Showing 9001 words to 12000 words out of 92772 words

Chapter 4 - KWANTAN BAUNA BOOK 1 COMPLETE by Nana haleema.txt

20 Jul 2024

17679

ka damu Abba alqawari na d'aukar maka sai naga bayan Asad, bai isa ya mulki garin nan ina numfashi a duniya ba, zan kawar dashi, zai zama bashi da amfani kamar y'an uwan sa. Asad zai zama tahiri sai dai a tuna shi ace Allah sarki." Murmushi mahaifin nasa yayi cikin jin dad'i yace, "Ina alfahari da kasancewar ka jinina Suhail, nasan zaka iya Allah ya bada sa'a." Mik'ewa tsaye yayi kafin yace, "Amin Abba, ka zuba idanu zaka yi kallo" yana fad'ar hakan ya mik'e zai fita Waziri yace, "Suhail."


Ya juyo ya kalle shi yace, "Kar kaji tsoro, kar kaji tausayi, kar kaji d'ar a zuciyar ka. Ka manta dani da mahaifin Asad uwa d'aya uba d'aya muke, ka manta da kai da Asad y'an uwane ka d'auka baka tab'a sanin sa ba a wannan lokacin aikin ka zai tafi yadda kake so." Suhail ya girgiza kai cikin gamsuwa da maganar ya fita daga falon mahaifin nasa zuciyar sa na k'ullawa masa abinda ya kamata yayi a kan Asad domin cikar burin sa.


*KWANTAN ƁAUNA*
FitattuBiyar 2023.


©️ *Nana Haleema.*


*003.*


Asad da ya bar wajan mahaifin sa wajan mahaifiyar sa ya wuce duk da dare ya fara yi amma yasan bata yi bacci ba,kamar koda yaushe a hankali yake takawa ma'aikatan dare na ta kai gaisuwa wasu yayi murmushi wasu ya d'aga musu hannu wasu ma ya share dan baya son takura. Lokacin da ya shiga ya tarar da Aliyu a zaune a kan kujera ya d'ora k'afa kan d'aya yana kad'awa ga ma'aikata a zagaye dashi ya bar su a tsaye bai sallame su ba yana aikin danna wayar sa.


Sallamar da yayi suka amsa duk suka duk'a suka gaishe shi ya d'aga musu hannu bai kalli inda Aliyu yake ba kai tsaye d'akin mahaifiyar sa ya shiga, Jim kad'an ya fito samun da yayi tana wanka ya zauna shima a kan kujerar da ta kasance suna zama in bata wajan bai magana ba. "Dan girman Allah ranka ya dad'e kayi hak'uri bana jurewa tsayuwa kayi min wani hukuncin dan Allah" wani daga cikin ma'aikatan da suke zagaye dashi ya fad'a k'afar sa na rawa sosai.


Kallon sa Aliyu bai yi ba balle ya bashi amsa cigaba yake da abinda yake yi, gumi ne yake ketowa daga dukkan kafofin tsohon k'afafun sa sai rawa suke haka jikin sa idanun sa yayi ja sabida wahala, baya yayi zai fad'i Aliyu da yake danna waya yace, "in ka fad'i k'asa ka tabbata yau a tsaye zaka kwana." Dafa kujera yayi jikin sa na cigaba da rawa hawaye na zuba daga idanun sa.


Dukka sauran ma'aikatan jikin su yayi sanyi dan ya fisu shekaru a cikin su kowa yasan bashi da lafiyar k'afa balle ya iya tsayawa, Asad da ya ke jin komai yaso ya basar sabida ba shiri suke da Aliyu ba amma ganin abin yayi yawa ne sosai ya saka shi ya kalli tsohon yace, "Zauna!." A sama dukka suka ji maganar tasa Aliyu ya juyo ya kalle shi amma kamar ba shine yace na hankalin sa ma baya wajan su.


Tsohon ya kalli Asad suka had'a ido da idanu yayi masa alama da ya zauna, kallon Aliyu yayi yaga shi yake kallo ya kuma kallon Asad yaga shima shi yake kallo duk sai ya rud'e ya rasa abinda zaiyi, maganar wa zaibi a cikin su duk sai ya diririce. Aliyu yace, "ka sake ka zauna wallahi gobe sai na saka an zane k'afafun ka an ji musu ciwo yadda zaka jima baka taka ba."


Asad ya mik'e tsam ya k'araso inda tsohon yake ya kama kafad'un sa ya zaunar dashi a k'asa kafin ya kalli Aliyu su had'a idanu ko wanne fuska a d'aure zaiyi magana Asad ya d'aga masa hannu yace, "Bana son hayaniya pls." Kallon ma'aikatan Asad yayi da hannu ya musu alamun me suke a wajan, d'aya daga ciki yace, "muna jiran ya bamu umarnin abinda zamuyi ne ranka ya dad'e" ya fad'a cikin girmamawa yana kallon Asad.


Da hannu yayi musu alamun duk su fita daman sun gaji babu b'ata lokaci suka fita tsohon da ya zaunar ya mik'e ya tafi kamar zai fad'i yayi saurin rik'o hannun sa ya tsaya cak sannan ya sake shi tsohon ya duk'a yace, "Allah ya kare ka a duk inda kake, ya baka kariya daga duk ka masu nufin ka da sharri, ya sanya ka zamo sarki a wannan gidan. Allah ya taimake ka ya biya maka dukkan buk'atun ka mai zuciyar alkhairi." Kai kawai ya d'aga masa ya fita da sha'awar rayuwar Asad duk da sarautar da izzar ta ratsa shi amma baya wulak'anta na k'asa dashi.


Kamar jira Aliyu yake su fita ya mik'e yana nuna Asad yace, "Kaga Asad ka fita daga rayuwata tun kafin ka tunzura ni nayi maka abinda har ka mutu baza ka manta dashi ba, me kake ji dashi har da zan kira ma'aikata ka saka su fita?, kawai rainin hankali kake ji dashi ko kuma tsabar raini ne?" Ya fad'a a fusace yana kallon sa.
Bai ce komai ba sai ma waje da ya samu ya zauna ya cigaba da danna wayar sa dan shi baya son hargagin Aliyu ko kad'an.


Hakan da yayi ba k'aramin sake harzuk'a Aliyu yayi ba ya koma gefe yana jan wuci yana k'arewa Asad kallo yana hasashen irin abinda ya kamata yayi masa wanda zai saka ya wuce takaicin da yake ji a zuciyar sa. Sallamar Hydar ta katse su Asad ne ya iya amsawa kawai banda Aliyu Hydar ya k'arasa ya xauna kusa da Asad kafin yace, "Our king how far."


Kai ya d'aga masa kawai baice komai ba ganin hakan shima sai ya share ya kalli Aliyu da yake wuce yace, "Ya dai bro?." Ji yayi kamar ya make Hydar ganin rainin hankalin da yayi masa, a gaban idanun sa ya kira Asad sarkin su sannan shi kuma ya kalle shi ya ce masa wai bro, k'wafa yayi yana jijjiga kansa dai-dai nan mahaifiyar su ta fito.


"Ya dai triples" ta fad'a tana kallon su ganin haka duk suka mik'e tsaye ta k'araso ta zauna a kan kujera suka zauna a kan carpet ta kalli Aliyu dashi bai zauna ba tace, "Aliyu wai me yake damun ka haka ne?."
"Ranki ya dad'e Asad shine yake damuna, har yana da ikon da zan kira ma'aikata zan saka su aiki ya ce su tafi?, me yake tak'ama dashi wanda bana tak'ama dashi?, ki ja masa kunne har ya harzuk'a ni nayi masa abinda bazai manta ba"


Kallon Asad tayi tace, "Ina ruwan ka da ma'aikatan sa? Asad Aliyu fa yayan kane why zaka dinga masa halaye irin wad'annan kamar ba jini ka ba?, meyasa bakwa shiri ne?." Asad ya kalli Mama yace, "wulak'anta su yake Mama, bana jure ganin ana wulaƙanta na k'asa dani."
"To ina ruwan ka dan na wulak'anta su?, kai na wulak'anta ko wani naka?, kai lallai mai zuciyar tausayi da Imani wa kafi a cikin mu!?" Aliyu ya fad'a da ihu yana kallon sa.


Yatsine fuska Asad yake yi ya mayar da idanun sa ya kulle Mama tace, "Aliyu bana son shirme zauna ka daina min shouting a kai na. Wannan halayen naka suna bani mamaki kamar ba jinin sarauta ba." Ba musu ya zauna yana jijjiga kai Mama ta kalli Asad tace, "Ina ruwan ka in ma dafa naman su kazo ka samu yana yi? Ba bayin sa bane?, yana da ikon yi musu duk abinda yake so babu abinda ya shafe ka a ciki, bana son shishshigi Asad dalilin da ya saka bakwa shiri kenan kai da shi."


Asad bai ce komai ba daman kuma itama tasan bazai ce ba tace, "Ku had'a kan ku dan Allah bana son wananan tashin hankalin a tsakanin ku, yadda kuke zaune lafiya da Hydar shima da Aliyun ku zauna lafiya."


Aliyu ya girgiza kai yace, "ki gafarce ni Mama, Ba'a nemi zaman lafiya ba matuk'ar aka bawa Asad mulkin garin nan, Ba'a nemi kwanciyar hankali ba ko kad'an." Mama ta kalle shi a gajiye da magana irin ta tace, "Wai kai Aliyu waye zai baka mulki ne?, baka kwana a gida sai sanda kaga dama, koda yaushe cikin yawon banza kake da shaye-shaye na banza da wofi, a haka za'a baka mulkin ragamar al'uma?. Ka ajjiye wannan tunanin a ranka ka taya d'an uwan ka neman sarauta domin indai yana raye kai baza kayi mulki ba sai shi."


Kallon mahaifiyar tasa yayi da jajayen idanun sa yace, "indai yana raye mahaifiyata tace?."
"Eh indai yana raye baza ka mulki garin nan ba, da ace babu shi ne babu kuma Hydar zan shiga na fita wajan ganin ka zama sarkin garin nan kodan cikar burina, amma kash! Asad ya fika duk wani 'karko da ake nema a wajan wanda za'a bawa mulki dalilin da ya saka mahaifin ku ya furta zai bar masa karagar kenan. Hydar ya fila qualities d'in mulkar garin nan tunda shi rashin lafiya ce kawai kuma sai lokaci zuwa lokaci take tashi kai fa?."


"In kin min izini zanje na kwanta" ya fad'a muryar sa har sark'ewa take sabida bak'in ciki.
"Mu tashi lafiya" ta furta bata kalle shi ba yace, "Godiya nake." Mik'ewa tsaye yayi yana kallon Asad da ba shi yake kallo ba ya lumshe idanun sa kalaman mahaifiyar sa na dawo masa cikin kansa a zuciyar sa sak'a yadda zaiyi da Asad tunda ta furta da dai baya raye ne sai ta san yadda zatayi tabbas zai zama baya rayen kuwa nan kusa, baice komai ba ya girgiza kai ya fita.


Asad ya kalli Maman nasu yace, "in anyi min izini zan tafi na kwanta nima." Da kai tayi masa alama da an bashi ya mik'e sannan ya duk'a yace, "Sai da safe" abinda yace kenan ya mik'e Hydar ma haka suka fita tare.


Tare suke tafiya Hydar yace, "Deaf bana son mulkin nan ya sub'uce daga hannun ka ya koma hannun Aliyu, babu abinda bro bazai iya ba indai a kan sarautar nan ne." Asad ya sauke numfashi kawai baice komai ya kalli Hydar har zaiyi magana sai kuma ya fasa cewa komai ya d'auke kansa.


Murmushi Hydar yayi yace, "ka koyi magana deaf domin nan da wasu kwanaki kad'an zaka zama shugaban wannan gari ba kuma za'ayi shugaba wanda baya magana ba."
"Hydar ya zanyi?!" Ya furta da wata irin murya da ya sanya Hydar kallon sa har lokacin tafiya suke yi yace,


"Kai kad'ai ka cancanta Deaf, in ba kai ba duk wanda aka bawa mulkin nan komai sai ya lalace, kayi hak'uri domin ya zamar maka dole." Bai bashi amsa ba daman shima yasan iyakacin maganar da zai samu kenan hakan ya saka shi jan bakin sa yayi shiru kawai yana kallon sa.


Yana son Asad sosai baya son ganin abinda zai cutar dashi kamar yadda shima yake son sa, yayi alqawarin taya shi yak'i da duk wani mak'iya da suka sako shi a gaba, zai taya shi nemawa kansa kariya a duk inda kariyar take. A haka suka k'arasa babban b'angaren su suka shiga daman sun san baza su samu Aliyu ba kowa ya wuce d'akin sa Hydar yana murmushi ya shiga nasa d'akin.
*☆☆☆*
"Rauda! Zo ki bani kud'in ciniki na, rainin hankali ne ma irin naki kin san ban karb'i kud'ina ba ina ke ina bacci?" Baba ya fad'a da k'arfi a k'ofar d'akin su.


Rauda da bacci ya d'auke ta ta jiyo amon muryar sa ba jimawa ta mik'e tana laluben k'aramar touch light d'in Umma ta d'auko ta kunna tana haska inda zata ga kud'in. Muryar Umma taji tace, "Suna cikin kayan ki kinyi bacci kin barsu shiyasa na b'oye miki."
"Wai baza ki kawo min bane?!" Ya sake fad'a cikin d'aga murya yana d'aga laluben d'akin.


"D'auko maka nake Baba" ta fad'a cikin muryar bacci tana dube ghana must go na kayan ta ta d'auko kud'in a bak'ar leda ta mik'e ta kawo masa ya karb'a ya kwance yana lissfawa, kallon ta yayi yace, "babu naira hamsin tana ina?."
"Fad'uwa tayi Baba."
"Kinci uwar ki keda fad'uwar, kaji min yarinya ni zaki kalla kice kin naira hamsin ta fad'i? Ina laifin ma biyar ta fad'i sai ki yarda har hamsin?."


"Kayi hak'uri Baba wallahi ban sani ba sai bayan na dawo dana irga naga babu."
"Daman ai kin saba, rik'e min canji ba wannan ya zama sabon ki dan kinga ina k'yale ki. Y'ar uwar ki cif ta kawo min kud'ina amma ke da yake bakya son tallah uwar ki ma bata so shine ake rik'e min canji dan nace na daina d'ora miki, to baki isa ba talla yanzu kika fara kuma wallahi sai kin biya ni hamsin d'ina."


Yana fad'a ya saki labulen ya tafi nasa d'akin yana mita. Umma ta kalle ta tace, "ya akayi kika yar masa da kud'i?." Idanun Rauda suke ciko da hawaye tace, "Banyi da niya ba Umma ban san ta fad'i ba wallahi."
"Da safe cikin cinikin alawar madarar da kike yi ki d'auki hamsin ki bashi in b haka ba kin shiga uku."
"To Umma."
"Kwanta sai da safe" komawa tayi ta kwanta tana share hawayen ta. Ko kad'an bata son wannan dabi'ar ta Baba baya d'aga k'afa akan kud'i ko waye kai.


Kamar kullum da asuba duk ya tashe su kowa ya fito sallah bayan an idar aka jira ya shigo kowa ya gaishe shi sannan aka koma aka kwanta. K'arfe bakwai Rauda ta tashi ta tashi Khairi da Khalil suka fara shirin tafiya makaranta ita kuma ta fara gyare-gyaren gidan.
Bata gama aikin ba ta shiga ciki wajan Umman su tace, "Umma gasarar Koko ta k'are gashi su Khalil zasu tafi makaranta."


Umma ta mik'e zaune tace, "bai baku kud'in awarar bane?."
"Bai bayar ba." Umma ta mik'e tace, "to bara naje naji yadda zamuyi dashi." Ta fad'a tana fitowa shima a lokacin Baba ya fito daga d'aki.


Ganin tana nufo shi ya saka yace, "ban kwana da ko sisi ba kar kizo min da maganar kud'i." Umma ta karyar da wuya tace, "ba batun kud'i bane gasara ta k'are ne gashi baka bada kud'in awara ba ga y'an makaranta suna shiri basu ci komai ba."
"Ki tafasa musu ruwa hamsin d'in da nake bin Rauda ku siyo ganyen shayi da sikari su sha su tafi."
"Bak'in shayi Malam? Kar ka manta fa in suka tafi sai azahar ta yaya zasu gane karatu basu k'oshi ba?."
"Kar su gane mana wani ma ai bai sha bak'in shayin ba, tun yaushe nake cewa ki dinga tura su gidan sarki suna karb'o sadakar taliya baki tab'a ba. Ita y'ar uwar ki ai gashi yanzu sun dafa sun ci har sun tafi sun bar naki suna kale."


Umma tace, "yanzu malam kana da kud'in da zaka bamu muci baza ka bayar ba har sai munje karb'o sadaka har gidan sarki? Ka duba nisan dake tsakanin mu mana."
"Ita wacce taje bata san ciwon kanta ba kenan? Da asuba Rahma take tafiya amma ke y'ar ki y'ar gwal ce baza taje ba sai ku zauna haka ni kinga tafiya ta" ya fad'a yana ficewa ya bar Umma a tsaye.


Ummulkhairi ta taso tace, "Umma barshi ba sai munci komai ba ni zan iya dawowa haka in kina da wani abun ki bawa Khalil kawai." Girgiza kai tayi tace, "A'a Ummulkhairi muje ina da naira d'ari biyu ku siyo awara kuci ku tafi." D'aki ta shiga ta d'auko musu Khalil ya siyo musu awara suka ci suka tafi makaranta.


Rauda bayan ta gama aikin gidan tayi wanka shiga wajan mahaifiyar tata ta same ta a zaune tayi tagumi tace, "Umma ki daina saka damuwa a ranki, indai batun abinci ne zan dinga zuwa ina karb'owa sai muje tare da Rahman mu dawo."
"A'a Rauda ban amince da fitar asuba d'in nan ba, ban kuma amince da ki nemo abinda zaki ci da kanki ba Allah bazai hanani abinda zan baku ba in ya hana mu. Kin san bana son rok'o ne ko yawan cewa a bani da y'an uwana duk wanda na tambaya sai ya bani, yanzu ma ina da shinkafa kwano guda da aka aiko min dashi har gida wanke ki dafa canjin awarar da suka kawo ki siyo mai na hamsin yaji na hamsin muci har dare." Da to ta amsa ta mik'e ta tayi abinda mahaifiyarta ta ta saka ta.




Gab da azahar Baba ya dawo ya kwab'e babbar riga ya shiga aikin dafa d'an wake ya gama nan da nan ya kwashe ya lissafa na nawa ne ya zuba masu ya fara kwala musu kira, ita da Rahma suka fito ya kalle su yace, "to gashi nan na naira dubu biyu ne ko waccen ku, wallahi Allah biyar d'ina baza tayi ciwon kai ba." Komawa Rauda tayi ta d'auko hijjabin da tayi sallah ta d'auki abincin ta fita itama Rahma ta fita ba wacce tace kanzil.


Daga can inuwa ta hango motar Anas ta ja tsaki a zuciyar ta ta sake d'aure fuskar ta dan ma kar yaga fuskar da zai kulata, hango ta yayi ta tawo ya fito daga motar yana murmushi tazo zata gifta shi kenan ta jiyo amon sautin muryar Baba yana fad'in, "ki tabbatar sai kin biya ni hamsin d'ina ta jiya dan ba bar miki na yi ba!."


Runtse idanun ta tayi cikin takaicin dizgi irin na Baba ganin wanda yake tsaye ya saka Baba k'arasowa yana fad'in, "Anas yau kaine da rana haka?." Murmushi Anas yayi ya duk'a har k'asa ya gaida Baba ya amsa da fara'a yana fad'in, "Gashi mutuniyar zata tafi wajan sana'ar ta, kana jina da ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login