Showing 75001 words to 78000 words out of 92772 words
Chapter 26 - KWANTAN BAUNA BOOK 1 COMPLETE by Nana haleema.txt
ba." Baba yace, "Bashi bane ba? Kuma Rauda ba wasa yake miki ba kuwa?."
Rauda tace, "Ya rantse min da Allah akan bashi bane ba." Baba cikin mamaki yace, "To amma dashi muka yi maganar ta kawai, da shi muka yi maganar keke napep d'in nan ya akayi wani daban yasan da ita?." Umma tace, "abinda ya d'aure min kai nima kenan." Shiru Baba yayi sai shiru can kuma yace, "Koma dai waye tunda ba sata nayi ba ai shikenan, ban kuma rok'i mutum ba Allah ne ya kawo min tsuntsu daga sama a gashe akan me zan ki ci ni kuwa?."
Umma tace, "Amma malam ya kamata a bincika." Baba yace, "Na bincika ina? Nida ke da kowa bamu sanshi ba ina zanje na bincika nace ga wanda nake nema nida ban sanshi ba?; kar ki d'aga min hankali ina zaune lafiya dan Allah."
"Assalamu Alaikum!" Aka fad'a daga soron gidan aka wuce Baba suka shigo cikin gidan mata uku maza biyu sai Mum ta hud'u. Baba da yake kallon ikon Allah ganin maza garada sun shige shi sun shiga tsakar gidan sa kai tsaye babu izinin sa ya k'araso yana kallon su yace, "Malamai lafiya kuka shigo min gida kai tsaye haka?."
Mum ta k'are masa kallo ta kalle gidan tace, "Au wai wannan gida ne?, ni na d'auka wani kango wanda y'an zaman banza suke zama suna shaye-shaye da yiwa yara fyad'e muka shigo, wai ashe gida" ta fad'a tana kallon wanda suka shigo sai suka fashe da dariya har da tafawa. Rauda ta kalle su tace, "Malamai lafiya zaku shigowa mutane gida kai tsaye?." Jin yadda tayi maganar cikin tsiwa ya saka Mum kallon ta tace, "Oh kece gurguwar kenan, astagafirullah" ta fad'a tana dariya kafin tace, "Yadda aka kwatanta min munin ki ma ashe kin wuce wajan, wannan sai kace ragowar y'an wuta; wanne bak'in zunubi kuka aikata kuka haifo wannan?" Mum ta fad'a tana kallon Baba tana nuna Rauda.
Rahma ta mik'e tace, "Dallah malamai me ya kawo ku gidan mu har kuke fad'a mana maganar banza?." Mum tace, "Koma gefe keda uwar ki y'an kallo ne. wajan ita da uwarta da uban ta muka zo ba ku ba, so ki tsaya kiyi kallo in kina da waya ki d'auko ki fara d'aukar video."
"Wacece ke da zaki zo kina fad'a mana maganar banza da wofi?" Umma ta fad'a tana mik'ewa tsaye. Baba yace, "Malama lafiya me ya kawo ku gidan nan?." Ta juya ta kalli Baba tace, "Jan kunne nazo nayi muku gabad'ayan ku akan gangancin da kuke neman aikatawa, ina so ku jawa y'ar ku kunne ta fita hanyar wanda take cikin hanyar sa, babu shi babu ita domin shi d'in ba sa'an ta bane tazarar su kamar tazarar sama da k'asa ne. Yafi k'arfin ta ya kuma fi k'arfin dangin ku gabad'aya."
Baba da gaban sa ya fad'i nan take Anas yazo ransa amma baice komai ba sai yace, "Akan wa kuke magana?." Mum ta gyara tsayuwa ta tofar da yawu tace, "Wannan gidan ai sai ka d'auki ciwo, bari kuga" ta fad'a tana d'auko facemask a jaka ta saka sannan tace, "Ina magana ne akan ASAD! Wanda kuka kamowa kurwa kuka asirice shi baya ganin kowa sai waccan bak'ar annobar, kaja mata kunne zata d'auko ruwan dafa kanta matuk'ar bata fita hanyar sa ba zatayi dana sanin da bata tab'a yin irin sa ba har abada."
Rauda dake zaune cikin fusata tace, "Waye Asad? Meye shi suna ne ko gari?, mutum ne ko aljani?" Ta fad'a cikin masifa tana kallon Mum da ba ita take kallo ba. Mum ta juyo ta kalle ta tace, "kin sanshi ai basai na fad'a miki ba, tunda har kuka iya bin bokaye kuke so ku kamo zuciyar sa ai kinfi kowa sanin sa. ke banda tsaurin ido ma da kwad'ayi irin na jikar talakawa ina ke ina Asad?, kalle ki fa kamar wacce aka d'auko daga cikin bak'in gawayi, tsabar bak'in da yake fuskar ki sai a d'auka jikar shaid'an ce ke, kalli k'afar ki abinda ya rage miki hawa kan titi ki fara bara amma ki fara tunanin Asad dan talauci ya toshe miki kwakwalwar ki."
"Kece dak'ik'iya mara hankali wacce bata san darajar d'an adam ba babu girma sai na jiki, shi wanda kike magana a kai bansan da zaman sa bama balle na d'aga idanuna na kalle shi, dan haka kija bak'ak'en k'afafun ki a fitar mana daga gida" ta fad'a cikin rashin kunya tana mata ihu. Mum ta girgiza kai tace, "lallai yarinya zan nuna miki ni ba sa'ar yin ki bace, ga sa'a ta nan" ta fad'a tana tsinkawa Umma dake tsaye mari ba zato babu tsammani. Baba ya yunk'uro zai zo wajan mazan suka rike shi gam ta juya yana kallon sa ransa a b'ace yace, "Ke wacce irin mahaukaciya ce shashasha? Ya zaki shigo har cikin gidana ki saka hannu ki daki matata?."
"Dan na nunawa y'ar ka itace abokiyar yina ba ita ba, kuma....." saukar marin da taji a tata fuskar ya hana ta k'arasawa ta juyo a razane taga Rauda a tsaye da sandinan ta tana wuci cikin b'acin rai Mum na juyowa a fusace Rauda ta sake bata wani sabon marin da batayi tsammani ba. Cikin fusata da rashin kunya da yatsa ta nuna ta tace, "A kaf duniya babu wanda ya isa ya tab'a min iyayena k'yale shi ciki kuwa har dake, in zafin kai kike ji dashi na fiki, in rashin kunya ce itama na fiki, in iskanci ne shima na fiki, duk abinda kike ji dashi a tafin hannuna kike na dame ki na shanye. Na rantse da Allah kika sake dukar min uwa ko kika sake tab'a min uba sai na sake marin ki sai naga abinda zaki min. Banza babbar banza mara hankali mai tunanin jakuna" ta fad'a tana hararar ta cikin b'acin ran da ya bayyana k'arara a ka fuskar ta.
Mum da take kallon ta hannun ta dafe da kuncin ta kasa cewa komai tayi sai jikinta da yake rawa sosai alamun b'acin rai tsanar ta na shiga ko wanne sak'o da lungu na jikinta, tunda take ba'a tab'a tozarta ta kamar yadda akayi mata yau, yarinya k'arama ta fad'a mata wannan magana mai zafi har ta mare ta..?. Hannu ta saka da k'arfi ta tankad'e Rauda ta janye duka sandinan ta kalli matan tace, "Me kuka jira ne ku fara aiwatar da abinda ya kawo mu ku nuna musu mu ba sa'anin su bace" ta fad'a tana marin Rauda da k'arfin gaske. Nan da nan suka shiga dukan Umma da Rauda kamar Allah ya aiko su Inna da ta shigo lokacin ita da Rahma suka zo ceto aka had'a dasu ana duka Baba yana hannu an rik'e shi ya kasa komai.
"Asad yafi k'arfin ta ku sake b'alla k'afar tata dan uban ta" Mum ta fad'a tana daga gefe ana dukan Rauda kamar zasu kashe ta. Baba yace, "Waye Asad din nan da kike magana a kansa? Bamu sanshi ba balle muyi abinda kuke so. Dan Allah ku bar dukan su ko waye zata rabu dashi."
"Ai ko baka ce ba sai ta rabu dashi, ka kuma ce mata ta karya asirin da ta yi masa in tana son zaman lafiyar ta da ta uwar ta har ma da kai ubanta. Ta fita daga sabgar Asad d'an sarki sai y'ar sarki ko y'ar mai kud'i ba d'iyar talaka y'ar tallah kamar ta ba."
Ganin sun duku ya saka tace, "Guys ku shigo ku d'aye min kwanukan rufin gidan nan naga inda zasu kwana yau daman naga langa-langa ne kawai" ta fad'a daga k'arfi sai ga maza uku sun kuma shigowa suka hau saman d'akin suka farar b'alle kwanon rufin d'akin wanda yayi gardmar cirewa suna huda shi da abu mai kaifi. Mum ta saki dariya tana tafa hannu ta kalli Rauda da bakin ta ya fashe jini na zuba a gefe tace, "Ke ba y'ar marasa kunya ba...? yanzu kika fara gani, har ni zaki saka hannu ki mara da yake baki da mutunci ko? ai kin tarowa kanki bala'i da masifa har ki mutu. Ku k'yale su haka kuzo mu wuce ai ko yanzu sun ji a jikin su; sai ku ja mata kunne in bata fita daga rayuwar Asad ba wallahi nan gaba sai mun saka an rushe gidan nan an kuma yi musu abinda yafi haka, banzaye mahaukata masu kai kansu inda Allah bai kaisu ba" tana fad'a ta shige ta fita suma suka bi bayan ta mazan saman suka diro suka bi bayan ta.
Suna sakin Baba yayo kan Umma a guje dan ita kamar bata numfashi ma gwara Rauda tana motsawa amma Umma na kwance sosai. Kuka Rauda take yi sosai Rahma da ta maku tana gefe ganin sun tafi ya saka tayo kan Rauda ta d'aga ta fuskar ta duk jini hawaye na bin fuskar ta. Baba ya fita da sauri hankalin sa a tashe ya yi sa'a mai chemist d'in yana nan ya tawo dashi gida aka fara duba Umma da take kwance. Fita yayi ya dawo da kayan aiki aka shiga yiwa Umma taimakon gaggawa aka samu ta farfad'o dukan fuskar ta aka gyara aka saka mata ruwa dan jikin ta yayi zafi sosai ga hannun ta an mata targed'e. Kan Rauda akayi aka gyara mata fuska aka bata maganin ciwon jiki dana ciwon da taji a fuskar ta har loksckn kuka take. Ba kukan dukan take ba kukan zuwa gida da akayi aka wulaƙanta su take yi in ta kalli Umman ta bata sanin sanda hawaye yake sake zubo mata.
Yana fita aka zo da mai gyaran targad'e ya gyara hannun Umma aka d'aure hannun sannan suka tafi Baba jikin sa duka yayi sanyi.
Kuka sosai Rauda take yi tana jikin Rahma Baba yace, "Rauda ban fahimci abinda matar nan take nufi ba, meye tsakanin ki Asad har hakan ta faru?." Kai take girgizawa tace, "Wallahi babu komai Baba, bansan wanda suke nufi ba; sun yi amfani da power sun zo sun wulak'anta mu sabida bamu da gata bamu da wanda zai bi mana hakkin mu. Wallahk Baba bazan yarda ba sai maganar nan taje gaban hukuma sai an bi mana hakkin mu, Baba sai an karb'a mana hakkin mu bazan amince da wannan cik mutuncin ba" ta fad'a tana kuka sosai.
Baba yace, "Nima bazan bari ba Rauda cin kashin yayi yawa. Tunda sukayi maganar Asad d'an sarki zanje wajan mai martabar da kaina na kai masa k'arar abinda ya faru, ai talauci ba hauka bane ba. Meye tsakanin mu dasu in ba silar ciwon nan naki ba? Dan kawai yana sauke nauyin da yake kansu na nema miki lafiya kawai sai azo har gida ayi mana wannan shirmen...? To wallahi bazan amince ba." Kuka take ita dai har lokacin tana kallon saman d'akin Umma da aka kwashe kwanon kai rana tar a cikin sa sai wani b'angaren da aka huda, a hankali bacci ya d'auke ta Allah ya saka akwai inuwar rumfa a wajan.
*☆☆☆*
B'angaren Asad bai san me yake faruwa ba suna tare da Hydar a company dan bai koma aiki ba yana wajan Asad, sai da sukayi azahar suka bar company suka koma gida dan yunwa Asad yake ji. Suna b'angaren su Suhaima tazo ta kawo musu abinci ta ajjiye ta zuba musu kamar ko yaushe, Asad ya d'auki wanda ta zuba masa ya d'auka zai kai bakin sa Suhaima ta kalli Hydar tace, "Yaya Hydar wai me ya faru ne naga ran Mama a b'ace?."
Hydar ya fara cin abinci kana yace, "Ina zan sani Suhaima nida na dawo yanzu?."
"Naji tana waya tana a dake su bata kai matsayin yin soyayya da wanda ta haifa ba, na d'auka ma ko kaine ka fara soyayya da wata poor lady d'in ta saka ayi mata punishment." Gaban Asad ya fad'i ya ajjiye cokalin daman tunda ta fara maganar bai kai abincin bakin sa ya kalle ta yace, "Suhaima me kika ji tace?."
"A yadda take maganar dai an tura gidan su yarinyar ayi mata duka amma ban san wacece ba. Naji tana a dake ta inda dama a sake b'alla k'afar ta babu abinda aka siya ayi." Mik'ewa Asad yayi ya d'auki key na mota da sauri ya fita, ganin hakan Hydar ma ya ture abincin ya mik'e tare da bin bayan sa suka fita Suhaima ta bi su da kallo.
Mota suka shiga suka tafi gidan su Rauda gaban Asad sai fad'uwa yake yi har suka faka a k'ofar gidan, babban burin sa bai wuce Allah yasa basu illatata ko wani nata ba.
Baba suka gani ya fito yana waige-waige ganin hakan ya saka Asad ya fito daga motar Hydar ma ya biyo bayan sa suka k'araso kusa dashi, Baba na ganin su tun kafin su gaisa yace, "Kamar kusan kune a raina, me muka yi muku haka da za'a aiko azo a ci mutunci na dana iyalai na?, me Rauda tayi muku har haka aka yi mata wannan hukunci....? dan Allah ku fad'a na baki hak'uri."
Asad ya kalli Hydar shima ya kalle shi kafin Hydar ya kalli Baba yace, "Baba meye ya faru?." Baba yace, "Kuzo muje ku gani" ya fad'a yana yin gaba suka bi bayan sa gaban Asad sai fad'uwa yake yi sabida fargaba da tashin hankalin abinda zai gani a cikin gidan.
*KWANTAN ƁAUNA*
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*022.*
A hankali suke takawa zuwa cikin gidan suka shiga da sallama idanun sa ya fad'a na Rauda da take zaune cikin ranar da bud'e har taje inda suke fuskar ta duk taji ciwo musamman bakinta da ya fashe. Runtse idanu Asad yayi ya kawar da kansa gefe daga kallon ta kafin Baba yace, "Kunga irin abinda aka yi mana. kalli mahaifiyar Rauda har targad'e aka yi mata, ga ita kanta Rauda da ta kasa tashi tsaye tun da akayi abun bamu sani ba ko an sake karya mata k'afa ne; kalli saman d'akin babar Raudan sun cire kwanon bayan sun dake ta. Me muka yi muku haka?."
Hydar ya gyara tsayuwa yace, "Kuyi hak'uri Baba bamu san abinda ya faru ba kenan sai yanzu muke jin labari shine muka tawo nan d'in kai tsaye dan muyu maganin abun, Mama kiyi hak'uri bamu san abinda ya faru ba kenan" ya fad'a yana kallon Umma. Rauda ta kalle shi ta zaro idanu waje cikin zallar b'acin rai da tashin hankali tace, "Ba tun yau ba daman in aka cuci mutum sai ace yayi hak'uri, in aka zalumci talaka sai ace yayi hak'uri ya yafe sabida bashi da gata da wanda zai shige masa gaba ya karb'i hakkin sa. dan an fimu kud'i da mulki ba hakan yana nufin an mufi daraja a duniya bane, muma mutane ne baza mu lamunci azo har cikin gidan mu a ci mana mutunci sannan a dake mu ba kuma ace muyi hak'uri; bazai yu ba wallahi. Meye ya had'a mu daku da za'a dake mu a kanku? Tsautsayi ne ya ratsa tsakani fa akwai shikenan sai ya zama abin tashin hankali?, naga tun kafin bayyanar ku cikin matsayin wanda suka bige mu ai rayuwar mu muke yi babu abinda muka nema muka rasa, daga shigowar ku rayuwar mu har an fara neman raywuar mu?" Ta fad'a cikin fusata da masifa tana kallon su dukkan ranta a b'ace ba.
Hydar yazo wuya ba'a tab'a yi masa irin wannan fad'an ba a duniya sai yau nan take ransa ya b'aci amma babu yadda ya iya yayi k'okarin b'oye fushin sa kana yace, "Na fad'a miki ko meye ya faru babu sanin deaf babu sani na, inda mun sani hakan ai baza mu bari ta faru ba. Yanzu ake sanar damu muka tawo dan muga su waye amma bamu same su ba, meyasa baza ki fahimta ba?."
"Zuwan ku d'in banza da wofi dashi gwara ku zauna a gida ku sha a.c yafi min wallahi. Sai da aka gama ci maa mutunci sannan zaku d'auko k'afa kuce wai kunzo to kuyi mana me? Ku bamu hak'uri kenan ko?. Ni abinda nake so naji ma akan wanne dalili zasu dake mu har su yiwa Ummana wannan rashin mutuncin?, suna zancen wani Asad ni meye had'ina da wani Asad?, su ya dama bani ba wallahi in ma wani sharrin aka je aka min can ta matse muku amma wallahi sai maganar nan taje gaba in ba haka ba na shiga radio na yayata abinda aka mana ko babu komai k'imar gidan ku zata ragu."
Hydar ya kalli Asad da ya zuba mata idanu kawai yana kallon ta ya girgiza kai yana cize bakin sa cikin zallan b'acin ran da yake ji a zuciyar sa, in badan Asad ba ta isa ta dinga fad'a masa wannan kalmai marasa dad'in jin ya tsaya yana kallon ta bai hukunta ta ba?. Ya daure yace, "Ni da kaina nace kuyi hak'uri muje a fara yi muku magani kafin komai." Kafin Baba yayi magana ta kuma cewa, "Bama so ku rik'e kayan ku talakawan da ake rainawa sun yiwa kansu magani kuma zasu karb'arwa kansu hakkin kansu."
"Wai ke meye haka ne? Ina baki hak'uri kina sake d'aga min murya kina fad'ar duk abinda yazo bakin ki?, wani dalili kawai ya saka nake tsaye a gaban ki ina baki hak'uri amma badan shi ba bazan zo inda kuke bama balle ki samu bakin fad'a min abinda kike so. Na fad'a miki kuyi hak'uri zaku ji abinda ya jawo hakan wanda ban sani ba shima wanda akayi dukan dan shi bai sani ba, meyasa kike haka ne?" Ya fad'a cikin fad'a yana kallon ta ransa a b'ace. Zata kuma magana Baba yace, "Muna so muji dalilin dan gaskiya sai maganar nan taje kunnen mahaifin ku sai