Showing 15001 words to 18000 words out of 86085 words
Chapter 6 - FEERYAL Part 3 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt
cikin kyakkyawan kula mai matukar kyau da tsada wanda ta ciro daga cikin kwalinsa.
ta jera kulolin kan wani tray na musamman.
har zata d'au tray'n ta fito ta tuna da Ammie'n ta bata girki batare da ta had'a da abin sha ba.
cikin mintuna kalilan ta had'a lafiyayyen lemun abarba da apple, ta juye cikin had'ad'd'en cup ta jefa kankara, ta d'aura kan tray'n ta d'auko tafito.
ta kaishi dinning.
tayi mamakin ganin an d'ibi girkin da tayi d'azu komai sai da aka d'iba aka bar saura,
flask d'in Sudan tea d'in kamma baya gurin.
batayi zaton zai zo ya d'iba ko zai san ita tayi ba Aunty ba...
ta d'au kwanukan safen ta kaisu kitchen ta wanke, ta gyara kitchen d'in tafito.
ta koma d'aki tayi wanka ta kwanta.
bata farkaba sai bayan la'asar.
yamma lis ta koma kitchen karfe 7 da 'yan mintuna tagama girkin dare, ta kwasa ta kaisa dinning.
sannan ta koma ciki, sai da tayi sallar isha kafin ta shiga wanka...
"Deen kabar kanka ya huta mana, 8 days kana narkawa kanka kwayoyi da barasa,
tun da anfi karfinka bakasamu lu'ulu'un nan ba, ka hakura mana, ka fantama cikin gari da wajen kasarnan zaka sami kamar ta ko wacce ta fita ma,
mttss naso ace kai ka auri yarinyar nan ka bani aron ta na more kayan alatu,
amma brother naku ya yi tsawon kafa ya yi gola ya tsare,
wannan ba karamin kaya yake d'iba ba."
Zaraddin ya janyo kwalbar giya, ya kafa a bakin sa sai da ya sha rabi kafin ya d'aga kwalbar ya yi wurgi da shi sakiyar parlour'n Ziyad kwalbar ta tarwatse.
ya shiga dukan table d'in gabansu yana fad'in
"Bazan bar masa ita ba! dole ya sake ta na aure ta!."
ya mike zumbur yana cigaba da fad'in
"Abdulrahim dole naji abin da kake ji a jikinta, yazama dole kuma kasake ta na aure ta."
ya d'aga kafa yana kokarin fita Ziyad ya taro sa yana cewa
"Deen me zakayi kabi ko mai a hankali fa, dan wannan Dr d'an zafin kai ne kar aje a sami matsala."
cikin hargagi da ihu ya ce
"Yau nine zan kwana da ita ba shi ba, daga nan zuwa gobe kuma idan bai saketa ba, sai na kashe shi na aure ta."
da sauri Ziyad ya rike hannunsa ya ce
"Deen ka dakata, kajira ka sauka a network kayi tunanin hanyar da zakabi wajen d'aukar wannan mataki, kaga yanzu a shaye kake, wannan lamari ba irin sauran da muka saba tinkara bane, katsaya kwakwalwar ka tagama caji, nima ina goyon bayan yasaketa mu samu, idan kuma ba haka ba mu sace ta."
hannunsa ya fizge yajuya da karfi yayi waje yana fad'in,
"Bazan bari sai gobe ba yau zan aiwatar da komai." yashiga motarsa da gudu yabar gidan, ya nufi AA FIYA STREET.
Ana idar da sallar isha yana isowa gidan a babban parking lot yayi parking.
ya zauna cikin motar bai fito ba, idanunsa a hanyanyar wucewa yana kallon matasan gidan da suka fito daga masallaci suka wuce side d'in su.
yakai minti 10 a zaune kafin yaga shigowar Abdulrahim.
sai da yakusa da side d'in sa kafin yafito a motar
a hankali yake tafiya yana d'an waige-waige, yana ganin shigewar sa dide d'in ya d'aga kafa da sauri.
yana isa bakin get d'in side d'in.
yatura karamar kofa,
mai gadi nazaune ya yi saurin mikewa, ganin d'an gida ne sai ya koma ya zauna, dan zaton shi tare suke da Abdulrahim d'in ganin yanzu shigowarsa.
ya ce
"Yallab'oi ya wuce gefen sa."
kai Zaraddin ya jinjina kana
yasa kai yanufi gefen Feeryal yana d'an waige-waige.
sai da ya iso bakin kofar gefen nata yaja ya tsaya.
yakuma waigawa, yaga mai gadi ma sha'anin sa yake, hankalin sa nata wani gurin.
ya kai hannu kan handle duk da bai sammace kofar a bud'e take ba, sai ko yajita a bud'e.
ai ko da sauri ya murd'a handle d'in yasa kai cikin hanzari ya shige.
yana shiga ya maida kofar ya rufe tare da murza key.
tsayuwa ya yi yana kalle-kalle, sai kuma da dauri ya nufi cikin parlour'n, yabud'e kofofin bedroom's guda biyu bai ganta ciki ba, ya juya da sauri ya nufi kofar da take ciki.
Tana tsaye gaban wardrobe fitowarta daga wanka ke nan.
towel ne kad'ai d'aure a kirjin ta, babu ko d'ankwali a kanta.
da sauri ta waiga a kuma razane jin an bud'o kofar da karfi.
ganin wanda ya shigo d'akin da yanayin yadda ya fad'o d'akin nata, tashiga mamaki kwarai da gaske.
murmushin karfin hali ta sake,
da sauri ta mika hannu tana kokarin janyo hijabi, tare da fad'in
"Ya Zaraddin kai ne inayini."
wani irin mayataccen kallo yake binta da shi yasoma takowa yana fad'in
"No no no! basai kinyi wahalar rufa wannan kyakkyawar jikin ba, yau kwana zanyi ina kallon sa."
a razane ta dube shi, ganin yana dumfarota gadan-gadan, tashiga ja da baya tana cewa
"Me kake fad'a ne Ya Zaraddin?."
bata kai ga rufa baki ba taji ya damko hannunta, wani irin sauti yaja
"Ahhh hannu kawai da irin wannan laushin, ina kuma dana lume cikin wannan kyakkyawa had'add'en jikin, baki gane yaren ba ne, shi wancan da kike kwana da shi bafa wani abu yafini ba,
yau zaki gane ni jarumi ne sai kin raina jarumtar sa."
wani irin bala'in tsoro ne ya kamata, da iya karfinta tayi kokarin kwatar hannunta.
sai ji tayi ya rungumo ta.
kara mai karfi ta sake
a take wutan side d'in ya d'auke gaba d'aya.
tsaoro mai tsananin ya kuma lullub'e ta, tashiga ihu da musu-musun kwatar kanta.
Da karfi aka banko kofar ji kake kyass! karan yanka wani irin gigitaccen kara Zaraddin ya sake ba shiri ya sake ta.
tayi baya a tsorace, duk da bata ganin abun da yake faruwa d'akin duhu sai hasken screen d'in waya da mai ita ya shigo, wanda bazata ce ko waye ba, tsoron da ya shige ta yanzu ya girmi na farko.
jin ta shige lungun wardrobe tadad'a makalewa tana b'ari.
Wani irin duka yashiga yiwa Zaraddin kamar zai rabashi da ransa.
tun yana ihu har ya dawo yin wani irin gurnani.
Feeryal ta kankame idanunta gam-gam a cikin duhu jikinta na kakkarwa, tana kuka da kiran sunan Ammie'n ta.
Janyo sa ya yi yafita da shi a d'akin, bai fasa bugun sa ba har ya fita da shi, daga gefen nata gaba d'aya.
ya yi parking lot da shi ya bud'e bot ya turashi ciki sannan ya rufe.
yajuyo yana huci, mai gadi ya karaso gurin da 'yar tocilan sa da sauri yana fad'in
"Yallab'oi haka kawai wutan ta d'auke, nayi iya kokarin gyarawa yaki."
baiyi magana ba ya soma tafiya, ya shige gefen sa yana shiga wutar ta kawo.
Wuta na kawo wa Feeryal ta kuma wani irin zamura ta mike, jiki na rawa.
a matukar razane takuma yin baya ta garu da jikin garu, jiki na kyarma.
ganin jini malale a kasan d'akin, ga kuma wuka a gefe.
takai hannu da karfi ta toshe bakin ta, nan da nan taji kanta na juya mata, a hankali ta sulale kasa, bata kuma sanin abunda yake faruwa ba...
Da sauri ya fito ga yadda yake taka kasa zaka fahimci tsagwaran b'acin rai tare da shi.
ya isa parking lot ya yi wa motar key, da sauri mai gadi ya bud'e masa get yafita.
tun kafin ya kara babban get yake hon,
a guje security suka wangale masa get, ya fice da mugun gudu.
Can gidan gona ya nufa yana isa ya bud'e yafito, yazo ta bayan bot ya bud'e ya janyo shi ya fado kasa.
ihun wahala yayi can kasan wuya, ko kansa baya iya d'agawa, sai juya fuskarsa yake akasa.
su Jaq da Tag suka karaso da sauri suka ciccib'eshi suka shi ga da shi ciki.
suna shiga suka sake shi kasa.
Abdulrahim ya sunkuya a gabansa fuska a shinfid'e da tsagwaran b'acin rai.
hannu ya mika musu tare da fad'in
"Kawo kayan d'inki."
da sauri Jaq ya je ya had'o kayan aiki ya miko masa.
wasu lafiyayyun maruka biyu ya d'auke sa da shi,
cikin kakkausan murya mai nuni da zallan b'acin rai, ya ce
"Zan jinyataka kafin nayi maka hukunci dai-dai da laifin da ka aikata!
kar ka d'auki wannan a matsayin hukinci zanyi ma hukunci bayan ka warke."
ya mirgina sa ta baya yankan da ya yi masa a baya sai fidda jini yake, yankan ya shiga kuma ya yi girma.
yasa hannu yakara yaga rigarsa ya masa allurar tsaida jini, dan tun a gida jinin yake zuba har kuma yanzu.
nan ya soma kokarin dinke gurin daya yanka shi.
Zaraddin sai juya kai yake ba bakin magana.
Ya b'ata lokaci wajen yi masa d'inkin, kafin yagama.
yana gamawa yasa su d'aga shi su shiga dashi cikin wani d'aki mai duhu, bayan ya yi masa duk abin da yakamata.
kana ya fito yashiga motar sa ya juya gida......!
Koda ya isa gida gefen sa ya shige, yarage kayan jikin sa, yabar gajeren wando da singilet.
har yakai kofar bathroom sai kuma yaja ya tsaya, gajeren tsaki yaja kana ya juya yafita ya nufi gefen ta. yana shiga ya tsaya daga a bakin kofar bedroom d'in.
ganin in da d'akin yayi kaca-kaca da jini.
idanunsa ya sauka a kanta, tana kwance a kasa, kusan rabin jikin ta a bud'e yake dan towel d'in daga kasa ya bud'e amma ba duka ba, yanayin fad'uwar da tayi shi ya baiwa towel d'in damar bud'ewa ya zamo ta gefen cinyarta.
daga sama kuma ya kunce sai dai bai zame daga kirjin ta ba.
bata ko motsi da alama dai suma tayi.
gefe yabi yataka ya isa in da take.
ya sunkuya ya mika hannu ya ciccib'ota.
a hankali ya had'a ta da kirjinsa.
wani irin harbawa zuciyar sa tayi, ba shiri ya rumtse idanunsa da karfi, sai kuma a sannu ya bud'e su a kan fuskarta.
a hankali ya soma d'aga kafarsa idanunsa a kan fuskarta bai janye ba, har ya tako bakin gado.
ya sauke ta a hankali ya kawar da kansa gefe tare da mika hannu ya gyara towel d'in yadad'a rufe mata jikin ta.
ya share jinin ya goge gurin tass kamar komai bai faruba.
Ya na gamawa ya d'au wukan ya fita.
Jim kad'an ya dawo rike da allura daya rigada ya ja a sirinji.
ya tako bakin gado allurar ya d'ago tare da cire murfin Kansa, d'an tsayuwa ya yi kamar mai nazarin wani abu.
gajeren tsaki yaja yakai hannu ta kasan towel d'in yarike sai kuma ya sake, tare da furzar da fuci daga bakin sa.
ya juya da sauri har yakai bakin kofa yakuma juyowa,
yadawo bakin gadon.
ya janyo bargo ya rufe ta daga kafafunta zuwa kugun ta.
sannan yajanyo towel d'in ya zaro shi daga cikin blanket d'in, ya d'an zamo bargon kasa kad'an dai-dai in da zai mata allurar yana luma allurar da sauri ya d'auke kai.
Ajiyan zuciya ta sauke sanda allurar ya shige ta, a hankali yake matsa ruwan allurar a jikin ta.
zabura tayi dai-dai san da ya zaro shi, ya d'au cup da yagani kan bedside da ruwa a ciki ya tsiyaya a tafin hannunsa ya wasa mata a fuska.
dogon numfashi ta sauke,
ta kuma zabura tare da ware idanunta, suka sauka kanshi.
cikin harhad'a kalmomi ta ce
"Kar..kar...kayimin allura."
tana fad'in haka jikin ta ya sake gaba d'aya bacci ya d'auketa cikin yanayin da take ciki.
ya juya da sauri yabar d'akin.
Sanyin asuba ne ya farkar da ita tayi mika gami da salati a hankali ta mike zaune tana mussike idanunta.
a sannu ta zamo bakin gado.
ta na saka kafafunta kasa ta tuna da kamar wani abu ya faru.
da sauri ta ware idanunta tana rarraba ido cikin d'akin,
d'akin fess babu komai. shiru tayi tana juya abun cikin ranta.
tabbas wani abu ya faru taga Zaraddin ya shigo d'akin nan, har yayi mata maganganu, daga nan kuma wuta ya d'auke wani ya shigo, taji ihun Zaraddin takuma ji alamun ana dukan sa.
daga baya wuta ya kawo taga jini a d'akin.
tana ta son tuna abun da ya faru bayan nan, amma duk iya tunanin ta nan ya tsaya.
ido ta dad'a warowa cikin d'akin babu jini hasali ma fess ya ke.
kai ta girgiza a fili ta furta
"Ko mafarki ne?."
sai kuma ta kwab'e fuska
"Mafarki ne ma me zai kawo Ya Zaraddin nan."
takuma fad'a
tare da kallon jikinta towel d'in dai data d'aura jiya ne bayan tayi wanka, ke nan bacci ne ya d'auke ta ke nan har ganin da ta wa Sahab ma a d'akin nan da allura a hannunsa duk mafarki ne?.
takuma kwab'e fuska, mafarkin sam baiyi mata dad'i ba.
ta mike a hankali ta shige bathroom.
sai da ta yi wanka da ruwa mai zafi dan tana jin jikin nata yana yi mata nauyi.
ta d'auro al'wala ta fito, ta saka kaya sannan ta haye sallaya ta tada sallah.
bayan ta idar tayi azqar, ta kuma kwanciya.
Karar ringing d'in waya ne yata da ita daga baccin da take.
a hankali ta mike zaune tana waige-waigen ta in da sautin ke tashi.
ta janyo wayarta tana mamakin ta yadda akayi sautin wayar nata ya koma haka.
da sauri ta waiga ta gefen da ta ji sautin na tashi.
ta zamo bakin gado ta sunkuya ta in da take jiyo sautin.
wayar ta gani a ta d'an karkashin gado, ta d'auko tana juya shi a hannunta da mamakin me yakawo waya nan.
kiran na yanke wa fuskar wayan ya bayyana, da mamaki take kallon hoton da yake fuskar wayan, yana zaune turawa sun sashi a tsakiya, dukkanin su da shigan likitoti.
fuskarsa d'auke da kyakkyawan murmushi mai burgewa.
mamaki yakuma kamata, a hankali abun da ya faru jiya yashiga dawo mata, Zaraddin ya shigo da gaske bayan nan kuma shima Sahab d'in ke nan tagani rike da allura azahiri ba mafarki ba.
to me ya kawo shi har ya bar wayarsa anan?.
baki ta cuno a kasan ranta ta ce
"Ai Sahab d'in nan mugu ne allura yayi min ina bacci, shiyasa naji nan namin zafi,
alhalin lafiya ta lau."
ta tab'a gefen mazaunan ta.
ta aje wayar ta mike tana tuno kalaman da Zaraddin yayi amfani da su a kanta, duk da har yanzu takasa banbance shin hakan yafaru ko mafarki ne,
to in dai mafarki ne to ya akayi wayar Sahab ya shigo d'akin ta.
fuska ta kwab'e jin tunani nason hargisa mata kwakwalwa.
ganin goma saura
ta mike rike da wayar ta tafi kitchen.
ganin lokaci ya tafi batayi wani breakfast mai wahalaba,
Sudan tea ta girka, sai chips. tana cikin yanka albasan da zata soya kwai wuka ya zarce ya yanke ta.
kara tayi tare da sakin wukan da albasan kasa, tashiga yarfe hannu...
Da shirin fita ya shigo d'aukar Sudan tea d'in sa, baya yayi tare da leko kitchen d'in kasancewar kofar kitchen d'in a bud'e yake.
idan ta kalli hannun sai taji ya kara zafi, sai yarfe hannu take d'an jinin da yake fita duk ya b'ata mata jiki.
tuni hawaye yacika idanunta, kad'an ya rage su zubo.
tana d'agowa suka had'a ido, a hankali ta sunkiyar da kanta tare da kwab'e fuska tana mai dad'a yarfe hannun.
kamar zai wuce dinning sai kuma ya juyo ya tako zuwa cikin kitchen d'in.
da d'an sauri ta d'ago tana duban shi, ganin yana takowa cikin kitchen d'in.
sai kuma ta kuma sunkuyar da kai, san da ya iso in da take.
hannun da tayi yankan ya ruko.
da sauri ta d'ago da idanunta da suka ciko da kwalla sai sheki suke kad'an yarage su zubo.
suka had'a ido, fuskarsa a d'aure.
a hankali ta kuma sunkuyar da kanta.
sakin hannun nata yayi sannan ya juya ya fita.
bayan sa tabi da kallo tana kuma yarfe hannun, ta jingina da jikin cabinet, tana son yin kuka.
jim kad'an ya dawo har lokacin tana tsaye tana sharar kwalla.
baki ya tab'e baiga wani yankan kirki ba sai raki take.
da sauri ta dago jin ya kuma kamo hannunta, taji ya manna mata abu a kan yankan.
'yar karamar kara tayi, ya sake mata hannun, ya juya yafita......!
Aikin da bata karasa ba kenan ta koma d'aki.
mintuna kalilan ta nimi zafin ta rasa.
Ko da ya fita sashin Daddy ya tafi.
yana zaune suna gaisawa su Ajmaal Shamsuddin da Faisal suka shigo.
a kasan carpet suka zauna, kana suka shiga gaida Daddy.
sannan suka juya ga yayan nasu.
Daddy ya dube su yana fad'in
"Zaraddin yau ma bai kwana a gida ba ko, na tambaye security sunce min shine kad'ai bai shigo ba."
Shamsuddin ya ce
"Eh Daddy bai kwana ba tun jiya da safe da ya fita bai dawo ba, yana can gurin gantalinsa, Daddy dama nace zan gaya maka har giya ranar yashigo da shi gidan nan."
Ajmaal yad'an tab'a shi ta kasa kan ya yi shiru, shiko yaci gaba da fad'in.
"Kuma wlh Daddy saran da ya samu yanzu, idan ya tabbatar da kasan ya dawo,
cikin dare yake fita ya tirsasa security sai sun bud'e masa get, sai gari ya waye kafin ya dawo."
Daddy ya yi shiru yana saurarar sa kana ya jinjina kai tare da fad'in
"Allah kashirya Zaraddin daya zamo jarabawa cikin ahali, zansa aje a nemo sa idan ba anyi masa hukunci ba bazai dai na abunda yake ba, daga nan musa ayi ta masa addu'a da saukan alkur'ani, Allah ya shiryar da shi."
Abdulrahim ya yi kwafa ya mike tare da taune gefen lips d'in sa, yanufi kofa.
Daddy yabi bayan sa da kallo.
su Ajmaal ma suka mike suka fita.
A kusa da sashin Hajiya Ajmaal ya iso shi suka shige sashin nata tare.
in da su Faisal kuma suka nufi b'angare iyayen su.
Hajiya na zaune a parlour suka karaso sai da ya fara zama kafin Ajmaal ya zauna.
Hajiya ta bishi da kallo tana fad'in
"Wai kai kam abokin turawa ko yaushe zaka sauya oho, kullum ya kullum fuska turnuke ba'a gane farincinka;
ko da yake iyayen ka su suka ja maka, kai kuma gaka mai jin maganar iyaye, bazaka iya tuburewa kace ba haka ba,
sai an karka da ranka anga bayanka,
ko d'iyar sarkin aljanu aka aurama zaka aminta,
bazakayi musuba duk rashin adalcin da aka maka haka zaka d'auke shi ka aza a kanka,
ba garama uwar taka mutum ta zab'a maka ba, shiko uban ka d'iyar ifiritu ya aura maka,
ina zaka sami farin ciki,
ai saukin ka d'aya ka fito da matar da kake so ni muka nasa dole uban ka ya aura maka ita."
Ajmaal ya ce
"Ke Hajiya daga shigowar mutum ko gaisawa ba'ayi ba, kibi ki ishe shi da magana, ai ke ma haka su Daddy suke yi miki biyayya, ke nan shi so kike ya bijire yaki yi masa biyayya,
dan Allah kibar mutane su huta."
"To dun uban ka bazan bar mutanen su huta ba, rashin hutu na nawa kuma, yawuce wan da ubanku ya d'aura masa, ai nan gaba sarauniyar aljanu zai kuma aura masa, iya shegen banza a hanani magana ga abun maganar,
kai ma in baka maida hankali ba jinnun za'a had'a ka