Showing 30001 words to 33000 words out of 86085 words
Chapter 11 - FEERYAL Part 3 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt
ta ce
"Shifa mugu ne bayi da imani kuma baya jin dan Allah."
murmushi sukayi mata kana suka sako mata wata hirar.
ko da Aunty ta shigo taga tana magana ita kad'ai fita tayi ta bata guri.
sai da sukaji an shiga sallar isha kafin suka tafi.
itama ta mike taje ta gabatar da sallah.
bayan tayi shafa'i da wuturi tayi addu'a kana ta mike ta nad'e sallayar tare da cire hijab d'in ta aje su. tana kokarin zama aka turo kofar ta d'ago tana fad'in
"Ammie.."
da sauri ta had'iye abun da take shirin fad'a ganin shi ne, tayi baya da sauri tana binsa da kallon tsoro.
ya tako a hankali har zuwa gaban ta, kana ya mika hannu ya janyo ta jikin sa.
idanunsa dake rikitata ya zuba mata yana rike da ita batare da ya saketa ba,
ya kai d'aya hannun sa kan goshinta ya gangara zuwa wuyan ta.
zafin jikin ya sauka sosai.
ya cire hannunsa a wuyanta ya zura cikin aljuhunsa, dad'a mannata ya yi da jikinsa, kana yayi kasa da hannunsa ya kamo kasan rigarta ya yi sama da shi.
da sauri tayi kokarin janye jikinta kirjinta na bugawa, ya dad'a mannata da kyau a jikinsa ya zagaye ta da hannayen sa, sannan ya d'an ja wandon jikinta ya soka mata allurar.
kara ta kwalla tare da kankameshi tana cusa fuskanta cikin kirjinsa.
bata sammaci allurar ba dan bata ko gani a hannunsa ba.
Aunty ta sako kai da sauri cikin d'akin jiyo ihun ta, ganin sa rungume da ita, ta juya da sauri tayi baya bata bari ya ganta ba, sam bata san da shigowar sa ba.
a hankali ya zare allurar yana mulmula gurin.
lamo tayi a jikinsa tana jan sheshsheka hawaye na gangara, tana jiyo bugun zuciyarsa da sauri-sauri. a hankali take shakar kamshin dake fita da kirjinsa,
gyara kanta tayi tana dad'a manna fuskarta da kirjinsa.
tana jin wani d'umi yana rasata har tana lumshe idanu tana jin wani bacci nason d'aukarta.
kamar an zabure ta ta zare jikinta ta matsa gefe tana kwab'e fuska da cuno kyakkyawan lips d'in ta gaba.
bayan hannunta ta kai ta na share hawayen fuskanta, tana mai dad'a cuno baki gaba,
tana kuma jan shashsheka.
a sannu ya juya yafice a d'akin,
ta zube bakin gado tana jin wani sanyi na shigarta, da sauri ta kwanta taja bargo ta rufe jikinta.
Bayan fitarsa Aunty ta shigo idanunta a lumshe bacci na son d'aukar ta.
ta bud'e lumsassun idanunta tana wani kwab'e fuska kamar zatayi kuka ta ke fad'in
"Ammie kice ya daina min allura bana so akwai zafi."
Aunty tayi murmushi tare da shafa kanta ta ce
"In ban da abinki 'yammatan Ammie ai sauki ake son sama miki, ke ya kika ji karfin jikin ki, na yanzu da d'azu kafin ayi miki na farko, kiyi hakuri in kika sami sauki ai baza'a miki ba, ana yi ne don lafiyar ki."
"Ammie akwai zafi fa."
ta fad'a murya a shagwab'e.
Aunty ta kuma shafa kanta ta ce
"Ai zafi shi ke cire zafi, idan kin warke shike nan, ke dai ki daure."
lumshe idanun takuma yi da take jin su suna shirin rufewa da kansu, allurar yafara tasiri a jikinta.
ai kuwa take bacci ya d'auke ta.
Aunty ta fice ta ja mata kofar bayan ta tofe ta da addu'o'i.
Kwana uku ya d'auka yake shigowa yi mata allura sau biyu a rana.
duk sanda yazo da kuka ake karewa, idan ya shammaceta sai dai taji shigar allura jikinta, idan kuma ta ankare haka zai matseta sai ya mata.
sannan ya saketa yayi tafiyarsa.
zuwa lokacin jikin ta ya warware sosai.
tun da yayi kwanaki uku yana shigowa yi mata allura kuwa bai kara shigowa ba.
har ta cika sati guda a sashin Aunty.
a ranar da ta cika satin ya shigo da daddare, suna tare da Aunty, fitowarta daga wanka kenan, tana zaune a kan gado d'aure da towel,
tana cin cake d'in da Aunty ta kawo mata.
Aunty na ganin sa ta mike ta fita bayan ta amsa gaisuwar da ya mata, kansa a kasa.
Feeryal ko fuska ta kwab'e tana kokarin zamowa bakin gado tagudu taji ya ruko hannunta.
ya maida ita.
murya na rawa ta ce
"Ni bana so kar kayi min allura."
"Ki natsu na gani idan ba haka ba allurai goma zan baki yanzu."
yayi maganar yana gimtse fuska.
yana tsaye daga bakin gadon ya turata ta kwanta da baya.
kana ya sa hannu guda yad'an danna ta ta inda bazata iya tashi ba, d'aya hannunsa kuma ya kamo kasan towel d'in jikinta yayi sama da shi.
wani irin zabura tayi, da sauri ya kuma danneta yana fad'in
"Wait, don't argue with me."
ido ta waro da karfi ta rirrike hannunsa tana fad'in.
"Aa Sahab dan Allah karka yi min wayyo Ammieee."
ta karasa da kiran Aunty da karfi.
yatsa ya d'aura kan lips d'in sa tare gimtse fuska sosai murya ba wasa ya furta
"Shut up Stupid!."
hannu takai ta to she bakin ta jikinta na rawa ta rumtse idanunta da karfi tana jin yadda yadad'a rirriketa yake ware kafafunta.
ya kunna flash d'in wayarsa ya haska hole d'in ta.
d'inkin yayi kyau saura kad'an gurin yagama warkewa.
da sauri ya janye idanunsa da yake jin suna wani irin fisga numfashin sa yana fita da sauri-sauri.
ya ja towel d'in ya rufe gurin. kana ya juya ya fice da sauri.
tana jin fitarsa ta juya takifa fuskarta jikin katifa takasa iya bud'e idanunta bare ta mike......!
Tun da yazo yaga d'inkin bai kara zuwa ba.
ranar da ta cika kwanan goma Daddy ya umurci Aunty ta mai da ita d'akin ta.
tun da Feeryal ta sami labari hankalin ta ya tashi.
tayi ta kuka tana fad'in ita bazata koma ba.
Aunty ta sata gaba tayi ta rarrashi.
da misalin karfe 8 na dare Aunty ta sako ta gaba bayan ta sha fama da rarrashi.
ta kaita har d'akin ta, da kyar Aunty ta zame jiki ta koma nata sashin, dan kuka Feeryal ta saka mata, shigowar su bedroom d'in ta.
gaba d'aya d'akin mugun tsoro ya bata,
dan nan take ta tuna da irin azabar da ta sha a cikin sa.
ta rab'e bakin gado ta rakub'e guri guda, ta rumtse idanunta da karfi bata son ta rika tunawa da abun da ya faru.
Motar Abdulrahim ne yayi hon a babban get d'in gidan.
security suka bud'e masa, yana sako hancin motar ciki kiran Mommy na shigowa wayarsa.
dan haka a babban parking lot d'in gidan ya paka motar ya fito ya nufi sashin ta.
yana shiga ko zama bata bari yayi ba, ta rufe shi da bala'i
"Nayima zuru na zuba ma ido naga gudun ruwan ka kai bakasan zuru ba ko,
tome kake jira har yanzu baka saki yarinyar can ba,
an mai da maka ita yau sabo da har yanzu burinsu bai cika ba,
an maida ita ta karasa aikin da bata kammala ba,
bokan su ya basu sa'a, sai sun ga bayanka kafin su hakura,
to ni ce nan na haife ka,
wato ni ban isa da kai ba ban isa nace ma ga abun da yakamata kayi ba,
uban ka ne kad'ai ya isa ya saka ya hanaka, ni uwar data rike cikin ka tsowon wantinni tara, nayi fad'i tashi babu kalar wahalar da ban sha a rike cikinka zuwa haihuwar ka da rainon ka har ka mallaki hankalin kanka ba,
amma ni ce na zamo banza ban isa na tsarama rayuwar da ta kamata da kai ba, sai ka bijere min,
sabo da ban isa da kai ba, na haifawa Hajiya Fatima da mayyar aljanar ruwa kai,
wato duk abun da na fad'a ma kan yarinyar nan baka ji ba sai da ka kusance ta,
wani jaraba ne zai kai ka ga wannan yarinyar?, to wlh ina mai tabbatar maka ni banshirya had'a jini da aljanu ba, tun da jarabarta ya kamaka tun marmaza kaje ka yi mata implant wlh bazaka tab'a had'a jini da ita ba,
sai nabi ta inda Hajiya Fatima ta bi na karya duk asirin da ta maka, bazata mallake ubanka ta mallakeka ba, ban haifa mata kai ba wlh,
tun marmaza kaje ka mata implant,
idan kuma bakayi abun da nace ba to ban yafe ba duniya da lahira."
yana tsaye ya kalmashe hannu a kirji, bai furta ko kalma d'aya ba,
ganin ta gama maganar ta yajuya ya fita.
yana jiyo ta tana kuma fad'in
"Ni dai na gaya maka idan bakayi abun da nace ba, Allah ya isa ban yafe ba,
yanzu kaje kayi mata idan ka bari gari ya waye ma ban yafe ba, kaji na gaya maka ke nan."
Yana shiga Bedroom d'in sa ya rage kayan jikin sa, ya shige bathroom yayi wanka yafito ya saka gajeren wando da singlet ya haye gado.
ya janyo laptop nasa.
11 ya rufe laptop d'in yayi addu'a ya kwanta.
idanunsa a lumshe maganganun Mommy suka shiga amo cikin kwakwalwa da kunnuwan sa.
gefen lips d'in sa ya taune, kana ya mike zaune ya zamo bakin gadon, yaja drowa yad'an bincika yad'au abun da yake bukata ya fito ya nufi gefen ta.
a hankali ya turo kofar, tana rakub'e a haka bacci ya d'auke ta.
a sannu ya tako cikin d'akin, ya iso bakin gadon.
ido ya d'an zuba mata idanunta a lumshe tana sauke numfashi a hankali, sai dai da kaga baccin zakasan a cikin tsoro tayi shi.
tsayuwar sa ya gyara sannun ya d'an rankwafo kanta, yad'an jan rigarta batare da yaja wandon baccin jikin ta kasa ba ya nitsa allurar dake rike a hannunsa ta saman wandon ta.
wani irin zabura tayi yayi saurin matse suwan allurar a jikin ta kana ya zare.
hannu takai ta dafe gefen mazaunnan ta tana ja da baya tare da binsa da kallon tsoro,
da kyawawan idanunta da suka cika tab da kwalla har suna walkiya.
idanunsa a kanta gaba d'aya ta daburce sai yarfe hannu take, d'aya hannunta kuma na dafe da inda ya mata allurar.
kai ya d'auke yana mai gimtse fuska, kana ya juya ya fice a dakin.
yana fita ta mike da sauri ta duro a gadon wani irin jiri me kamada bacci taji ya d'ibeta,
ba shiri ta koma ta zube kan gado kafafunta yana rito a kasa, a take idanunta ya rufe bacci ya yi gaba da ita.
20min da faruwan haka ya shigo.
ya gyara mata kwanciyarta kana ya zauna bakin gadon, yaja hannun rigarta zuwa can saman kafad'ar ta, sannan ya mata allura a in da ya dace daya sa mata implant d'in, mintuna kalilan ya d'auke sa ya saka mata sannan ya kwashi abubuwan da yayi amfani da su ya fita yaja mata kofar.
Daddy da Abbie da Dad ne zau ne a parlour Hajiya.
Daddy na rike da waya a kunnen sa yana magana
"Kun bincika ko wani club da hotel baya can?."
daga cikin wayar akace
"Allah ya taimaka babu hotel da club d'in da babu bincika ba a garinnan baya nan, amma mun dad'a fad'ad'a bincike dan mu gano ko ya sallaka ne yafita a garinnan ko wajen kasar nan, a bamu daga nan zuwa fad'uwar rana zamu gano inda yake."
Daddy ya jinjina kai yana kashe wayar.
Hajiya data zuba masa ido tana son taji shin an ga Zaraddin d'in ne ta ce
"An gano in da yaje?."
Daddy ya ce
"Aa ana dai kan bincike."
Hajiya ta ce
"Yanzu shi wannan yaro Zaraddin ya kyauta wa kansa ke nan, yatafi mil ya b'ata shiru babu waiwayan gida, ba gara shima ayi masa auren ba kawai a huta, amma ace yatafi kwana da kwanaki, baka tunanin ma kana da iyaye wani hali zasu shiga idan suka nemeka suka rasa, yaran yanzu da rashin tausayin iyaye yayi musu katutu, 'ya'yan da dako layi aka zana aka ce kada ka ketare baka isa ka ketare ba,
Shamsuddin ya gaya min wai har giya ya fara sha,
a cikin gidan nan ace wai an sami mashayin giya,
wani irin musifa ce wannan iye, duk ya gama karad'e gari da shaye-shaye da biye-biyen matan banza, ana samo shi ku had'ashi aure da Saddiqa, itama ranar Bilkisu take fad'a min wani yana zuwa d'aukar ta, to kafin su cigaba da shafa wa gidan nan bakin fenti gara a had'a su aure kawai a huta."
Dad ya ce "Wlh Hajiya narasa yadda zanyi da yaron nan, duk abun da zan fad'a masa bashi zai sa yaji ba, so yake mu yafe shi mu kore shi cikin 'ya'yan mu."
da sauri Daddy ya ce
"Korin shi a jikin mu bashi ne samun maslaha ba, tamkar mun bashi tiket na dad'a gurb'acewa ne, mu jashi a ajiki mu nuna masa abinda yake yi ba dai-dai bane, Allah zai taimake mu ya shirya mana su,
abun da Hajiya ta ce shine kawai za'ayi, idan ya dawo za'a d'aura musu aure da Saddiqa insha'allah hakan zai zamo silar shiryuwan su duka."
Abbieh ya jinjina kai ya ce
"Haka ne dama duk musulmi mai imani, Allah sai ya jarafcesa, ta hanyar dukiya ko 'ya'ya ko mata ko lafiyar sa,
wannan jarabawar mu ce Allah ya bamu ikon cin jarabawa, ya shiryar mana zuri'a baki d'aya."
duk suka amsa da amin amin.
taro ya watse Dad ya nufi gefen sa, yana sakar zuci, ga dukkan alamu dai zuciyarsa abu biyu take karonto masa yarda da had'a auren, dakuma son bijirewa yana tunanin kada had'in ya ruguje masa shirinsa.
Ko da ya sanarwa Mom abun da ke faruwa, Mom tayi tsalle ta dire ta ce
wlh ba dai a had'a Zaraddin da 'yar da aka zubar wa ciki ba.
labari ya isarwa Umma Karima ta niko garin ta tayiyo sashin Mom.
yau anga Mom da Umma Karima a rana dan kuwa fad'a sukayi har da fad'e-fad'e da tone-tone da yiwa juna gori.
Hajiya kuwa ta ce in zasu kashe kansu Zaraddin na dawowa za'a d'aura mishi aure Saddiqa.
Tun da Feeryal ta dawo Aunty ke turo musu da abinci, wajen satin ta guda kenan da dawowa.
bata sashi a idanunta ba, tun a ranar da ta dawo ya shigo ya yi mata allura.
tana daga cikin bedroom wani sa'in zata jiyo motsin sa ya shigo d'ibar abinci da Sudan tea d'in sa.
hakan kuwa ya mata dad'i har ta d'an saki jikinta, kullum tana tare da kawayen ta Chuchu da Chulu.
Miemie ma tana shigowa jifa-jifa.
Feeryal na d'aki tajiyo muryar Miemie da gudu ta fito ta rungume ta tana fad'in
"Oyoyo Miemie shine ina jiya baki zo ba."
ta janye tana tura baki.
Miemie ta zauna kan kujera tana harar Feeryal da fad'in
"Ko yaushe zaki fahimci ke ma mata ce oho,
gata can wancan matar tasa naganta tafito yi masa rakiya zai fita, sai wani mannuwa da shi take, ke kuma gaki nan sai dai ki shiga ki kulle kanki a d'aki,
bazaki tsaya ki kula da mijin ki kinuna masa soyayya ba, kin fita komai da komai kin tsaya wasa, sai kin zamo 'yar kallo ai."
baki Feeryal ta tab'e ta zauna kan hanun kujera ta ce
"To ni na ce miki ina son yayan ku ne bare ma ya dame ni, kinga ita da take son sa ai ta damu da shi."
"Ai wlh kinyi asara Feeryal, ke har zakice bakya son Ya Abdulrahim ai Ya Abdulrahim abun so ne,
in ni ce na sami miji kamar Ya Abdurrahim na rantse rigimar da zanyi ma bazai fad'u ba, itama da take kinibibin ai dan tasan wani irin miji take aure,
Murad d'ina ma kenan da bai kai ko kwatan Ya Abdurrahim ba nake tattalashi bare kuma had'ad'd'en miji irin mijin ki,
in nice da miji kamar Ya Abdurrahim na rantse za'a sha kallo."
Feeryal dai baki tab'e tana cewa
"Ni Miemie ba wannan ba so nake kirakani gyaran gashi gobe."
Miemie ta waro ido ta ce
"Wa ni rufa min asiri kisa mijin ki ya kai ki, in kuma baki san yadda zakiyi ki tarairaye shi ya kai ki ba sai kiyi ta zama."
baki Feeryal ta rike ta ce
"Shine zai kai ni?."
"Ke ai bansan yaushe zaki shigo birni ba, Allah ya ganar min da ke."
dariya Feeryal tayi ta ce
"Da a kauye nake?."
"Kusan hakan ai."
cewar Miemie tana hararar ta, ta mike tana fad'in
"Ni na tafi ma, bazan sake zuwa ba idan baki gyara kinsan ke matar Dr AA FIYA bace."
ita dai da murmushi ta bita...
Tun da aka maida Feeryal d'akin ta Umma Karima bata zauna ba, tana ta kai kawo a gurin bokanta, har yau da Feeryal ta cika watanni biyu da dawowa.
hakan kuwa yayi dai-dai da lokacin tafiya umura,
masu niyya duk an tafi ciki kuwa harda Daddy.
bayan tafiyar Daddy da kwana biyu,
Umma Karima tayi sammakon tafiya gurin bokan ta.
koda ta dawo sashin Mommy ta zarce.
ganin yadda ta fad'o parlour'n Mommy ta mike zumbur tana fad'in
"Yaya dai Hajiya Karima lafiya?."
kirji ta buga ta ce
"Ina ko lafiya gurin wani malami na fito yanzun nan, yagaya min wani magana mai tada hankali, wlh Hajiya Halima idan baki farka daga nannauyar baccin nan da kike ba, ana daf da shafe ki ke da d'an ki, ya ce kwana biyu ya rage wa d'anki a gama da shi har abada, san nan a waiwayo kanki, ni dai na isar da sako na, zab'i ya rage naki, idan kin so ki barsu su ga bayan shi sannan su juyo kanki, kwana biyu ya rage muku."
Mommy ta ce
"Tabd'i jam! Hajiya Fatima kinyi kad'an yanzu zan nuna miki ni na haifi Abdulrahim."
ta juya fuuu sai sashin Abdulrahim, kai tsaye gefen Feeryal tawuce tun kan ta karaso ciki ta ke fad'in
"Ina kike fito nan aljanar ruwa, aje a kare rayuwa a in da aka fito,
d'ana yafi karfin ki narantse da Allah yau sai kin bar sashin nan, yau zama da d'ana ya kare miki."
Mommy ta karaso ta bubbuga kofar bedroom d'in ta da karfi tana fad'in
"Fito munafuka yau karshen makircin ku ya zo, sai dai kibi wani sarkin ba dai d'anaba wlh."
Feeryal jiki na rawa ta fito.
Mommy ta bita da kallon banza ta ce
"Tattara inaki-inaki yau bazaki sake kwanan sashin nan ba, munafukar Allah ta'ala yau kulle-kullen ku ya kare yau zakibar sashin nan."
Abdulrahim da ke kokarin shigowa gefen nata cikin shirin tafiya asibiti, yajiyo muryar Mommy yana karasowa Mommy ta juyo kansa
"Yauwa dama daga nan gurin ka zanyi, na rantse maka da Allah yau yarinyar nan bazata kara kwana sashin nan ba sai ka saketa."
Mommy ta gyara tsayuwar ta da kyau sannan ta ce
"Abdulrahim!."
ta kira sunan sa cikin kakkausar murya.
ya d'ago ya kalleta, ta ce
"Yanzu yanzun nan umurni nake baka bana so ka kara minti biyu ka rubuta mata takardan saki yanzu ka bata!
Abdulrahim na ce ka saketa ko na tsine maka!!."."
kasa yayi da kansa yana damke side bag d'in system nashi dake sakale a bayan sa gefen kafad'ar sa.
rumtse idanunsa yayi da karfi jin kalamar Mommy na karshe yana shirin tarwasa kwakwalwarsa.
"Zaka saketa ne ko sai na sine maka!."
Mommy ta kuma jifansa