Showing 39001 words to 42000 words out of 92772 words
Chapter 14 - KWANTAN BAUNA BOOK 1 COMPLETE by Nana haleema.txt
numfashi yace, "to in kun shirya zan saka a kai ku a mota sabida k'afar tata kafin kuje ku saka a gyara mata inda zata zauna, zan baku magungunan da zata dinga sha da abubuwan da ya kamata ta cigaba da ci in sun k'are a kuma siya. Kuyi hak'uri dan Allah na rasa yadda zanyi ne."
"Haba likita meye na bada hak'uri? Ai kayi k'ok'ari ko kaine ka buge ta ai sai haka."
Rauda ta tab'e baki tace, "Daman su y'ay'an masu kud'in nan babu abinda suka sani sai kansu, yanzu inda girmamawa ai yaci ace wani nasa yazo ya cigaba da d'aukar nauyi na tunda sune silar komai. Tunda bashi da lafiya an bar maganar daman ba gata ne dani ba sun yiwa banza. Allah wadaran wasu masu kud'in" Rauda ta fad'a a fusace.
Dr yace, "Wallahi Hydar bashi da wannan halin baki ga yadda ya tsaya akan ki ba rashin lafiya ce dashi in ta tashi sai ya kwashe sati uku a sume bai farfad'o ba, yanzu zancen da nake miki tun da yazo nan ciwon ya same sa bai tashi ba har yanzu."
Umma tace, "kai ka biye mata ai likita ai ko iya haka aka tsaya yayi k'ok'ari sosai, wanda in sun buge ka suke guduwa fa su kuma ace musu me?."
"Umma maganar da ta fad'a gaskiya ce ya kamata ace wani nasa ya tsaya, amma da zaku san waye shi ku kuma san abubuwan da suke faruwa da ku kan ku kun tausaya masa shida y'an uwan nasa."
"Allah ya kyauta" Umma ta fad'a.
A wannan lokacin aka had'a magungunan Rauda da komai nasu aka saka Rauda a ambulance Umma ma ta shiga aka wuce da ita gida. Kafin suje Inna ta gyara d'akin Umma an yiwa Rauda shinfid'a aka shigo da ita a akan gadon aka zaunar da ita aka basu maganin ta suka koma.
Umma ta cire mayafi ta ajjiye tace, "Daman na gaji da zaman asibitin nan, zaman asibiti sai dole." Rauda tayi shiru bata ce komai ba haka kawai take jin haushin wanda ya kad'e ta a ganin ta bai d'auki lafiyar ta da mahimmaci ba tunda ita talaka ce.
Ummulkhairi da Khalil sai dawowa sukayi suka ga su Umma a gida suka dinga murya Umma ta dawo.
K'arfe biyu na rana Baba ya diro gidan ganin k'ofar Umma a bud'e ya saka shi ya lek'a ya gansu a zaune Rauda tace, "Baba sannu da dawowa." Kallon su yake da mamaki kafin yace, "Me kuma ya dawo daku?." Umma tace, "Kud'in wanda ya kad'e tane ya k'are a asibitin kuma bashi da lafiya shiyasa aka dawo damu gida." Baba yaja dogon tsaki yace, "Kai amma ban so hakan ta faru ba, yanzu shikenan bazan kuma ganin sa ya bani wani abun ba? Abin takaici wallahi."
Rauda tabi mahaifin nata da kallo da mamaki kafin ta d'auke kanta Allah ya sani abinda yake yi yana bata takaici kawai dan babu yadda zatayi ne uba uba ne. Juyawa yayi ya fita yana fad'in, "To Rahma a fito." Ba musu Rahma ta fito da hijjabi ya nuna mata kular yace, "gashi nan na dubu uku ne ayi aje a dawo." Da to ta amsa ta d'auki kular ta fita ranta a b'ace.
Inna ta fito daga d'akin ta ta kalle shi tace, "Tsakani da Allah malam nima da nake goya maka baya na gaji da wannan tallan da kake d'orawa yaran nan, ka duba halin da Rauda take ciki ta dalilin talla ni na d'auka zaka saduda sabida hakan amma ko gezau bakai ba."
Kama k'ugu yayi yace, "To uwata kama kunne na zakiyi ki fad'i maganar nafi fahimtar ki sosai." Inna ta d'auke kanta gefe yace, "in ban d'ora musu tallan ba a gida kike so su zauna naita kallon su su ba aure ba ba kuma samari ba?, meye amfanin su in basu yi tallan ba?."
"Abinda kake sakawa suna yi ba shine zai kawo musu miji ba, aure kuma ai lokaci ne in yazo kamar ba'a zauna ba."
"To bazan daina ba, tallah yanzu suka fara siyar da abinci ba ki d'auka yanzu aka fara wallahi sai sunyi. Inda Allah ya bani manyan y'ay'a maza ya za'ayi na saurare su?, haihuwar y'ay'a mata a farko ma ai asara ce."
Umma da take d'aki tace, "Haba malam, da kanka kake furta wannan maganar?, abinda Allah ya baka ne fa kake cewa asara?."
"Asara mana inda wad'anda na aurar suke gidan mazajen su ne y'ay'ana maza da yanzu sune suke taimaka min ko d'awainiyar ku suka d'auke min ai na huta amma duka mata ne kuma suka auri talakawa ba uwar abinda nake mora, su kuma wannan da suke zaune ba miji sai na zuba musu idanu haka kawai ina ciyar dasu a banza bana k'aruwa?."
"Daman hakkin ciyarwa a kanka yake ba kan su ba" Inna ta fad'a tana kallon sa. Yace, "wannan kuma ku kuka jiyo tallah dai yanzu na fara in kunji haushi bakwa so suyi ku dinga ciyar da kan ku kuga zan basu tallah ko bazan basu ba" yana fad'ar hakan ya fita Inna tace, "nidai na gaji da wannan dabi'ar wallahi." Umma bata kuma cewa komai ba balle kuma Rauda da take zaune.
Ba jimawa Yaya Ummi tazo ta fara shiga d'akin Inna ta gaishe ta sannan ta shiga d'akin Umma tana fad'in, "Allah ya taimaka banje can ba kika min waya Umma." Ta fad'a tana zama Umma tace, "Shiyasa na sanar dake ai dan nasan tsaf zaki iya wucewa." Gaisawa sukayi ta kalli Rauda tace, "Sannu Rauda, kin ajjiye k'iba kinyi haske da yake babu inda kike zuwa." Murmushi kawai tayi bata ce komai ba.
"Ni gwara ma da kuka dawo gidan wallahi k'afar taki ai tayi kyau da yake asibitin kud'i ne kamar ba karaya ba."
Umma tace, "haka nace nima wallahi, ai yayi k'ok'ari yaro."
Ledar da ta shigo da ita ta bud'e ta mik'a mata tace, "karb'i kazar hausa ce kici ance ana so masu karaya suci kaza." Karb'a Rauda tayi tace, "Na gode Yaya Ummi, Umma kici." Umma tace, "ki ci k'oshi tukunna, naji dad'i ma dasu Khalil sun tafi islamiyya." Ba musu ta fara ci suna hira sama-sama kawai sai ganin Baba sukayi kamar an cillo sa.
Kafin suce wani abun ya saka hannu a kwanon hannun Rauda ya d'auki k'atuwar b'angare daga cikin kazar ya saka a baki yana fad'in, "Daman sai dana aiyana wani abun kika kawo kika k'unso a leda to Allah yayi da rabona, yaushe rabon da a gamu da kaza?" ya fad'a yana taunawa tare da lumshe idanun sa. Umma takaici kamar me haka take ji amma ya zatayi haka tayi tagumi tayi shiru suma haka ba wanda yace uppan ya cinye ta hannun sa ya kuma d'aukar wata yana ci.
Yace, "Ke Mamana yaushe mijin naki yayi kud'in siyo miki kaza har kika bayar?." Yaya Ummi tace, "ba shine ya siyo ba bashi na karb'o a mak'ota na na dafa mata ganin mai karaya ce, ina yaga halin da zai siyo min kaza Baba?."
Baba yana b'alla k'ashi yace, "yauwa koda naji" ya fad'a yana fita ya sha ruwa ya dauraye hannun sa ya fita. Umma tace, "Allah ya kyauta." Da amin suka amsa kafin Rauda tace, "Amma Yaya meyasa zaki karb'i bashi?."
"Ke k'arya nake ba bashi na karb'a ba wasu y'an kud'i Abban su Islam ya samu ya siyo mana guda uku yace na kawo miki guda d'aya. Kin san halin Baba ina fad'a masa hakan gobe a gidana zaiyi sallama yace masa bashi da kud'in cefane."
Dariya Rauda tayi tace, "kinyi farar dabara." Umma ma dariya tayi bata ce komai ba Yaya Ummi tace, "ke ai kece a ruwa kika auri wannan yaron Anas ai kun shiga uku da rok'on Baba wallahi." D'aure fuska tayi tace, "nifa bashi zan aura ba Allah zai kawo min miji na."
"Allah ya kawo k'anwa ta burina naga anyi auren ki. Allah ya kawo wanda ya fishing mu sha biki." Da amin suka amsa ta cigaba da cin kazar kafin ta ragewa Umma.
*☆☆☆*
A zaune ya same ta kamar koda yaushe ya k'arasa ya zauna a kan carpet ta kalle shi tace, "tun yaushe nace kaje gidan su Jidda?." Yayi shiru bai amsa ba ta kuma cewa, "ba magana nake maka ba?." Asad yace, "tun kwanaki."
"Sabida ban isa dakai ba ya saka baka je ba kenan ko?." Kai ya girgiza alamun a'a yace, "Tuba nake."
"To me ya hana ka zuwa?."
"Na manta ne."
"Yanzu na tuna maka ai saura ka kuma cemin ka manta. Kunyi waya da mahaifin ka?."
Kai ya d'aga tace, "yaushe zai dawo?."
"Jibi" ya bata amsa a tak'aice yana kallon k'asa. Zatayi magana Aliyu ya shigo cikin k'ananu kaya mara sa tsayi a jikin sa ya mayar da gashin fuskar sa bak'i kamar na Asad daman shine yake banbanta su sai suttura kuma. Shima k'asa ya zauna Mama ta kalle shi tace, "Lafiya na ganka haka?." Ya cize bakin sa har zai magana sai kuma yace, "babu komai."
"Kai dai ka sani" ta fad'a tana kallon Asad kafin tace, "na gama dakai zaka iya tafiya." Ba musu ya mik'e yace, "Ki tashi lafiya" ya fad'a yana fita. Aliyu ya kalle ta yace, "Allah ya taimaki Mamana maganar me naji kuna yi dashi?." Mama tace, "to wanda ya haife ni bani umarni sai na fad'a maka." "Allah ya wuci zuciyar ki, tuba nake. Ki tashi lafiya" ya mik'e yana girgiza kansa ya fita ta bishi da kallo cikin takaici.
Asad yana fita mota ya hau ya tafi company dan akwai abubuwan da dole sai yaje da babu abinda zai kai shi, yana zama a office yaji kansa yayi mugun sarawa ya dafe kan da duka hannu biyu ya kulle idanun sa, "Prince lafiya?" Hafiz ya fad'a yana shigowa. D'ago kai Asad yayi ya kalli Hafiz da ya zauna ya girgiza kai kafin yace, "kaina."
"Sorry."
"Ina files d'in nan?." Hafiz ya mik'e ya kawo masa yana dubawa Hafiz yace, "akwai abinda yake damun ka deaf, tell me please." Baice komai ba ya koma ya jingina da kujera yana sauke ajiyar zuciya amma baice komai ba.
Hafiz yace, "i don't know why yanzu baka sanar dani damuwar ka." Asad yace, "no ba haka bane, babu ne" ya fad'a yana mik'ewa tsaye ya d'auki key da wayar sa yace, "in ka gama ka same ni gida."
"Okay, akwai meeting da kamfanin k'asar Dubai yarjejeniyar suke so a k'ara musu tsahon lokaci."
Asad yace, "Kuyi komai" yana fad'a ya fita Hafiz ya bishi da kallon tausayi gabad'aya ya canja kamar ba shi ba.
Bai koma gida ba yawo yayi tayi a gari bai koma gida ba sai magriba, yana shiga apartment d'in su yaga giftawar mutum kamar iska alamun rashin gaskiya ya dawo da baya ya ganta ta juya baya tana waya ya k'arasa kusa da ita ya tsaya yaji ana cewa, "na saka tun wancan lokacin har yanzu kuma yana cikin d'akin nasa." Juyo da ita taji anyi ta zaro idanu waje shima nasa idanun ya wara ganin wacece ya Bud'e baki yace "Suhaima!."
*Ba'a fara komai ba ku shirya kawai.*
*KWANTAN ƁAUNA*
FitattuBiyar 2023
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*012.*
"Na'am Yaya Asad" ta bashi amsa tana kallon sa shima kuma ita yake kallo da mamaki shinfid'e a kan fuskar sa. kallon k'ofar falon yayi ya dawo da kallon sa gare ta sai tace, "Mama ce ta bani fresh milk tace na saka maka a fridge shine nake waya nace na saka." Kai ya jinjina kafin yayi gaba sai kuma ya tsaya ya juyo ya kalle ta yace, "bayan yau ta tab'a aiko ki?." Kai ta girgiza alamun A'a tace, "bata tab'a ba, yau d'in ma dan bata fito bane ba ya saka ta bani, ni kuma bazai koma ciki ba shiyasa nake sanar da ita a waya."
Baice komai ba ya shiga d'akin wajan fridge ya nufa ya bud'e yaga madarar a ciki ya kulle ya shiga d'akin sa yana k'are masa kallo kamar wanda yake neman wani abun kafin ya sauke ajiyar zuciya ya tsaya a jikin mudubi yana kallon kansa. Wani abu ya gani ya gifta ta bayan sa bai juya ba ya cigaba da kallon mudubin ya sake ganin giftarwa abu hakan ya saka shi ya juya da sauri amma bai ga komai ba.
Wajan da yake ganin abun yake nufa amma baya ganin komai hakan ya saka shi kulle idanu ya bud'e tunda ya fara mafarkan nan sai ya dinga ganin abun kamar a zahiri ne yake faruwa.
Bai jima sosai ba ya kuma fita yaje masallaci ya dawo suka had'u da Hafiz a k'ofar shiga falon suka shiga tare, suna zama Suhail ya shigo da sallama Asad ne kawai ya amsa banda Hafiz ya samu waje ya zauna yana fad'in, "kwana biyu kowa ya b'uya." Asad girgiza kai kawai yayi Hafiz ya kalli Suhail yace, "ko zaka iya bamu waje magana zamuyi." Suhail ya kalli Asad ya kalli Hafiz ya murmusa ya mik'e tsaye yace, "okay babu damuwa."
"Noo zauna" Asad ya fad'a yana danna wayar sa jin hakan Suhail ya koma ya zauna Hafiz takaici ya sake kama shi ya girgiza kai amma baicr komai ba
Shiru wajan ya sake d'auka dan shi dai Hafiz bazai yiwa Asad magana Suhail yana nan ba shi kuma Asad bazai yi maganar ba, Suhail ya mik'e yace, "Sai da safe" yana fad'a ya fita Hafiz kamar jira yake ya kalli Asad yace, "Abinda kake yi fa sam ba mai kyau bane ba, kasan manufar Suhail a kanka amma ka dinga zak'ewa kana barin sa kusa dakai bayan nida kai mun san dama kad'an yake nema a kan ka ya halaka ka amma kake bashi fuska har haka."
Shiru yayi kamar bazai amsa ba jikin sa wani iri yake ji cikin kwanakin gabad'aya baya son zaman gidan yana jurewa ne kawai sabida Mama amma da tuni ya bar k'asar, "Ka nunawa wanda yake neman ka da sharri baka san yanayi ba yafi riba" ya bashi amsa yana kallon sa shima yana kallon sa.
"Amma kasan....." dakatar dashi Asad yayi yace, "Bana son magana a kan hakan. Muyi abinda nace."
"Okay better" ya bashi amsa shima kafin ya mik'e ya fita dan bazai yi maganar ba shima ya fasa.
Murmushi Asad yayi bayan ya fita cikin su biyun shi dai ya rasa wanda yafi sonsa ko wanne burin sa ya bashi kariya shiyasa yake ji dasu baya so yaga an tozarta wani a gaban sa. Duk da shi ba wani sakewa yake da abokai ba amma babu laifi su kan danyi hira sama-sama.
Tashi yayi ya fita daga apartment d'in gabad'aya yana takawa a hankali kamar ko yaushe ana zubewa ana kwasar gaisuwa yana amsawa a ciki, zaga gidan kawai yake badan akwai abinda zaiyi ba sai dan haka zuciyar sa take bashi umarni, har yazo b'angaren da yake da duhu sosai har ya gota sai kuma ya dawo da baya jin abinda ake cewa, "ku bari kawai shima Asad d'in maganin sa zamuyi yadda muka kwantar da Hydar shima haka zamu kwantar dashi, ko muyi masa kurciya ya bar k'asar gabad'aya bazai sake dawowa ba har abada." Dariya yaji anyi kafin yaji ance, "Allah yaja zamanin Master planer, Asad bazai tab'a mulkar garin nan ba in sha Allah, jinin Rabi'atu baza suyi sarauta ba in Allah ya amince."
Motsi yaji alamun za'a fito ya tsaya a wajan cak yana jiran yaga wacce zata fito, rad'ad'in da ya kawo masa ziyara a idanun sa ya saka shi kulle su ba tare da yayi niya ba yana juya kansa yana so ya bud'e amma ya kasa idanun nasa ruwa suke yi, hannu ya saka a aljihu ya d'auko tissue yana goge idanun nasa hankalin sa na wajan da yake jin maganar amma baya gani sosai, sai da ya d'an samu sauk'in idon ya d'auko wayar sa ya kunna haske ya sake haska wajan amma babu kowa alamun da gangan aka saka masa abu mai yaji a idanun sa.
"Asad me kake yi a nan?." Jin tambayar daga bayan sa ya saka shi ya juya yaga Hajiya a tsaye tana kallon sa. Mamaki ya kama shi uwar gidan sarki mai zai kawo ta wajan a wannan lokacin da ba kowa yake yin hanyar ba..? amma bai nuna mata mamakin sa ba sai ya goge idanun sa yace, "babu komai" yana fad'a ya wuce tabi bayan sa da kallo ta murmusa kafin ta bar wajan.
D'aki Asad ya koma yana zagaye hankalin sa a tashe matuk'a, bai tab'a jin tashin hankali akan abubuwan da suke faruwa ba kamar yadda yake ji yau. Babban tashin hankalin sa sunan Hydar da yaji suna ambata kenan duk rashin lafiyar da yake yi sune suka jawo hakan?. Suna saune suke kwantar dashi dan rashin imani..? Su waye ma a tak'aice....?. Kama k'ugu yayi ya furzar da iska mai zafi yana sauke numfashi, "me ya kai Hajiya wajan a yanzu?" Ya tambayi kansa nan ma babu amsa ya had'd'iye saliva a jikin sa yake jin lokaci yayi da kowa ya kamata yasan waye Asad.
*Bayan wasu kwanaki.*
"Malam dan Allah in ka fita ka biya ta wajan sarkin d'ori ku tawo da ko yaron sane yazo a duba k'afar Rauda. Gashi dai ta samu lafiya amma k'afar ta nakasa yazo ya