Showing 1 words to 3000 words out of 92772 words

Chapter 1 - KWANTAN BAUNA BOOK 1 COMPLETE by Nana haleema.txt

20 Jul 2024

17677

*KWANTAN ƁAUNA*
October/FitattuBiyar 2023.


©️ *Nana Haleema.*


_*Da Sunan Allah mai rahma mai jinqai, Tsira da amincin Allah su tabbata ga annabi Muhammad S.A.W. Godiya ga Allah mad'aukakin sarki da ya bani iko da damar sake d'ora alqalami na akan sabon labarina mai take KWANTAN B'AUNA, ba dabarata bace, ba wayona bane,ikon sane shine ya nufa da bai nufa ba da bamu zo nan ba. Ina rok'on Allah yadda ka bani damar farawa lafiya ka bani ikon gamawa lafiya.*_


_Masoyana gani na sake dawowa a cikin wani sabon salon ina fatan zaku bani had'in kai fiye da wanda kuka bani a baya wajan ganin mun isar da sak'on da yake cikin labarin nan yadda ya kamata. Wannan tafiyar daban take da ko wacce, kuma doguwa ce sai kun shirya, salon daban yake ina tabbatar muku da hakan. Kunce kunyi kewata ko? To gani na dawo zan gani da gaske anyi kewar ko kuwa dai dad'in baki ne.😅 Gabad'aya labarin fiction bai faru a gaske ba, in yayi kama da naka ko naki to ayi hak'uri rashin sani ne._


_Warning: Ban amince a canja min labari zuwa wata siga daban ba, documents, audio ko a d'ora akan wani blog ba batare da izini na ba, a kiyaye dan Allah._


*001.*


*BAUCHI STATE,*
*MASARAUTAR AZARE KATAGUM.*


*Mafari.*
*1994.*


Dare yayi duhu ya mamaye gari hannun ka baka gani sabida yadda garin yayi duhu matuk'a yayi tsiitt baka jin motsin komai ko ba'a fad'a ba yanayin garin zai tabbatar maka da dare ya tsala. Mata ne guda biyu suke tafiya da sassarfa cikin siririyar hanya mai d'auke da ciyayi da shuke-shuke, sauri suke sosai babu kamar wacce take a gaba ta bayan biye take da ita duk inda ta jefa k'afar ta itama nan take saka ta ta.


Hasken aci balbal suke hango a gaba hakan ya saka ta k'ara kaimi wajan sassarfa har suka iso inda suke gano hasken ta kalli wacce take bayan ta tace, "Dakata a nan." Cikin girmamawa tace, "An gama ranki ya dad'e, ki fito lafiya." Gaba tayi zuwa inda hasken yake da sauri kamar zata kifa domin burin ta ta isa wajan, dutse ne babba a wajan sai yadi kalar ja da aka yane dutsen dashi da kawunan rago a sak'ale anyi ado dasu wasu suna zubar da jini wasu sun fara bushewa wasu kuma sun zama k'ashi.


Zubewa tayi a k'asa tace, "Ta haihu! Ta haifi yara maza har guda uku a lokaci d'aya!" Yadda take fad'ar maganar muryar ta rawa take yi kana ji kasan cikin tashin hankali da d'imauta take. Baza ka d'auka akwai halitta a wajan da take ba sabida yadda wajan yake da duhu sosai aci balbal d'in a farkon wajan take kana shiga ciki babu hasken ta.


"Ha!Ha! Bana fad'a miki daman zata haihu ba?. Mun riga mun ga haka zata haihu kuma y'ay'an zasu girma." Ya fad'a cikin murya mara dad'in sauraro mai bada tsoro da firgita wanda yake sauraron ta. Abin mamakin bata tsorata ba sai sake gyara zaman ta da tayi tace, "Ya zanyi? Bazan iya jurewa hakan ba ko kad'an, ka nema min mafita kaine k'arfin guiwata. In y'ay'an nan suka girma na shiga uku."
"Me kike so a yiwa yaran?, A kashe su? A haukata su? A lalata rayuwar su ta gobe? A juyar da tunanin su? A sace su?. wanne kike so ayi musu a ciki? Ko wanne kike so zamu taimaka miki."


D'aure fuska tayi alamun rashin imani ya d'arsu a zuciyar ta cikin kaukasar murya tace, "Bana so a kashe su; ina so su rayu su d'and'ana irin kalar rayuwar dana tanadar musu, bana so su haukace sabida so nake da hankalin nasu amma su kasa sarrafa shi, bana so a lalata rayuwar su domin da nutsuwar su nake buk'atar su, bana so a sace su; domin a gidan su nake so su tashi inda suna ji suna gani su da gidan su zai bare ya fisu daraja da mahimmaci a cikin sa. Ina so su rayu amma ko wanne su asan abinda za'a saka masa wanda dalilin hakan suna ji suna gani sarautar zata fi k'arfin su nan gaba. Bana son jinin Rabi yayi wani kwakwkwaran motsi sai naso, bana son jinin Rabi ya d'aukaka a duniya, yadda take jin tafi kowa ina so na nuna mata ita ba kowan komai bace face farcen susa a wajena."


Ya kuma sakin dariya mai munin sauraro yace, "ki d'auka wannan an gama, ki jira girman su ko wanne a cikin su zaki ga da kalar dabi'ar da zai tashi, nine nace zanyi in na fad'a bana fasawa sai na tabbatar. Amma da sharaɗi!."
Murya na rawa tace, "Meye sharaɗin?."
"Komai zai faru daga baya babu ruwan mu, aikin mu mun riga munyi in kika ga wani canji to ki tabbatar kin sab'a abinda zan fad'a miki nan gaba."


Farin ciki ya mamaye zuciyar ta tace, Na amince da ko wanne irin sharaɗi, duk wahalar sa, duk qalubalen sa, duk tashin hankalin sa na amince zanyi. Godiya nake, inda kai bazan zubar da hawaye ba ni na sani."
"Tashi kije, abinda kike so zai biyo baya!" ya fad'a a firgice ta mik'e da sauri ta juya ta bar wajan da sassarfa zuciyar ta cike da farin cikin ta samu cikar burinta.


*☆☆☆*
Sarki Dr Nasir Sa'ad Muhammad shine sarki na goma sha uku a masarautar Azare dake cikin garin bauchi a arewacin Nigeria, jika ne wajan Mai martaba sarkin Azare Muhammad Nuhu mahaifin Sarki na goma sha d'aya. Mahaifin sa Sarki Sa'ad shine sarki na goma sha biyu a yankin fulani, bayan shi sai Nasir Sa'ad wanda ya kasance na goma sha uku. Yana da tarin y'an uwa da dama wanda suka had'a da uwa d'aya uba da d'aya da kuma uba d'aya, shi kad'ai Allah ya zab'a a cikin su ya baiwa sarautar Katagum duk da tarin y'an uwa manya da yake da.


Sarki Nasir Sa'ad sarki ne mai ilimi da wayewa a matakin boko yana da matakin PHD a b'angaren addini ba'a cewa komai domin yafi zurfi a wannan b'angaren, shugaba ne mai ilimi da kuma adalci da sanin ya kamata da tausayin talakawan sa ta ko wacce fuska, baya lamuntar zalunci ta ko wanne b'angare ko waye kai ko kuma d'an waye yayi ba dai-dai ba masarauta zata hukunta shi sai dai an b'oye ba'a bari labarin ya bayyana yazo kunnen sa ba.

Yana da yawan taimako da sadaka musmaman ga wanda basu dashi, y'an mata da za'ayi aure babu kayan d'aki yana k'ok'ari wajan yi musu dan daman can mai kud'i ne bada aljihun gwamnati ya dogara ba, Wannan dalilin ya sanya mutanen Azare da kewaye suke matuk'ar k'aunar sa dashi da iyalan sa baki d'aya kowa fatan alkhairi yake masa sabida in alkhairin sa bai same ka ba zai sami wanin ka.


Matan sa uku babbar cikin su itace Fulani Sa'adatu itace uwar gidan sa auren saurayi da budurwa, tun kafin a bashi sarauta ta aure shi suna da yara biyar hud'u mata d'aya namiji wanda ya kasance shine k'arami cikin yaran ta. Mace ce makira a bayyane zata nuna maka duk duniya babu wanda take so sama dakai amma a b'oye tafi kowa cin dunduniyar ka. Burin ta guda d'aya ne tal yadda d'an ta namiji ya kasance k'arami bazai gaji sarautar katagum a wannan lokacin kada wani ya gada a cikin y'ay'an abokan zamanta.


Matar sa ta biyu itace Fulani Rabi'atu y'ar sarki kuma jikar sarki sannan matar sarki, y'a ce a wajan sarkin Kano wanda mahaifin ta ya gaji sarautar a wajan mahaifin sa, Ya aure ta bayan an bashi sarauta ba jimawa.


Mace ce mai izza da k'asaita da nuna zallar iko a kan komai, kai da ka ganta da yanayin maganar ta da yanayin takun ta kasan jinin sarauta ne yake yawo a jikin ta. Fara ce tass kyakykyawa domin ta b'angaren mahaifiyar kyawawa ne sosai. Tana da ilimi a waye take idanun ta sun bud'e kar take kallon kowa domin duk wata harqalla ta gidan sarauta ta santa dan a gidan ta tashi.


Yaran ta hud'u maza uku mace d'aya haihuwar ta uku kacal a duniya domin haihuwar ta ta farko yara uku ta haifa duka maza, bayan su ta sake haifar wani namijin Allah ya yi masa rasuwa daga nan ta haifi mace a wannan haihuwar ta dakatar da haihuwa a cewar ta ta samu abinda take so, domin a ganin ta da tunanin ta haihuwar y'ay'a maza a gidan sarauta shine riba. Yaran ta sune manyan maza a kaf gidan kasancewar wad'an can mata ne kuma sun yi aure nata sune a kan gaba komai za'a yi na sarauta tabbas dasu za'a dama. Ta raba y'ay'an ta da y'an uwan su ta kebence su waje d'aya har ta kai ta kawo da d'aya a cikin su zaiga yaran y'an uwasa mata sai dai su yaran su gane su amma su baza su gane su ba sabida basu san su sosai ba babu zumunci a tsakanin su sam, a ganinta ba daidai suke dasu ba nata daban suke.


Fulani Rabi'atu babban burin ta a rayuwa bai wuce ta kasance babar sarki kuma kakar sarki ba, burin ta d'an ta ya gaji sauratar garin Katagum ya mulke ta yadda ta tsara masa sannan jikan ta ma ya gada. itace zatayi mulkin domin yadda take so komai ya tafi sai abinda tace shiyasa ta zab'i mafi soyuwa da yi mata biyayya a cikin yaran ta, wanda yafi ilimi da kud'i a hannu kamar ba matashi ba, sai dai me?, manyan mazan da suke kasance guda uku sun kasance dukkan su basu da qualities d'in da za'a basu ragamar al'uma amma duk da hakan bata hak'ura ba kullum gani take yaran ta sune zasu gaji sarauta koda basa so, ko da tsiya koda tsiya-tsiya sai hakan ta kasance.


Fulani Rukayya itace matar sa ta uku mace mai sanyin hali wacce bata d'ora ranta abinda wand'an can suka d'orawa kansu ba, y'ay'an ta hud'u itama mata uku namiji guda d'aya tal itama kuma shine k'arami a cikin y'ay'an ta duka manyan mata sunyi aure d'aya ce ta rage a gabanta.


*☆☆☆*
Babban falo ne na isa da girma da kuma k'asaita da alfarma, kana kallon falon kasan na manyan mutane ne masu tak'ama da aji da kuma sarauta, domin kuwa kalar adon da akayi masa da kalar kujerun cikin sa kana kallon sa kasan bana talaka bane sai na mai arzuk'i arzuk'in ma irin na y'ay'an masarauta.


A zaune take ta d'ora k'afar ta akan pillow mata guda biyu suna matsa mata k'afafun ta a hankali hannun rik'e da waya tana dannawa hankalin ta a kwance.
Fara ce sosai mai kyau kana ganin ta kasan ta manyan ta amma kasancewar kud'i da hutu bai nuna ba in ka ganta baza ka d'auka tana da manyan yara ba, mulki,k'asaita, izza, ko in kula ya ratsa jikin ta sosai dan ko yanayin da take danna wayar da izza take yin ta.


Maza uku ne masu kama sak da juna samari matasa masu jini a jika suka shigo cikin falon nata da sallama. A k'alla zasu yi shekara ashirin da tara zuwa da talatin da haihuwa dogaye kyawawa masu kama da mahaifiyar su masu zagayayyen gashi bak'i a fuskar su. Farare ne dukkan su kana kallon su kaga y'an uku domin kamar da suke ta b'aci musamman guda biyu a cikin su babu abinda ya banbanta su sai adon gemu, dukkan su manyan kaya ne a jikin su irin na sarauta sun d'ora riga mai zanen sarauta a sama ko wanne da kalar tasa sunyi kyau sun amshi jikin su sosai duk da yanayin fuskar ko wannen su ya banbanta.


Zubewa bayin gaban ta suke suna kwasar gaisuwa amma babu wanda ya kula su a cikin su k'asa suka zauna kusa da k'afafun mahaifiyar su suka gaishe ta a tare ta amsa tana kallon su, Murmushi take tana kallon su alfahari yana sake mamaye zuciyar ta, ko a wannan b'angaren tasan ta yiwa abokan zaman ta fintinkau itace da gida, itace da katagum, ta kalli bayin nata sai jikin su ya fara k'yarma suka mik'e suka fita da sauri domin yanayin kallon da tayi musu sun fahimci me take nufi.


"Tun d'azu na aika kuzo dukkan ku sai yanzu kuka ga damar fitowa?." Wanda yake danna waya ne ya d'ago ya kalle ta yace, "Allah ya wuci zuciyar ki, Lokacin ina wanka ne." Hararar sa tayi jin abinda yace ta gane waye a cikin su tace, "kodai kana waya da y'an matan ka?." Baice komai ba ya d'auke kansa ya kalli k'asa.


Girgiza kai tayi kafin ta kalli na gefen ta tace, "Kai nasan daman indai kiran yazo wajan ka zaka iso kai bana jin ka Hydar" ta fad'a tana kallon sa.


Asad ta kalla wanda yake kallon k'asa yana wasa da gashin carpet d'in falon da farin hannun sa mai d'auke da azurfa kalar golden ta haska hannun sa sosai, shi kansa hannun nasa abin kallo ne. Tasan kome za'ayi bazai furta komai ba kallo ma bazai kalle su ba balle magana. "Asad!." D'ago idanu yayi ya kalle ta amma bai amsa ba, ta san bazai amsa hakan ya saka tace, "meyasa baka je zaman fada ba d'azu?."


Kansa ya mayar k'asa baice komai ba tace, "ba magana nake maka bane?, meyasa baka je fada ba matsayin ka na magajin wannan gida ko hukuncin mai martaba bai zo kunnen ka bane?."
"Allah yaja da ranki Mama ni banga dalilin da zai saka kina kiran sa magaji ba bayan nine babba a cikin mu, baki tab'a kira na magaji ba meyasa sai shi?" Aliyu ya fad'a yana kallon k'asa da alama ya gaji da jure yawan kiran sa da magaji da take yi.


Kallon sa tayi tace, "A hakan zaka zama magajin sarauta Aliyu? A hakan zaka mulki katagum?." Shiru yayi bai amsa ba ta dawo da kallon ta ga Asad tace, "Ko baza kayi magana ba nasan kana ji na Asad, duk wani abun da kake ji dashi a kanka ka ajjiye shi ka dinga zama kusa da mahaifin ka kana fahimtar yadda tsarin sarauta yake, kai kad'ai ne damar da nake da ita na zama mahaifiyar sarki kasan shine burina ya zamar maka dole ka cika min ita."


Rausayar da kansa yayi cikin muryar sa da bata fita sosai sabida taushin ta yace, "Allah yaja zamanin ki Mama, Bana so!."
"Dole kaso tunda ni ina so, kai kad'ai ne burina domin cikin y'an uwan ka gasu a zaune duk ka fisu quality, kai mahaifin ka ya zab'a har ya furta kai zai bawa kujerar sa sabida kullum k'arfin sa k'arewa yake dole kayi abinda nake so Asad koda kai baka so."


Runtse idanun sa yayi ya sake mayar da idanun sa k'asa Aliyu da yake ji kamar ya shak'e wuyan Asad sabida bak'in ciki yace, "Mama wai meye laifina ne ni da baza'a bani ragamar rik'e magajin masarautar katagum bane?, Asad baya so ni ina so meyasa baza'a bani ba ni?" Ya fad'a a tausahe duk da ransa a b'ace yake bai bari yayi mata magana da k'arfi ba sabida girman biyayya.


"Sabida baka dace ba Aliyu, baka da wadattacen ilimin addini, banzayen dabi'un ka na neman matan tsiya waye zai baka ragamar al'uma a hannun ka?. har bayin gidan nan baka bari ba badan na saka an binne zancen baiwar da ka lalata ba na saka a mayar da ita k'auye da yanzu mahaifin ka bai hukunta ka ba?." Shiru yayi bai amsa ba ta ja tsaki ta nuna shi da yatsa tace, "kar ina maganar sarautar gidan nan ka sake saka min baka, baka dace ba ba kuma zaka dace ba Aliyu. Asad shine magaji shine zai gaji mahaifin ku shine zai mulki masarautar katagum ba kai ba!."


Ran Aliyu ya kai k'ololuwa wajan b'aci ya cize bakin sa yace, "in kinyi min izini zan iya tafiya?." Mama ta bishi da kallo tace, "Tashi ka bani waje." Ba musu ya mik'e yace, "A huta lafiya" ya fad'a yana fita daga falon zuciyar sa a cushe.
Dawo da kallon ta tayi ga Asad tace, "kaji abinda nace maka ko?." D'aga kai yayi alamun eh tace, "tashi kaje anjima zan neme ka." Mik'ewa tsaye yayi baice komai ba ya fita aka bar Hydar a zaune kusa da ita.


Hydar ta kalla ta ga yana ta murmushi itama tayi murmushin tace, "Hydar Allah ya baka lafiya, bana son yawan ciwon nan naka ko kad'an" Murmushi yayi yace, "Amin Mama. Amma Allah yaja da ranki sai nake ganin da ki k'yale Deaf da batun sarautar nan baya so." D'aure fuska tayi tace, "ka daina kiran sa da kurma na fad'a maka rashin magana yake da ita amma shi ba kurma bane ba, sarauta kuma sai yayi da izinin Allah." Yace, "Allah ya wuci zuciyar ki, ina neman afuwa."


Numfashi ta sauke ta koma ta jingina da kujera tana kad'a k'afar ta, babban burin ta a rayuwar ta a yanzu shine Asad ya gaji sarautar masarautar katagum kamar yadda mahaifin sa yake son hakan, bata so sarautar ta fita daga gidan domin matuk'ar ta bar gidan zata cigaba da zaga dangin mahaifin sa ne maimakon y'ay'an ta da jikokin ta, "dole ma Asad ya karb'i mulkin nan koda baya so, tunda har mahaifinsa ya furta shi zai bawa mulkin nan komai zai tafi yadda na tsara."


Asad koda ya fita fadar cikin gida ya nufa domin amsa kiran mahaifin sa, tafiya yake a nutse kana kallon sa izza da k'asaita da tak'ama ta gama ratsa ko wanne b'angare na jikin sa, kasancewar sa mai nutsuwa sai akayi sa'a aka had'a nutsuwa da sarauta sai suka bada kalar izza ta musamman wacce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login