Showing 51001 words to 54000 words out of 92772 words
Chapter 18 - KWANTAN BAUNA BOOK 1 COMPLETE by Nana haleema.txt
ta tashi kamar kuma ba itace ba, zuba mata ido yayi ta jikin glass d'in motar ganin fa da gaske ta kasa tashi ga kuma babu yawan mutane a wajan sai ya b'alle murfin motar ya fito duk da zuciyar sa na hana shi hakan amma gangar jikin sa tak'i karb'ar umarnin zuciyar tasa ya tsallako. Khamshin da taji a kanta ya saka ta d'ago kai ta kalle shi mamaki ya hana ta magana har ya kama kafad'ar ta kamar jiya ya tasar da ita tsaye bata san anyi ba.
Lallai ma wannan mutumin yana raina mata hankali, shi kuwa fuskar ta yake kallo da babu niqab ko face mask zahirin tace a bayyane. d'auke idanu tayi dan yana yi mata kwarjini jin baice komai ba ya saka tace, "wai fuska biyu ce da kai wani lokacin kamar mutumin kirki wani lokacin mutumin banza ne kai, in zaka yiwa mutane fuska biyu banda ni domin na riga na gama gano kai d'in ba komai bane face mahaukaci wanda bai san darajar d'an adam ba. ban tab'a jin tsanar halitta kamar yadda nake jin tsanar ka ba. Na fad'i duk abinda yake bakina in ka dama ka saka a kashe ni a nan shine zaka nuna min lallai kana da k'arfin ikon mulki da sarauta. Ni kuma zan nuna maka k'arfin sarautar Allah domin ahi kad'ai nake jin tsoro a duniyar nan" ta fad'a tana d'ago ido ta zuba masa banzar harara mai d'auke da zallar tsana da k'yama.
Baice komai ba daman bazai ce ba dan ya gama fahimtar duk abinda take fad'a ba dashi take ba babban abinda yake d'aure masa kai a ina suke had'uwa da Aliyu?, "Lahh Yaya Aliyu!" Aka fad'a daga bayan sa cikin mamaki. Bai juya ba hakan ya saka Khairi k'arasowa da sauri ta tsaya kusa dashi tana dariya tace, "Ashe dai zan gane ka, ina wuni Yaya Aliyu?."
Kallon ta yake yana so ya tuna inda ya santa ganin hakan ya saka Khairi tace, "Wacce ka siyawa Yayar ta kayan fruits a k'ofar asibitiiiiii....?" Ta fad'a tana jan kalmar asibitin lallai sai ya gano.
Murmushi yayi kad'an alamun ya tuna ganin hakan ya saka tace, "Kaga yayar tawa nan ita ka siyawa. Anty Rauda ina lokacin da kina asibiti Baba ya bada d'ari biyu na siyo miki lemo a wajeeee.. Har Umma ta dinga min fad'aaaaaa? To kin ga wanda ya siya miki yace na kawo." Juyo da kallon ta tayi ga Asad tace, "Yaya Aliyu kaga Antyna ta koma mai yawo da sanda ko? Wanda ya buge ta ya daina zuwa inda take ance kuma sai an mata aiki zata warke mu kuma bamu da kud'in biyan kud'in, shikenan Antyna ta zama gurguwa" ta fad'a kamar zatayi kuka.
Takaici, bak'in ciki, b'acin rai suka tararwa Rauda lokaci d'aya bata san sanda ta tsinke Khairi da mari ba ta jawo ta kusa da ita ciki fad'a sosai ta zare mata idanu tace, "in baki min shiru ba sai na fasa miki baki, banza wacce bata iya shiru a rayuwar ta. Wa kika tab'a gani yana kula wanda basu san darajar mutane ba irin wand'an nan? Wa kike ganin yana kula masu shaye-shaye da neman mata eyeee?."
Khairi da take hawaye tace, "Wallahi yana da kirki Anty." Bai ji mai tace mata a gaba ba tafiya suke yi shi kuma ya juya zuwa cikin motar sa, duk da kalamai ta fad'a masu muni amma sam baiji komai a ransa ba dan maganar ta ta tabbatar masa da Aliyu yake bada shi ba.
A kan sitiyarin motar ya saukar da kansa yana furzar da iska a hankali yana jan numfashi yana saukewa, kallon inda suke yayi yana hango su da alama fad'a take yiwa Khairi dan yaga tana magana a fusace, duk taku d'aya da take yi tana nisa dashi ji yake kamar ana d'igo masa kewa wacce bai san dalilin ta ba a zuciyar sa tana yin gaba yana sake jin kewar na k'aruwa har ya daina hango su.
_Ya akayi ta san Aliyu?, a ina suke had'uwa haka?. Da gaske silar Hydar ta zama gurgurwa?._ tambayoyin da yake yiwa kansa a zuciyar sa kenan amma babu mai bashi amsa sai ita d'in. Sake kallon layin nasu yayi ya sauke numfashi sunan Rauda na yi masa amsa kuwa a cikin kunnuwan sa. "Inda Aliyu ta fad'awa hakan da me zai faru?" Ya furta a bayyane har lokacin yana kallon inda suka bi dan yasan tabbas sai dai wata ba ita ba, babu abinda zai saka Aliyu bai mata mummunan hukunci ba.
Yarinyar cikin mafarkin sa yake tuno fuskar ta idanun ta da goshin ta yake ganowa kamar ko yaushe, bud'e ido yayi ya tuno lokacin da Rauda ta bud'e idanun ta tana yiwa Khairi fad'a gabad'aya yanayin ta ya koma irin na yarinyar mafarkin sa. "Itace ko A'a" Ya tambaya yana dafe kansa da duka hannayen sa guda biyu jin bak'on abu wanda bai tab'a jin irin sa ba yana cigaba zuciyar sa da ko ina na jikin sa.
*KWANTAN ƁAUNA*
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*015*
Fuska a had'e Rauda ta shiga cikin gidan su Khairi na bayan ta tana gurshek'en kuka sai Khalil da yake biye dasu a baya. Ganin su haka ya saka Umma ta kalli Rauda tace, "Tun d'azu Rauda sai yanzu?." Zama Rauda tayi kafin tace, "Sai da naje titi." Umma tace, "Ke kuma Ummin ce ta dake ki kike kuka?."
Khairi tace, "Anty Rauda ce, dan kawai naga wanda ya siya mata fruits a asibiti na yi masa magana shine ta mare ni" ta k'arasa fad'a tana sake fashewa da kuka.
Umma ta kalli Rauda tace, "Akan me zaki mare ta Rauda bayan abin arzuk'i tayi? Ai ba laifi bane da taga wanda yayi mata alkhairi ta nuna ta san shi. Inda arzuk'i kema gaisawa ya kamata kuyi dan taimakon ki yayi." Rauda tace, "Umma bai cancanci a kula shi ba, bai san darajar d'an adam ba kwata-kwata." Da mamaki Umma tace, "Ke ya akayi kika sani?."
"Umma ina wannan d'an sarkin da muka had'u dashi a gidan sarki..? Wanda muka sake had'uwa dashi har Khalil yake cewa yace na shiga mota nak'i...?. dashi muka kuma had'uwa yau, shine fa wanda take cewa ya siyi kayan marmari dan tsabar k'arya."
"Wallahi ba k'arya nake ba shine Umma" Khairi ta fad'a tana kuka. Umma ta kalle ta zatayi magana Rauda tace, "Sai sake marin fuskar ki sannan zakiyi mana shiru naga alama. Bashi da kirki fa ko kad'an Umma yau ma baki ga kalar rashin mutuncin da yayi min ba."
Umma tace, "Kuma dai?." Rauda tace, "Kin san Khairi da shegen surutu ta dinga zuba a gaban sa maganar da ba'a tambaye ta ita take furtawa shiyasa na mare ta, wannan ai ba wanda za'a kula bane ba. Habiba tace min har neman mata yake yi garin haka in yayi mata wani abun fa tunda yasan babu abinda zamu iya?." Umma ta rik'e baki tana nuna Rauda da yatsa tace, "Ina raba ki Rauda da irin wad'annan zantuttukan wallahi, kinga ki kiyayi bakin ki kar ki jawo abinda zaki zo kina dana sani. Ina ruwan ki da sabgar sane wai? Ba abinda ya had'a ku ki dinga k'okarin gefa rayuwar ki a hatsari sabida tsiwa. Kuma kar na k'ara ji kince yana neman mata tunda kedai bai neme ki ba bai kuma nema a gaban idanun ki ba, ki kiyayi tsayuwa gaban Allah."
"Wallahi Allah na tsane shi tsana mai muni Umma, ban tab'a jin tsanar wata halitta a duniya kamar sa ba, bana son ganin koda fuskar sa ce." Umma bata ce komai ba ta wuce tana d'aura alawar magriba dan bata ga amfanin yi mata magana ba.
Bayan an idar da sallah suna zaune cikin k'aramin hasken fitilar tsakar gidan Baba ya shigo kamar an cillo shi har tuntub'e yake yi, "Ke Rauda maza jeki ga Anas can yana jiran ki." Abincin hannun ta ajjiye dan tasan ko bata ajjiye ba tunda yace ta tashi sai fa ta tashj tana k'okarin mik'ewa cikin fad'a yace, "ki k'arfafa jikin ki malama ki tashi." Babu wanda ya tanka ta tashi ta saka hijjabi ya d'auki kujerar da take zama da kansa yayi gaba tana bin sa baya.
Sanyin khamshi taji tunda ta shigo soron gidan nasu Baba ya ajjiye mata kujerarya kalli Anas da yake tsaye yace, "Gata ta fito maka da ita da kaina, zauna mana" ya fad'a yana kallon Rauda. Ba musu ta zauna Anas ya duk'a har k'asa yace, "Allah ya saka da alkhairi Baba." Baba ya amsa da amin ya fita.
Zama yayi kan irin tata kujerar yana kallon ta cikin hasken fitilar da aka ajjiye a soron ga hasken wayar sa da ya kunna gana waje wanda yake shigowa, bata d'ago ba shi kuma baiyi magana ba.
Jin shirun yayi yawa ya saka ta d'ago sai suka had'a ido karon farko tayi murmushi mai kyau tace, "Ina wuni." Jinjina da kujerar Anas yayi ji yayi in bai jingina ba iskar soyayya da take kad'a zata iya d'auke shi ta kai shi wani wajan shiyasa ya nemi mafita tun da wuri. Bai jima sosai ba ya kalle ta yace, "Dan Allah ki sake min murmushi da kika yi yanzu." Bata san lokacin da murmushin ya sub'uce mata ba ya sauke ajiyar zuciya yace, "Na gode my love, Allah ya biya ki da aljanna."
"Baka amsa ba na gaishe ka" ta furta a hankali.
"I'm sorry My love, murmushin da kika yi min a karon farko a rayuwa ta ya saka na manta duk abinda kika ce. Lafiya lau ya jikin ki?."
"Da sauk'i."
"Allah ya k'ara lafiya. Kiyi hak'uri na nemi wayar Baba lokacin da abin ya faru ban same shi ba, ina can hankali na yana kan ki Rauda duk da tarin aiyukan da suka min yawa."
A sanyaye tace, "haka Allah ya k'addara, babu komai a hakan ma na gode sosai, mun ga abubuwan alkhairi Allah ya saka da alkhairi ya biya buk'ata. Umma tace nayi maka godiya sosai." Murmushi yayi yace, "Babu komai Rauda kar ki damu."
Shiru ya sake biyo baya kafin yace, "Munyi magana da Baba akan aikin k'afar ki in sha Allah tafiyar ki zata dawo kamar dah indai ina da rai tunda aikin ba wani mai wahala bane indai aka bar nigeria, cikin satin nan in Allah ya amince za'a yi aikin." D'ago ido tayi suka had'a idanu yayi murmushi sai tace, "Na gode."
"Haba Rauda ni dake babu godiya wallahi, fatana ki amince da soyayya ta ki yadda dani har ta kai mu ga aure."
Murmushi tayi kad'an bata ce komai ba domin ita kam bata d'auka zai sake dawowa inda take ba sabida lalurar da ta same ta.
"Naga kin gaji sosai ga sallah ana yi, zan koma amma in sha Allah gobe zan yiwa Baba bayanin aiki da za'ayi in sha Allah." Kai ta girgiza kafin tace, "Allah ya saka da alkhairi."
"Amin. Amma kin san wacce irin addu'a nake so kiyi min?."
Kai ta girgiza alamun a'a yace, "Ki min addu'a Allah ya mallaka min ke a matsayin matata." Murmushi tayi sai tace, "Ban d'auka zaka yi wannan fatan ba duba da irin iftila'in da ya same ni." Murmushi yayi yace, "Wai da sai na guje ki kenan?."
Ya sake yin murmushi yace, "Ni Rauda nake so ba abinda yake tare da Rauda ba, zuciyar Rauda nake so ba gangar jikin Rauda ba. Ilimi, halayya, tarbiyya, nutsuwa, iya magana, girmama na gaba, su nake so a tare da Rauda ba k'afar ta ko hannun ta ba. Rauda a yadda nake jin ki a zuciyata ba fata nake ba ko ido da k'afa da hannu kika rasa wallahil azim ni mai iya auren ki ne, soyayyar gaskiya nake miki ba soyayya dan wani abun ba. Ina fatan ki fahimta?."
Murmushi tayi mai d'auke da jin dad'in kalaman sa ko babu komai ta tabbatar da soyayyar ta ta gaskiya ce a zuciyar sa tace, "Na amince da duk abinda ka fad'a, ina kuma alfahari da hakan." shima yayi murmushi yana kallon ta yace, "A karo na farko da nake ganin murmushi a kan fuskar ki har kike min doguwar magana haka lallai addu'ar da nake ba dare ba rana Allah ya karb'a ya kuma fara biya min." Murmushi ta kuma yi ya kalli agogo yace, "Ana ta sallar i'sha zan tafi."
"Ka gaida gida da mutanen gidan."
"Zasu ji in sha Allah. A gaida Umma da kowa da kowa." Ta amsa da to kafin suyi sallama ta koma cikin gida.
Sallah Umma ta samu tana Khalil ya d'auko mata kujerar ta ta zauna dan ita ba sallar zatayi ba, bayan Umma ta idar da sallah Inna ma na zaune ita da Rahma Umma tace, "Har ya tafi?." Kai ta d'aga alamun eh.
Baba ne ya shigo da sallama suka amsa ya nemi waje ya zauna yana fad'in, "Ke Rauda Anas yace zai biya ko nawa ne ayi miki aikin k'afar ki, zuwa gobe zan nemi likitan da ya amince da aikin sa ayi komai a gama."
Umma ta kalli shi tace, "Amma malam hidimar yaron nan bata yi yawa ba? Ka duna irin abubuwan da aka kawo mana fa yanzu kuma ya kuma biyan kud'in aiki...? Bafa ayi auren nan ba kar a fara zagin mu a gari."
"Bafa rok'on sa mukayi ba shi yayi niya ya bayar."
"Allah ya saka masa da alkhairi ya biya shi" Umma ta fad'a kawai dan babu yadda zatayi.
Baba yace, "Abinda ya kamata kice daman kenan." Yana fad'a ya juya zai fita Inna tace, "motar kwadayi in ka hau zata sauke ka a tashar wulaqanci." Juyowa yayi ya kalle ta yace, "kinga munafurcin ki da bak'in cikin ki shine ya saka ga y'ar ki nan a zaune kusa dake babu wanda yake tayawa, kuma wallahi in baki kiyaye ni ba sai na bayar da ita sadaka a masallaci."
Bata ce komai ba ta mik'e ta shiga d'aki Rahma ma ta bi bayan ta yaja tsaki ya fita. Umma ta kalli Rauda bayan sun bar wajan tace, "Rauda kin masa godiya yadda ya kamata kuwa?."
"Nayi Umma."
"To ya kike jin sa a ranki yanzu? Nidai ina miki sha'awar auren sa badan yana da abin hannu ba sai dan yana son ki, duk da abinda ya faru dake bai guje ki ba sai ma sake bibiyar ki da yake yi wannan alamu ne na masoyin gaskiya."
Shiru Rauda tayi bata ce komai ba Umma tace, "kiyi tunani ki kuma yi addu'a in shine alkhairi Allah ya tabbatar, in ba alkhairi bane Allah ya watsar da maganar ya kawo miki mai alkhairi." Shiru nan ma tayi bata amsa ba ta lumshe idanun ta nan take fuskar Asad ta ziyarci fuskar ta sai ta bud'e idanun ta tana tsaki.
Umma ta kalle ta ganin bata ce komai ya saka ta ja bakin ta itama tayi shiru.
*☆☆☆*
Asad yana barin wajan a mota gida ya koma dan ya samu kiran mai martaba, yana ajiiye mota b'angaren mahaifin sa ya nufa aka yi masa iso ya shiga ya same shi kad'ai kamar ko da yaushe a zaune a falo. Da sallama ya shiga yayi masa izinin zama ya zauna kafin yace, "Barka da dawowa, da fatan an dawo lafiya." Mai martaba yace, "lafiya lau, ya jikin naka?."
"Na samu lafiya."
"Amma yanayin ka bai gwada hakan ba."
Shiru Asad yayi bai ce komai ba mai martaba yace, "Asad yanayin ciwon da nake ji a jikina kullum sake gaba yake yi, bana son Allah ya d'auki raina ban bada amanar talakawana a hannun nagartaccen mutum ba, dan haka zan dawo da bara bana."
Asad yace, "Amma Takawa....." Mai martaba ya dakatar dashi yace, "Abinda za'ayi kenan Asad, kai kad'ai ne nayi istikhara akan haka yfi sau babu adadi tunda kaga ina ta maimaita maganar ka d'auka kaine alkhairin katagum. Har yanzu kana mafaran da ka fad'a min?."
Asad yace, "Na kwana biyu banyi ba." Kai ya girgiza kafin yace, "ka cigaba da addu'a ka kuma cigaba da kula ba komai zaka yarda dashi ba, mak'iyan ka na kewanye da kai. wanda kake d'auka masoyin kanewani lokacin shine mak'iyin ka, wanda kake d'auka makiyin ka wani lokacin shine masoyin ka."
Asad cikin gamsuwa yace, "in sha Allah za'a kiyaye."
"Mahaifiyar ka ta sanar dani tayi maka mata za'a gaggauta maganar auren ka ana gama shagalin bikin zan sauka daga karaga na baka." Shi dai Asad bai iya cewa komai ba dan ba wannan ne a zuciyar sa ba, zuciyar sa bugawa take yi da sauri har sautin ta yana ji a kunnen sa.
Mai martaba yace, "zaka iya tafiya."
"Godiya nake, a tashi lafiya" ya fad'a da girmamawa ya fita mai martaba ya bishi da kallon burgewa da kuma sha'awa.
Sai da akayi sallah ya shiga wajan Mama ya samu bata nan ya k'arasa ciki inda Hydar yake yana nan kwance kamar koda yaushe.
Yana fitowa daga d'akin ya ganta a zaune a kan kujera tana waya yadda take maganar ya tabbatar da k'anwar ta take waya, zama yayi a gefen ta yana sauraron ta kammala wayar. Bata jima sosai tana wayar ba ta yanke ta kalle shi tace, "lafiya na ganka wani iri?"
"An nemi a k'asar Dubai zanyi....." ganin yadda ta d'aure fuska sai ya kasa k'arasa maganar yayi shiru tare da sunkuyar da kansa.
Fuska a d'aure tace"kalle ni." Ba musu ya kalle ta tace, "ko k'asar Dubai zasu d'auka su mallaka maka baza kayi ba Asad, zaman ka a nan shine burina ba barin ka k'asar ba. Akwai abinda ka nema ka rasa ne a nan d'in?." Kai ya girgiza alamun a'a tace, "to kar na sake jin irin wannan maganar a bakin ka, hukunci ne na yanke babu kai babu wani aiki sai na mulkin garin nan."
"Toh. Allah ya wuci zuciyar ki." ya amsa a tak'aice.
"Ya kuka yi da mahaifin ka?."
"Babu komai." Ta d'auke kanta daga kansa kafin tace, "kaji