Showing 60001 words to 63000 words out of 92772 words

Chapter 21 - KWANTAN BAUNA BOOK 1 COMPLETE by Nana haleema.txt

20 Jul 2024

17689

bata dawo ba sai biyar sannan Khairi ta shigo ita da Khalil da Sammani, bayan shigowar su ba jima Habiba ta shigo tunda taga fuskar ta tana ba'a yi nasara ba. Kusa da ita ta zauna ta kalle ta tace, "Wallahi duk yadda naso ganin Asad abin ya gagara, amma kiyi hak'uri gobe zan same shi in Allah ya yarda." Idanun Rauda yayi rau-rau zatayi kuka Habiba tace, "kiyi hak'uri dan Allah, haba komai zai tafi daidai in Allah ya amince ki yadda dani wallahi zan masa magana. Kamar ba ke ba kinbi kin rud'e keda na sanki da dakakkiyar zuciya wacce babu tsoro a cikin ta."


Kai ta girgiza tace, "Habiba wannan fad'an yafi k'arfina, bawai ina jin tsoron saba bane ina jin tsoron abinda zaiyi min ne Habiba."
"In sha Allah babu abinda zai miki."
"Na gode Habiba." Habiba ta mik'e tace, "Kar ki damu zan neme shi gobe in Allah ya amince."
"Na gode" ta furta a hankali daga haka sukayi sallama ta tafi.


Fitar ta ba jimawa Umma ta dawo su ma su Rahma suka dawo, bayan anyi sallar magriba Baba ya dawo bayan yaci abinci ya shigo tsakar gidan ya zauna ya kalli Rauda yace, "Rauda." Tace, "Na'am Baba."
"D'azu Anas ya kira ni ya sanar dani tafiya ta taso masa ta gaggawa bai samu yayi magana da likitan naki ba, amma ba jimawa zaiyi ba da zarar ya dawo za'ayi komai a gama. Ya aiko da waya yace dan Allah a baki yana so ku dinga magana na kuma karb'a, gata" ya fad'a yana mik'a mata ledar Khairi da take kusa dashi ta karb'a ta mik'a mata.


Umma ta kalli Baba ta kasa jure abinda take ranta tace, "Malam wai ka bawa yaron nan auren Rauda ne?." Ya kama k'ugu yace, "Me yasa kika tambaya?."
"Sabida naga kana karb'ar hannun sa da yawa, tsakani da Allah bai kamata ba a dinga karb'ar kud'in yaron nan ko abin hannun sa ba tunda ba'a yi auren su ba, ko maganar aure fa bata shiga tsakanin su ba."


Baba yace, "to fad'a min ke kika haife ta, dad'in ta nima dani aka haife ta ba ke kad'ai kika kawo ta duniya ba. Na riga na bashi auren ta koda bana raye shi zata aura ba wani ba, ko ban isa bane ba?" Ya fad'a yana kallon Umma. Umma bata kuma cewa komai ba ta kawar da kai yaja tsaki ya fita.


Rauda tunda aka bata wayar ta rik'e a hannun ta ko bud'ewa ta kasa yi sabida ba wannan ne a zuciyar ta ba abinda yake zuciyar ta daban wannan daban, sai da suka shiga d'aki zasu kwanta sannan Khairi ta bud'e wayar a kwalin ta ta ciro ta kunna har da sim card a kai, Khairi ta kalle ta taga ba ita take kallo ba tace, "Anty Rauda keda kike da burin rik'e waya yau Allah ya cika miki burin ki amma ban ga kina farin ciki ba."


Umma tace, "ta yaya zatayi farin ciki ana zubar mata k'ima wajan saurayi ana karb'ar komai daga hannun sa?, ai farin ciki ba nata ba." Rauda ta kalli wayar hannun Khairi ta ganta mai kyau babba ga bayan ta nan da logo d'in Samsung. D'auke kai tayi ta kwanta kawai bata ce komai ba domin ita ba wannan ne yake damun ta ba.


*☆☆☆*


Asad kuwa da ya bar gida gidan su Jidda ya tafi ya riga ya cewa Mama zashi baya son sab'a alqawari a rayuwar sa musmman ma maganar Mama. Kasancewar gidan sa ba bak'on sa bane Mama tana aiko shi wani lokacin har cikin gidan ya ajjiye motar.
Fita yayi daga motar ya shiga cikin gidan da sallama ya samu falon babu koma sai k'anwar Jidda mai suna Eman.


Ganin sa ta saka tayi murmushi tace, "Yaya Aliyu ina wuni."
"Lafiya, Ina Mum?."
"Tana sama bara na fad'a mata" ta fad'a tana hawa sama. Bai zauna ba ya tsaya a tsaye kafin ta lek'o tace, "Tace ka hayo." Ba musu ya k'arasa stairs d'in ya hau saman a nutse ba tare da wata fargaba ba. A babban falo ya tarar dasu ita da Jidda a zaune ganin sa ya saka Jidda mik'ewa ta k'araso gare shi da niyar hugging d'in sa.


Baya yayi yana kallon ta ta k'asan ido, sanye take da riga da wando yan kanti kanta babu d'ankwali gashin ta ya sauka har kafad'a tayi kyau kamar baturiya, ganin kallon da yayi mata sai gaban ta ya fad'i ta kauce ya k'arasa ya zauna kana yace, "Mum ina wuni."
"Lafiya lau Aliyu, Ya Maman?."
"Lafiya lau" ya furta a tak'aice bai kuma cewa komai ba.


Jin shiru ya saka Mum ta kalle shi dan tasan Aliyu baya wannan dabi'ar in yazo gidan da tuni ya rungume Jidda sun koma gefe suna hirar su tace, "Aliyu kayi shiru yau kamar ba kai ba."
"Asad!" Ya furta a tak'aice bai kalli Mum d'in ba. Jin abinda yace ya saka Mum da Jidda suka kalli Juna Mum ta d'aga mata gira suna murmushi Mum tace, "Au daman Asad ne ka barni ina ta kiran ka da Aliyu?." Baice komai ba itama bata damu yace ba dan tasan bazai ce ba ta kalli jidda tace, "Jeki ki kawo masa abin tab'awa mana kin tsaya kina kallon sa." Da sauri ta juya ta sauka Mum tayi murmushi tana kallon sa tace, "nidai nayi mamaki nasan Aliyu baya irin wannan bakuntar a gidan nan."


In table d'in dake gaban sa ya amsa to tabbas shima ya bata amsa sai ma kawar da kansa gefe da yayi yana jin sa a takure, bata damu ba dan tasna halin sa daman a lokacin Rauda ta dawo da tray a hannun ta ta ajjiye masa ta zauna a gefen sa Mum ta mik'e ta basu waje. Suna zaune shiru babu mai magana zuciyar sa ta tafi tunanin kenan daman ta saba hugging d'in Aliyu duk wanda yazo tunda gashi da ta ganshi ta d'auka shine har ta nufo shi da niyar hugging d'in sa. Cize baki yayi Allah ya sani baya son yaga wani ya rabi abinda aka ce nasa ne indai har da gaske nasa d'in ne baya so yaga wani abun ya rabe shi, baya son hakan sam.


"My Asad" ta furta a hankali tana kallon sa. Bai kalle ta ba ya sauke ajiyar zuciya yace, "Zaki iya d'aukar wayar ki?" Ya fad'a da harshen laranci. Kallon sa tayi alamun bata gane ba tace, "Bana jin Arabic." Yamutsa fuska yayi yace, "Take your phone."
"Okay." ta furta tana d'aukar wayar ta. Sai kuma ya tsaya kallon wayar tasa tunawa da yayi bashi ma fa da number ta balle suyi chart ya fad'a mata abinda ya kawo shi.
D'an k'aramin tsaki yaja ya ajjiye wayar kamar zai magana sai kuma ya fasa.


Sun d'an jima a haka kafin ya mik'e ta mik'e itama tana kallon sa yace, "my regard to Mum" yana furtawa ya sauka daga saman gabad'aya bai kuma kallon ta ba balle ta saka ran magana ko wani abun. K'ugu ta kama tana kallon sa tana fad'in, "Lallai ma wannan gayen ya raina min wayo da hankali, shikenan har anzo zancen an tafi?, wacce irin izza da k'asaita yake ji da ita har haka?."


Mum da taga saukar sa take jin abinda take cewa tace, "D'an sarki ne fa, jikin sarki ne, shine yake niyar zama sarki. Wacce izza kike so ki gani a tare dashi in ba wannan ba?." Ta kalli Mum tace, "Amma Mum tunda fa ya zauna bai ce min komai ba haka za'a yi auren?." Dariya Mum tayi tace, "Sai aka ce miki haka zamu bar shi?, zamu sark'afo wuyan sa ta yadda ko uwar sa Rabi'atu sai dai ta sallama miki shi. Duk wannan kurmancin nasan zai shigo hannu ne sai ya zamar miki kamar rakumi da akala wallahi, barni dashi tunda har ya fara zuwa gidan nan da niyar zuwa wajan ki ai zance ya k'are duk da dai nasan itace ta turo shi."


Jidda tace, "Amma Mum ya raina min wayo wallahi." Mum ta dafa ta tace, "k'yale ni dashi Jidda barshi ya shigo hannu tukunna, da zarar ya shigo hannu to wannan kuma lokacin mu ne." Jidda ta tab'e baki ta shiga d'akin ta duk ranta a jagule.


Shi kam Asad ya kasa fassara yanayin da yake jin zuciyar sa haka ya tuk'a motar zuwa gida ransa duk ya b'aci sam baya son auren Jidda amma babu yadda zai iya Mama tace dole sai ya aure ta. Babban abinda yafi b'ata masa rai game da ita ya lura tana da kusanci da maza sosai wayewar ta tayi mata yawa shi kuma Allah ya sani irin matan nan basa cikin tsarin sa ko kusa.
Ko wajan Mama bai shiga ba ya shiga d'akin sa ya zauna ya kunna TV yana kallo.


K'aramin tsaki yaja ya kashe TV ya hard'e hannayen sa waje guda, yana son barin Nigeria ko umra ce yaje ya dawo amma zuciyar sa tak'i k'arfafa masa guiwa a kan hakan, ya rasa abinda yake damun zuciyar sa bata tuna masa komai sai yarinyar mafarkin sa da kuma yarinyar da Hydar ya buge. Tsaki ya kuma yi ya jingina da kujera zuciyar sa nayi masa zillo akan abinda bai kai ya kawo ba yake jin d'aci da suka a cikin ta. Mik'ewa tsaye yayi ya kashe hasken d'akin gabad'aya sannan ya shiga band'aki.


Washe gari.


Tunda Rauda ta tashi take jin bata san zaman gidan gabad'aya sabida gani take kamar za'a zo a d'auke ta a kaiwa Aliyu ita, ko kuma a yiwa yan gidan su wani abun. zaman gidan yak'i mata dad'i komai nata sanyaye take yin sa har magana bata iyawa sosai. Umma na lura da ita bata tanka mata ba itama kuma bata ce ga abinda yake damun ta ba.


K'arar waya taji a kusa da ita abin ka da ba'a saba ba sai ta manta an bata waya sai da ta katse aka kuma kira sannan ta kalli gefen ta taga ANAS a rubuce a kan screen d'in wayar. Numfashi ta sauke ta jawo wayar tana kallo tana tunanin ta yadda zata d'auka dan bata iya ba, garin ta d'auka ta katse kiran aka kuma kira bata san ya akayi ba taga seconds sun fara tafiya alamun ta d'auka.


A kunne ta saka wayar bata ce komai ba daga can b'angaren yace, "Amincin Allah ya tabbata a gare ki ya kyakykyawar matata." Murmushi tayi kad'an wanda iyakacin sa kan fuskar ta tace, "Amin, kaima amincin Allah ya tabbata a gare ka." Y'ar dariya yayi yace, "Ni mijin ki?."
"Uhum" ta furta kawai bata ce komai ba. Jin hakan sai yace, "da fatan kin tashi lafiya."
"Lafiya lau, ya aiki?."
"Alhamdulillah, ya jikin ki?."
"Da sauk'i" ta bashi amsa a tak'aice.


"Allah ya k'ara sauk'i." Ta amsa da amin kafin yace, "Ina Umma, ina fatan lafiya take?."
"Lafiya lau kowa yake."
"To ma sha Allah, haka nake so naji."
Shiru ne ya biyo baya kafin yace, "Kiyi hak'uri Rauda wallahi aiki ne ya taso min da gaggawa wanda dole ya saka ni tafiya Abia ban shirya ba, amma in sha Allah nan kusa zan dawo zan nemi wani likitan ayi aikin nan a gama dan wanda na sani ya sanar dani baya k'asar nan."


"Babu komai, Allah ya taiamaka, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi ya biya buk'ata." ta bashi amsa a tare.
"Amin. Amma k'afar bata miki ciwo ko?."
"Bata yi" ta fad'a a hankali.
"Naji dad'in hakan."
Shiru ya sake ratsa tsakanin su kafin yace, "bara na barki ki huta anjima zan kira ki." Da to kawai ta amsa dan daman ta gaji ba wannan ne a gaban ta.


Umma ta shigo d'akin ta kalle ta tace, "Da Anas d'in kuke waya?." Kai ta d'aga alamun eh kafin tace, "Umma ni gidan Yaya Ummi zanje yau zaman gidan bana jin dad'in sa, ko naje gidan Yaya Shamsiyya."
"Sai kin dawo ai" Umma tana fad'a ta fita ta k'yale ta.


Sai azhar ta fito daga gidan ta nufi titi da nufin shiga mota ta tafi gidan Yaya Shamsiyya. maza ne guda biyu a bayan ta suna ganin ta d'aya daga ciki ya d'auko waya daga aljihun sa ya danna kira ya kara a kunne, ana d'auka yace, "Allah ya ja zamanin yarima mai jiran gado, yanzu muka ganta ta fito daga gidan su." Shiru yayi alamun ana bashi amsa kafin yace, "To ranka ya dad'e, a huta lafiya" yana fad'a ya yanke kiran suka cigaba da bin ta.


Rauda kuwa bata san ana binta ba tafiyar take har taje titi ta hau mota zuwa gidan Yaya Shamsiyya. Da nisa gidan sun jima suna tafiya kafin su zo unguwar babu jama'a sabuwa ce ba'a cika ba sosai. Tana sauka ta biya mai keken kud'i ta shiga layin gidan.


Da sallama ta shiga gidan Yaya Shamsiyya na aikin ta amsa tare da juyowa ganin Rauda ce ya saka ta sauri tashi ta k'araso ta rik'o ta tana fad'in, "Rauda me ya fito dake da rana ke ba lafiya ba?." Sai da suka k'arasa ta zauna akan benci ta kalli Yaya Shamsiyya tace, "Ina wuni."
"Lafiya lau, ya jikin naki?."
"Da sauk'i Yaya, ina su Amir?."
"Sun je gidan kakar su anjima zasu dawo, me ya fito dake ana rana haka Rauda?."
"Na gaji da zaman gidan ne kawai Yaya."


"Da gajiya kam gaskiya, sannu Allah ya k'ara lafiya." Ta amsa da amin suka fara hira har akayi la'asar tayi musu wainar fulawa suka ci Rauda bata fito ba sai biyar da wani abun. Har bakin titi Yaya Shamsiyya ta raka ta sai da taga ta shiga mota sannan ta juya ta koma gida.
Napep d'in da Rauda ta shiga suna cikin tafiya suka ga an sha gaban su da mota k'atuwa bak'a mai tsaho, gaban Rauda ya fad'i ganin manyan zagage sun fito daga motar sun k'araso inda suke tsaye.


"Kee fito!" D'aya daga cikin su ya fad'a yana kallon ta. Cikin k'arfin hali irin nata tace, "Akan wanne dalilin zan fito?." Mai napep din yace, "malamai lafiya muna tafiya zaku tsaya a gaban mu?."
Bulala d'aya daga cikin su ya d'auko yace, "kana kuma magana sai ta sha jinin jikin ka. Zaki fito sai mun d'auko ki?."


Ganin mai napep d'in ya tsorata yayi shiru dan ganin bulalar ma abin tsoro ce ya saka ta dogaro sandar ta k'asa ta sauko dan har lokacin bata daina jin zafin bulalar jiya ba. Sai da ta fito da sandar ta d'aya ya kalli d'aya. yace, "Zata b'ata mana lokaci fa" yana fad'a masa haka kawai ya sunkuya ya d'auki Rauda cak ya k'arasa motar ya saka ta shi kuma dayan ya kwashi sandinan ta ya k'arasa da sauri ya shiga motar suka ja a guje. Mai napep a kan idanun sa akayi komai ya koma da baya dan yaje ya sanar da wacce ta rako ta amma bai san gidan ba tunda a kan titin kawai ya gansu dole ya hak'ura ya kama gaban sa amma zuciyar sa babu dad'i ko kad'an.


Gudu suke sosai da Rauda a mota sai ihu take tana kuka amma babu mai jinta tunda gilasan a kulle suke gasu bak'ak'e na waje baya ganin ka sai dai kai ka ganshi. sun yi nisa sosai sannan suka tsaya a kan titin da babu kowa sai motoci suma sai ayi mintina goma wata bata wuce ba. Tsayawar su babu wahala suka fito daga motar aka bud'e ta suka jawo ta suka fito da ita ta fad'i a k'asa. Kallon wajan take babu kowa kamar ma daji ne domin shiru ga duhun magriba hakan ya saka hankalin ta ya sake tashi ta sake rud'ewa lokaci d'aya.


"Dan Allah kuyi hak'uri ban san laifin da nayi muku ba amma ku yafe ni dan Allah ku barni na tafi" ta fad'a cikin kuka sosai jikin ta har rawa yake sabida tsoro. Waya taji kusa da kunnen ta ana fad'in, "ke jinin talakawa, ni kika kalla kika kira da mahaukaci ko? Zan nuna miki dabi'un hauka yanzun nan, ko nan gaba aka sake cewa ki fad'awa wani irin abinda kika ce dani bazan ki kuma. Kuna jina?." Da sauri suka amsa da, "muna ji ran ka ya dad'e."
"Ku yi duk abinda kuke so da ita in kun gama ki sakar mata Bobby ku k'yale ta a wajan, in kuka yi akasin hakan taku tukunyar ce zatayi zafi" yana fad'a ya yanke wayar suka kalli juna kafin su dawo da kallon su ga Rauda da take kuka tunda taji komai.


D'aya ya kalli d'aya sannan yace, "Sako Bobby ya fara yaga naman ta kafin muyi namu." Ba musu suka k'arasa kusa da bak'ar motar su suka bud'e, Katon bak'in k'are ya fito daga boot d'in motar yana zaro harshe jikin sa har rawa yake sabida k'oshi da zallar mugunta a tare dashi. "Bobby ga nama can" d'aya daga cikin su ya fad'a yana nuna masa Rauda da yatsa yana dariya amma a zuciyar aa tausayin ta yake ji.


Karen sai da yayi wata girgiza gashin jikin sa ya mik'e sannan ya fara nufo ta a hankali yana sake zaro harshen sa, idanun sa ma da jikin sa abin tsoro ne shiyasa tunda ya tunkaro ta ta runtse idanun ta tana salati dan ta tabbatar k'arshen tane yazo babu abinda zai hana Karen bai kashe ta ba. Razananniyar k'arar da tayi shine ya saka su kallon inda take da gaggawa.
*KWANTAN ƁAUNA*


©️ *Nana Haleema.*


*Book 1*
*018.*


Cizo ya kawo mata karen shine ya saka ta yin k'ara ta kulle idanun ta tana jiran taji sukar hakoran sa a a naman ta amma sai taji shiru, ta bud'e idanun ta a hankali taga karen baya gaban ta kamar d'azu ta juya gefen ta ta ganshi a tsaye ya juyo yana kallon ta kusa da wanda bata tantance waye ba. A hankali yake takowa yazo kusa da ita suka had'a ido sai jikin ta ya cigaba da tsuma ya had'e hannayen ta waje guda tana kuka amma ta kasa magana.


D'auke kai yayi daga kanta ya kalli wad'anda suka sato ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login