Showing 69001 words to 72000 words out of 86085 words

Chapter 24 - FEERYAL Part 3 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt

ido tana kallon sa sai kuma ta turo baki ta kwab'e fuska tana shirin kuma fashewa da wani kukan.
"Ke ya isa mana."
"Ni dai ka fita."
ido ya tsura mata sai kuma ya rungume ta, a hankali murya can kasa ya ce
"Kiyi wankan fita zamuyi, kar ki b'a lokaci yanzu ki zo ina jiran ki a mota."
yayi maganar yana matso nonon ta.
kafad'a ta make tana kuma kwab'e fuska.
"Bazaki je ba?." yayi maganar yana leko fuskarta.
kwantar da kai tayi a kirjin sa tana kuma make kafad'a.
ido ya lumshe ya bud'e su a kanta.
nan ya soma tsarrafata cikin bayin sai da ya tsotse ta tass kafin ya fita.
ya barta tana sauke numfashi jikinta gaba d'aya ya mutu.

Kamar jiya yau ma Aunty bayan sa ta hango yana fita daga parlour'n tayi mamakin yaushe ya shigo,
nan take ta tuna d'azu kamar taji ihun Feeryal.

Da kyar ta iya karasa wankan, dan ba kad'an ba ya kashe mata jiki.
ta shigo ta shirya ta haye gado ta kwanta tayi lamo.
Aunty ta shigo ta karaso bakin gadon tana fad'in
"Ke Feeryal baki da hankali ne, zaki rika yiwa mijin ki ihu duk duniya suna ji, wani irin shirme ne wannan."
fuska ta kwab'e ta ce
"Ammie razana ta fa yayi."
"Dalla tafi can kar na sake jin irin wannan shiriritar, taso muje kiyi breakfast."

Da daddare Aunty suna tare da Daddy ta nisa tana cewa
"Daddy ya kamata a maida wa Abdulrahim matar shi, dan alamu sun nuna yana bukatar matar sa, kar a shiga hakkin sa da yawa."
Daddy ya ce
"Shi ya fad'a."
Aunty ta ce "Aa bai fad'a ba amma a yadda alamu suka nuna yana bukatar matarshi a kusa, duk kawaici irin na Abdulrahim haka yake d'auko kafa ya taho ni wani lokacin ma bana sanin sanda yake zuwa sai dai naga fitarsa."
Daddy ya ce
"Baza a mai da masa ita ba tare da yazo ya yi biko ba."
Aunty ta yi murmushi ta ce
"Daddy biko kuma?."
ya ce "Eh biko yazo ya rutsuna wata kila idan akaji tausayin sa a mai da masa ita, a hakan ma sai an ji ta bakin ta idan tace zata koma sai a mai da masa ita."
Aunty zata kuma magana Daddy ya ce
"Kar ki ce ko mai ki rabu da shi idan bai zo ya nimi alfarma ba baza'a mai da masa ita ba."


Beirut babban birnin kasar Lebanon.
motocin da suka fito yiwa Alhaji Aliyu Tahir Abbas rakiya ne suka haura kan titi,
motoci biyar ne biyu a gaba biyu a baya sannan nasa a tsakiya.
motoci masu d'auke da tambarin
S.A
(شهرا) (عَلِيّ) .
Duk in da suka gifta girmamawa da gaisuwa na ban girma ake musu,
airport d'in babbar birnin Beirut na kasar Lebanon suka isa.
in da jami'an tsaro larabawan da ke cikin sauran motacin suka firfito suka zageye motar da Alhaji Aliyu Tahir Abbas yake ciki,
in da jami'ai biyu sukayi saurin bud'e masa kofar mota, ya sauko da sauri ya nufi cikin airport d'in, wasu jami'an sukayi saurin shiga gaban sa wasu a bayan sa a haka suka isa gurin jirgi.
duk wad'an da suke gurin kuwa baya sukayi suna d'aga hannu da had'e shi suna mika masa gaisuwa cike da girmamawa.
sai da ya shige cikin jirgi kafin sojojin suka matsa baya, basu bar airport d'in ba har sai da jirgin ya tashi.


Abba ne ya shigo da sauri rike da waya a hannunsa ganin yadda ya shigo da sauri Hajja Umma ta d'ago tana duban sa da cewa
"Yaya dai Alhaji lafiya?."
ya ce
"D'anki ne Aliyu yanzu ya kira ni yake sanar min wai jirgin su zai taso, karfe biyu da rabi zai sauko Nigeria."
Hajja Umma ta mike cike da fara'a ta ce
"Masha'allah Allah ubangiji ya kawo shi lafiya, zuwa haka ba sanarwa sai a ranar da za'a zo,
to hakan ma munyi farinciki shekara nawa sai dai gani ta waya."
Abba ya ce "Amin amin sai ki sa masu aiki su fara shirya masa abinci."
"Ni da kaina zan shirya masa ba masu aiki ba."
ta fad'a tana mike wa ta nufi kitchen, Abba kuma ya yi waje.

karfe biyu da rabi agogon Nigeria.
Arab Lebanon airplane ya sauka a airport d'in babban birnin taraiya Abuja.
wan da tun karfe biyu motar gidan Alhaji Tahir Abbas ya isa airport yake jiran isowar sa.
direba ya d'auko sa suka nufo gida.
kafin su karaso gida kaf dangin su da suke abuja sun hallaro gidan suna zaman jiran isowar sa,
wan da suke nesa wato wasu garurruwan suka so tahowa Abba ne ya ce kowa ya zauna, idan ya huta zai zaga kan su duk baki d'aya.
da isowar sa gidan
zo kaga murna gurin Hajja Umma da Abba da dangin su.
hatta yaran da basu wuce shekaru ashirin ba murna suke da ganin sa, dan da yawa basu sanshi ba sai a waya da kuma hoto.
kwarya kwaryar liyafa aka had'a domin farinciki da murnan zuwan sa.
har dare aka kai ana shagalin farincikin zuwansa.
kafin aka watse kowa ya koma gida.
washegari ya shirya yace zai fara ziyara domin hutun kwana 7 ya d'auka zai koma,
ya ce zai fara da Abuja gurin kanwarsa Fatima wato Aunty, dan ita ce kanwarsa ta biyu, wacce take binsa Hajiya Zainab ita tana nan cikin Abuja take aure,
kuma jiya da ita aka tare sa.
tun a daren jiya ya shirya tafiyar in da aka sanar masa washegari karfe 9 jirgi zai tashi.
bai b'ata lokaci ba ya isa airport kafin 9.
karfe shad'aya da rabi suka sauka a Lagos.

Tun da gari ya waye Aunty bata zauna ba, tayi nan tayi can dan shiryawa d'an'uwan nata tarba.
Daddy da kansa ya tafi airport tarbansa da direban sa.
Aunty tana jin isowar su ta fito da sauri cike da matukar son ganin d'an'uwan ta,
kamar zatayi yaya dan farin cikin ganin sa.
suka d'unguma suka shigo parlour'n ta Daddy yana ta zolayar ta wai murna ya hana ta zama, ita dai sai dariya take.
nan da nan ta cike shi da kayan ciye-ciye da na sha.
ta zauna bayan ya d'an tab'a abincin, suka soma hirar yaushe gamo har da Daddy.
cikin hirar tasu Aunty ta ke cewa
"Yaya Aliyu ya kamata kayi aure yanzu, ace tun bayan rasuwar Sheehrah shekara kusan goma sha takwas, ace bakayi aure ba har yanzu,
idan baka sami balarabiyar data maka acan ba, to me zai hana kazo nan gida Nigeria ka auri 'yar kasar ka,
zama haka ba mata bazai yi kyau da kai ba a matsayin da kake yanzu, ya kamata kafin ka tafi ka sami mata anan kayi aure."
Daddy ya ce
"Kwarai kuwa abun da yakamata ke nan, amma shekarun sun ja da yawa, wanda ya mutu ya musu sakanin mu da su addu'a da fatan muma Allah ya kyautata namu bayan nasu."
ya ce
"Insha'Allah yanzu kam zanyi aure, dama akwai kanwar Sheehra da mahaifin su ya bani, idan na koma za'ayi bikin insha'allah."
Aunty da Daddy sukayi masa fatan alkhairi.

Feeryal tana sashin su Miemie labari ya isar mata Yayan Ammie'n ta da yake kasar Lennon ya zo.
suka d'unguma ita da Ameerah da Miemie da Sumayya suka taho sashin Aunty, Ammah ma ta biyo bayan su.
Feeryal na sako kafar ta parlour'n Uncle Aliyu ya mike zumbur yana kallonta da furta
"Wlh tsak kamar ita!."
cikin rashin fahimta Aunty ta ce
"Kamar wa Yaya Aliyu?."
da sauri ya ce
"Sheehra kamar Sheehra tamkar ita babu banbanci."
sai kuma da sauri ya d'au laptop nasa daya zo da shi yana ajiye a kan hannun kujerar da yake kai.
har hannunsa na rawa yashiga latsa laptop d'in hotuna suka bayyana ya dannan kan hoton wata kyakkyawar balarabi hoton ya mamaye fuskar laptop d'in.
hoton ya nuna
yana fad'in.
"Ga ta nan Sheehra kamar ta."
Daddy da Aunty har suna rige-rigen leka hoton.
kyakkyawar mata mai tsananin kama da Feeryal kama sosai,
sai dai ta d'an fita girma a yadda take a yanzu shekarun ta 18 na hoton kuma zata iya kaiwa 25.
Ammah Miemie Ameerah Sumayya suma suka karaso da sauri suna kallon matar da take tamkar photocopy Feeryal.
Daddy ya ce
"Ikon Allah ka dubi wani irin tsananin kama, wa zai iya wannan in ba Allah ba."
Feeryal ko hannu ta kai ta shafo fuskarta tana kallon mai kama da ita tsak.
Uncle Aliyu ya kautar da wannan hoton yana nuna musu wasu hotunan nata,
yana zuwa kan wani hoton jaririya
da sauri Aunty ta ce
"Dakata Yaya Aliyu wannan hoton akwai irin sa ina da irin sa."
ta juya da sauri mai had'e da gudu ta shiga d'aki,
ta shiga binciko ta in da ta saka kwandon da aka tsinci Feeryal ciki, wanda tayi masa kyakkyawar ajjiya.
ta fito da sauri rike da kwandon da sauri ta aje kan kujera, ta shiga d'ago kayayyakin ciki wan da kayan da suka tsince ta da shi a jikin ta ne, da kuma sarka da abun hannun gold da hoton da taga irin sa cikin laptop nasa.
ta d'ago hoton ta kalla, tare da kallon na cikin laptop d'in,
da sauri ta mikawa Daddy tana fad'in
"Daddy ka kalla ka gani wannan hoton ne."
Daddy ya karb'i hoton yana qkallon su duka ba sai an fad'a ba hoto ne guda biyu iri d'aya.
Uncle Aliyu kuwa ba takan hoton yake ba kwandon ya d'auka a hannunsa yana d'ago abun hannu da sarkar gold d'in da ke cikin kwandon
"Lu'ulu'ul Fahsia!."
Aunty Daddy da sauran mutanen parlour'n duk suka juyo inda ya ke.
da sauri ya juyo yana kallon Feeryal ya yin da idanunsa suka ciko da kwalla.
ya ce
"Abun da ya taso da ni daga Lennon ke nan ganin tsananin kaman da suke yi, ranar da na fara ganin ta ta waya da kika had'a mu mu gaisa, a lokacin da kika ambaci sunan ta shi kad'ai sai da naji fad'uwar gaba, dana ganta kuwa zuciya kamar zata faso, lallai ke jinin masarautar Lennon ce FEERYAL SHEEHRA AL'AYZAAN tabbas ke d'iya ta ce, taho nan Feeryal Sheehra Al'Ayzaan......!
Ameerah da Sumayya Miemie har suna rige rigen fita da gudu dan zuwa shaidawa sauran 'yan gidan abun da ke faruwa.
ai kuwa suka d'ungumo dan zuwa ganin wanda yazo yake fad'in
Feeryal 'yar sa ce.
ba iya mamallakan gidan ba har da ma'aikatan gidan maza da mata.
Abdulrahim da yake shirin fita a mota,
Ajmaal ya shaida masa abin da ke faruwa, ya share maganar yayi kamar zai tafi,
sai kuma ya kashe motar ya shigo sashin Aunty dai-dai san da Uncle Aliyu ya ke fad'in
"Wannan lu'u'lu'u masarauta ne,
duk wani jinin masarauta shine kad'ai ke da shi,
wannan shine tambarin masarautar su,
babu wani a fad'in duniyar nan da yake da irin sa,
sabo da tambari ne da masarauta suke yin sa na shai dar da ke nuni da jinin masarauta,
wannan shine lu'ulu'un masarautar Beirut, wan da yake mamalkin masarautar,
da su kad'ai ke da irinsa, wanda yake haramun ne kera irin sa masarautar su ne kad'ai ke da ita,
kamar dai yadda sauran masarautu ke da irin nasu suma,
hakika wannan lu'lu'un Sheehra Al'Ayzaan ne data mallakawa d'iyarta Feeryal, wacce ta b'ace a lokacin da take da kwanaki goma a duniya."
wasu hawaye suka zubo wa Uncle Aliyu ya kuma mika hannu yana fad'in
"Taho gareni d'iyata mun rasaki a lokacin da muke farinciki da samin ki, sai gashi na kuma samin ki a lokacin da kad'aici ya zagaye rayuwa ta na rashin ki da mahaifiyar ki, da rashin ki ya haifar mata da bugun zuciya har ta kai ga rasa ranta."
Feeryal ta soma d'ago kafarta tana takowa in da yake.
Uncle Aliyu ya rungume ta yana hawaye da fad'in
"Hakika ke jinina ne Feeryal d'iya ga Sheehra Al'Ayzaan 'yar sarkin Beirut babban birnin kasar Lebanon,
ke ce muka rasa shekaru 18 baya,
a ranar da kike da kwanaki goma da haihuwa, kina a kwance a kan gadon ki kina bacci, mu kuma muna parlour da mahaifiyarki,
muka shigo muka tadda bakya nan,
mukayi ta nima bamu same ki ba,
abun al'ajabi abin da ya shigewa kowa duhu, ke da kike d'aki a kwance muka neme ki muka rasa, babu kuma wan da ya shigo gidan, dan gida ne mai matukar tsaro,
kakanki mahaifin mahaifiyarki sarki Al'Ayzaan yasaka bincike mai tsanani, ciki da wajen garin sakamakon b'atar ki,
amma ina ba'a sameki ba,
bayan niman ki da mukayi muka rasa da kwanaki uku itama mahaifiyar ki Sheehra Al'Ayzaan, ta bar duniyar sabo da bugun zuciyar da ta samu sakamakon rasa ki,
nayi kukan rashin ku nayi kukan rasa Sheehra data nuna min halacci duk da kasancewar ta d'iya ga sarki Al'Ayzaan sarkin larabawa na Beirut babban birnin kasar Lebanon,
bata dubi kabila ko jinsi ba ko banbanci kasa ba,
muka kulla soyayya a makaranta in da mahaifina ya kaini karatu kasarsu,
soyayyar da take nuna min shi ya kaiga mahaifinta dattijon arziki bani ita a matsayin mata,
shima bai nuna banbancin kasa ko kabila ba,
amma ya ce da sharad'in zan zauna da ita a kasar su,
bayan mun kammala karatun mu
gwamnatin kasar ta bamu aiki
da muke d'aukar albashi mai tsoka,
da har ta kai mu gina manyan masana'antu masu reshe daban da ban a fad'in duniya, wanda yake mallaki na ni da ita, mai tambarin sunan mu.
S.A
(شهرا) (عَلِيّ)
Wan da har a yau gwannatin kasar bata fasa biyan Sheehra Al'Ayzaan albashi ba, duk da bata raye,
sannan iyayen ta basu yadda su karb'i ko sisi cikin kud'in albashin ta da kuma wanda masana'antun mu suke kawowa ba, kud'in albashin ta yana nan a ajiye a wani banki na kasar,
duk wata nan ake tura mata albashin ta,
masana'antun kuwa mahaifinta ya ce na rike duka basu karb'i ko d'aya daga ciki ba."
Feeryal ta kifa kanta a kafad'ar Uncle Aliyu tana jin sanyi cikin ranta hawaye na gangara a fuskarta.
ta mike ta dawo jikin Aunty ta rungume ta, tana murmushi hawaye na zuba a idanunta,
Aunty bakin ta ya kasa rufuwa sabar farinciki.
Uncle Aliyu ya dube su yana cewa
"Ashe dama Fatima da kike gaya min kun tsinci yarinya a cikin ruwa ashe 'yar ki kika tsinta,
ta ya akayi ita da take Lebanon me ya kawota Nigeria, kuma a cikin ruwa."
da sauri ya daddana computer yana kiran wata lamba na kasar Lebanon.
wata farar dattijuwar balarabiya mai matukar kama da Feeryal ta bayyana tare da yin sallama.
Uncle Aliyu ya amsa sallamar yana gaisheta cikin harshen larafci, kana ya d'ago sarka da abun hannun nan ya nuna mata kafin ya yi magana ta rigashi magana cikin harshen larafci.
"Lu'ulu'ul Fahsia lu'ulu'un masarautar Beirut,
a kaf ahalin masarauta babu wanda nashi baya wajen sa, sai na Sheehra Al'Ayzaan, daya b'ace da jikata."
Uncle Aliyu ya je ya kamo hannun Feeryal ya kawo ta gaban laptop d'in,
dattijuwar tana ganin ta ta dafe kirkinta tare da fad'in
"Lahaula walakuwwata'illabillah, idona ne ke gane min Sheehra ko kama ce, wani irin kama ne wannan irin na Sheehra, hakika mutuwa d'aya ce kuma idan anyi ta ba'a tab'a dawowa,
na yadda Sheehra ta mutu shekaru masu dama,
wannan ita kuma wace ce?."
ya ce "Jikarki ce Feeryal gatanan cikin dangina su suka tsince ta, tsintuwa mai ban mamaki."
ya bata labarin in da su Aunty suka tsinceta.
dattijuwar ta fashe da kuka ta soma tafiya cikin sauri,
ta bayyana cikin wani ramb'asheshen parlour, ba sai an fad'a ba kasan na masarauta ne irin na kasashen larabawa.
tun kafin ta karasa take fad'in
"Ya Al'Ayzaan ga jikarka Feeryal d'iya ga Sheehra."
dattijon ya mike zumbur da jin abun da ta fad'a ta karaso da sauri ta mika masa wayar tana cewa
"Feeryal ce tabbas ita ce."
sarkin Beirut Al'Ayzaan ya kura mata ido yana kallonta zuciya da fuska taf da farinciki mai gauraye da al'ajabi.
Uncle Aliyu ya d'ago gold d'in yana sakashi a hannun Feeryal.
dattijon balaraben ya jinjina kai cike da kamala da dattako ya ce
"Tabbas Feeryal Sheehra Al'Ayzaan ce wannan, lale marhaban jikata."
larabawa maza da mata suka rika tuttud'owa suna zuwa bayan dattijon suna leka Feeryal,
tun da sukaji dattijuwa ta ambaci sunan d'iyar 'yar'uwar su data rasu.
'yarta kuma ta b'ace.
duk wan da yayi ido biyu da ita,
cewa yake tabbas jinin su ce koda babu Lu'ulu'un masarautar su tare da ita,
tabbas sunga Sheehra a jikinta,
iya haka ma ya tabbasar musu ita d'in d'iyar 'yar'uwar su ce.
suka rika d'aga mata hannu suna sanar mata da farincikin da sukayi na ganin ta.
Feeryal dai sai murmushi take musu itama tana d'aga musu hannu,
dan ba duka maganar nasu take fahimta ba tsinta-tsinta take jin larafcin wanda a islamiya aka koyar da ita.

Sarki Al'Ayzaan ya yi wa su Aunty da Daddy godiya sosai da suka zame mata uwa da uba,
batare da sanin wace ce itaba.
ya ce ikon Allah ne ya jefo ta Nigeria, ta fad'a a hannun su mutanen kwarai, uwar da ta raine ta bata san cewa d'iyar d'an uwan ta ba ce ita.
ya kuma bukaci Uncle Aliyu ya zo musu da ita, domin taga dangin mahaifiyar ta.


kowa ya cika da mamaki da al'ajabi, Daddy bakin sa ya kasa rufuwa sai fad'in
"Alhamdulillah Alhamdulillah."
yake, Abdulrahim yana tsaye daga bakin kofa.
Hajiya Mommy Mom Ammah da sauran mutane kowa na tsaye da d'in bin mamaki.

Feeryal na tsaye sai gani akayi ta yanki jiki ta fad'i kasa.
salati parkour'n ya d'auka har da su Sarki Al'Ayzaan da sauran mutanen da suke tare da shi,
suke kallon abun da ke faruwa ta cikin waya.
wani irin d'ago kafa ya yi ya karaso cikin parlour'n,
yana isowa kanta da sauri cikin wata iriyar murya na maza ta ce
"Aa Garkuwar god'iyar mu, mu ba macuta bane kuma bamuzo dan mu cutar da ita ba,
hasali ma mune masu bata tsaro a lokacin da baka tare da ita Garkuwa,
munzo ne don mu fayyace duhun da ya shigewa kowa cikin lamarin b'atar god'iyar mu a lokacin da take jaririya,
sunana Waziri Kutup nine Wazirin Sarkin Aljanu."


A wani karni shekaru masu tsawo alokacin da zalunci ya yawaita,
baga bil'adama ba ga jinnu ba.
ta ko wani fanni zalunci ya yi yawa,
kwasam aka haifo shugaba Matip ya taso da farar zuciya, yaci burin gyara al'umman sa,
ya yi yaki da karfin sa wajen ganin azzaluman aljanu da wad'an da suke baiwa jinsin bil'adama bokaye da matsafa sa'a,
wajen yin bokanci da tsubbace-tsubbace masu surkulle da 'yan bori, ya rushe sansanin su da karfin izzarsa.
yasa kowa ya rusuna bisa gwaiwowin sa, dan dolen su sukayi murabus da zaluncin da suke yi, cikin jinsin mutane da 'yan'uwan su aljanu.
ya shafe babin azzalumai aka daina zalunci, ya zame mana sarki.
tun daga lokacin adalci ya wanzu kwasam bayan shud'ewan wani lokaci.
aka sami munafukin shaid'ani daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login