Showing 81001 words to 84000 words out of 92772 words
Chapter 28 - KWANTAN BAUNA BOOK 1 COMPLETE by Nana haleema.txt
yace, "angama ranka ya dad'e, in sha Allah zaka ji komai daga bakina kamar yadda ka umarta. Allah ya k'ara lafiya da nisan kwana, ya jiqan iyaye ya sanya suna Aljanna." Da amin suka amsa dukkan su kafin mai martaba ya kalli Hydar yace, "A mayar dasu gida, a kuma tabbatar an basu kulawar da ya kamata bana so su nemi wani abun su rasa." Ba musu Hydar ya tashi suma suka tashi akayi godiya suka fita.
Falon ya rage daga Asad sai Mama sai mai martaba babu mai magana a cikin su kowa ta ciki na ciki, hawayen bak'in cikin da Mama take b'oye ne suka zubo mata daga idanunta ta share tana kallon wani wajan daban zuciyar ta nayi mata zafi da k'una sabida k'askantar da akayi a gaban talakawa.
"Dole ki kawar da kai gefe ai domin abinda kika aikata kin san ba abu bane mai kyau, da ace yarinyar nan bata furta ta hak'ura ba wallahil azim ko wanne hukuncin da take so ayi miki sai an miki sai dai hakan ya zama silar bugawar zuciyar ki sabida bak'in ciki. Yarinyar da Hydar ya buge har ta samu matsala a k'afar ta ki saka a kore ta daga asibiti kawai sabida banza ra'ayin ki..? Ke kullum a idanun ki talaka da mai kud'i suna da banbanci, dan ta kasance talaka wannan Allah ne ya k'addara amma d'anki ne yayi silar nakasar ta amma ke ko yaushe tunanin ki daban yake dana kowa. kin kyauta ai abinda kika aikata yayi miki kyau" ya fad'a yana mik'ewa dole ta mik'e Asad ma ya mik'e tsaye.
Ya sake kallon ta yace, "Ko nan gaba kika sake aikata wannan kuskuren Rabi'a sai na saka anyi miki hukuncin da baki tab'a tunani ba, sai na nuna miki talaka daidai yake dake a duniya tunda ke mutum ce shima mutum ne. Ki kuma ji tsoron ranar da zaki je neman alfarma a wajan talaka" ya fad'a da zallar b'acin raina tare dashi.
Tare suka fita da Asad yana kallon irin kallon da take masa take gaban sa ya cigaba da fad'uwa har suka koma b'angaren mai martaba Asad baya tare da nutsuwar sa nutsuwar sa. Ganin hakan ya saka yace, "Kada ka damu Asad zan tsaya maka a wannan karon sai naga ka samu abinda kake so koda ita d'in bata so, bazata cigaba da tauye maka hakki ina kallo ba a wannan karon alqawari nayi maka."
Kamar zaiyi kuka ya kalle shi yace, "Abba amma zatayi fushi dani kuma ni ban saka Hydar ya fad'a maka abinda yake faruwa ba, at least ban tabbatar da abinda nake ji akan yarinyar ba, a janye maganar Abba." Mai martaba ya dafa kafad'ar sa yace, "kana sonta, Asad na tabbatar da kana sonta. itace mace ta farko da saka kanka a cikin lamuran ta, kuma fuskar ta kake gani a mafarkin ka Asad. Akwai tarin alkhairi a zaman ka da ita nayi istikhara akan hakan Allah ya nuna min kaima yana da kyau kayi. Ka bawa zuciyar ka abinda take so kar ka cutar da kanka a wannan lokacin kamar yadda ka saba yi a baya, ka daure ka zama namiji ka Jajirce kar barazanar babar ka ta baka tsoro ka tsaya a akan ra'ayin ka. Shigowar ta rayuwar ka itace zata canja komai Asad, ka rubuta ka ajjiye koda bana raye hakan zata kasance amma dole ka jure, ka ajjiye wannan raguwar zuciyar taka ka zama namiji kamar kowa dan Allah" mai martaba yana gama fad'a yana kallon sa.
Asad kansa yana sunkuye mai martaba ya kuma cewa, "Yau ba gobe ba ina so kaje gidan su yarinyar ka fara yak'in neman amincewatar, tana da ilimin addini babu abinda ban sani ba a kanta. Tana da tarbiyya mai kyau duk da ta kasance kuna da banbanci ta b'angaren matsayi amma itace daidai da kai tunda kana sonta. Ilimin ta da tarbiyyar ta shine ya saka na sake baka goyan baya d'ari bisa dari ta ko wacce fuska bata da aibu haka dangin ta. Ka nemi amincewar ta umarni nake baka Asad." Yana gama fad'ar hakan ya shige ciki ya bar Asad da sanyi jiki dole ya jawo k'afar sa ya nufo b'angaren Mama k'irjin sa na bugawa.
Zagaye take hankalin ta a tashe ita kad'ai fuskar ta har ta fad'a sabida tashin hankalin da k'unar zuciyar da take ciki, jin motsin da taji ya saka ta juyo ta kalle shi ya sunkuyar da kansa k'asa baice komai ba ta gyara tsayuwa ta fuskance shi tace, "Asad kayi gaggawar samun mahaifin ka ka fad'a masa kai ba son yarinyar nan kake ba, ka janye maganar nan tun kafin nayi maka baki Asad" ta fad'a tana nuna shi.
Asad ya sauke numfashi amma baice komai ba ta kuma cewa, "in ma asiri tayi maka zan warware shi amma baza ta tab'a zama mallakin ka ba ko bayan raina, babu kai babu ita tsakanin ka da ita taimako ne bayan shi babu maganar aure Asad!."
Yadda ta d'aga murya ya saka shi runtse idanu zai iya cewa lokaci na farko kenan da Mama ta d'aga murya dan kowa yasan bata d'aga murya in tana magana a ganin ta fad'uwa ne a gare ta ya bud'e a hankali kana yace, "Ina sonta Mama!."
Tassss shine sautin abinda ya sauka a kuncin sa daidai lokacin da kalmar mama ta gama fitowa daga bakin sa. Rai a b'ace take kallon sa tana nuna shi da yatsa da yake tsaye har lokacin tace, "K'arya kake Asad! Baka isa ba ba kuma zaka isa ba. Meye a wajan ta da zaka so ta?, me take dashi?, bak'a, gurguwa, y'ar talakawa, y'ar tallan abinci a kan titi me zaka nema a wajan ta wanda Jidda bata shi?. Meyasa baka son Jidda sai ita?."
Yayi shiru zuciyar sa na zafi rana ta farko kenan da Mama ta d'aga hannu ta mare shi duk sai yaji duniyar tana yi masa zafi komai yana fice masa daga ransa.
"Asad Jidda itace daidai kai mahaifin ta ambassador ne, na zab'e ta sabida ita kanta a k'asan ka take talakar kace dalilin da ya saka ban nemo jinin sarauta irin ka ba dan bana son matar da zaka aura ya zama tana had'a kanta da matsayin ka. Ita ta dace da rayuwar ka ba waccan banzar ba, ka tuna kai d'an sarki ne, wanda ya haifi mahaifin ka sarki ne, wanda ya haifi mahaifiyar ka sarki ne, wanda ya haifi mahaifin mahaifiyar ka sarki ne, kaine kuma sarki mai jiran gado me zakayi da y'ar talaka mara ilimi da wayewa!?."
Ta bugi kujera ta cigaba da fadin, "Kask'anci ne a gare ni da dangi na gabad'aya matuk'ar ka auri yarinyar nan, baza ka aure ta ba indai ina da rai ka ajjiye wannan batun indai kana son farin cikina, in kuma ka dage akan kud'irin ka ka tabbatar min da y'ar talakawa ta fini a wajan ka." ta fad'a tana nuna shi da yatsa idanun ta a waje sabida bala'i da bak'in ciki.
Muryar sa a tausashe kamar ko yaushe yace, "K'addara ce ta had'a ni da ita Mama ba soyayya ba, kece mahaifiyata wacce ta haife ni ta raine ni na tsahon shekaru da dama har gobe take kan bani tarbiyya. Ta yaya zan had'a matsayin ta da nata wacce na tsince ta a sama?, ta yaya zan fifita wata a kanta?. Ki amince min Mama ki yarje min kaddarar da ta had'a ni da ita na d'auke ta tamkar jarabawa ce wacce Allah ya k'addaro min, ki bani dama na amshe ta hannu biyu-biyu na rubuta nayi nasara. Agajin ki nake nema akan komai a wannan gab'ar ma yarjewar ki nake nema. ki duba yanayin da abin yazo ban shirya zuwan sa ba balle nayi rigakafi tun kafin lokacin, K'aunar ta nake ba sonta nake ba, ki amince min a wannan lokacin na gayyato ta zuwa rayuwata" ya k'arasa fad'a yana runtse idanun sa dan shi kansa ji yake kawai maganar na fitowa daga zuciyar sa zuwa kan harshen sa.
K'are masa kallo take cike da dunbin mamaki jin doguwar maganar da ya tsaya yana yi mata akan wata mahaukaciyar yarinya da bata wuce mai bawa doki abinci a gidan su ba, ba k'aramin hasala ta sake yi ba tace, "baka isa ba Asad! wallahil azim baka isa ba, dole a wannan karon ma kaso abinda nake so in ba haka ba zaka jawowa yarinyar bala'i da masifar da baza ta iya fidda kanta ba; zan iya sakawa a kashe ta kuma na kashe banza da wofi kai ka sani, ina tabbatar maka matuk'ar ka bari abinda mai martaba ya fad'a ya tabbata wallahi sai kayi dana sani!."
Idanun sa sunyi jahh sosai sabida tashin hankalin da zuciyar sa take ciki, zai iya rantse da Allah bai tab'a tsintar kansa a yanayi mara dad'i kamar wannan lokacin hatta yanayin fuskar sa ya koma ja. K'asa tayi da murya ta juya masa baya tace, "Yau ni kake fad'awa doguwar magana akan wata banzar mahaukaciyar yarinya ko Asad?, baka tab'a min irin wannan maganar mai tsaho ba sai yau sabida ta fini a wajan ka, ina cewa ga abinda nake so kana cewa kai ba shi kake so ba sabida ita ko Asad....?" ta k'arasa maganar a sanyaye sai kuma ta ta zauna akan kujera tana hawaye.
Ganin hakan hankalin Asad ya tashi ya bita ya zauna a k'asan carpet yace, "Allah ya wuci zuciyar mahaifiyata, ina rok'on mahaifiyata akan tayi hak'uri ta daina zubar da hawaye akan Asad" ya fad'a a sanyaye yana dafa guiwar k'afar ta kamar shima zaiyi kuka.
"Asad kar ka aure ta, bana sonta wallahi na tsane ta kar ka aure ta Asad" ta fad'a tana rik'e hannun sa gam hawaye na zuba a idanun ta.
Kamar zaiyi kukan yake ji zuciyar sa tayi rauni matuk'a tana cigaba da bugawa rana ta farko da Maman sa take kuka a kansa hakan ya saka yace, "Zan iya hak'ura da komai akan Mamana duk k'aunar da nake masa, Allah ya wuci zuciyar ki."
Hydar dake tsaye a bayan su ya shigo yana fad'in, "A karo na farko meyasa Mahaifiyata baza ta amince da ta amince da abinda Asad yake so ba....? ya bar aikin sa da yake buri tun yana yaro sabida Maman sa, ya bar damammaki da yawa a rayuwar sa sabida Mahaifiyar sa abinda Mama take so shi yake yi. Baya son Jidda amma ya amince da ita duk sabida Mama tana so yau kad'ai Mama ya nuna yana son Rauda meyasa mahaifiyar mu bazata amince masa ta bashi goyan baya ba?. Meye aibun ta kawai dan ta kasance ta fito daga jinin talakawa shikenan ba abar so bace ba?. Dan Allah dan annabi ranki ya dad'e a yiwa Asad adalci a karon farko a barshi ya aure ta tunda yana sonta" ya fad'a a sanyaye yana durk'usawa a gaban Mama cikin girmamawa.
A fusace tace, "Hydar ba da kai nake magana ba dashi nake magana, ka fice ka bani waje." Hydar yace, "Allah ya wuci zuciyar ki, ina neman afuwa in abinda na fad'a ya b'ata miki rai" ya mik'e ya kalli Asad yace, "kazo muje takawa yana son ganin ka."
Jin abinda Hydar yace ya saka Asad mik'ewa Mama tana rik'e da hannun sa har lokacin tace, "kar ka amince Asad, na yadda zan bar ku kuyi mata ko wanne irin taimako amma banda aure tsakanin ku bazan iya jure ganin wannan ranar ba, zuciyata zata iya bugawa a lokacin da hakan ta faru. Na rok'e ka matsayina na mahaifiyar ka Asad ka sanar dashi baka sonta." Kai Asad ya girgiza kawai ya fita Hydar yabi bayan sa.
Hanyar wajan mai martaba Asad ya nufa Hydar yace, "Zo muje ba wani kiran mu da yake yi, na fad'a ne dan ka taso kalaman ta zasu karya maka zuciya ka hak'ura da abinda kake so" ya fad'a yana jan hannun sa suka nufi hanyar apartment d'in su. Bayan sun shiga Asad ya kalli Hydar a sanyaye sosai yace, "Hydar zan hak'ura kamar yadda Mama take so, bazan iya ganin Mama a halin da take ciki ba ina da damar cire ta kuma na barta; zan hak'ura kawai kome nake ji a zuciya ta zan jure Hydar; ba yau ne na fara rasa abinda nake so ba" ya fad'a a sanyaye yana zama akan kujera ya dafe kansa.
Tausayin sa ya kama Hydar domin yasan soyayya tayi masa mugun kamu lokaci d'aya ba tare da ya shirya ba ya zauna kusa dashi yace, "Baza ka hak'ura ba deaf, sai ka mallake ta domin itace wacce kake so ba Jidda ba. Kana fa da hakki akan Mama ba itace kawai take da hakki a kanka ba tauyen ka da take yi yayi yawa a ko yaushe kanta ta sani bata duba kai halin da zaka shiga in ka rasa abinda kake kawai cikar burin tane a gabanta." Ya juyo ya fuskanci Asad ya rik'e hannun sa yace, "Deaf u lovers her right?."
Ya lumshe ido yace, "Hydar!." Hydar ya katse shi yace, "Na tambaye kane kawai ka amsa min." Shiru yayi yana tunani kafin yace, "eh ina sonta Hydar, but yanzu na bar batun ta sabida Mama."
"Baza ka bari ba abu nawa ka bari sabida Mama a duniya? Meyasa ita baza ta yi maka adalci a wannan lokacin ba?. Tana so ka auri wacce take so kaji zaka aura amma kaima zaka auri wacce kake so ba shikenan ba anyi equal why zata ce kai sai ka hak'ura?."
"Hydar mu bar maganar nan dan Allah" ya furta yana dafe kansa da hannu d'aya kansa yana harbawa yana ajiyar zuciya.
Hydar yace, "Na bari; amma inaso ka sani bazan zuba ido ka rasa abinda kake so a karo na babu adadi ba deaf, zanyi iya yina wajan ganin ka mallake ta" yana fad'a ya tashi ya fita daga falon ya bar Asad a zaune yana sauke numfashi.
_Suna zancen wani Asad ni meye had'ina da wani Asad?._ kalaman Rauda suka fad'o masa a zuciyar sa ya runtse idanu zuciyar sa na bugawa da sauri-sauri ya lumshe idanu yana tuno yadda fuskar duk taji ciwo, wani abu yaji yana masa suka a zuciya ya runtse idanun sa da k'arfi yana cize baki, bud'e ido yayi ya kalli falon kamar mai neman wani abun kafin ya tashi ya shiga d'aki jikin sa duk a sanyaye.
*☆☆☆*
Umma da take sauraron abinda Baba yake fad'a mata da mamaki take binsa da kallo jin abu kamar a shirin film ko a hausa novel tace, "Malam wai auren Rauda ake nemawa Asad d'in? Nifa ban gane ba ka saka ni a duhu wallahi." Baba yace, "Abinda kika ji na fad'a shine, Asad d'in ne da kansa yace yana son tane shiyasa mahaifiyar sa ta turo ayi mana wannan aikin dan daman nasan labarin ta ana cewa bata son had'a jini da talaka; shiyasa ta d'auki wannan matakin kafin abin yayi nisa."
Umma ta rik'e baki tace, "Tabd'ijam, ni kuma fa gani nake kamar da wata manufa akace yana sonta in badan haka ba ina matsayin sa ina Rauda...?, banda abin su ina shi ina Rauda? Kalli yadda take fa?" Ta fad'a tana kallon Rauda da take zaune a gefe. Baba yace, "to Allah ne masanin gaibu ni bana ce komai ba." ya fad'a cikin rashin sanin mai zaice.
Umma tace, "Ina zamu kaita inda za'a wulak'anta ta?, da ta aure shi azo ana wulak'anta ta wallahi gwara ta auri talakan da bashi da komwi zai kula da ita. To ita da bama sonsa take ba ina maganar aure?."
"Ke kinji illar ki wallahi, meye to in ta aure shi? ai tunda yana sonta ko ita bata son shi magana ta k'are, kuma kaf dangin ki da nawa wacece ta taka matsayin da Rauda ta taka in ta aure shi?. D'an sarki fa kuma mai kud'i ki kuma tuna shine sarki gobe wannan ai abin alfahari ne a gare mu gabad'aya."
Umma ta kalle shi da mamaki ta girgiza kai tace, "Shi kuma yanzu Anas ka dawo daga rakiyar sa kenan ko?." Baba yace, "ke muna so mu shiga aljanna amma a aljanna ma firdausi muke nema" ya fad'a yana wara hannayen sa. Umma ta d'auke kai daga kallon sa tace, "to ke Rauda wanne tunani kike akan wannan?."
Rauda tace, "Umma wanne tunani zanyi?." Umma tace, "kece kike da tunani Rauda, amma a zahiri ina ke ina Asad?, Ga k'iyayayar da babar sa take miki tun kafin aje ko ina har ta fara turowa har gida ayi miki wulaƙanci dan kiji tsoro ke kya shiga gidan nan?. Ga badaqalar da take cikin gidan sarauta, da karancin shekarun ki a haukata min ke ko a kashe ki a barni da zubar da hawaye, bana fatan ma ki aure shi wallahi." Baba yace, "Sai ki hana ai in an tashi auren, ko in Allah ya rubuta kije ki goge." Umma bata ce komai ba Baba ya tashi ya fita ta kalli Rauda tace, "Rauda ke kina ji a ranki zaki iya zama dashi?."
Rauda tace, "Bana kawo hakan Umma, hasalima ni haushi yake bani duk abubuwan nan da suke faruwa bai tab'a cemin yi hak'uri ba a haka kuma zan zama matar sa?. Bada ni ba yaje can ya nemi wata ni kam bazan iya ba dan ni zuciya ta ma hasaso mun take akwai wata manufa a son da yace yanayi min wata k'ila amfani zasu yi dani daga baya su wulak'anta ni dan sun ga suna da mulki da kud'i. Bana sha'awar hakan ma ni sam Umma."
Umma ta sauke ajiyar tace, "ashe kin hango abinda nake hangowa. Meyasa ya zabe ki bayan tarin matan da suke son su aure shi? Dan nasan bazai rasa ba duba