Showing 30001 words to 33000 words out of 92772 words
Chapter 11 - KWANTAN BAUNA BOOK 1 COMPLETE by Nana haleema.txt
gefen sa wanda aikin sa duk inda sarki yake yana kusa dashi sune kawai a d'akin kowa yana waje ya kalle ta yace, "meyasa ba'a bar shi a asibitin ba?."
"Nan yafi safe."" ta bashi amsa a tak'aice tana kallon sa itama.
A tare suka kuma fitowa ana ta kallon su bayi masu gulma suna yi tuni har an kaiwa sauran labari tun kafin su gama ma abinda ya fito dasu. Inda Asad yake suka shiga har cikin d'akin sa, mai martaba ne ya shiga d'akin kawai bai jima ba ya fito daga d'akin ana kirari aka raka shi har b'angaren sa.
Bata zauna ba ta koma nata b'angaren mai martaba shi kansa abin ya d'aure masa kai sosai duk da yasan ciwon ciki lalura ce amma ya tabbata na Asad yana da sila baya so ya nuna mata ne ya sake tunzura zuciyar ta shiyasa yayi shiru.
B'angaren Hajiya da labari yazo mata Asad yana kwance sai ta damu tana ta zaga d'akin ta cikin tunani dan dai ita ta tabbatar bata sakawa Asad komai a cikin zogale ba wanda ta bashi ko ita zata iya ci, amma meyasa akace bayan yaci yana ciwon ciki?, meye dalilin ciwon cikin nasa?, Anya babu wanda ya jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya?. Ta jima tana wannan tunanin kafin wayar ta d'auki k'ara, d'auka tayi taga sunan mai gidan ta Yana kiran ta ta d'auka a kunne ta saurari abinda yace kafin ta yanke wayar.
Numfashi ta fesar ta fito cikin takun isa da k'asaita ta tafi amsa kiran mai martaba.
Daga shi sai Wambai sai Mama a zaune ta shiga da sallama ta zauna gaban ta na fad'uwa sosai zuciyar ta duk ta cika da tsoro, mai martaba yace, "Rabi'atu gata." Mama ta kalle bowl d'in gaban ta da yake d'auke da ragowar zogalen a ciki ta fito da farar takarda tace, "wannan shine sakamakon gwajin ragowar zogalen nan da akayi ya tabbatar kuma an bawa Asad guba kuma itace wacce ta bashi yaci." Hajiya ta dafe k'irjin ta da yayi mugun bugawa fuskar ta tayi kalar tausayi ta kalli mai martaba shima ita yake kallo kafin yace, "Sa'adatu ya akayi haka?."
"Allah ya taimake ka wallahi Allah ban bawa Asad wani abu a cikin zogalen nan ba, inda nayi niyar cutar dashi bazan bari yasan nice na bayar ba sai dai yaci. Ko ni zan iya ci ban san ya akayi hakan ta faru ba, mai martaba yasan bazan rantse a kan k'arya ba" ta fad'a muryar ta na rawa sosai.
Mai martaba ya kalli Mama yaga ta kawar da kanta gefe alamun bata ma yarda ba kafin ya kalli wambai ya dawo da kallon sa a gare su yace, "zaku iya tafiya. Amma bana so na sake yin maganar nan a barta a wajan nan kar na kuma ji. Zaku iya tafiya." Ba musu suka tashi suka fita mai martaba ya kalli Wambai yace, "Mubarak mai ka fahimta game da lamarin nan?."
"Allah ya ja zamanin ka abu ne a bayyane kai tsaye baza'a ce Hajiya ce ta bashi gubar ba, kai tsaye kuma baza'a ce Fulani itace ta mata sharri ba. Komai zai uya faruwa kowa yana da gaskiya a cikin su." Mai martaba ya sauke numfashi yace, "Sa'adatu bazata bashi guba ba ni nasan da hakan, koda ma ace zata bayar d'in kamar yarda tace baza tayi yadda za'a gane ba ta taka sahun b'arawo ne tabbas akwai wanda yake son ganin bayan Asad a cikin gidan nan, amma waye?."
Wambai yace, "koma waye Allah zai tona asirin sa. Asad mutum ne mai addu'a kuma power of du'a tana canja destiny komai girman ta, kafin mummanar k'addarar ta samu Asad addu'a ta canja ta." Mai martaba ya girgiza kai zuciyar sa taf da tunani yace, "Rabi'atu dole ta shiga damuwa yau ta shirya zuwa Kano ga Asad ba lafiya ga kuma Hydar a kwance ba'a san ranar da zai farfad'o ba."
"Gaskiya ta b'angaren yaranta tana karb'ar jarabawa daga Allah, amma in ta kwantar da hankalin ta Asad sai ya zamarwa makiya ciwon ido."
"Allah yasa mu dace" mai martaba ya furta ya amsa da amin.
B'angaren Hajiya tunda ta koma take zagaye hankalin ta ya tashi sosai ganin maganar har taje gaban mai martaba, babban tashin hankalin ta bai wuce yardar da mai martaba yayi da ita kar ta zube ba hakan ya saka ta shiga d'aki can k'arshe ta d'auki waya ta kira Waziri. kira 1,2 ya d'auka yana d'auka kafin tayi magana yace, "kin bawa Asad zogale yaci yanzu kuma yana ciwon ciki an yi binciken ragowar da ya rage an gano akwai guba a ciki, hankalin ki ya tashi domin kedai kin san baki saka komai ba kar hakan ya jawo rushewar yardar da kike so Asad yayi dake, shine kawai tashin hankalin ki amma bawai dan yaci guba ba haka ne?."
Da zallar mamaki tace, "duk ya akayi kasan wannan bayan kai kana wani wajan daban ina nan daban?." Murmushi yayi mai sauti yace, "kar ki raina basira da y'an leken asirin da master planer take dashi a gidan nan, itace ta sanar dani duk abinda ya faru gashi kuma na tabbatar hakan ne."
"Wai wacece master planer d'in nan? A ina take?, ya akayi ta san duk abinda yake faruwa a gidan nan bayan bata cikin sa?, su waye suke sanar da ita har abinda ya faru a falon mai martaba?. Lamarin ta ya fara bani tsoro fa na fara zargin tana kewaye damu a cikin gidan nan koma wacece" ta fad'a tana girgiza kanta.
"Hhhhhh kar lamarin ta ya baki tsoro tsabar mayar da hankali ne akan abinda aka saka a gaba. Tace ki kwantar da hankalin ki ki cigaba da abinda kika fara kar abinda ya faru ya baki tsoro, baki saka guba a cikin zogale ba itama ta sani kawai dai akwai wanda yake so yayi amfani dake ne a cikin gidan shiyasa ya d'ana miki tarko kuma kika fad'a. Tabbas bayan mu akwai wanda yake son ganin bayan Asad tambayar itace waye? Ko wacece? Ko kuma su waye?, ita kanta master planer bata gano waye ba."
"Gano ko waye shine abinda ya kamata mu saka a gaba in ba haka ba akwai babbar matsala tunda aka fara haka."
"Kada ki damu ki kwantar da hankalin ki komai zai zo mana da sauk'i tunda master planer tana tare damu, kedai ki cigaba da abinda yake gaban ki, ke kan ki kinga nasara a tafiya da master planer a jiya tace sai Hydar ya kwanta ciwo ya kwanta, a jiya tace za'a hana Rabi'atu zuwa Kano gashi kuwa duka ta faru. Ki mayar da hankali muyi abinda yake gaban mu nasara a tare damu take" yana fad'ar hakan ya yanke wayar tabi wayar da kallo.
"Kenan akwai wanda yake son ganin bayan Asad bayan mu? Waye yake k'okarin shafa min kashin kaji?, wanne bak'in fenti yake k'okarin shafa min....?" Bata da wannan amsar hakan ya saka ta sauke numfashi tana sake tafiya duniyar tunani zuciyar ta cike da tsoro.
A b'angaren Mama lokacin da ta koma kanta ta kulle a d'aki tana neman mafita dan zuwa lokacin kanta ya kulle, sai da ta jima sosai sannan ta fito ta tarar da Jidda da Suhaima a zaune bata ce komai ba ta shiga d'akin da Hydar yake. Yana nan yadda yake ta k'arasa kusa dashi tana shafa kansa tayi masa addu'a sannan ta fito ta sake komawa d'akin ta.
Babban tashin hankalin da ya addabe su dukkan su shine su waye suke son ganin bayan Asad.....?.
*☆☆☆* _Ina nan zan iso a gare ka zan baka kariya ga dukkan makiyan ka, makiya sun saka ka a tsakiya ka tashi tsaye kayi yak'i dasu kafin isowata gare ka, zan zo nan bada jimawa ba kafin na k'araso ka tabbatar ka tsaya da k'afafun ka, ina nan zuwa.....!_ a firgice Asad ya mik'e zaune yana zare idanun sa jikin sa yayi bala'in mutuwa ga ciwon cikin da yake damun sa har lokaci. Tuno mafarkin da yayi yake yi tiryan-tiryan suna dawo masa kansa ya dafe kai da duka hannu biyu yana yanutsa fuska.
Kusan kwanaki goma kenan a jere kullum sai yayi mafarki da yarinyar da baya ganin fuskar ta sai dai yaji maganar ta itama kuma baya jin maganar tarrr dan baya tunanin zai iya gane mai maganar a zahiri, "who is she?" Ya tambaya a bayyane yana dafe cikin sa yana cize bakin sa.
Tsaye ya tashi ya kalli agogo yaga har lokacii ya tafi yana dafa bango ya shiga band'aki yayi wanka da alwala ya fito ya tayar da sallah ya idar lokacin akayi la'asar yayi. Shiryawa yayi cikin manyan kaya maroon d'in yadi mai zane yayi masa bala'in kyau ya saka hula kalar aikin sumar kansa da sajen face d'in sa sai d'aukar ido suke yi. K'aramar riga mai zanen adon sarauta ya dauka kalar ta maroon itama ya d'ora akan ta saman hatta takalmin sa zanen sarauta ne a jiki.
Cize baki ya kuma yi domin yana jin ciwo har lokacin ya furzar da iska ya d'auki wayar sa ya fita zuwa falo. a zaune ya tarar da Hafiz ganin fitowar sa ya kalle shi yace, "Prince ya jikin?." Kai ya d'aga alamun da sauk'i yana cize bakin sa har lokacin. Baice komai ba ya fita direct wajan mahaifinsa ya tafi aka masa iso ya shiga ya same shi babu kowa sai shi kad'ai yana duba littafan addini kamar koda yaushe.
Ganin Asad ya saka shi ajjjiye littafin yana kallon sa ganin ya rame lokaci guda idanun sa sun fad'a yace, "Aliyu na, gadanga kusar yak'i, mai zuciyar maza, zaki mai firgita makiyan sa, ya akayi ne?." Murmushi yayi jin kirarin da mahaifin sa yake masa ya had'd'iye saliva ya kalle shima shi yake kallo mai martaba ya kuma cewa, "Yau sarautar ake ji da ita kenan ko?." Nan ma Murmushi yayi yace, "Barka da yamma."
Mai martaba yace, "Ya jikin naka?."
"Alhamdulillah" ya furta yana gyara zaman sa kafin mai martaba ya kuma cewa, "Naji dad'i da naga ka samu lafiya Asad, Kar ka saka komai a ranka Asad nasan mahaifiyar ka zata sanar dakai guba aka baka kaci a zogale amma bana so hankalin ka ya tashi domin duk mai son ganin bayan ka da iznin Allah kaine zaka ga bayan sa. Kana gani yanzu gashi an baka guda amma ko awa biyar ba'ayi ba ka tashi cikin k'oshin lafiya kamar ba kai ba. Ka cigaba da addu'a ka dage da addu'a kar kayi wasa da addu'a makiya sun saka ka a tsakiya kai kana gefe dole sai ka kai kukan ka wajan wanda ya halicce ka shine kawai zai kawo maka garkuwa da mafita nan kusa."
Kallon mahaifin nasa yayi jin yana maimaita kusan irin abinda yarinyar da yake mafarki take fad'a masa hakan ya saka yace, "in an min izinin zan iya bawa mahaifina labari?."
Mai martaba yace, "labari da kanka? Ina jinka."
"Allah ya kara maka lafiya ina yawan mafarki da yarinya tana fad'a min kusan abinda mai martaba yake, amma bana ganin fuskar ta bana kuma gane maganar ta......" ya dafe mai martaba yace, "huta sai ka cigaba da fad'in min, Allah ya yaye maka wannan rashin son maganar taka kullum sai nayi maka addu'a akan hakan ina kuma da yak'inin Allah zai sassauta ka dinga magana koda bamai yawa ba."
"Tana cewa zata zo gare ni nan kusa amma kafin nan na tashi nayi yak'i makiya na, Allah ya taimake ka ban san me hakan yake nufi ba" ya fad'a yana kallon mahaifin nasa shima kuma shi yake kallo. Da hannu ya masa alamu da ya matso kusa dashi ya matsa sosai ya rik'e hannun sa yace, "Asad kaine garkuwar wannan masarauta matuk'ar kamar yadda nake fad'a maka ko yaushe, in wani ya karb'e ta ba kai ba zata watse ta tarwatse talakawa zasu yi kuka. Ko bana raye ka tsaya kai da fata wajan ganin ka mallaki kujerar nan matsayin taka." Asad yayi shiru ya sauke kai k'asa.
"A mafarkin ita yarinyar ta tab'a taimakon ka?."
Kai ya d'aga alamun eh kafin yace, "ba sau d'aya ba ba kuma sau biyu ba." mai martaba yace, "garkuwar kace Asad zata shigo rayuwar nan kusa sai dai bamu san da wacce fuska zata shigo ba, ina ji a jikina alkhairi ce a gare ka gashi bamu santa ba balle mu nemo ta. Tabbas itace zata kasance magani ga duk wani mak'iyin ka, itace zata kasance katanga a gare Asad. ka nemeta alkhairi ce a rayuwar ka, ba ko wanne mafarki ne yake zama gaskiya ba amma kwatankwacin abinda kake gani zai faru Asad."
Numfashi yake saukewa a hankali ya dafe cikin sa mai martaba yace, "daure Asad nasan kana jin ciwo sosai an baka ne dan a kwantar dakai ciwo ko a kashe ka."
"Abbana sai nake ganin kamar Hajiya baza ta cutar dani ba." Murmushi yayi yace, "Asad kenan, zuciyar ka wankakkiyar ce ka amince da kowa shiyasa kake ganin kowa irin taka zuciyar ce dashi. Bance zata cutar da kai ba amma ka kula da wanda suke kusa da kai da yawan suna yi ne dan su cuce ka, furta zanyi murabus da nayi shine kuskure babba da nayi dan daga lokacin mak'iya suka sako ka a gaba kowa so yake yaga bayan ka. Duk da daman kana dasu tun a da yanzu ne suka k'ara yawa."
Asad ya girgiza kai mai martaba yace, "ka cigaba da addu'a duk abinda ya tunkaro ka ka fuskance shi ka daina cin abincin kowa sai wanda Maman ka ta baka itace kad'ai ce baza ta cutar da kai ba dan itace ta haife ka bayan ita kar ka amince da kowa hatta y'anuwan ka na jini ban d'auke kowa a cikin su ba sai kuma wanda zuciyar ka ta amince dasu."
"In sha Allah Takawa zanyi abinda aka umarce ni" ya fad'a da girmamawa kamar ko yaushe kansa yana kallon k'asa.
Mai martaba yace, "Allah ya bada iko. Kak'i kayi aure wata k'ila matar taka ce garkuwa a gare ka Allah yake nuna maka tun yanzu, ka daure ka nemo mata kayi aure a kwanakin Asad."
"In sha Allah zanyi" ya bashi amsa yana murmushi.
Murmushin shima yake yana kallon sa, kaf y'ay'an sa babu wanda yake so kamar Asad a baya yaso Aliyu amma a yanzu halayen sa sam sun saka ya fita a ransa amma Asad shine a kan gaba a kaf cikin yaran sa. Shi kad'ai ne zai zauna dashi yayi doguwar hira haka shima Asad d'in shi kad'ai yake iya fad'awa damuwar sa hakan ya saka in suka zauna waje d'aya sai su shafe awa d'aya mai martaba bai ga kowa ba sai shi kawai.
Bai wani jima sosai ba ya fito yana takawa a hankali kasancewar yamma tayi iska na kad'a shi yana kallon kowa na aikin sa ana ta gaishe sa yana d'aga hannu ko ya d'aga kai. Wajan Mama ya tafi yana shiga duk da bayin da suke zaune a wajan bai hana ta tashi ta k'araso wajan sa ta rik'e shi tana fad'in, "Asad ya jikin naka?."
"Mamana ta kwantar da hankalin ta naji sauk'i, ina Hydar?" Ya fad'a yana tafiya d'akin da hydar yake tabi bayan sa. Gadon Hydar ya dafa yana masa addu'a yana kallon sa dan kaf cikin y'an uwan sa yafi son Hydar dan shima yana son sa.
"Asad ka daina jin ciwon cikin?" Mama ta tambaya tana kallon sa. Kallon ta yayi yace, "eh Mamana, da sauk'i."
"Abinda nake nuna maka baka ganewa shine ya faru Asad, zogalen da kaci a cikin gubar take, da ka mutu ya zanyi...?.."
Murmushi yayi yace, "Mamana ban mutu ba kuma na gane duk abinda mahaifiyata take fad'a min." Murmushi tayi tana kallon sa tace, "na gode Asad, Allah yayi maka albarka ya baka lafiya ya kare ka a duk inda kake." A iya labban sa taga ya amsa da amin.
Tare suka fito tana gaba yana binga ta kalle shi tace, "yanzu ina zaka je?." Shiru yayi bai amsa ba tace, "kar ka fita ka huta Asad please." Ya d'aga kai a lokacin Jidda ta fito daga d'aki tana ganin sa tayi murmushi, "Mama Bro deaf ne right?."
"Yeah, but ki daina kiran sa deaf fa." Murmushi tayi tana kallon sa tace, "ya jikin?." Kai ya d'aga kawai kafin ya wuce ya fita baice komai ba. Zuciyar Mama fal farin ciki ganin yaji sauk'i sosai kamar ba shi ba taji dad'i duk da kuma Hydar na kwance.
Asad lokacin da ya fita jakadiyar Hajiya ta zube a gaban sa tana fad'in, "Allah ya ja zamanin yarima mai jiran gado, Allah ya kare zakin mu, Allah ya kiyaye ka ya baka kariya daga mak'iya." Shiru yayi jin hakan ya saka tace, "Gimbiya uwar gidan mai martaba tace ayi maka magana tana son ganawa dakai."
Da hannu yayi mata alamun da su je, gaba yayi tana bayan sa tana kirari har sai da ya juyo ya kalle ta tayi shiru