji,
ina d'aukarsa muna fita hotel nayi ciki uku a bayan ta, ina zuwa asibiti a gwada idan akaga mace ce sai na sa a zubar,
daga baya na hakura na soma shirin d'aukar matakin na kashe Alhaji na kawar da 'ya'yan Hajiya Halima maza, dan na mallaki dukiyar Alhaji,
sai dai tun da Feeryal tazo gidan nan take bani matsala dan duk shirin da nayi dan cimma burina ita take rushewa,
ta b'ata min shiri, badun wanzuwan ta a gidan nan ba da yanzu ba wannan batun ake ba."
Gaba d'aya kallon Umma Karima ake kamar TV, zuciyoyi da fuskoki duk sun ciki da d'inbin mamaki mara misaltuwa.
ba'a ankara ba akaga Umma Karima tayi sama, kamar wacce aka janyota da kugiya.
Feeryal tayi baya da sauri dai dai san da Umma Karima ta b'ace a ka daina ganin ta.
da karfi Feeryal ta ce
"Ku matsa za'a sako ruwa kada ya jika ku."
tayi maganar idanunta a sama.
bata rufa baki ba ruwa ya zubo dai dai inda Umma Karima tayi ta zubar da jinin bakinta da take magana tana goga bakin a kasa.
a take kuma ruwan ya shanye kamar komai bai tab'a gun ba.
ido ta rumtse da karfi tana fad'in
"Wayyo suna dukanta."
ji tayi an damke hannunta da sauri ta bud'e idanunta ta waiga gefen da aka rike hannun nata.
suka had'a ido kai ya girgiza mata tare da mata alama da tayi shiru kada ta kuma magana.
fuska ta kwab'e tare da cuno lips d'in ta gaba, ta kuma d'aga kanta sama babu kowa sun b'acewa ganin ta.
baki ta kuma cunowa ta zame hannunta, ta matsa gefe.
shiko ya taka ya wuce side d'in sa.
tuni gurin ya kaure da hayaniya.
'ya'yan Umma Karima sai kuka musamman Nabila, da take jin kamar ta kashe kanta ta huta.
Sule direba ya sud'ad'a yana kokarin gudu security sukayi ram da shi suka soma dukansa.
Daddy ya ce su kyale shi ya d'auki 'yarsa su tafi.
Hajiya da tayi zaman dirshem a kasa ta ce
"Da kata Sule zo ka had'a da sauran duk ku tafi, dan ni ban yarda da sauran yaran ma na Abubakar bane, ashe duk shegu a ka tara a gidan shi yasa duk suka kasa auruwa, tattara su ku tafi Allah ya had'aka da musifa Sule munafuki maciyi amana, tattara shegun duk ku koma kasarku Niger."
Bappa Salihu ya ce
"Aa baza'ayi haka ba Hajiya Hanne, ai bata ce da wata bayan Nabila ba, ita d'in dai ya d'auki 'yarsa su tafi."
Nabila ta kuma fashewa da kuka.
Aunty ta girgiza kai tana share hawayen da suka zubo mata,
ina amfanin bad'i ba rai......!
Nabila mai ikirari da gadara da gidan uba, sai gashi tabar gidan babu tsuntsu babu tarko.
Sule direba yasata gaba cike da d'inbin kunya suka bar gidan,
tana kuka da waigen gidan tana ji tana gani tasa kafa tabar cikin daular data rayu cikinsa take d'agawa da kafafa da nuna ita wata ce,
da nuna gaskanci da kyara wa Feeryal da suke wa kallon ita ba kowa bace,
face tsintacciya mara galihu...
Mommy ta fashe da kuka ta zube bisa goiwawin ta na fad'in
"Hajiya Karima ta cuce ni, ta jima tana d'aurani a hanyar halaka, tana amfani da ni wajen cimma burin ta,
ban tab'a jin cewa wayo take min tana sarata ta kasa ba,
sai bayan data ingizani har na kaiga kashe jikoki na da hannuna."
ta rarrafo gaban Aunty da Feeryal tana cewa
"Hakika na aikata abubuwa masu yawa, wanda a yau nake jin kunyar tuna duk abun da na aikata,
dan girman Allah Hajiya Fatima kiyi hakuri ki yafe min abubuwan dana jima ina aikata miki,
wlh sharrin zuciya ce da zugar Hajiya Karima, ita take angiza ni wajen aikata komai,
ashe zurani take arami tana kokarin afka min kasa a ka,
wlh nayi nadama nayi dana sani, naji kunya matuka dan Allah kiyi hakuri ki yafe min dan nasan na cutar da ke."
Aunty ta girgiza kai tana cewa
"Wlh ni ban tab'a rike d'ayanku a zuciya ba, duk abun da kukayi min a gurin nake wasar da shi,
abu d'aya na kasa mancewa yaran da kika salwantar da su."
Aunty ta share kwalla tana cigaba da fad'in
"Naji mugun zafin rasa yarannan a lokacin da nake murna da farincikin samin su,
nake ji a raina nima yanzu nasamu nawa ta hanyar 'yata Feeryal,
sai dai ina dama ba masu rayuwa bane Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, Allah ya yafe mana baki d'aya."
Mommy ta sharb'e hanci tana rarrafowa gaban Feeryal ta had'e hannayen ta bibbiyu tana fad'in
"Bansan ta ya zanyi na roki gafarar ki ba,
abun da na sani dai na cutar da ke, na zalunceki zalunci mafi muni,
idan kinso zaki iya yafe min amma nasan ban cancanci yafiya a gare ki ba,
amma wlh shine Allah nayi nadama da danasani."
Mommy tafashe da kuka mai ban tausayi tana cigaba da fad'in
"Feeryal kiyi hakuri ki yafe min, idan baki yafe min ba nasan rayuwata bazatayi kyau ba."
ta rike kafafunta ta kifa fuskarta saman kafafunta tana wani irin gunjin kuka, da fad'in
"Ki yafe ni, ki yafe ni, ki yafe ni, Feeryal!."
Feeryal tayi saurin sunkuyawa ta dafa kafad'ar ta
tayi matukar jin nauyin ganin babba kamar Mommy a durkushe a gabanta tana niman yafiyan ta.
cikin yanayin ta mai sanyi ta ce
"Mommy ki tashi dan Allah."
"Feeryal bazan tashi ba har sai sanda kika so kika ya fe min."
cewar Mommy tana kuma kifa fuskarta jikin kafarta.
da sauri Feeryal ta ce
"Ni kam na yafe Mommy na yafe."
Mommy ta d'ago tana share hawaye had'i da yin murmushi.
ta ce "Nagode Allah da yasa kika d'auko zuciya irin na uwar da ra raine ki,
badun haka ba da ban san ina zan sa rayuwa ta ba."
ta mike ta zo gaban Daddy ta durkusa.
ta had'e hannu biyu tashiga ni man gafarar Daddy.
"Alhaji dan girma da darajar Allah, kayi hakuri ka yafe min duk abun da nayi maka, tun daga farkon zaman mu har kawo yau,
kayi hakuri ka yafe min dan Allah in sha Allah zan gyara zan zamo yadda kake so."
Daddy ya juya batare da ya ce komai ba ya nufi sashinsa.
Mommy ta share kwalla tana bin bayan sa da kallo.
kana ta rarrafo gaban Bappa Salihu kafin tayi magana, ya d'aga mata hannu ya ce
"Kije ki fara dai-dai ta sakanin ki da mijin ki da kuma d'anki,
wala Allah da yuwuwar na iya yafe miki."
Bappa Salihu shima ya juya yabar gurin.
tazo gurin Hajiya tana fad'in
"Dan Allah Hajiya ki tayani ki ce su yafe min,
wlh na tuba anyi walkiya anga kowa gaskiya ya bayya."
Hajiya ta sharb'e hanci sannan ta ce
"Zasu yafe miki Halima ai tun da aka gano gaskiya zance ya kare,
kije kiyi abun da babanki ya fad'a, je ki sami abokin turawa, sannan ki koma ki sami Abubakar."
Mommy ta juya ta nufi sashin Abdulrahim.
Duk 'yan gidan jikin su ya sanyaya musamman Ameerah da Farida data zo ana saka da lamarin, Sumayya ce ta kirata ta zo cikin gaggawa.
tana tsaye rungume da 'yarta jiki a sanyaye.
Ajmaal sai murmushi yake yana jin komai ya zo karshe,
Mommy'n su ta gane gaskiyar daya dad'e yana son ganar da ita.
Bilkisu Rahma Saddiqa sun kasa dai na kuka, sun rab'e gefe guda sun rasa madafa.
Aunty ta kalle su sanan ta girgiza kai, duniya ke nan me mai da akawu kuku,
yau ba uwar da zasu fake a jikin ta.
A hankali aka rika watsewa kowa yana cike da alhinin lamarin.
Bilkisu da Rahma da Saddiqa suka bi Hajiya sashinta, tamkar marayun da suka rasa uwa da uba.
A parkour'n sa Mommy ta iske shi, ta zube kasa tana niman yafiyar sa.
"Abdulrahim na kasance azzalumar uwa a gare ka, duk da haka bai hanaka yimin biyayya a matsayi na na mahaifiyarka ba,
ka yafe ni d'ana ka yafe ni,
wlh zugan Hajiya Karima ce da biyewa sharrin zuciya,
yakai ni ga aikata maka komai har ya kai ni ga kashe maka yayan ka, jikoki na na kashe da hannu na! kaico na hakika ni Halima nayi asara a rayuwa ta."
Mommy ta fashe da kuka tana rike hannun d'an nata.
ido ya lumshe ya bud'e sannan ya gyara zaman ya ce
"Shike nan Mommy."
kalmar daya furta ke nan a takaice.
Mommy ta dad'a kankame hannun sa tana fad'in
"Nagode nagode Feeryal ma tace ta yafe min."
ta mike ta fita da sauri.
Ta tafi gurin Daddy tayi ta niman yafiyar sa, da kyar ya ce ya yafe mata.
naga nan ta je gurin Bappa Salihu ta shaida masa kowa ya yafe mata, sanna shima ya yafe mata.
Tun daga ranar Ameerah ta kwantar da kai,
ta yada makaman rashin mutuncin ta.
ta dawo bin Miemie ta sami kofar shishigewa Feeryal.
Farida ma yanzu idan tazo gidan sai ta je sashin Aunty.
tayi ta kwantar da kai rashin mutunci an aje shi a gefe.
su Bilkisu kuwa suna nan rab'e a gefen Hajiya, Aunty mace mai dattako haka tarika jan su a jiki, tana sakar musu fuska, suna zuwa sashinta sosai suyi hira, kyauta kuwa sosai take yi musu, musamman take d'aukarsu su tafi shopping.
a kwan a tashi sai ga Aunty ta zame musu ginshiki fiye da uwar da ta haife su,
dan sabon tarbiyya take basu, wacce Umma Karima ta gaza basu.
cikin kankanin lokaci gidan ya dawo normal, irin gidan da ko wani magidanci yake fatar gidansa ta kasan ce.
sosai Mommy take jan Feeryal a jiki, duk da har yanzu Feeryal bata sake da ita ba,
Mommy
tana jin dama ace ta koma auren d'anta, sai dai tabar hakan a ranta dan batasan wazata tinkara da batun ba..
Kamar yadda Abdulrahim ya fad'a idan Zaraddin ya kai uzu sitti zai dawo da shi gida,
hakan ta kasance a ranar yaje ya d'auko sa ya dawo da shi gida.
anyi mamakin ganin su tare,
da ganin yadda Zaraddin ya zamo shiryayye a zahiri, domin kuwa farar jallabiya har kasa ne a jikinsa,
da hula a kansa, hannunsa kuwa rike da carbi, sai sunkuyar da kai kasa yake yana gaida kowa cikin girmamawa, da maganar sa daya koma irin na ustazai.
ko da Daddy ya tambaye sa in da ya samo shi, bai b'oye ba ya ce shi ya d'auke sa ya b'oye sa,
ya bashi horo ya kuma sa arika koyar da shi.
Bappa Salihu da ya sami labari ya kirasa a waya yayi ta sanya masa albarka, yana cewa
"Ko yau iyayan ku suka mutu kai zaka zame musu uba na gari."
Mom tana ganin Zaraddin ta mike cike da murna gami da kewar d'an nata ta rungume shi, tana fad'in
"Ina ka shiga Zaraddin ka sani shiga damuwa da tashin hankali, har na fara zaton saceka akayi."
murmushi yayi yana cewa
"Ba sace ni akayi ba Mom, Ya Abdulrahim ne ya d'auke ni ya kai ni can gidan gona, ya canza min rayuwa ta."
Mom ta turnike fuska tana cewa
"Wannan Abdulrahim d'in ba karamin d'an kutumar uba bane, ta kanta ya koma kuma."
cikin muryar sa daya mai da shi irin na uztazai da sauri ya ce
"Ya subhanallah astagfirullah astagfirullah, ya salam Mom Ya Abdulrahim ai mutumin kirki ne,
ya haska min hanya ya sani a saiti a lokacin da nake daf da b'ata gaba d'aya,
Mom a da sai na wuni banyi sallah ba, idan kuma zanyi bai fi nayi salloli biyu a rana ba,
sallar da ban ma san me zan karanta masa ba,
cikakkiyar fatiha idan aka tarke ni bazan iya kawo shi cikakkiya yadda addini