Showing 69001 words to 72000 words out of 92772 words

Chapter 24 - KWANTAN BAUNA BOOK 1 COMPLETE by Nana haleema.txt

20 Jul 2024

17692

"ban sani ba ai da banje na same shi yanzu ba tunda komai ma ya wuce. Amma nayi murna da za'a yi miki aikin k'afar nan Allah ya sa ayi a sa'a."
"Amin."
"Kika dinga zagin wanda ya kad'e ki kina ganin kamar wasa ne babu wani rashin lafiya ashe gashi wanda muka sani ne ma."
"Wallahi kuwa, na d'auki hakki."


"Ina Anas ne wai?." Rauda tace, "Yaje Abia."
"Masoyin ki kenan, wai har yanzu baki bashi dama ba?."
"Na bashi Habiba tunda ina sauraron sa yanzu. Tunda ya siya min maganin da aka wulak'anta ni a kai ya kawo mana kayan abincin da ko rabin rabin sa bamu ci ba wallahi nake ganin k'imar sa sosai. Ta silar abincin nan Baba ya daina d'orawa Rahma tallah."


Habiba tace, "Ai yana son ki wallahi zaiyi komai sabida ke; Allah ya saka masa da alkhairi."
"Amin."
"Kin fara son sa kenan?."
"Ina fa, kedai Allah ya kyauta." Habiba tayi dariya ta amsa da amin kafin su cigaba da hira suyi sallama ta tafi.
Maganar Habiba ta dinga tunawa musamman halayen Asad sai taji ya burge ta sosai ko babu komai baya wulak'anta talakawa kamar Aliyu.


B'angaren Asad bai dawo ba sai dare direct ya wuce b'angaren mahaifin sa sai da aka bashi izinin shiga sannan ya shiga, baya babbar fada ta farko ya shiga ta biyu nan ma baya nan hakan ya bashi tabbacin yana d'aki kenan. Shi kad'ai mai martabawa yake lamuncewa ya shiga amma gudun kar ya shiga ya tarar da wata matar tasa a ciki ya saka yaja tunga tunda ba girkin Mama bane ba. Kamar kuwa ya sani yana nan tsaye Ammi ta fito ganin sa ya saka tace, "Asad daman kai yake nema kuwa, kaje ciki" ta fad'a tana wucewa shima ya shiga d'akin da ya san mallakin mahaifin sane.


A zaune ya same shi a kamalance ya k'arasa ya zauna a akan carpet yace, "Barka da dare Takawa." Murmushi yayi yace, "Barka dai Asad."
"Ya k'arfin jikin?."
"Jiki Alhamdulillah ana ta samun lafiya."
"Allah ya k'ara lafiya yasa kaffaara ce."
"Amin Asad. Allah ya yi maka albarka ka rayu cikin aminci da walwala."


A labban sa ya amsa da amin kafin mai martaba yace, "Ya batun zuwa taron malamai masu shekarun naka a Dubai?."
"Mama ta hana Abba" ya furta a sanyaye.
Kai ya girgiza yace, "Rabi'atu manya, ko kad'an bata so kayi nisa dani gudun kar ka tafi a bawa wani sarauta ba kai ba, tana mantawa da Allah ya riga ya rubuta wanda zai gaje ni."


Shiru Asad yayi bai ce komai mai martaba yace, "Ta hana ka aikin da kake mafarki tun kana yaro, ta hana ka komawa Dubai kamar yadda sarkin su ya nema, ta hana ka aiki da Saudia yanzu kuma ta hana ka zuwa taron kwana bakwai kacal; in kana so ka shirya ka tafi na baka damar hakan."
"Allah yaja zamanin mahaifina, tunda tace na bari na bari d'in."


Mai martaba yayi murmushi mai kyau yace, "Shiyasa albarka take baibaiye dakai a koda yaushe, indai nace kar ayi ko tace kar ayi baza kayi koda a bayan idanun mu. Amma tauye ka da take yi yayi yawa nan gaba indai aka kuma zuwa irin wannan gab'ar bazan bari ta tauye ka sai kayi abinda kake so." Shima murmushi Asad d'in yayi yana kallon mahaifin nasa.


"Ya batun yarinyar da take nema maka?." Take fuskar sa ta koma yadda take a d'azu yace, "bata dace dani ba Abba, na sanar da Mama tace ba haka ba ita ta zab'a min, amma na karb'a."
"Da zarar ka samo wacce kake so ko wacece a fad'in duniya ka sanar dani Asad, zan shige maka gaba wajan ganin ka mallake ta ko waye mahaifinta a garin nan ko a k'asar nan."


D'ago idanu yayi suna had'a ido da Abban nasa kwarjini ya saka ya sauke kai k'asa ba tare da ya shirya ba yaji bakin sa yace, "Ko y'ar talakawa ce?."
Mai martaba ya tashi sosai yace, "Ko y'ar wace Asad; shi talaka ba mutum bane? Ko y'ar shugaban k'asa ce indai ba y'ar gidan sarauta bace y'ar talaka ce a gidan sarauta. Indai da tarbiya da ilimin addini zance ya k'are. Inda za'a samu matsala in aka bincika aka gano wata dabi'a a tare da ita ko tare da dangin ta, kasan gida irin wannan baya d'auko irin wannan yaran."


Jin abinda mai margaba yace sai kuma ya rud'e amma bai nuna hakan ba shima mai martaba ya lura bai san yayi maganar ba sai ya murmusa kawai baice komai ba.


"Ina neman izinin tafiya" ya fad'a kai a k'asa. Mai martaba yace, "Dan kada a fad'a min wacece sirikar tawa ya saka zaka gudu?, to Allah ya tashe mu lafiya." Murmushi sosai Asad yayi har hakoran sa suka bayyana yana son zama da mahaifin sa shine yake damuwa da damuwar sa sab'anin Mama da kanta kawai ta sani. Mik'ewa yayi ya fita yana jin sanyi a zuciyar sa.


_Na bayyana a zahiri na a gare ka yau Asad, kayi gaggawar kawo ni rayuwar ka kafin su hallaka, Asad kana da tarin mak'iya na jikin ka sune mak'iyan ka, zanzo gare ka Asad amma akwai tarin qalubale a gaban mu, sai ka jure sai kuma ka daure._ a firgice ya tashi zaune ya dafe kansa abinda ta fad'a masa yana dawo masa cikin kansa, tabbas Rauda ce domin fuskar ta yau ta bayyana sosai a gare shi, itace domin ya ganta ido da ido sosai ta fito tarr itace.
"Meyasa take taimako na tun a mafarki?." Ya tambayi kansa gabad'aya a rud'e yake hankalin sa kuma a matuk'ar tashe.


Agogo ya kalla yaga karfe biyu na dare ya tashi ya shiga band'aki ya d'auro alwala ya fito ya tayar da sallah. Ya jima yana sallah har k'arfe hud'u kafin ya koma lazimi yana zaune har lokacin k'irjin sa bugawa yake yi bai dawo daidai ba. Ana kiran sallah ya tashi ya fita zuwa masallacin cikin gida.


Safiyar asabar yaji gabad'aya babu abinda yake so ya gani ya kuma saka a idanun sa face fuskar Rauda, ya kasa kai komai bakin sa Rauda kawai yake son gani, k'okarin daurewa yake amma abin yaci tura zuciyar sa sake azalzala masa take yi a kan haka dak'yar ya iya zama a gidan bai fita yaje gidan su ba.


Koda ya fita daga gidan Company ya wuce ya tarar da Hafiz suna ta had'a kayan wanda sukayi order za'a kai ya wuce office gabad'aya jikin sa babu k'wari. Bai bar company ba sai yamma wajan cin abinci yaje yaci ya gito ya shiga mota ya nufi unguwar su Rauda kan sa tsaye.
A k'ofar gidan ya tsaya yana kallon gidan nasu amma ya rasa me ya kawo shi sai kallon gidan yake kawai amma ya rasa dalilin da ya kawo shi, hango ta yayi a tsaye da sandinan ta tana dariya ita da wata babbar mace mai shigen maka da ita da alama Yayar tace.


K'arewa mata kallo yake cikin hijjabi mara tsaho fuskar ta a washe da kyakykyawan murmushi a kan fuskar ta, lumshe idanun sa yayi gaban sa na fad'uwa sosai yana kallon ta domin ta k'ara yi masa kyau ga annuri da take fitarwa. Numfashi ya sauke mai nauyi bai daina kallon ta ba bai kuma sauke glass ba har matar da suke tsaye ta bar k'ofar gidan ita kuma koma cikin gidan.


Sai da ta bar wajan ya lumshe ido ya dafe saitin zuciyar sa da take bugawa da sauri ya bud'e ido daidai lokacin da wayar sa ta sake cika masa kunne da ihu, sai da ya dawo hankalin sa ya dawo nutsuwar sa duk da zuciyar sa na bugawa, kallon wayar yayi yaga sunan Mama bai yi k'asa a guiwa ba ya d'auka ya saka a kunne, "Asad ka dawo gida Hydar ya farka!" ta furta daga can b'angaren baice komai ba ya yanke wayar ya tashi motar sa zuwa gida.


_tirkashi fan's mai Asad yake nufi da Rauda ne?._


*KWANTAN ƁAUNA*


©️ *Nana Haleema.*


*Book 1*
*020.*


Lokacin da Asad ya shiga falon Mama ya tarar da Hydar a zaune ya rame sosai yayi haske jikin sa babu k'arfi sai idanu da yake bin mutane dashi, a nutse ya tako ya zauna kusa dashi ya kalli Mama da take zaune itama a gefen sa sai Suhaima da take tsaye yace, "Sannu Hydar, ya kake ji?."
Maganar sa bata fita sosai yace, "da sauk'i."


"Asad ka taimaka masa yayi wanka ya sai yaci abinci." Asad ya kalli Hydar yace, "Zaka iya tashi?." Kai ya d'aga alamun eh ya rik'e shi suka tashi zuwa d'akin da yake kwance. A nan yayi wanka aka kawo masa kaya ya saka yayi sallah ya fara cin abinci. Suna zaune zagaye dashi ya gama cin abincin ya sha magani kana ya kalli Asad yace, "Akwai yarinyar dana buge deaf a tambaya min Dr Yasir tana ina."
Ran Mama ya b'aci jin da abinda ya fad'a tace, "na saka an sallame ta." Hydar ya kalli Mama ya dafe kansa yace, "meyasa Mama? Yarinyar tana buk'atar taimako sai an mata aiki fa."


Mama tace, "kuma indai nice na haife ka dole ka bar maganar ta ba, bana son sake jin zancen wata wacce ka buge a bakin ka ya wuce ka manta da babin ta." Zaiyi magana Asad ya d'an ja rigar sa sai yayi shiru ya saukar da kansa k'asa baice komai ba. Tsaki Mama tayi tace, "kana farkawa ka rasa da abinda zaka tashi sai maganar wata banza y'ar talakawa, kenan daman da ita ka kwanta a ranka da yake baka da hankali, na tsani yarinyar tsana mai muni." Babu wanda ya ce komai ba sukayi shiru zuwa lokacin magariba ta kawo kai.
Tare suka fita da Hydar sai a sannan jama'ar masarautar suka san da farkawar sa aka dinga gaishe shi zai amsa duk da ba wani k'arfi ne dashi ba.


Bayan an idar da sallah suka je wajan mai martaba daga nan suka dawo apartment d'insu. Aliyu baya nan Hydar ya zauna a falo jin jiri yana d'aukar sa yana sauke numfashi yace, "Deaf ban san inda zan ga yarinyar ba, basu da kud'in da za'a yi mata aiki in wani abun ya same ta Allah sai ya saka mata."
"Relax" abinda Asad yace kenan daga nan bai kuma cewa komai ba.
"Deaf ina cikin damuwa tunda na tashi itace tazo raina, ta yaya zan ganta ina so na ganta wallahi."
Wani irin kallo Asad yayi masa jin abinda yace nan take sai gaban sa yayi mugun fad'uwa amma bai nuna masa ba bai kuma yi masa magana ba.
Hydar ya yi shiru amma zuciyar sa gabad'aya tana ga tunanin inda zai ganta gabad'aya hankalin sa yana kanta gashi bai san inda zai nemo ta ba abin duk ya dame shi.


Washe gari Asad tare da Hydar suka fita zuwa company dan ya samu k'arfin jikin sa suna tare har yamma, a yamman aka kawo masa passports d'insu Rauda an buga musu visa ticket ya rage a siya, bayan tafiyar wanda ya kawo passports Hydar ya kalle shi yace, "Passports d'in su waye?." Bai bashi amsa ba sai da ya gama abinda yake yi ya tashi suka shiga mota suka bar company.
Gidan su Rauda ya wuce Hydar bai san gidan ba yaga dai sun tsaya a k'ofar gidan ya kalli Asad yace, "Ina ne nan?."


Bai magana ba ya sauke glass d'in motar nan ya hango Khalil yana ta wasa ya yafito shi da hannu ba musu ya k'araso Asad ya kalle shi yace, "Abban ka yana nan?." Khalil yace, "Eh yana nan."
"Jeka kace ana sallama dashi" yana fad'a ya ja bakin sa yayi shiru Khalil ya shiga cikin gidan.


Hydar yace, "Asad ban gane ina muka zo ba fa." Kallon sa yayi baice masa komai ba a lokacin Baba ya fito ganin haka ya saka Asad ya fito daga motar shima Hydar ganin ya fita shima ya fito lokacin Baba ya k'araso, hango Asad sai ya washe baki ya k'araso da sauri yana zuwa yace, "Barka da zuwa ranka ya dad'e." Murmushin k'arfin hali Asad yayi suka gaisa da Baban Hydar ma ya gaishe shi kafin Asad yace, "Shine Hydar wanda ya buge ta jiya ya farka daga rashin lafiya" ya fad'a yana nuna masa Hydar.


Baba ya washe bakiyace, "Allahu Akbar! Naso na gane fuskar sa yadda ya rame ya saka ban gane shi ba, sannu Hydar ya jikin ka?." Fad'ar hakan nan take sai Hydar ya gane shi shima yace, "Alhamdulillah, ya jikin ta?."
"To jiki da sauk'i dai za'a ce."
"Zan iya ganin ta?" Hydar ya fad'a yana kallon Baba.


"Mai zai hana, bara na sanar dasu shigowar ku" ya fad'a yana komawa ciki da sauri Asad baice komai ba har Baba ya dawo yace su shigo. Yana gaba suna binsa a baya Hydar na k'arewa gidan kallo har suka shiga ciki. suna zaune dukkan su a kan tabarma a tsakar gidan suka shigo da sallama cikin takun nutsuwa da k'asaita, dukkan su manyan kaya suka saka sun karb'i jikin su sosai tunda suka shigo khamshi ya mamaye gidan. S tare suka amsa Rauda da take zaune a akan kujera ta d'ago ido suka had'a ido da Asad nan take gaban ta ya fad'i tayi saurin janye idanun ta.


"Bismillah ku k'araso mana" Baba ya fad'a yana nuna musu wajan zama. Basu musa ba suka zauna suka gaisa da Umma kafin Hydar yace, "Mama ayi hak'uri nayi fama da rashin lafiya ne shiyasa ban kuma waiwayon ta ba, amma in sha Allah komai zai wuce yanzu." Umma tace, "Babu komai lafiya ai tafi gaban wasa, Allah ya k'ara lafiya." Hydar ya amsa da amin kafin ya kalle ta yace, "Ya jikin ki?."


Sai da ta saukar da kanta k'asa kafin tace, "Da sauk'i." Bai kuma cewa komai ba Asad daman tunda aka gaisa bai sake magana ba. Khalil ne ya shigo yana fad'in, "Baba ga Yaya Anas yazo." Baba yace, "To ina zuwa." Hydar yana so ya basu kud'i amma bai fito da komai ba duk sai yaji kunya tana baibaye shi ganin hakan Asad ya d'auko kud'i a aljihun sa ya ajjiye kusa da Umma sannan yace, "ku fara shiri tafiyar ku baza ta wuce nan da sati ba" yana fad'ar hakan ya mik'e sai Hydar ne yayi musu sallama dan yasan Asad ya gama magana suka fita tare da Baba.


A tsaye jikin mota suka ga Anas Baba ya k'arasa gare shi suna tare dasu Asad, har k'asa Anas ya gaida Baba kafin Baba yace, "Ranka ya dad'e wannan shine Anas mai neman auren Rauda, yana ta d'awainiya damu hatta maganin ta shine yake siya duk da lalurar da ta same ta bai saka ya guje ta ba" ya fad'a yana kallon Asad yana fad'a masa fuskar sa a washe da a nutsuwar magana da kamar Asad.
Abinda Asad yake ji a zuciyar sa sabida abinda Baba yace bai tab'a jin irin sa ba tunda Allah ya kawo shi duniya, k'irjin sa har d'agawa yake sabida bala'in tashi hankalin da bai san zai same shi ba a lokacin, bai tab'a jin k'una da rad'ad'in da yake ji ba tunda yazo duniya. Suka yake ji a zuciyar sa in ya tuna kalaman Baba da yake cewa 'mai neman auren Rauda' nan take sai yaji kamar jiri zai d'auke shi ya fad'i k'asa.
Kai kawai ya d'aga sukayi gaba Baba ya biyo bayan su yana godiya Asad ya bashi kud'i bai iya cewa komai ba suka shiga mota suka bar wajan.


Gudu sosai Asad yake yi hakan ya saka Hydar kallon sa dan yasan shi ba ma'abocin gudu bane in kaga yans gudu ransa a b'ace yake ko kuma wani abun na damun sa,shiru Hydar yayi ya fara tariyo abinda ya faru tun daga farkon zuwan su har yazo inda yaga yanayin sa ya canja inda suke magana da Anas kenan dan shidai yasan har suka fito daga gidan su Rauda yanayin sa bai canja ba. Kallon Asad ya kuma yi yana nazarin sa kafin ya girgiza kai baice komai ba shima.


Anas bai ga Rauda ba sai da akayi magriba aka kunna hasken soron sannan ta fito suka gaisa cikin soyayya yake kallon ta kana yace, "Naga wanda suka buge ki Baba yace min y'ay'an Sarkin garin nan, amma sun kyauta gaskiya abubuwan da sukayi ba ko wanne d'an mai mulkin ne zai shi ba; a ganin wasu da banbanci tsakanin su damu." Rauda ta d'aga kai tace, "Sosai ma kuwa sunyi k'ok'ari."
"Yanzu yaushe ce tafiyar taku Egypt d'in?."
"Ban sani ba gaskiya; ya dai ce bazai wuce sati ba."
"Allah ya nuna mana, nima da ni za'ayi tafiyar in sha Allah."


Murmushi kawai tayi kafin yace, "Rauda magana nake so zamuyi dake." Ta kalle shi tace, "Ina jin ka."
"Tsakanin da Allah kina sona ko a'a?." Gabanta yayi mugun fad'uwa ta runtse idanun ta domin bata san me zatace masa ba komai ta fad'a tasan k'arya take, in tace tana son sa tayi k'arya in tace bata son sa nan ma tayi k'arya.
"Kin yi shiru Rauda, ki bani amsa koda zata cutar dani gaskiya kawai nake son ji." Nan ma shiru bata bashi amsa ba yayi murmushi yace, "Na riga da na fahimci amsa ta Rauda, har yanzu baki bani wani matsayi a zuciyar ki ba, bazan sare ba zan cigaba da nemawa kaina gurbi har na samu ko za'a kai shekara goma nan gaba zan jure."


Tausayin sa taji ya kamata ta kalli kanta ta ganta da k'afa guda d'aya gata ita ba kyau ne da ita ba amma namiji mai kyau da kud'i kamar Anas yana sonta duk da abinda ya same ta bai guje ta ba ya nuna shi dai ita yake so sai taji wani iri a zuciyar ta ta sunkuyar da kai a hankali tace, "Nifa ban ce ba." Murmushi yayi yace, "Nima ban ce kin ce ba ai Rauda, na fahimta ne kuma fahimta ta itace gaskiya."
Zatayi magana Ummulkhairi ta fito

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login