Showing 48001 words to 51000 words out of 92772 words
Chapter 17 - KWANTAN BAUNA BOOK 1 COMPLETE by Nana haleema.txt
sha Allah kuma zai taimaka."
"Allah ya sa" Umma ta furta jikin ta a sanyaye ta juya ta fita. Baba yana ganin ta fita ya k'arasa wajan ajiyar kud'in sa ya tsohuwar riga duk ta yage baza ka tab'a d'auka akwai kud'i a cikin ta ba ya fiddo da kud'in yana kalla, murmushi yayi yace, "da zan iya da an siyi maganin amma bazan iya cire kud'i masu yawa akan magani kawai ba gwara a fita neman taimakon shima riba ce" ya fad'a yana tattare kud'in ya mayar dasu ma'ajiyar su ya fito daga d'akin.
Da gari yayi haske Rauda ta tashi babu laifi taji dad'in k'afar ta yi wanka ta karya tana zaune a kan farar kujerar da take zama sabida sauk'in tashi tsaye.
"Sallamu alaikum wai ana sallama da Rauda a waje." Yaro k'arami ya fad'a daga soron gidan.
Umma ta d'ago labule ta fito tana fad'in, "Sallama da Rauda kuma? In ji waye?."
"In ji Bala mai pharmacy" ya bata amsa yana kallon Umma. Umma tace, "to jeka kace gata nan." Yaron ya Juya ya fita Rauda ta kalli Umma tace, "Umma naje nayi masa me?."
"Jeki Rauda bamu sani ba ko hak'ura yayi ya kawo miki maganin."
"Ni dai Umma bazan je ba babu cin fuskar da bai min ba jiya."
"To ni bara na je" Umma ta fad'a tana niyar juyawa ta shiga d'aki ta d'auko mayafi.
Mik'ewa Rauda tayi tace, "Zanje" ta fad'a tana d'aukar sandinan ta tana tafiya a hankali har ta fita soron gidan ta tarar dashi a tsaye da leda a hannun sa. Yana ganin ta yayi murmushi yace, "Rauda sannu, ya k'arfin jikin?."
"Da sauk'i, lafiya kake nema na?."
"Lafiya lau. Maganin na kawo miki nazo kuma na shaida miki duk bashin da yake kan ki an biya an kuma siya miki maganin da zaki ta sha har ki warke, dan haka daga wannan ya k'are azo a karb'a a waje na."
Kallon sa take tana kallon maganin da yake mik'o mata a leda kafin tace, "An siya min? Kuma an biya min bashi?, waye wanda ya siya har ya biya min bashi?." Bala ya gyara tsayuwa yace, "to wanda ya siya d'in aiko min akayi ba shi yazo da kansa ba, amma dai an siya miki."
"Waye wannan wanda zai siya min magani?" Ta fad'a a bayyane fuskar ta d'auke da zallar mamaki.
*Nima kaina abin ya bani mamaki waye ya siyawa Rauda magani kuma?.*⛹♀️⛹♀️⛹♀️
*KWANTAN ƁAUNA*
FitattuBiyar 2023
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*014.*
A sanyaye ta shiga gida hannun ta rik'e da leda ta zauna a inda ta saba zama Umma ta kalle ta tace, "Lafiya yake neman ki?." Ledar hannun ta ta nuna mata kana tace, "Wai cewa yayi nayi hak'uri da abinda ya faru jiya ga maganin wani ya siya min kuma ya biya bashin baya ya kuma bada kud'in wanda zan karb'a nan gaba." Da mamaki Umma ta rik'e baki tace, "ikon Allah! Waye kuma ya biya?."
"Ban sani ba Umma, na tambaye shi yace shima turo wani aka yi amma wanda ya siya d'in bai zo da kansa ba."
"Wanne d'an albarkan ne da wannan aikin?."
"Nima kaina ya kulle Umma."
Umma ta nisa kafin tace, "to wama zai miki haka in ba Anas ba? Shi kad'ai ne saurayin da yake zuwa wajan ki yanzu shine zai shiga lamarin ki, Jikina yana bani shine ya siya miki."
Rauda tace, "Amma kuma Umma Anas baya garin nan tun ranar da muka had'u had'uwar k'arshe ya cewa Baba zaiyi tafiya ban kuma ganin sa ba, bai ma san halin da nake ciki ba a yanzu." Umma tace, "Ke kamar ba y'ar zamani ba Rauda? Kin manta yanzu waya tana isar da ko wanne irin sak'o a kuma duk inda kake a duniya?."
"Haka ne Umma, amma ina tantama gaskiya."
"To in ba shi ba waye Rauda?."
"Babu kowa" ta fad'a a sanyaye Umma tace, "to kin gani, amma Allah ya yi masa albarka ya raba shi da iyayen sa lafiya."
Rauda ta murmusa har cikin zuciyar ta take jin farin ciki tace, "Amin Umma Karon farko kenan a rayuwar ta da naji ya burge ni" ta fad'a farin ciki na shiga zuciyar ta sosai. Umma tace, "kin ga bara na kawo miki ruwa ki sha maganin nan jiya kin sha wahala" ta fad'a tana mik'ewa ta kawo mata ruwa a kofi ta sha maganin ta shafa na shafawa ta ajjiye ragowar.
Inna da take d'aki taji komai ta fito fuskar ba yabo babu fallasa ta wuce su bata ce komai ba daman Umma tasan baza ta ce ba dan idan magana ce akan Anas k'arara zata nuna miki tana bak'in ciki da ba Rahma yake so ba. Baba ne ya shigo a gigice fuskar sa taf fara'ar da basu tab'a ganin irin ta ba yana fad'in, "mutanen gidan nan kuna ina! Kuzo kuji abin arzuk'i da farin ciki" ya fad'a yana shigowa yana kallon su. Umma tace, "Malam lafiya?."
"Bari kedai, ai babar ki ta iya haihuwa da ta haifo ki na aura kika haifo min Rauda. Bawan Allah shigo mana" ya fad'a yana kallon k'ofa.
Mutumin ya shigo sanye da k'ananu kaya hannun sa rik'e da leda ya durk'usa har k'asa ya gaishe su kafin yace, "An turo ni akan na kawowa Baba keke napep guda biyu, sannan ance na bawa mahaifiyar Rauda wannan kud'in" ya fad'a yana d'auko kud'in daga leda. Da hanzari Baba ya kaiwa kud'in cafka mutumin ya hana shi ya kalle shi yace, "Ita aka ce na bawa Baba."
Yak'e Baba yayi yace, "Daman zan mik'a mata ne ai."
Mutumin ya k'arasa wajan Umma ya ajjiye kud'in a gaban ta yace, "sannan yace a gaida wacce bata da lafiya shima baya jin dad'i ne da ya zarar ya samu lafiya zai baro inda yake yazo in sha Allah. Gashi yace a bata" ya fad'a yana sake d'auko kud'i a rufe a takarda ya sake ajjiyewa Umma.
"Sannan akwai kayan abinci da yace a tawo dasu gasu can za'a shigo dasu yanzu." Umma da ta saki baki tana kallon mutumin tace, "bawan Allah waye ya turo ka da wad'an nan abubuwan haka?."
Kafin yayi magana Baba yace, "Anas mana, da shi mukayi maganar zai siya min abin hawan da zan dinga samun kud'i dashi, gashi kuma ya cika alqawari." Umma ta jinjina kai tana kallon mutumin tace, "Amma hidimar tayi yawa bai kamata mu karb'i abin hannun sa ba tunda babu wata magana mai k'arfi tsakanin sa da Rauda, gaskiya a mayar masa."
Baba yace, "ai na riga na ba shi auren ta, ko bana raye shine mijin Rauda tun ba yau ba na mallaka masa ita" ya fad'a hakora a bud'e dan kar ma a mayar da kud'in. Mutumin ya murmusa ya mik'e tsaye yace, "Za'a shigo da kayan yanzu" ya fad'a yana fita jim kad'an aka fara shigo da kayan abinci babu abinda babu harda yankakkun kaji da d'anyen nama. Bayan an gama shigowa da su yace, "To Baba zan wuce ni." Umma tace, "Bawan Allah da gaske Anas d'in ne ya turo ka?." Zaiyi magana Baba yace, "Kina da matsala Binta, in ba shi ba waye zai aiko mana da wannan abin arzuk'in? Shine an fad'a miki sai faman maimaita magana d'aya kike yi."
Umma tayi Jimm sai tace, "mun gode bawan Allah kayi magana godiya dan Allah. bamu da bakin gode masa sai dai muce Allah ya biya masa dukkan buk'atun sa na alkhairi."
Ya amsa da amin Umma tace, "Tsaya bawan Allah a baka tukwici." Yayi dariya yace, "Haba hajiya ki bar shi na gode sosai. Sannan Baba yace a fad'a maka dan Allah kar kace zaka ja keken da kanka ka bayar a dinga yi maka ana kawo maka kud'i har gida."
Baba yace, "In sha Allah hakan ce zata kasance, Allah ya biya buk'atar duniya da lahira."
"Amin ya Allah. sai an jiman ku" ya fad'a yana fita Baba yabi bayan sa.
Rauda dai ta kasa cewa komai bakin ta a bud'e tana kallon abincin da kuma kud'in dake kusa da Umma zuciyar ta na mugun bugawa da sauri-sauri bakin ta ya mutu murus ta rasa wacce irin kalma zata furta. Umma ta kalle ta tace, "Rauda baki ce komai ba bayan duk abinda ya faru ta silar ki ne." Kamar kuma an mata allura a lokacin ta sauke ajiyar zuciya tace, "Umma na kasa magana ne gabad'aya ban san me zance ba."
"Haka zaki ce kuwa Rauda domin duk abinda aka bamu ta dalilin kine."
Kafin tayi magana Baba ya shigo fuska washe yana kallon kayan abincin yana fad'in, "yau ko fita kasuwar ma bazan ba a dafa mana kajin nan muci mu karya k'asusuwa."
Umma ta kalle shi bata ce komai ba ya kalli Rauda yace, "Allah ya yi miki albarka Rauda, ke farar haihuwa ce wallahi ko cikin y'ay'ana ke ta daban ce." Inna da take tsaye tace, "Su kuma bak'ak'en haihuwar sai a zubar dasu ace ba'a so" tana fad'a ta shiga d'aki ya bita da kallo baice komai ba ya cigaba da santin kayan abinci.
Umma tayi dariya tana girgiza kai jin yau Rauda ake cewa ko a cikin y'ay'an sa ita ta dabance, ita yake yiwa wannan fara'ar har yana ce mata farar haihuwa. "Allah yayi mana arzuk'i" Umma ta furta a bayyane tana sauke numfashi.
Umma ya kalla yace, "Nawa ne kud'in da aka baki?." Yana fad'ar hakan ta d'auke takardun kud'in da nata dana Rauda ta rik'e bata ce komai ba ganin hakan ya saka yace, "Ga b'arawo zan sace miki kud'i shine kika d'auke ko?." Ita dai bata furta ba ya girgiza kai.
Ranar Umma ke da girki abinda baya faruwa a gidan ranar shine ya faru, lafiyayar shinkafa da miyar kaji aka yi a gidan kowa y'an makaranta suka dawo cikin ikon Allah akayi bak'i a yayyen su mata duk suka zo aka ci aka sha kowa da farin ciki a zuciyar sa ana ta santin auren Anas da Rauda. Rauda sai taji alfahari a zuciyar ta ganin ana ta santin abinda ta dalilin ta ya samu lokaci d'aya taji Anas yana samu kyakykyawan gurbi a zuciyar ta.
*☆☆*
A jingine yake da fuskar gado idanun sa a lumshe kana kallon yanayin sa kasan bashi da cikakkiyar lafiya haka zalika baya jin k'wari a jikin sa dan fuskar sa da yanayin sa ya gwada hakan. kamar wanda aka yiwa magana ya bud'e idanun sa yana kallon d'akin kafin ya sauke numfashi ya kalli k'ofar da za'a shigo d'aki jin motsi.
Mama ya gani ta shigo ya tashi zaune sosai yana kallon ta ta k'araso da sauri ta zauna kusa dashi ta tab'a fatar kansa tana kallon sa tace, "Asad ya jikin? Tun d'azu nake zuwa kana bacci."
"Naji sauk'i, Barka da safiya."
"Ka tabbata lafiya lau ka ke?" Ta furta ba tare da ta amsa gaisuwar ba. "Naji sauk'i" ya sake fad'a yana kallon ta. Fuskar sa ta rik'e tana kallon sa tace, "ka rame Asad yanayin fuskar ka ya nuna min akwai abinda yake damun ka bayan ciwon da kake fama dashi, meye?."
"Mama kwana biyu ta daina zuwar min cikin mafarkina, ina so na ganta ban san inda take ba, ina kewar ta sosai" ya furta yana kulle idanun sa yana nuni da tsantsar abinda yake zuciyar sa kenan.
Da mamaki mai had'e da fad'uwar gaba Mama tace, "Wacece take zuwa mafarkin ka har kake so ka ganta?." Bud'e ido yayi yaga ta kafe shi da idanuwa sai kuma ya dawo hankalin sa tunawa da wacece a zaune kusa dashi ya sauke kai k'asa baice komai ba.
"Magana nake maka wacece?."
"Margayiya Hajiya mai babban d'aki" ya furta a hankali ba tare da ya kalle ta ba. Nannauyar ajiyar zuciya tayi jin abinda yace sai ta murmusa tace, "Ka dinga mata addu'a itace zata amfane ta a yanzu. Ni har ka bani tsoro na d'auka wata ce take kutse cikin mafarkin ka." Shiru yayi bai amsa ba gaban sa mugun fad'uwa haka kawai ba tare da ya san dalilin hakan ba.
Tashi tayi ta fita jim kad'an ta dawo da abincin sa da kanta ta zauna kusa dashi ta had'a masa duk abinda zai buk'ata ta bashi tace, "maza ka cinye akwai maganin da Abie ya aiko dashi zaka sha." Bai ki ba ya ci abincin daidai yadda zai iya ya bar sauran ya sha maganin da ta cika masa a k'aramin kofi.
Kallon sa tayi bayan ya shanye maganin tace, "mahaifin ka ya dawo d'azu in ka samu lafiya sai kaje ku gaisa. Sannan na hana kowa shigowa apartment d'in nan koda Hafiz ne ko Suhail ban lamunci su zo nan ba, in suna son had'uwa da kai suje wani wajan amma banda gidan nan na lura masu son ganin bayan ka suna da yawa." Kai kawai ya girgiza dan bazai kuma iya cewa komai ba.
Fita tayi daga d'akin ya sauke ajiyar zuciya ya d'auki ruwa ya sha, "Rauda!." Ya ji bakin sa ya furta ba tare da ya shirya hakan ba ya runtse idanun sa yana hango idanun ta da goshin ta ya bud'e yana cize bakin sa ji yake kamar ya tsinke kansa da mari. Yadda yake jin begun zuciya da fad'uwar gaba abin har tsoro yake bashi ya kalli gefen k'irjin sa yaga yana d'agawa a hankali.
Tashi tsaye yayi yana dafe da kansa sa ya kalli agogo inda ya nuna masa k'arfe hud'u na yamma ya sauke numfashi a karo na babu adadi ya shiga band'aki, bai jima sosai ba ya fito ya shirya cikin manyan kaya kamar koda yaushe yayi kyau sosai duk da ya rame amma kyawun sa bai b'uya ba.
K'ofa aka bud'e aka shigo bai kalli wanda ya shigo ba dan yasan bazai wuce jinin sa Aliyu ba shi kad'ai ne zai shigo babu izinin sa, "ya jikin ma?" Aliyu ya tambaya yana kallon sa. Juyowa yayi ya kalle shi da niyar bashi amsa sai maganar ta tsaya ganin abinda bai tab'a gani ba tun bayan girman su shi ya gani a tare dashi. kayan da yake jikin Asad irin sa Aliyu ya saka hatta hular kan su iri d'aya ce kamar su ta fito sak babu wanda zai banbance Aliyu babu wanda zai banbance Asad.
"I'm fine, thanks you" ya furta a tak'aice bai kuma kallon sa ba. Aliyu bai damu ba bai kuma kallon sa ba shima ya fita daga d'akin. Sosai Asad yake cikin mamakin canjawar da Aliyu yayi ya koma sak irin sa, hatta yadda yake magana shima ya mayar da tasa hakan babu ta yadda zaka ce ba shi bane in kaga Aliyu a canjin da ya samu abin yana d'aure masa kai. Waya da key na mota ya d'auko duk da baya jin k'arfi a jikin sa ga jiri da yake ji amma baya son zaman gidan ya fito falo. Babu kowa a falon ya wuce ya fita zuwa harabar apartment d'in nasu.
A sannu yake takawa sabida yadda kan yake masa ciwo cikin nutsuwa yake giftawa khamshi yana tashi. ganin yadda ake gaishe shi jiki yana rawa ya fahimci d'auka suke Aliyu ne dan shi ya fara fitowa sun gane kayan jikin sa hakan ya saka shi fita daga gidan da sassarfa.
*☆☆☆.*
"Khalil! Khalil!!, baka ji ina yi maka magana ne?" Umma ta fad'a daga d'aki tana fitowa amma babu Khalil babu dalilin sa. "Lallai ma yaron nan nace ya jira ni zan aike sa sai ya fice?." Rauda da take zaune tace, "yammar tayi ai ya tafi ball balle yau da garin yake a rufe ba rana" ta fad'a tana cigaba da karanta azkar.
"Ina Khairi?."
"Ta tafi kara Yaya Ummi bakin titi."
"Rahma kuma basa nan?."
"Duka sun fita" Rauda ta sake bata amsa tana kallon ta.
Umma tayi k'wafa tana girgiza kai Rauda tace, "A kira miki shi ne?." Umma tace, "k'yale ni bara na fita da kaina na kira shi."
Da sauri ta ajjiye littafin hannun ta ta mik'e tace, "Haba Umma bana so kina fita irin haka wallahi, bara na kira miki shi da kaina." Umma tace, "in yayi nisa ki k'yale shi kar ki yi nisa kema." Da to ta amsa ta saka hijjabi ta fita tana dora sandinan ta.
Batayi nisa ba ta hango yara ana ta ball ta kalle su tace, "Ina Khalil?." D'aya daga cikin yaran yace, "Yanzun nan yayi titi." Rauda ta girgiza kai ta bi hanyar titin dan ta kira shi kar ayi magariba yana ball. Titi ta fito amma dai bata ganshi ba, ta dinga kallon titin amma baya nan taja tsaki ta juya da niyar komawa taji kamar tayi karo da mutum.
Gaban ta yayi muguwar fad'uwa shakar khamshin turaren da bazata manta dashi ba tayi saurin d'agowa ta kalle wanda ta buge. dogon tsaki Aliyu ya ja ya saka hannu biyu ya bangaje ta ta fad'i k'asa ya cize bakin sa cikin takaici da tunanin irin hukuncin da ya kamata yayi mata. kallon ta ya kuma yi itama shi take kallo haushi da tsanar sa take ji a zuciyar ta yace, "Mahaukaciya!" Abinda ya furta kenan ya wuce ya bar wajan zuciyar sa cike da jin haushin zuwan sa ma wajan, in badan mai martaba ba mai zai kawo shi unguwar talakawa kamar wannan, badan mutane da suke kai kawo ba babu abinda zai hana bai sake b'alla mata k'afa ba.
Kafin Rauda ta farga bata kuma ganin sa ba sai k'urar motar sa ta gani ta kyad'a kai tana jin zafi a hannun ta ta furta, "kaine dai mahaukaci bani ba, wanda bai san darajar na gaba dashi ba. Na tsane ka wallahi naso kuma ka tsyaa dana tabbatar maka da kaine mahaukaci bani ba." ta fad'a tana k'okarin Mik'ewa.
A hankalin motar Asad kirar range rover ash colour take yin slow daga gefen ta, wajan yake kalla yaga tabbas a nan suka had'u ya sake kallon gefe yaga kamar itace take so