Showing 72001 words to 75000 words out of 86085 words
Chapter 25 - FEERYAL Part 3 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt
cikin masarautar ashe ya dad'e yana munafurtar sarki Matip,
ya kafa sansanin sa a gefe batare da sanin sarki ba,
ya jone da bil'adama bokaye da matsafa, suna zalunci a bayan fage.
da labari ya zowa sarki Matip yasa aka hukuntashi sannan aka koreshi a fada, dama hukuncin duk wanda aka kama da laifin zalunci ke nan.
yana barin fada ya je ya kafa sansanin sa in da ya rika jan ra'ayin wasu daga cikin mu duk suka tattara suka koma karkashin sa,
kafin wani lokaci ya tattara kusan rabin fada da iya makircin sa,
daga nan ya nad'a kansa a matsayin sarkin bakaken aljanu,
ya fara wanzar da zalunci, cikin Aljanu da mutane,
ya baiwa bokaye lasisin cin karen su ba babbaka zalinci ya wanzu.
kafin wani lokaci yayi karfi fiye da sammani ya zamo shine mai fad'a aji,
fadarsa tayi karfi fiye da tunani.
a lokacin ya shirya yaki da sarki Matip ya shiga fadarsa da mayaka suka yake mu, aka karkashe da yawa daga cikin mu in da wasu kuma da yawa sukayi mubaya a suka koma bayansa, wasu kuma suka sami nasarar gudu subar gurin,
daga nan ya shiga yakama sarki Matip da ni wazirinsa ya sa aka d'aure mu, ni aka jefani a kurkuku,
Sarki Matip kuma akayi masa kejin karfe mai tsananin karfi, wanda in duniya zasu taru bazasu iya b'allashi ba,
kejin da aka kerashi da manya-manyan matsafa aljanu da mutane aka tsafe kejin karfen,
wanda bashi da makari sai abu guda, hawayen jaririya macen bil'adama 'yar baiwa mai idon ganin wasu jinsin da ba iya jinsin mutane ba,
shine kad'ai makarin sa,
da zai iya bud'e kejin karfen,
sai idan jaririyar tayi kuka hawayen ta ya d'iga a jikin kejin daga nan kejin zai bud'e.
aka d'auke sa aka jefashi a tsakiyar tekun Matip tsawon shekaru dari uku, Sarkin bakaken aljanu ya ke shinfid'a mulkinsa yadda yaga dama.
sai da nayi shekara d'ari uku a kurkuku sannan aka sake ni a matsayin bawa,
mai bautatawa fadar sarkin bakaken aljanu.
kwasam wata rana ina cikin aiki a fad'ar na tsinci maganar bakaken aljanu da mabiyansa wanda suke kusa da shi sosai,
da kuma bil'adama bokaye, suna cewa sunyi bincike sun gano an haifo irin yarinyar da zata iya kub'utar da Sarkin Aljani Matip,
'yar baiwa da Allah ya halitta mai iya ganin jinsin da ba nata ba kad'ai, suka kuma tabbatar da cewa sun gano kasar da aka haifeta,
dan haka zasuje kasar domin bincikota, su kashe ta kafin ta zame musu matsala, dan sun san idan sarki Matip ya kub'uta bazai kyale su ba.
Tun da naji labarin a ranar na zurfafa bincike har na gano a kasar Lebanon aka haifo ta,
washegari aka tura dakarun bakaken aljanu domin su je su d'auko ta,
ni na rigasu tafi.
tun da aka gano na gudu a fadar aka tura dakaru nima na,
akayi ta jefa kifiyar tauraru tana sukana,
mutuwa ce kad'ai banyi ba amma nasha wuya sosai kafin na isa ga in da take,
dan naci alwashin sai na kub'utar da ita daga zalincin su, sannan na kaita ta taimaki shugaban mu.
na sauka a gidan su na d'auke ta tare da sarkar masarautar mahaifiyarta domin na tabbata komin daren dad'ewa zata had'u da danginta,
ta sanadin lu'ulu'un masarautar su,
na had'a da hoton ta na sakata a kwando na tafi da ita.
ina fita na bayyana a babban tekun Bahar Rum.
na tafi ta sama har na shigo kasar nan na sako ta a dai-dai tsakiyar tekun Matip,
in da yake d'aure a karkashin tekun, ta isa kasan tekun taje ta ceto shugaban mu,
shugaba bai barta ta halaka ba a lokacin data ceto shi, aka fito da ita sararin duniya."
Sanda Waziri Kutup ya kawo nan
Abdulrahim cikin b'acin rai ya damki wuyar ta yana fad'in
"Da kun sa ta mutu fa! ina ruwan ta da lamarin ku ita tana mutum ku kuna aljanu, kuje ku magance lamarin ku mana!."
Waziri Kurup ya yi dariya ya ce
"Haba Garkuwa d'an sassauta rukon,
da mun barta ai da dakarun sarkin bakaken Aljanu sunje sun kasheta,
a cikin ruwan da muka barta tana yawo ai ba ita kad'ai bace a rike a hannun yaran mu take,
bazasu bari komai ya same ta ba, duk da muna da tabbacin zata fuskanci kalubale a duniyar nan,
dan munsan sarkin bakaken Aljanu bazai kyale ba,
bamu barta ita kad'ai ba kullum a cikin bata tsaro muke,
ko kuda bamu yadda ya sauka a kanta dan cutar da ita ba,
kwasam binciken mu ya gano mana kai, ta hanyar jefa taurarun bincike,
muka gano wasu tarukan baiwa a tare da kai,
da tabbacin kaine Garkuwar ta
har lokacin da ka bayyana a gareta, hakika kai Garkuwa ne a gareta tsaron ka a kanta yafi namu, domin kai d'in Garkuwa ne,
kana da wasu sirrukan da kai kanka baka san kana da shi ba, kai d'in daban ne acikin mutane."
Fuska ya murtuke ya ce
"Babu ruwan ku da wannan ku kauce ku bamu guri, kar ka sake mu kara gamuwa."
"A gafarce mu Garkuwa."
tana fad'in haka ta sauke wasu tagwayen atishawa jikin ta ya sake.
parkour'n ya kacame da hayaniya.
acan fadar Sarki Al'Ayzaan kuwa da suke biye da wayar suna ganin komai ta cikin waya,
Uncle Aliyu ya sanar musu abunda ya faru da harshen larafci,
suma suka cika da al'ajabi.......!
Rasheedat S Director
Mommyn Twins ce🤙🏻
Kowa yacika da d'in bin al'ajabi.
Allah ke nan buwayi gagara misali, su Hajiya jiki ya dad'a sanyi hakika sarki ya tabbata ga Allah.
su Ameerah kowa sai ido wacce ake ta wa gori a baya ita ba kowa ba, sai gashi tayi musu fintinkau.
jinin larabawa jinin sarauta uwa da uba hamshakan masu kud'i.
Mommy ko sai sunkiyar da kai kunya ya dad'a lullub'e ta.
kowa ya watse da al'ajabin abun.
Tuni labari ya isarwa su Abban Abuja da Hajja Umma, Feeryal 'yar Uncle Aliyu ce, farincikin su bazai fad'uba.
ashe jinin su ce ita shiyasa suke jin ta a cikin ransu.
labari ya zaga dangin su gaba d'aya, sukayi murna sukayi farinciki mara misaltuwa.
a ranar Uncle Aliyu ya koma Abuja wanda ya so tafiya da Feeryal a ranar Abuja sabo da su wuce Lebanon ya kaita wa dangin mahaifiyarta kamar yadda suka bukata.
Daddy ya ce ya bari ta shirya tukun ana gobe zai koma zataje Abujan ta same shi sai su wuce.
Ana gobe zata je Abuja, da daddare tana zaune tana kara bra cikin a kwatin ta, da Aunty ta ce ta kara kan wanda ta saka mata su ciki, dan Aunty'n ce da kanta ta shirya mata kayan.
Abdulrahin ya shigo ya tako bakin gadon.
yana isowa ya ture akwatin gefe ya zauna ya janyo ta jikinsa,
ya saka hannu ya zagaye ta tare da sauke mata kiss a gefen wuya kana ya d'ago yana kallon cikin idon ta.
"Kina shiri waya baki damar tafiya?."
ya yi maganar idanunsa cikin nata.
kasa tayi da idanunta tana turo lips d'in ta gaba,
ta kuma sinkayo muryarsa
"Idan kikayi wasa babu inda zakije."
fuska ta kwab'e ta ce
"Daddy ne fa ya ce naje."
"Shi ke nan baza'a tambaye ni ba sai ayi ta yanke hukunci, to bazakije ba."
da sauri ta d'ago ta kuma kwab'e fuska kamar zatayi kuka, tana kallon cikin idanunsa kamar yadda shima yake mata.
a hankali ya matso da fuskarsa daf da nata ya d'aura lips d'in sa kan nata, ya cafke ya d'an tsotsa, lumshe idanunta tayi tare da kawar da fuskarta,
ta kifa fuskar nata a kirjinsa tana matso kwalla.
a hankali ya ciro kanta yana kallon kwayar idanunta da suke tsiyayar da kwalla,
a ransa yake mamakin saurin kuka irin nata.
a sannu ya kuma had'e bakin su yashiga tsotsar bakin ta.
ya yin da ya tura hannunsa cikin rigar baccin jikinta yana matso ababen kirjinta.
sai kuma ya zaro bakin sa da sauri ya zare rigar a jikinta,
tana kokarin janyewa tuni
ya kwantar da ita ya bi jikinta, ya shiga tsotsar ta.
da zafi zafi yake shanye ababen kirjinta, ya d'ago ya na kokarin zare wandon jikin ta, da sauri ta rike hannunsa jiki a mace dan ya saukar mata da kasala,
ta ce "Sahab kar ka cire."
huci ya furzar tuno a in da suke, ya mike ya sauko a gadon yana rumtse idanunsa ya fice a d'akin.
a bakin kofar d'akin sukayi kicib'us da Aunty da ke kokarin shiga d'akin, Aunty tayi baya da sauri, bata san yana ciki ba dan bataga shigarsa ba.
ya sunkuyar da kai yana gaisheta, kana
yasa kai ya shige yana kawar da kansa dan a fili ake hango yanayin da yake ciki.
Aunty ta juya ta koma d'akin ta bata kuma shigowa d'akin Feeryal ba sai washegari.
da safe Daddy ya kaita airport da kasan.
Feeryal ta isa Abuja da wuri.
a cike ta sami gidan da 'yan'uwa har da wanda bata tab'a sanin su ba.
Maryam ma ta zo daga Ogun da d'anta.
kamar yau suka fara sanin ta, wani sabon kauna da soyayya suka rika nuna mata.
musamman Hajja Umma da Abba.
kwana d'aya tayi a Abuja washegari, jirginsu ya d'aga ita da Uncle Aliyu zuwa Lebanon,
tana like da mahaifin ta a jirgi ga sit d'in shi ga nata,
duk da a baya bata tab'a jin maraicin uwa da uba ba,
dan
Daddy da Aunty sun maye mata gurbin su,
amma sai gashi ta tsinci kanta cikin jin nutsuwa mai cike da tarin farincin kasantuwar ta da mahaifinta.
haka Uncle Aliyu ko motsi tayi sai ya tambaye ta tana lafiya.
Jerginsu na sauka a Beirut na kasar Lebanon, tun daga airport
taga tsantsar tsagwaran kauna da sosayya,
zuga guda 'yan taran su motoci sunfi goma.
maza da mata rungumar Feeryal suke, kamar zasu had'iyeta, ganin ta ya tuna musu da 'yar'uwar su.
wani gida ne da girman sa ya kai girma tsaruwa bazai fad'u ba,
nan Feeryal ta tsinci kanta.
suna shiga gidan wasu zugan suka kuma yiyowa kanta,
kamar bazasu barta ta taka kasa ba tsabar kauna.
wata dattijuwar mata ta fito tunda ga can take yi mata murmushi hawaye kuma na sauka a idanunta,
ganin Feeryal ya tuna mata da d'iyarta Sheehra,
itama Feeryal ta gane ta ta waya da ta ganta sanda Uncle Aliyu ya had'asu ta waya.
ta taho ta rungume Feeryal tana mata maraba da zuwa tana murmushi gami da share hawaye.
nan ta ruko hannunta ta jata sukayi ciki da ita.
Uncle Aliyu yabi bayan su.
wani babban kayataccen parlour suka bayyana cikin sa,
bayan sun wuce wasu palukan sama da biyar.
dattijo sarki Al'Ayzaan na ganin ta ya mike daga kan kujerar sa ya mika hannu yana cewa
"Taho nan jikata lale marhaban da zuwa masarautar Beirut."
cikin harshen larafci yake maganar.
ta fahimci abun da yake nufi ta tafi izuwa gare shi, ya rungumeta yana fad'in
"Sarki ya tabbata ga ubangijin halitta daya sanya kamannin Sheerah Al'Ayzaan a gare ki, hakiki muna farinciki da zuwan ki, nan gidan ki ne Feeryal Aliyu Sheehra Al'Ayzaan."
Uncle Aliyu ya yi murmushi yana gaya mata abun da ya fad'a.
Dattijon ya sake ta yana dafa kanta, tare da sanya mata albarka.
yana jin ta a ransa sosai ya yi farincikin ganin ta matuka.
Ranar Feeryal sai da taji a ranta ashe itama wata ce,
dan kuwa taga kaunar da ya sata jin itama wata ce ashe.
Nigeria
Legos
Mommy ce ta shigo parlour'n Daddy yana zaune yana duba wasu takardu.
ta nimi guri ta zauna tayi masa barka da warhaka.
ya amsa batare da ya janye idanunsa daga kallon takardun ba.
Mommy ta d'an muskuta bakin ta na d'an motsi alamar magana ce d'auke da ita,
ta ce
"Alhaji dama magana nazo muyi akan batun Abdulrahim da Feeryal, na ce me zai hana a maida auren su idan ta dawo,
kayi hakuri Alhaji ina mai kara baka hakuri amma wlh nayi nadama nayi danasa mara misaltuwa, sharrin shaid'an ne da Hajiya Karima."
Daddy ya d'ago ya dube ta yana fad'in
"Sabo da yanzu kinsan asalin ta shiyasa zakice a maida auren ta da d'anki ko."
da sauri ta ce
"Ba haka bane Alhaji wlh na jima da wannan abu a raina narasa ta ya zan tinkare ka da batun ne, bansan taya zaka fuskanci lamarin ba,
amma Allah ne shaida wlh tun ranar dana gano gaskiya nayi nadamar abun da na aikata,
wlh Alhaji nayi na dama."
Mommy ta saka bakin mayafin ta tana share kwalla da gaske yake hango nadama tare da ita.
Daddy ya girgiza kai sannan ya ce
"Abdulrahim bai saki Feeryal ba, lokacin da kika matsa masa sai ya sake ta, ba saki ya rubuta cikin takardan ba kalmar hakuri ya rubuta ya mika mata."
Mommy ta d'ago da sauri tana murmushi da fad'in
"Allah na gode maka daka takaita yawan zunubaina."
ta mike da sauri tana share hawayen fuskarta ta fice da sauri tayi sashin Hajiya.
tana zuwa ta rungume Hajiya tana fad'in
"Hajiya Abdulrahim bai saki Feeryal ba, ashe da na ce ya sake ta ba saki ya rubuta mata ba."
Hajiya ta ce
"Ah to madallah aikuwa dama ina shirin sa Abubakar ya kuma d'aura musu aure, ai ko fad'uwa tazo dai-dai da zama."
Ajmaal Shamsuddin Zaraddin Faisal, Goggo Bishira Bilkisu Rahma da suke zaune, suna hira da Hajiya duk sukayi farinciki da jin labarin,
Mommy baki ya kasa rufuwa kowa sai da yasan da labarin Abdulrahim bai saki Feeryal ba.
ta kira 'yan Yelwa tarika sanar musu..
Lebanon
Feeryal
kwanan ta biyu a masarautar aka d'auke ta akayi ta zagawa da ita, ana nuna mata inda dangin mahaifiyar ta suke,
duk in da sukaje kuwa sai sunyi kuka da farin ciki wai ta tuna musu da 'yar'uwar su Sheehra.
haka zasuyi ta riritata kamar zasu goyata.
A ranar da tayi kwana uku kuma Uncle Aliyu da kansa ya d'auke ta a mota, ya kai ta gidan da sukayi rayuwa da mahaifiyarta har da d'aki da gadon da aka d'auke ta akai,
ya nuna mata hotunan sa da hamaifiyarta.
Feeryal tasha kuka sosai dan taji kewar mahaifiyar tata.
Suna dawowa cikin masarauta, Feeryal ta kule
babban d'akin da a ka yi mata masauki, ta kira Aunty tana ganin ta taji kewar uwa daya baibaye ta ya gushe,
tayi ta zuba mata shagwab'a kamar yadda ta saba, Aunty na biye mata.
Aunty ta ce yaushe zata dawo dan tayi kewar ta Feeryal ta ce
"Bari Uncle yazo na tambaye shi yaushe zai mai dani, d'azu ya ce min wai kakana ya ce sai nayi musu wata, nima ina so na dawo Ammie nayi kewar ki."
Aunty ta rike baki ta ce
"Baban naki ne Uncle."
sai kuma tayi dari ta ce
"Wata guda kuwa yakamata kiyi musu, suma suna bukatar ki a tare da su."
hira sosai sukayi Aunty tana tambayar ta ya kasar yake, dan duk fitar da take kasashen waje bata tab'a zuwa kasar ba.
daga bisani sukayi sallah.
Ranar da Feeryal ta cika kwana biyar, aka fita da ita ganin kadarorin mahaifiyarta, da kamfanonin mahaifinta da mahaifiyar ta,
sai yamma suka dawo gida.
tana shiga parlour'n kakarta mace ta tadda mutane da yawa cikin parlour'n kamar ko da yaushe,
tana kokarin karasowa cikin parlour'n
tayi burki da mamaki take kallonsa, suna zaune da wani da akace mata d'an kawun ta ne shi, suna hira cikin harshen larabci,
ga yadda suke hirar zaka fahimci ba sabon rana d'aya bane, sun jima da sanin juna.
Duk suka d'ago suka kalleta.
dattijiwa kakarta Ummuh da ke zaune a gefen su tayi mata alama da hannu ta karaso.
a hankali take d'aga kafarta idanunsa a kanta har ta karaso gefen ta ta zauna.
kakar nata take cewa
"Munyi farincikin da shi ya kasance mijin ki, dan yaron kirkine shi abokin d'an 'uwan ki ne shi, tare suke aiki a can kasar Germany."
Rubah dake gefen su take maida mata abun da take fad'a da turanci.
shiru tayi batayi magana ba.
zuwa can ta mike ta tafi masaukinta.
Washegari tana fitowa ta hango shi shi da Uncle Aliyu, ta kauce bata bari sun had'a ido ba.
san da ta shiga gaida sarki Al'Ayzaan, takuma ganin su tare.
mamki take ganin yadda shi ya fita shiga da fita a cikin gidan.
suna gama gaisawa ta koma.
karfe goma da rabi dattijiwa kakarta Ummuh ta shigo ta ruko hannunta kamar kullum tun san da ta zo gidan,
suka fito kan babban dinning mai zagaye da kujeru talatin, an jera abinci kala-kala kan dining d'in,
jikoki da 'ya'ya sune zagaye da gurin,
tun kafin ta karaso ta hangosa zaune shi da wannan d'an uwan nata abokin aikin sa, da wasu mazan suna zagaye da shi suna ta yi masa magana da harshen larabci,
ga takardu a gaban sa da alama dai hannu yake saka musu cikin takardun.
a sannu ta karaso suka rika mikewa suna rumgumar ta, kamar yadda larabawa suka saba wajen gaida d'an uwan su,
har da mazan gurin.
fuska ya d'aure yana aika mata wani kallo.
ta kawar da kanta kusa da Rubah ta zauna aka zubo mata abinci kala-kal,
batawa ni ci abincin kirki ba dan dama ita ba ma'abociyar cin abinci bane, sannan bata saba da cin kalar abincinsu ba,
abun da zata iya ne ta d'an tab'a, ta tsulale ta bar gurin, dan kallon da yake ta jefa mata ya hanata nutsuwa.
Da rana suna zaune da 'yammatan gidan, dattijiwa kakarta Ummuh tazo ta ruko hannunta suka tafi parlour'n Al'Ayzaan.
anan suka tadda mahaifinta zaune.
kakar nata ya dafa kansa yana sanya mata albarka, kana ta nimi guri ta zauna.
ya dube ta da kulawa ya na cewa
"Yake jikata ki shirya gobe zaki koma da mijinki, zai kuma dawo mana da ke bayan wani lokaci."
Feeryal ta d'ago da sauri dan ta ji wani abun da ya fad'a.
Uncle Aliyu ya ce
"Gobe idan Allah ya kaimu zaki koma da mijin ki, idan an kwana biyu zai dawo da ke ki kuma ganin danginki."
Feeryal ta sunkuyar da kai tana tankwashe 'yan yatsun ta, ko ba'a fad'a ba tasan shirin nan na Sahab ne.
Goma na arziki suka had'a mata
in da aka mallaka mata dukiyar mahaifiyarta.
akace idan suka dawo Nigeria za'a transfer dukiyar ta dake aje a banki zuwa bankin Nigeria.
Ummuh ta bata wani sarkar gold ta ce ta kaiwa Ammien ta.
motoci goma na masarauta suka fito rako su airport.
tana rike a hannun dattijuwa kakarta Ummuh ta bud'e motar da yake ciki shi kad'ai ne a baya sai direba ta ce ta shiga, ta shiga ta zauna Ummuh tayi musu fatan isa gida lafiya,
yana amsa mata da larafci.
Ummuh ta share kwalla dan ba shakka bataji dad'in rabuwar su ba.
motocin sukayi layin fita suna haurawa titi ya juyo inda take,
ya janyo ta jikinsa cikin yin kasa da murya ya ce
"Kar na sake ganin kin tsaya wani kato ya rungume ki."
da sauri ta d'ago ta kalle shi ya jinjina mata kai alamun tabbar wa.
kasa tayi da idanunta bata ce ko mai ba, yana rungume da ita har suka isa airport.
ai kuwa da suka sauka ana ta rungumar juna na bankwana duk namijin da zai rungume ta sai ta matsa ta bishi da murmushi,
ji tayi an sakalo ta ta gefe ta juya da sauri shine ya rungume ta ta gefe a haka suka