Showing 78001 words to 81000 words out of 92772 words
Chapter 27 - KWANTAN BAUNA BOOK 1 COMPLETE by Nana haleema.txt
naji dalilin dukan da aka yiwa iyalai na har cikin gida."
"Firstly ku fara ganin likita a duba lafiyar ku, please Baba kuzo muje" Hydar ya sake fad'a yana kallon Baba. Rauda ta kalli Asad da idanun sa yake yawo a kanta amma in baka fahimta ba baza kace ita yake kallo ba taja dogon tsaki tace, "Wanda akayi dan shi d'in yana tsaye k'ikam shi bazai bada hak'uri ba sabida bamu kai ya bamu hak'uri ba an dake mu an daki banza kenan, to wallahi sai na d'auki mataki ina k'yale komai banda a tab'a min iyayena." D'auke kai yayi daga kanta Baba ya kalle ta yace, "Ya isa haka Rauda bana son sake jin bakin ki, ke Rahma tashi mu taimaka mata ta tashi aje asibitin."
Tare da Baba suka fita Rahma da Inna suka fito da Umma da Rauda suka shiga bayan mota Baba ma ya shiga Hydar ya shiga mazaunin driver dan yasan Asad bazai iya tuk'i ba ya ja motar suka tafi asibiti. Babu wanda yake magana a cikin su har suka je asibitin ya saka aka duba su aka sake gyara ciwon hannu Umma aka sake wanke ciwukan fuskar su duk da ba masu yawa bane ba. A d'akin da suke suna hutawa bayan an gama Umma taji dad'in jikin ta su Hydar sunje sun dawo Asad ya kalli Umma yace, "kiyi hak'uri Mama."
Umma tace, "To ya zanyi in ba hak'urin ba?, babu komai." Hydar yace, "Baba zaku koma wani gidan daman kafin a gama gyara wancan zan kai ku yanzu suma wad'ancan zan koma na kai su gidan, in kawai abinda kuke da buk'ata sai a d'auko muku." Baba yace, "to sai muje tare in yaso akwai k'anwar Rauda nasan zuwa yanzu ta dawo daga makaranta sai ta d'auko musu abinda zata d'auko." Rauda Hydar ya kalla da take kallon wani wajan daban ya kalli Asad da yake a tsaye baice komai ba shima ya d'auke kansa.
"Baba muje" Asad ya fad'a yana kallon su suka tashi suka fito zuwa inda motar take suka shiga suka tafi. Kusa da unguwar su suka tsaya jikin wani gida babba flat mai maroon d'in gate da maroon d'in fenti yayi kyau sosai kamar sabo dan kana gani kasa ba'a zama a cikin sa kawai yana ajjiye ne. Asad ya fito Hydar ma ya fito suka cewa Baba shima ya fito.
Gidan suka shiga Jim kad'an suka fito Baba yace, "Kuzo muje ciki." Umma ce ta fita Rauda kam k'in fitowa tayi Baba yace, "baza ki fito bane ba?." Ta kalli Baba zuciyar ta kamar ana tafasa ta sabida b'acin rai tace, "Zan fito daga baya." Shi da Umma suka shiga gidan ta bisu da kallo tana kiyasta adadin matakin da zata d'auka a zuciyar ta.
Hydar ne ya shiga gaban motar ya zauna bai kalle ta bayace, "ki ajjiye abinda kike ji dashi a kanki ki fahimci abinda zan fad'a miki yanzu. Ina so ki fahimci abun dakyau kiyi tunanin kalaman da suka fad'a miki akan Asad ki gano me hakan yake nufi." Shiru tayi dan har lokacin a fusace take kafin ta girgiza kai tace, "A yanayin maganar su yayi kama da b'atan kai sukayi suna so suje wajan wacce take sonsa ko dai abinda yayi kama da haka." Hydar yace, "good girl. Ba b'atan kai sukayi ba Rauda tabbas kece."
"Nice me?."
"Kece wacce Allah ya d'orawa Asad k'aunar ta a zuciyar sa!."
Gaban Rauda ya fad'i har ta dafe k'irji bata san tayi ba ta kalle shi cikij tsananin bugawar zuciya a firgice tace, "Me kake nufi?."
Hydar ya juyo ya kalle ta yace, "Ina nufin Asad yana sonki yana kuma fatan auren ki dalilin da ya saka wanda basa goyan baya suka fara d'aukar mataki a kanki, dan farawa akayi in maganar ta cigaba tabbas akwai wasu abubuwa a gaba wanda zan iya cewa sunfi wannan. Na zab'i na fad'a miki ne ba tare da ya sani ba dan kisan dalilin da ya saka akayi miki haka." Shiru Rauda tayi ta kasa magana sai zuciyar ta da take bugawa da sauri-sauri tana sake maimaita kalmar yana sonta a zuciyar ta cikin mamaki da tsoro da ya bayyana a gare ta.
"Sona fa kace? Ta yaya zan amince da hakan bayan matsayin sa da nawa akwai banbanci?, har yaushe mukayi had'uwar da zai fara sona?, har yaushe ya sanni? Yaushe ya ganni da zai soni?. Wad'an nan kalaman naka sun sake bani tsoro sun tabbatar min da akwai wani abun da kuke nema dani shiyasa tun yanzu kuka fata bayyanar da nufin ku a gare ni. Shin me nayi muku?." Murmushi Hydar yayi yace, "Inda akwai abinda muke nema dake da tuni mun aiwatar dashi babu wanda ya sani basai anzo yanzu ba. ki tuna abinda Aliyu yayi miki wanda babu wanda ya sani har kawo gobe kinga da munyi niya zamu iya aikata abinda yafi haka babu wanda yasan mune muka aikata, in munso har ranki zamu iya d'auka babu wanda sai san mune to a kan me dan muna da wata manufa a kanki sai biyo ta wannan hanyar?. In muna da manufa a kan ki bazan tankare ki da wannan maganar ba domin furta tama ba ga ko wacce mace ya dace ba sai wacce ta isa, ke kin san su waye mu basai an fad'a miki ba." Kalaman sa sun shige ta sosai bakin ta ya mutu murus ta kasa furta komai domin ta tabbatar da abinda yace gaskiya da akwai manufar da suke da ita baza su tunkare ta ba, kallon window tayi zuciyar ta na zillo a lokacin Asad yazo wajan shida Baba.
Baba ya bud'e mata yace, "fito ki huta zamu jemu tawo da sauran." Jikinta ya mutu Baba ya rik'o ta suka shiga cikin gidan da ta kasa kallon sa sabida tunanin abinda aka fad'a mata ya tsaya mata a zuciya kamar an soka mata mashi a zuciyar ta haka take ji. Gida ne babba sosai mai babban ma'ajiyar mota sai babban tsakar gida sai kuma k'ofa guda uku a tsakar gidan. Guda d'aya suka shiga sai gasu a falo babba mai kyau wanda babu abinda babu a cikin sa har da a.c da duk wani abun buk'ata akwai shi a falon ya zaunar da ita ya koma.
Basu jima ba suka dawo dasu Inna bayan sun d'auko kayan sawa da abin buk'ata suka shiga ciki Baba ya tsaya yace ya kalle su, "To mun gode muku Allah ya saka da alkhairi, kunyi bakin k'okarin ku akan mu badan ku ba da bamu san inda zamu je mu zauna ba. amma duk da haka inaso maganar nan tazo gaban mai martaba." Hydar yace, "Kar ka damu Baba mu da kanmu zamu sanar masa baza a bar maganar ba in sha Allah. Za'a kawo abinci yanzu." Baba ya amsa ya shiga ciki suma suka shiga motar Hydar ya fincike ta zuwa gida.
A can gida kuwa Mum tana wajan Mama ranta a b'ace take zayyanawa Mama abinda ya faru tana had'awa da k'arya akan abinda Rauda tayi mata, "Wai ni yarinyar nan zata d'aga hannu ta mara? Har tana fad'a min wai me zatayi da Asad a fad'a masa shi da ya nace mata ya daina zuwa inda take?. Ranki ya dad'e meyasa Asad zai mana haka dan Allah? Kinga yarinyar kuwa?; ai duk yadda kike musalta munin ta ya wuce haka wallahi. kaf unguwar gidan su yafi na kowa lalacewa, gaskiya Asad bai kyauta mana ba wannan cin mutunci ne a gare mu gabad'aya."
Ran Mama ya sake b'aci ta girgiza kai tace, "Ta mare ki!, lallai yarinyar nan tana buk'atar babban mataki ba k'arami ba. Zan yi maganin abun da gaggawa bazan d'auki wannan cin kashin ba, k'aryar Asad wallahi babu shi babu ita dole ya rabu da ita matuk'ar yana son zaman lafiya. Ina shi ina wannan yarinyar?" Ta fad'a tana dafe kai cikin zallar takaici.
"Ai kuwa ranki ya dad'e bazai rabu da ita ba, Gwara ma mahaifiyata ta dajna tunanin hakan dan bazai yau ba" Aliyu ya fad'a yana shigowa ciki yana kallon su.
Mum ta kalle shi tace, "Haba Aliyu! meyasa zaka ce haka?." Yace, "To abinda yake zahiri na fad'a ai Mum, kuna nan kuna tunanin kun d'auki mataki kunyi maganin ta shi kuma yana can yaje gidan su ya d'auke su da kansa ya kaisu asibiti an musu maganin ciwon da suka ji ya mayar dasu d'aya daga cikin guest house d'in sa, yanzu maganar da nake suna cikin gida mai a.c da TV kamar gidan ki." A fusace Mama ta tace, "da gaske kake ko da wasa Aliyu?."
"Ni na isa nayi wasa da mahaifiyata? Abinda na fad'a gaskiya ne bazan yiwa Mamana k'arya ba."
Mum tace, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un. mun shiga uku, me yarinyar nan ta yiwa Asad ne haka?." Mama ta fusata tace, "ko me tayi masa dole ya sake shi bazan lamunci abinda yake niyar tunkaro ni ba, wannan raini ne da k'askanci a idanun mutanen gidan nan a gare ni. ya zama dole Asad ya bar maganar nan matuk'ar yana son zaman lafiya a cikin gidan nan." Aliyu yace, "ko kuma Mama ta hak'ura ba ta bar shi da ita domin kuwa da zarar maganr taje gaban Takawa zancen ta ya k'are kuma yanzu haka suna kan hanyar zuwa gare shi."
A haukace Mama tace, "Kira min shi Aliyu, maza ka kira shi" ta fad'a jikin ta har rawa yake tana zaga falon tana ji kamar zuciyar ta zatayi bindiga ta fashe. "Mama baiyi picking ba nasan daman ko Mama ce ta kira shi yanzu bazai d'auka ba balle kuma ni" yana fad'ar hakan ya fita daga falon hankalin Mama da Mum ya sake tashi Mama kamar ta zubar da hawaye haka take ji.
A b'angaren su Asad ana idar da sallar la'asar Asad ya shiga b'angaren su Hydar ya fita bai wuce ko ina ba sai wajan mai martaba ransa a b'ace. Basu san mai ya faru ba dukkan su sun samu kiran gaggawa daga gare shi har Asad suka isa b'angaren nasa ba tare da sanin abinda ya faru ba. A zaune Asad ya tarar da Mama ga Hydar a gefe nan take gaban sa ya fad'i abinda ya faru yazo ransa ganin su kad'ai ne a ciki ya samu waje ya zauna Mai martaba yace, "Asad abinda Hydar ya sanar dani haka ne?." Shiru Asad yayi dan bai san mai Hydar yace ba ya d'ago ya kalli Hydar d'in kafin ya girgiza kai yace, "Haka ne takawa."
"To ma sha Allah. Bazan ce komai ba a yanzu zan tura aje a tawo min da mahaifin yarinyar da kuma ita yarinyar, Hydar kaje kazo dasu ka kai su b'angaren baya dan bana son cikin gida su san abinda yake faruwa in yaso in kazo dasu ka sanar dani zan zo da kaina."
Hydar ya amsa da to ya tashi ya fita babu wanda ya kuma magana a cikin su mai martaba baice komai ba ran Mama a b'ace tana ta hararar Asad shi kuma kansa na k'asa baya ganin me take yi. Ba jima Hydar yazo da girmawawa ya sanar dashi gasu can yazo dasu ya yace, "Ku je can gani nan zuwa." Tashi sukayi Mama kamar ta shak'e wuyan Asad haka take ji sai binsa take da kallo tana kwafa suka fita shi kuma ya kasa ma had'a ido da ita.
Ta wata k'aramar k'ofa mai martaba ya fita babu wanda ya lura da fitar sa sai gashi ya bayyana a harabar b'angaren da yace a ajjiye su ya shiga falon kowa ya mik'e tsaye banda Rauda da take k'okarin tashi ya kalle ta yace, "yi zaman ki" ya fad'a yana k'arasowa ya zauna a akan kujera duk suka zauna a k'asa.
Mai martaba ya kalli Baba yace, "Malam Adam mun same ku lafiya?." Baba jikin sa har rawa yace, "Allah ya ja da ran mai martaba, lafiya lau."
"To ma sha Allah. Ya akaji da abinda ya faru kuma?."
"Mun gode Allah ranka ya dad'e."
"Muna sake baku hak'uri akan abinda aka yi muku tabbas ba'a yi muku adalci ba. Meye sunan naki?" Mai martaba ya fad'a yana kallon Rauda.
"Rauda" ta furta a hankali mai martaba yace, "Kiyi hak'uri kinji Rauda duk abinda aka aikata muku ga wacce ta saka nan, babu babu wanda yasan abinda ya faru sai bayan ta saka an aikata d'in da baza mu bari hakan ya faru ba" ya fad'a yana nuna Mama da take zaune a gefe kana yace, "Mahaifiyar su ce komai ya faru itace ta saka ayi muku. gaku gata nan in kun yafe mata a k'yaleta in baku yafe ba kuma a yi mata hukunci daidai da ita kowa yasan mulkina baya lamuntar zalunci koda jinina ne ya aikata."
Rauda zatayi magana Baba yayi saurin katse ta yace, "Allah ya k'arawa sarki lafiya, babu komai mu hakan ma da akayi mana an nuna mana mahimmacin mu, an nuna mana muna muna da darajar da Mai martaba da kansa sai bamu hak'uri,ya wuce mun gode sosai." Mai martaba yace, "ka barta tayi magana ita aka yiwa ba kai ba, Fad'i abinda yake ranki."
Rauda ta kalli Baba yana kallon ta tace, "Babu komai ya wuce." Mai martaba yace, "kin tabbatar ya wuce ba'a takura ki ba?."
Rauda tace, "Ya wuce ranka ya dad'e."
Mai martaba yace, ma sha Allah. Rabi'atu basu hak'uri" ya fad'a yana kallon Mama.
A firgice ta kalli Mai martaba suka had'a ido kallon da yayi mata ya saka ta d'auke kai tana girgiza kai tare da taune leb'en ta na k'asa cikin wani abu wai shi bak'in ciki da taikaici ta kalli Rauda da take kallon ta itama ido cikin ido ta cize bakin ta kafin tace, "Ayi hak'uri." Murmushin jin dad'i Rauda tayi har cikin zuciyar ta taji abinda aka yi musu ya wanke tass ko babu komai mace mai izza ta basu ko iya nan sun ci riba.
Baba ya washe baki yace, "babu komai ranki ya dad'e, ya wuce." Mai martaba yace, "mun samu labarin an buge wata yarinya kwanaki amma bamu san ba'a kula da lafiyar ta ba tunda Hydar ya kwanta ciwo, Shima muna neman afuwa a kan hakan kuma nasan Asad zaiyi duk abinda ya dace in sha Allah." Baba yace, "Allah ya taimaki Mai martaba, komai ya wuce mu a wajan mu. Kamar yadda mai martaba yace Asad yana iya bakin k'okarin sa akan rashin lafiyar Rauda."
Mai martaba ya girgiza kai yace, "mun gode da karamcin ku a gare mu baki d'aya, muna tabbatar muku da babu abinda zai sake samun iyalan ku ta k'ark'ashin wannan gida in sha Allah."
Shiru babu wanda yayi magana kafin mai martaba yace, "Tunda hakan ta kasance ina neman wata alfarma a wajan ka." Baba yace, "A wajena kuma Ranka ya dad'e?."
"Eh wajan ka."
"Umarni shine naka a gare ni ba alfarma ba."
"Alfarmar dai nake nema ka amince na fad'i abinda nake so."
"A shirye nake da sauraron ka, Allah ya ja zamanin ka."
Mai martaba ya kalli Asad yaga kansa yana k'asa ya kalli Mama yaga tana kallon sa kafin ya kalli Baba yace, "D'ana Aliyu wanda nakewa lak'abi da Asad gashi a gefe yaga y'ar ka Rauda ya yaba da hankalin ta da kuma tarbiyyar yace yana so. Bama shi ba ni kaina na yaba da ilimin ta da kuma tarbiyyar ta da nuna b'acin ranta a kan abinda zai tab'a iyayen ta. Muna neman alfarmar a bashi ita inda damar hakan!." A take k'irjin mutane hud'u suka buga a wajan, Mama, Asad, Rauda, da Baba. A tare suka kalle shi shi kansa Asad d'in ya gigice bai san abinda zai fad'a ba kenan dan bai shiryawa hakan ba a lokacin kwata-kwata.
Baba baki na rawa yace, "Allah yaja zamanin mai martaba, maganar da naji ce nake kokwanto anya ba mafarki nake ba?." Mai martaba yace, "ba mafarki kake ba Malam Adam abinda kaji gaskiya ne. Amincewar ka da tata amincewar nake so a d'aura auren ranar juma'ar nan mai zuwa dan bana son a d'auki lokaci. amincewar ku kawai nake nema amma babu dole in taga bai mata ba karta takura kanta, in kaga kaima baza ka iya bashi auren ta ba duka ba abin damuwa bane. Ina tambayar ka a matsayin siriki ne ba matsayin shugaba a gare ka ba, ka kalle ni matsayin sirikin ka ka fad'a min amsar da take zuciyar ka. Zaka iya bawa Asad auren Rauda ko A'a?!."
Tirk'ashi!🏃🏼♀️😂
#Vote
#Share
#Comments
*KWANTAN ƁAUNA*
Fitattubiyar 2023
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*023.*
Kallon kallo ake tsakanin Baba da Rauda da kuma Mama kowa fuskar sa d'auke da rud'ani, Asad dai kansa yana k'asa ko motsin kirki ya kasa balle ya iya d'ago idanun sa yace wani abun yayi shiru yana jiran yaji abinda za'a ce dan zuciyar sa duka take kamar ana doka ganga. Baba ya kasa magana shud'ewar wasu dak'ik'u kana Baba yace, "Allah yaja da ra. mai martaba, abin ne naji shi wani iri shiyasa na kasa magana."
Mai martaba yayi murmushi irin nasu na manyan mutane yace, "Kar ka damu na baku lokaci kuje kuyi shawara in tana sonsa Alhamdulillah haka muke fata, in kuma bata so kar ayi mata dole a barta da ra'ayin ta. Ina sauraren ku nan da wasu kwanaki da kun yanke hukunci a sanar dani ayi komai a gama cikin watan nan bana so a d'auki lokaci mai tsaho."
Baba