Showing 27001 words to 30000 words out of 92772 words

Chapter 10 - KWANTAN BAUNA BOOK 1 COMPLETE by Nana haleema.txt

20 Jul 2024

17681

yana fad'in, "Allah ya fidda ni lafiya" ya Fad'a shima yana bin bayan ta.


Yana shiga ta kalle shi tace, "a had'a komai zamu tafi dashi gida." Kai ya girgiza da sauri ya fita aka had'a mota nan da nan aka turo gadon da yake kai aka saka shi a mota ita da Suhaima suka shiga bayan wata motar ta kalli Dr tace, "a tabbatar yarinyar nan ta bar asibitin nan."
"In Allah ya amince ranki ya dad'e." Daga haka aka ja motar aka tafi.


Har k'ofar apartment d'in ta aka je da motar aka bud'e da gaggawa aka tura gadon da yake kai zuwa cikin babban d'akin da yake kusa da nata, a kan gadon da yake kai aka barshi Dr ya jona masa abubuwan da aka tawo dasu ya tabbatar komai yayi sannan ya tafi. Kallon sa take ta zauna a gefe ta rik'e hannun sa jikin ta duk yayi sanyi domin abubuwan suna neman fin k'arfin ta.


B'angaren Asad bai san abinda yake faruwa ba dan bai ma kalli wayar sa ba ya fito daga d'aki zuwa falo babu kowa daman dai yasan Aliyu baya nan amma yayi mamakin rashin ganin Hydar, numfashi ya sauke ya juya zai koma yaji maganar Hajiya a bayan sa tana fad'in, "Asad."


Juyowa yayi yana kallon ta ya d'an saki murmushi kad'an yace, "barka da rana Hajiya."
"Barka ka son, ya komai da komai."
"Alhamdulillah" ya amsa yana d'auke kansa gefe.
"Mafarki nayi da mai babban d'aki daren jiya sai ta tuna min da k'aunar ka da zogale hakan ya saka ni shiga kitchen da kaina na had'a maka, ina fatan zakayi farin ciki?" ta fad'a tana mik'a masa bowl da aka rufe shi da foil.


Ba musu ya sanya hannu ya karb'a ya murmusa yace, "Godiya nake." Itama ta fad'ad'a murmushin ta tace, "Babu komai kar ka damu Asad" ta fad'a tana juyawa ta fita baice komai ba ya ajjiye bowl d'in ya shiga d'aki. Jim kad'an ya fito ya tarar da bowl d'in kamar yadda ya barsa ya zauna ya bud'e, zogalen ya burge shi sosai yaki kayan had'i yadda ya kamata hakan ya saka shi deba da hannun sa ya kai baki sai kuma ya dakata.


_Hajiya kamar Mama take baza ta bani abinda zai cutar dani ba, yeah baza ta cutar dani ba tana sona._ ya fad'a a zuciyar sa ya kai zogalen bakin sa yana taunawa a hankali. Sosai yayi masa dad'i ba kad'an ba dan ya jima bai ci ba ya cigaba da ci har ya kusa cinyewa sannan yaji ya ishe shi ya tashi ya bar shi a wajan ya shiga d'aki.
Yana fitowa daga d'akin yaga Mama a tsaye ita da Suhaima ya kalle ta ya durk'usa har k'asa yace, "barka da fitowa."


Bata kalle shi ba tace, "Daman yau a cikin abinda ake kawo maka breakfast har da zogale?." Mik'ewa tsaye yayi ya kalli bowl d'in ya kalle ta yace, "A'a Hajiya ce ta kawo min d'azu." Mama ta wara idanu tace, "wacce Hajiya kenan?."
"Hajiya dai."
"Amma dai baka ci ba ko?." Kallon bowl d'in yayi ya kalli Mama yace, "ki gafarce ni,na ci."


"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Asad why" ta fad'a a gigice tana kallon sa kamar zata zubar da hawaye. Marairaicewa yayi baice komai ba yana kallon ta, "Asad meyasa baka ganewa ne kai? Meyasa kake d'auka yadda zuciyar ka take mai kyau haka ta kowa take da kyau?, meyasa yadda kake ganin baza ka cutar da kowa ba haka kowa yake?. Baka san a yanzu ba abincin kowa zaka ci ba?, meyasa kaci abin hannunta?, akan me baka sanar dani kafin kaci ba?!" Ta k'arasa fad'a cikin fad'a tana kallon sa.


Runtse idanun sa yayi ya sunkuyar da kansa baice komai ba, sake tunzura ta yayi ganin yayi mata shiru tace, "baza kayi magana ba sai na mare ka?." D'agowa yayi ya kalle ta a sanyaye yace, "Allah ya wuci zuciyar ki."
"Asad meyasa kaci yanzu in ta zuba maka guba a ciki ka mutu fa? Ya kake so nayi kenan?." Nan ma shiru yayi baice komai ba ta rik'e hannun sa tace, "muje duk yadda zakayi ka amayar da abinda kaci zai maka illa Asad" ganin duk ta rud'e sai ya rik'e nata hannun shima yace, "Calm down Mama, babu abinda zai same ni sai Allah ya nufa."
"Asad tana so ta cutar da kai ba tun yau ba zata iya aikata komai wajan ganin ka cutu, kar ka kuma cin abin hannun ta dan Allah" ta fad'a kamar zata zubar hawaye tana kallon sa.


Kai ya girgiza alamun to yana kallon Maman tasa da girmamawa kamar ko yaushe kallon sa take itama kafin tace, "Baka jin komai a jikin ka?." Kai ya d'aga alamun eh kafin tace, "jikin Hydar ya tashi Asad kazo muje ka gan shi" ta fad'a tana fita shima ba musu ya biyo bayan ta. D'akin da yake suka shiga yana kwance kamar ko wanne lokaci Aliyu na tsaye a gefen sa yana kallon sa Asad ya k'arasa d'aya barin yana masa addu'a yana tofa masa a fuskar sa.


"Mama garin ya hakan ta faru?" Aliyu ya tambaya yana kallon Mama. Mama tace, "akan wata banza y'ar talakawa ya fita da safe, yarinyar nan da ya buge wai yaje dubawa da safe nayi masa warning akan zuwa inda take amma baiji ba gashi ya kwashi sanyi ciwon sa ya tashi." Aliyu ya tab'e baki yana kallon gefe baice komai ba.
"Assalamu alaikum, surprise" aka fad'a daga baya ana shigowa d'akin.


Dukkan su kallon k'ofar suka yi banda Asad da har lokacin yake wa Hydar addu'a, Suhaima ta wara idanu tace, "Sis oyoyo" ta fad'a tana hugging nata itama ta rike ta tana murmushi. Har k'asa ta duk'a ta gaisa Mama ta amsa da fara'a tace, "lallai kam surprise, ina Mum d'in?."


Murmushi tayi wanda ya bayyanar da asalin kyaun ta tace, "Mom tana gida. Mama Yaya Hydar ne babu lafiya?." Kai ta d'aga mata kawai ta k'arasa inda Asad yake tsaye tana kallon Hydar. Sai kuma ta kalli Asad da bai kalle ta ba ta d'an bugi kafad'ar sa tace, "Kana gani na ko magana babu ko bro? I'm sorry in kaji babu dad'i jiya bance maka zan zo ba, ina so na baka mamaki ne."


D'ago idanun sa yayi yana kallon ta nan take gaban ta ya fad'i ta d'an yi baya ta kalli Suhaima da take kunshe dariya tace, "deaf kenan, ga Bro Aly nan kina gani." Wara idanu tayi tana kulle bakin ta tana kallon Asad ya d'auke kansa daga kallon ta takaici kamar ya kashe shitace, "Sorry Boss."


In ta samu kallon arzuk'i ma da ta godewa Allah ta bar wajan ta koma inda Aliyu yake shima bai kalle ta ba tace, "Yau sai naga kai ka koma min shi shi ya koma min kai."
Irin kallon da ta samu daga wajan Asad shi yayi mata shima sai ta kalli Mama sai taga Mama tayi murmushi tace, "Yau suna so su rikita ki ne." Sai kuma Aliyu ya murmushi ya mik'a mata hannu alamun su gaisa.


Sai tayi murmushi ta bashi nata hannun suka gaisa kafin yace, "Welcome" yana furta hakan ya mik'e tsaye har lokacin hannun sa na cikin nata yana binta da kallo itama haka kafin ya zame hannun sa ya fita. Mama ta kalle ta tace, "Jidda kije ki huta, Asad kaje ina zuwa." A hankali yake takawa ya fita ta bishi da kallo tana murmushi Mama na kula da ita itama ta murmusa bata ce komai ba suka fita aka bar Hydar dake kwance.


Asad tunda ya bar wajan zuciyar sa take masa zafi har ya koma apartment d'in su ji yake kamar ya fashe da kuka sabida takaici. A bakin window ya tsaya yana furzar da iska mai zafin gaske jikin sa har zafi ya d'auka sabida takaici da zallar bak'in ciki. Ta yaya Mama zata ce wannan yarinyar ce zata kasance matsayin matar sa nan gaba?, yarinyar da a gaban sa take gaisawa da namiji wanda ya kasance yayan sa kuma jinin sa, kenan sun saba tunda gashi yana bata hannu ta bashi suka gaisa. dogon tsaki yaja lokacin da ya tuna dukan kafad'ar sa da tayi alamun sun saba ma irin wannan banzayen halayen da Aliyu.


Kowa yasan shi yana da kishi ko takalmi akace wannan mallakin sane tofa bai aminta yaga wani da takalmin ba sai shi kad'ai balle matar aure, kai yake girgizawa a hankali yace, "Mama bazan iya auren ta ba, I'm sorry" ya fad'a yana barin wajan.


So yake ya bar gidan yaje company amma ya kasa baya son fita gabad'aya wani irin abu yake ji a jikin sa kamar ana zare masa kuzarin jikin sa.
Zama yayi a kan kujera yana furzar da iska kafin ya buɗe idanun sa ya mik'e zaune yana wara idanun sa a bangon d'akin, dafe kai yayi ya jingina da kujera ya rasa gane fuskar yarinyar da yake mafarki da ita amma yana jin tashin amon muryar ta a kunnen sa amma fuskar ta tak'i tsayawa a idanun sa.
Ko yanzu yaji maganar ta zai iya ganewa amma banda fuskarta gashi ta maqale a zuciyar sa kowa ya motsa sai ya tuna da ita.


B'angaren Mama suna shiga d'aki ta kalli Jidda tace, "Amma kwanaki zaki mana ko?." Ta yi farrr da idanun ta kana tace, "A'a Ranki ya dad'e anjima da daddare zan wuce."
"To kije yanzu wajan Asad ku gaisa amma nasan Aliyu abokin kine ki daina nuna hakan a gaban Asad, lemme tell u something about your husband to be. yana da kishi, in ya nuna abu aka ce wannan naka ne yace kuma inaso to duk duniya babu wanda zaiyi amfani da abun nan sai shi kad'ai, in kuwa yaga wani ya rab'i wannan abin da yake so tabbas zai bar masa ne shi ya hak'ura. So u have to be very careful Jidda in kuna tare bakya ganin kowa sai shi koda Aliyun ne in ba haka ba zaku yi fad'a" ta fad'a tana kallon ta.


Juya idanu Jidda tayi jin abinda akace mata sai farin ciki ya mamaye mata zuciya cikin muryar ta mai dad'in ji tace, "In sha Allah zan kiyaye ranki ya dad'e, bara naje wajan sa" ta fad'a tana ficewa Suhaima ta bita da kallo ta kalli Mama tace, "Mama Asad da Jidda sunyi bala'in dacewa, wannan suka tashi haihuwar yara za'a ga larabawa." Murmushi kawai Mama tayi dan ita badan kyau ta had'a su aure ba akwai manufar ta kafin ta fita ya koma d'akin da Hydar yake kwance.


Asad yana zaune a inda yake aka shigo da sallama ya amsa ba tare da ya kalli wacce ta shigo ba yaji an zauna kusa dashi bai kalle ta ba tace, "barka da hutawa my Asad." Bai kalli inda take bama balle ta saka ran zai amsa. Daman tasan za'ayi haka tayi murmushi cikin shagwaba tace, "Kayi min magana mana." Nan ma bai kalle ta ba idanun sa a kulle suke.


"Dan kai fa na baro gida nazo nan amma shine baza ka kula ni ba?" Ta fad'a a shagwab'e. Nan ma banza babu amsa ta kuma cewa, "My Asad please." Numfashi ya sauke ya juyo ya kalle ta baice komai ba ya sake d'auke kansa yana cize baki lokaci d'aya yaji cikin sa na k'ullewa.


Ganin hakan sai tayi shiru bata sake magana ba dan tasan kallo na kin ishe ni ne hakan ya saka ta yin shiru tana kallon sa yana yamutsa fuska. Sun jima a haka a zaune kafin ya cize bakin sa ya furta, "Ya salam!." Mugun ciwo cikin sa yake yi bai san sanda ya furta hakan ba idanun sa lokaci d'aya sun canja kala zuwa jajaye haka fuskar sa ma tayi ja jikin sa har rawa yake yi.


"Asad!, Asad me ya faru!?" Ta fad'a tana kallon sa ganin lokaci guda ya canja. Idanun sa da taga ya kulle yana sauke numfashi hannun ta na rawa ta kira number Mama tana d'auka tace, "Mama Asad zai mutu! Kizo Mama" ta fad'a da k'arfi tana kallon Asad da yake jingine a kan kujera kamar baya numfashi..
*KWANTAN ƁAUNA*
FitattuBiyar 2023


©️ *Nana Haleema.*


*Book 1*
*009.*


Tunda Mama tazo inda yake hankalin ta yake a tashe tana zaune kusa dashi tana fad'in, "Asad me kake ji a cikin naka? Kayi min magana dan Allah. Yaushe ya fara yi maka ciwo? Me kake ji?, zafi yake kome?." Bud'e idanu yayi ya zauna sosai yace, "Mama, I'm okay fa."
"Ban amince ba Asad, kalli face d'in ka fa yadda ya koma, tashi muje asibiti da sauri daman nasan babu ta yadda za'ayi kaci abincin Hajiya ba tare da ka samu wani abun ba."


Hannun ta ya rik'e duk da ciwon da cikin sa yake masa yace, "Mama kar ki tayar da hankalin ki."
"Ta yaya bazan tayar da hankali ba Asad? Abincin fa ta baka kaci gashi har kana ciwon ciki wanda baka tab'a yi ba, hankalina kake so na kwantar ko me?." Shiru yayi bai amsa na kafin ya lumshe idanun sa yace, "bacci zanyi."
"Baza kayi bacci ba Asad sai munje asibiti, kar ka kulle idanun ka ka bud'e mu tafi." Suhaima ce suka shigo tare da Dr Yasir Mama na ganin sa tace, "Zo da sauri ka duba shi." Da saurin kuwa ya k'arasa yana yanayin jikin nasa yana tambayar sa abinda yake ji duk da yasan babu lallai ya basa amsa.


Allurar ciwon ciki yayi masa kafin ya d'ago ya kalli Mama yace, "Ranki ya dad'e ba wani abin tayar da hankali bane nayi masa allura zai daina ciwom." Jidda tace, "are you sure zai daina?."
"I'm very sure." Mama tace, "in akwai damuwa muje asibiti ko scanning ne ayi masa."
"A'a ranki ya dad'e zai ji sauk'i." Kai ta d'aga shi kuma ya fita da sauri baya so tayi masa maganar Rauda da take asibiti.
Aliyu da ya shigo a lokacin ta kalls tace, "Ka rik'e shi ku shiga d'aki ya kwanta, please Aliyu take care of him bana so wani abun ya same shi."


Mik'ewa Asad yayi ya tafi d'akin da kansa Aliyu ya kalli Mama yace, "basai na taimaka masa ba kin gani" yana fad'a ya shiga d'akin da yake kusa da na Asad d'in ya kullo k'ofa. Fita Mama tayi suma su Suhaima suka fito suka ga ta mik'e alamun b'angaren mai martaba zata je su suka kuma koma ciki.
Mai martaba yana zaune shi kad'ai kamar ko yaushe aka mata izinin shiga ta shiga da sallama ta nemi k'asa ta zauna tana kallon wani wajan daban.


Ganin hakan sai ya murmusa yace, "Rabi'atul adawiya ya akayi ne?."
"Allah yaja da ran mijina burin mutanen gidan nan suga bayan y'ay'ana me suka tare musu? Hydar gashi can ciwo ya tashi, ga Asad ma Hajiya ta bashi zogale yaci gashi can a kwance yana ciwon ciki. Ya suke so nayi ne me na tare musu?." Mai martaba ya mik'e daga kashingidar da yayi yace, "Ciwon Hydar ya tashi baki sanar dani ba?." Ta kalle shi tace, "Na rud'e ne gabad'aya ana kira na naje asibitin da je duba wata yarinyar da ya buge a can ciwon ya same shi na dawo dashi nan, ga Asad ma a kwance ya suke so nayi ne?" Ta fad'a kamar zatayi hawaye.


Mai martaba yace, "kar ki zubar da hawaye ban sanki da raguwar zuciya ba ki daure kamar yadda kike daurewa a koda yaushe. Yanzu ya jikin Asad d'in?." Idanunta ta goge tace, "yayi bacci. zogale yaci wanda Hajiya ta bashi daman na tabbatar ba da zuciya d'aya ta bashi ba, yanzu gashi can a kwance babu lafiya, burin su suga Asad ya mutu sai sun kashe sa hankalin su zai kwanta."


Mai martaba ya kalle ta sosai yace, "bana son zargin da kike saurin yi ki fara tabbatar da abinda kika ga gani kafin ki yanke hukunci."
Bata ce komai ba hakan ya saka ce sake cewa, "kar ki damu duka zasu samu lafiya babu wanda ya isa yayi musu abinda Allah bai nufa ba, Asad yana da ibada sosai k'aramin abu ko babba bazai kama shi ba sai wanda Allah ya nufa. Hydar zai samu sauk'i nan kusa ki daina tayat da hankalin ki."


Bata ce komai ba a nan ma amma ta d'an ji sanyi a zuciyar ta yace, "muje na duba jikin su da kaina" ya fad'a yana mik'ewa tsaye ita kuma bata mik'e ba. Ganin hakan ya saka hannayen sa da kansa ya mik'ar da ita tsaye yana kallon fuskar ta da murmushi yace, "kar ki bada ni mana, ko yaushe ina fad'in ke jaruma ce samu mace mai irin tsayayyiyar zuciyar ki abu ne mai wahala ya zaki bani kunya kum?. Come on ban san ki da haka ba, muje."


Tare suka fito ganin fitowar mai martaba babu tsammani aka tawo a guje aka saka masa takalmi aka bud'e lema tana takawa a hankali tana gefen sa ana zuba masa kirari har cikin d'akin da Hydar yake. Daga shi sai ita sai shamaki a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login