Showing 33001 words to 36000 words out of 92772 words

Chapter 12 - KWANTAN BAUNA BOOK 1 COMPLETE by Nana haleema.txt

20 Jul 2024

17683

ya cigaba da tafiya tana bayan sa, yana zuwa ya shiga ita kuma tana tsaya a bakin k'ofa ya shiga da sallama. K'annen sa maza da y'an matan ta guda biyu Khaleesat da Juwairiyya ya gani suna ganin sa kowa ya mik'e suka gaishe shi ya amsa da murmushi kana yace, "kun b'oye." Mamaki suke jin ya musu magana Khaleesat tace, "naje duba ka d'azu kana bacci." Kai ya d'aga kai kafin Juwairiyya tace, "Hajiyan tace ka shiga ciki."


Kai ya kuma d'aga ya shiga ya same ta a falon ta ita kad'ai tana ganin sa ta mik'e tana cewa, "Asad wallahi ban baka komai dan na cuce ka ba, ina kallon ka kamar d'an dana haifa akan me zan kashe ka kona kwantar da kai ciwo....? kayi hak'uri ban san waye ba" ta fad'a kamar zatayi kuka.


"Babu komai Hajiya, na amince Hajiya tamkar Mamana."
"In kai ka amince mahaifiyar ka baza ta amince ba Asad, gani take kashe ka zanyi." Kai ya girgiza yace, "babu komai" ya furta da murmushi yana kallon ta kafin tace, "na gode Asad, Allah ya baka lafiya. Zan cigaba da aiko maka da ganye kamar yadda nasan kana so, wallahi da zuciya d'aya nake maka badan wani abun ba."


"Na gode." Tace, "Zaka iya tafiya." Baice komai ba ya juya zai tafi tabi bayan sa da kallo tana murmushi har ya fita kafin ta gyara tsayuwar ta tace, "Yanzu aka fara wasan Rabi'atu, yanzu kafcen ya fara, mu jira muga ni dake waye zaiyi nasara wa za'a bawa lambar girmamawa.....? Dan ni Sa'adatu bazan tab'a barin Asad ba sai naga bayan sa!" tayi murmushi ta shafa fuskarta ta shiga d'aki zuciyar ta kar.........


*KWANTAN ƁAUNA*
FitattuBiyar 2023


©️ *Nana Haleema.*


*Book 1*
*010.*


Asad lokacin da ya koma d'akin sa gaban mirror ya tsaya yana kallon kansa fassarar mafarkin da mahaifin yayi masa yana dawo masa cikin kansa tiryan-tiryan, kenan akwai mace da zata shigo rayuwar sa matsayin mata? Wacece ita?, a ina take Allah ya had'a su tun a mafarki?. Shin ita tana mafarkin sane ko batayi?. Sam baya so wata mace ta shigo rayuwar sa ko kad'an sabida shi kad'ai yasan illar dake tattare da hakan.


Lumshe idanun sa yayi tuno Jidda ce zab'in Mama ya bud'e idanun a zuciyar sa yana tambayar kansa kodai Jiddan itace yarinyar mafarkin...? Numfashi ya sauke a hankali kammanin ta suke bayyana a idanun sa kamar lokacin yake mafarkin.


Wara idanun sa yayi yana hango zubin ta da kammanin ta amma basa fita tarrr amma yana iya hango ta a idanun sa kamar almara, agogo ya kalla yaga yamma tayi sosai bazai yu yaje Abuja ya dawo a ranar ba da babu abinda zai hana shi zuwa Abuja wajan abokin sa Zaid ya zana masa fuskar da yake gani a mafarki ko zai iya gane ta in ya ganta, da ace yana kano ma a lokacin zai tafi amma yasan yana Abuja.. Haka yayi ta zaune da wannan tunanin kafin ya tashi ya d'auki makullin mota ya fita.


*☆☆☆*


"Dan Allah Malam ka bani koda duba d'aya ne a kud'in na siyo mata kayan marmari ta sha bata iya cin abinci, koda tana ci ma ba'a son mai karaya tana cin abu mai nauyi sabida zagawa band'aki" Umma ta fad'a tana kallon Baba da yake tsaye a cikin d'akin.
Baba ya gyara zaman hula yace, "Kinga ni babu komai a jikina kud'in ma da aka bani na adana su sai auren ta yazo sai ayi amfani dasu, ga shinkafa da manja nan ai nasan tana san cin abinci da manja shiyasa na saka aka dafa mata."
"Yanzu Malam mai karayar ce zata ci shinkafa da manja? Kazar gida fa ita ake so masu karaya suci sabida tabi jikin su."
"To ba'a haifo ta inda zata ci kazar ba in baza ta ci shinkafar ba ta hak'ura."
"Amma Malam kud'in da aka bayar fa duk nata ne tunda itace take jinya."


A fusace yace, "Amma ji kikayi nace ai na adana mata sai lokacin bikin ta ko? Ko saka su a gaba nayi naci banza da wofi dasu?." Jin yadda yake magana Rauda dake kwance tace, "Umma a bar shi zanci shinkafar." Umma tace, "ta ina zaki ci shinkafa Rauda?, baki san ba'a san mai karaya ya dinga cin abu mai nauyi ba sabida yawon band'aki?. Dan Allah malam ka bani koda naira d'ari biyar ce."


Tsaki yayi ya saka hannu a aljihu ya d'auko naira d'ari biyu yace, "gashi nan a siyo mata." Ba yadda Umma ta iya haka ta karb'a ta kalli Khairi da Khalil da suke gefe tace, "Khairi ina za'a samo mata kankana da lemon zak'i tasha?." Khairi tace, "Umma wajan asibitin nan akwai amma da gani zaiyi tsada tunda kinga asibitin manya ne."
"Jeki dai ki duba mana ko za'a samu" ta fad'a tana bata kud'in ba musu ta karb'a ta tafi.


Tana fitowa wajan asibitin kuwa suna nan masu kayan zak'in ta tsallako ta nufo su tunda ta tawo kowa ya tashi dan daman an san siyayya za'ayi ta k'arasa wajan d'aya tace, "Sannu Baba." Yayi murmushi yace, "yauwa y'ata me za'a baki?."
"Kankana nake so ta naira d'ari lemo ma na d'ari" ta fad'a tana mik'a masa kud'in. Kallon ta yayi ya kalli kud'in ya kalli asibitin da ta fito sai ta girgiza kai yace, "yarinya babu na kud'in sai dai na baki lemo guda biyu ko wanne naira dari."


Wara idanu tayi tace, "a unguwar mu naira ashriin-ashirin ne, bar shi bara na tambayi na gaba." Koda taje na gaban ma shima haka sukayi ta je na kusa dashi shi ce mata ma yayi babu ta tsaya cak kawai tana kallon su cikin rashin sanin abin yi.


Mota ce ta faka a kusa da ita aka sauke glass dai-dai lokacin da take cewa, "Yayata aka kwantar a nan kuma bata iya cin abinci dan Allah ku taimaka min ku bani kankana da lemo na d'ari biyu ita kad'ai ce damu itama dak'yar Baba ya bayar."
"Dallah malama bamu dana kud'in ki ki wuce ki bawa mutane waje, y'ar aiki kawai" daya daga cikin su ya fad'a ta juyo idanun ta ya fad'a kan Asad da yake kallon su mai siyar da Apple yana masa magana ma amma baiji ba.


Gaban Asad ya fad'i haka kawai ya tsaya yana kallon fuskar ta kamar dai yana so ya san mai irin ta amma bai a ina ba, ya motsa bakin sa ya kalli wanda yake masa magana yace, "ku bata komai." Jiki na rawa yace, "an gama alhaji" ya fad'a yana komawa ya fara had'a mata kaya da yawa. Murmushi tayi tace, "na gode sosai Yaya Allah ya saka da alkhairi, Yayata ce aka kwantar da ita a nan bata iya cin komai akace nazo na siyo mata kuma d'ari biyun kenan damu itama dak'yar Baba ya bayar" ta fad'a tana kallon sa.


Kallon ta shima yake jin tana magana kamar ta had'd'iye radio ba commer babu full stop zuba kawai take yi, kallon asibitin yayi ya dawo da kallon sa gare ta ganin asibitin da suke zuwa ne kuma wanda yake k'ark'ashin kulawar Mama to meya kawo yarinya kamar wannan cikin sa bayan yasan hundred percent na kud'i ne kud'i ma kuma ba kad'an ba..?. A lokacin aka kawo mata manyan ledodoji guda uku an cika su da kayan marmari da murna ta kalli ledar lokacin da yake karb'ar tasa ta apple tace, "na gode Yaya, dan Allah ya sunan ka?."


Sai ya samu kansa da yin murmushi a hankali yace, "Aliyu."
"Na gode Yaya Aliyu, kuma wallahi kana da kyau kamar mutanen nan na tv da nake gani a gidan Yaya Ummi, kuma gashi kana jin hausa, dan Allah d'an garin nan ne kai?." Shi dai Asad kallon ikon Allah kawai yake ganin yarinya mai shegen surutu kamar wata y'ar tsana.
Sai kuma tace, "Umma zata min fad'a tace ina na samo kud'i na siyo wannan zata kuma ce rok'ar ka nayi."


Shi kam ya gaji da surutun ta ya d'aga glass sama bai ce komai ba yaja motar sa ya tafi ta bishi da kallo ta kinkimi ledojin dak'yar ta shiga asibitin. Tana tafiya tana hutawa har ta shiga d'akin ganin ta da leda har uku Umma tace, "Ke bashi kika karb'o ne?."
Tana haki ta ajjiye tace, "Wani ne ya siya min ganin suna tayi min wulaƙanci sunce baza su bani duka a d'ari biyu ba wai sai dai lemo guda biyu d'ari biyu, shine ya siya min duka. Umma baki ganshi ba mai kyau kamar baya jin hausa ya kuma cemin sunan sa Aliyu."


"Ummulkhairi yaushe zakiyi hankali ne wai ke? Baki da girma sam ke sai na jikin ki? Akan me zaki karb'i abin hannun wanda baki sani ba?, rok'on sa kika yi ko?."
"Wallahi Umma ban rok'e sa ba shine fa ya bani, kuma ban tambaya ba muje a tambayi masu siyarwar." Baba da yake sauraren su ya bud'e leda d'aya ya d'auki apple ya ci yana lumshe ido yace, "ni nasan halin ki baza ki tambaya ba, d'auki ki sha kema ki dandali arzuk'i." Umma ta kalle shi kafin ta girgiza kai ta tashi ta d'auki wuk'a ta yankawa Rauda kankana da gwanda da tufa d'in ta k'arasa kusa da ita tana bata tana ci a hankali.


Sai da Baba ya cika cikin sa dam da kayan marmari ya goge baki yace, "oh yarinyar nan dai ana ta samun alkhairi tunda kika kwanta a asibitin nan, a haka ma fa wai dan Anas baya nan ai da nasan kullum sai munci kaji wallahi. Kai Allah ya dawo dashi kafin a sallame mu." Babu wanda ya tanka ya mik'e yace, "to zan koma Rahma zata kawo muku abinci inda wani abun sai amin waya."
"Basai an kawo komai bama wannan zai isa muci."
"To Khalil, Ummulkhairi muje, sai da safen ku."
"Allah ya tashe mu lafiya."


Bayan fitar su Umma tace, "tsabar san kud'i ya dinga fatan wai kar a sallame ki har sai wani ya dawo kawai dan a basa kud'i, Allah ya kyauta ni ban san irin zuciyar baban ku ba nikam ba haka nake ba wallahi." Rauda tana ji bata ce komai ba idanun ta a rufe tana tauna kankana.


*☆☆☆*
Asad haka ya gama zagayen sa a gari bai koma gida ba sai bayan sallar i'sha sai da ya shiga wajan Mama yaga Hydar sannan ya wuce d'aki yana shiga d'akin Ummulkhairi ta fad'o masa a rai ya murmusa tuno surutun ta baice komai ba ya shiga band'aki yayi wanka tare da alwala ya fito yayi shafa'i da wutur ya jima yana addu'a sannan ya kwanta.


Abu yaji kamar yana shiga jikin sa ya tashi ya yaye zanin gadon da yake shinfid'e a kan gadon ya dawo zallar katifa yana kallon tsurar katifar amma baiga komai ba, mayarwa yayi ya yafa zanin gadon ya koma ya kwanta ya rasa meyasa yake jin hakan duk sanda ya kwanta a kan gadon sa. Ya jima kafin bacci ya d'auke shi yana juyi yana jin abu na shiga jinin sa kamar tiriri ne yake fitowa daga katifar yana shiga jinin sa.


K'arfe uku na dare ya tashi kamar ko yaushe yayi alwala ya tayar da sallah, ya jima yana sallah sai da assalatu ya rage mintina arba'in sannan ya fara addu'a yana rok'on Allah har akayi kiran Asuba ya fito daga d'akin. Masallaci ya shiga akayi sallah yabi mai martaba har cikin b'angaren sa suka gaisa sannan ya shiga wajan Mama ya gaishe ta ya duba jikin Hydar sannan ya fita da niyar komawa d'akin sa.


Kamar giftarwa mutum ya gani da sauri ya tsaya cak ya kalli dan lungun da yaga an bi da sauri, ya taka a hankali ya k'arasa wajan amma duhun asuba bai ga kowa ba ya shiga yana takawa a hankali yana bin wajan haka kawai yaji bai yadda da wajan ba, a hankali ya jiyo tashin murya ana fad'in, "na saka, na saka dak'yar" sai kuma ya daina jiyo maganar bai ga kuma kowa ba. _me aka saka? Wa kuma aka sakawa?._ ya tambayi zuciyar sa amma babu mai bashi amsa ya koma da baya sai kuma ya sake kallon wajan amma babu kowa.


D'akin sa ya wuce ya tarar da Aliyu a zaune da alama dawowar sa kenan ma gidan dan gashi nan da kayan jiya da daddare ga warin sigari na tashi a falon, kallon sa yayi ya girgiza kai kawai ya shiga d'akin sa ya d'auki alkur'ani ya karanta suruti yasin yayi azkar sannan ya kwanta.
_na saka, na saka dak'yar._ abinda ya dawo masa zuciyar ya juya yana tunanin abinda aka saka ake cewa an saka dak'yar da wannan tunanin bacci ya d'auke shi.


_k'atuwar kujera ce ta tsakiya ita bata sauka ba kuma bata sama k'asa wuta ce gefe namun daji ne ko wanne ya bud'e bakin sa, Asad ne a kan kujerar saura kiris ya fad'i k'asa in ya fad'a wuta ce in kuma ya zauna a kai namun dajin nan sai sun cinye shi, ya rasa yadda zaiyi gashi babu kowa a wajan. k'ato kuma k'osasshen zaki ya kawo masa cizo Asad ya runtse idanun sa gab da cize shi yaji kamar anyi sama dashi an d'auke shi daga kan kujerar. Fad'a sosai yaga yarinyar sun fara ita da namun dajin nan suna k'ok'arin cizon sa tana tarewa duk sun cize mata jiki cikin d'aga murya tace, "Ka kashe wutar kai kuma! Ka kashe ta!! Kar ka bar ko kad'an!!." Ba musu ya d'ebi k'asa yana zubawa wutar tana sake yin sama kamar zata kamo hannun sa yana sake zubawa a hankali take mutuwa zuwa lokacin ta kusa k'arar da namun dajin da take fad'a dasu. Lokacin da ya gama kashe wutar ya hango wani k'atoton maciji ta bayan zai sare ta ya yayi tsalle ya janye ta ya tura ta baya ya fillewa macijin kai da takobin da bai san daga ina take ba ya ganta kawai a hannun sa. Kallon tarin namun dajin da ta kashe yake yi ya kalle ta yaga wasu sun yakushe ta a fuska wasu a hannu har da cizo a hannun ta, da sauri ya rik'e hannun ta yana kallon cizon ta fizge hannun ta tace, "Meyasa baka son nemawa kanka kariya ne? Meyasa kake yadda da kowa? A halin da kake ciki bada kowa zaka amince ba..... Kai sarki ne ya zama dole ka kula....in ba haka ba za'a ga bayan ka cikin sauk'i....!." Asad da yake kallon ta yace, "Wacece ke? Meyasa kike son ki taimake ni? Meyasa kika tsaya suka cutar dake sabida ni? Ban san ki ba a ina kike?." Kai take girgizawa tana yin baya tace, "zaka sanni amma kafin lokacin yazo za'a jima, za'a sha qalubale kafin nazo rayuwar ka, kayi abinda nace, ka tashi tsaye ka bar batun zuwa na ka yak'e su kafin su kashe min kai......" zai kuma magana yaji an rik'e hannun sa ta baya yana juyawa yaga Mama tace, "Zo mu tafi Asad, baza ka bita ba zo mu tafi." Kallon ta yake tana sake yi masa nisa Mama na jan sa yana sake waigawa yana kallon ta daidai lokacin da ta juyo ta ta masa alamun jinjina._


A firgice Asad ya sake tashi yana kallon jikin sa amma bai ga wani tabo ko alamun wahala ba kamar a mafarkin, kammanin ta yake so ya tuna amma ina ya kasa ya runtse idanun sa ya nutsu ya tsayar da kwakwalwar sa waje d'aya cak a hankali yake ganin kammanin suna washewa a idanun sa, iya idanun zuwa goshin yake iya gani sujjud mark d'in dake goshin ta bak'i shi yake sake gani a idanun sa sai idanun ta. So yake ya tuna ta gabad'aya amma ya kasa iya abinda yake gani kenan ya daki kansa yace, "Why?."


Mik'ewa tsaye yayi ya tsaya a jikin mirror yana kallon kansa a madubin muryar ta nayi masa amsa kuwa a kunnen sa, sosai yaji ya gane maganar ta rasss kamar ma ya tab'a jin mai irin ta amma ya manta a ina. "Meyasa a koda yaushe take taimako na? Wacece ita?,A ina take? Yaushe zata zo inda nake? Meyasa Mama ta janye ni daga gare ta a mafarkin...?" K'aramin tsaki yaja ya d'auki wayar sa yana dannawa jim kad'an ya ajjiye ya shiga band'aki.


Bai jima ba ya fito yana fitowa ya shirya cikin shigar sa ta manyan kaya ya saka d'auki key d'in mota da wayar sa ya fita, direct airport d'in Bauchi wuce yana tsayawa ya bayar da mota ajiya ya shiga ciki ya hau jirgin k'arfe sha d'aya na safe zuwa Abuja. Mintina kad'an suka kawo shi Abuja yana sauka ya d'auki waya yana kiran wajan wanda yazo, ba jimawa aka zo da mota aka d'auke shi suka wuce.


Har cikin gidan aka shiga dashi aka masa iso har cikin gidan kafin a k'yale shi ya shiga shi kad'ai, babban falo ne katafare ma kuwa yana shiga ya hango Zaid a zaune daga shi sai wando three quarter sai bodyhop a jikin sa yan zaune yana danna laptop, ganin Asad ya shigo ya saka shi jan tsaki yace, "Ina jin dai bashi kake bina ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login