Showing 15001 words to 18000 words out of 92772 words
Chapter 6 - KWANTAN BAUNA BOOK 1 COMPLETE by Nana haleema.txt
d'in sa ne."
"Nooo ga public a falon nan in ma ba shi ba why not kayi using dana Hydar."
Suhail ya kalle shi shima shi yake kallo kafin yace, "okay" abinda yace kenan ya juya zuwa band'akin da yake falon ya shiga badan zaiyi wani abun ba sai dan ya kawar da shakku. Babu wanda ya yi magana a cikin su har ya fito ya zauna nan ma babu wanda ya tanka kowa da abinda yake yi.
Sun jima a haka babu wanda ya motsa kafin Hydar ya tashi ya shiga d'akin sa ya barsu a falo, shi Hafiz yana so Suhail ya fita dan baya son barin sa wajan shi kad'ai shima kuma yana so ya tafi domin ya cimma k'udurin sa.
Dukkan su haushin juna suke ji babu wanda yake magana babu wanda kuma yayi yunk'urin motsawa.
Ganin Hafiz yana yi masa wani kallo na rashin gaskiya kawai sai ya tashi ya fita ya bar masa falon da sabuwar niya da kuduri a zuciyar sa.
*☆☆☆*
Rauda kuwa bayan sallar azahar ta dawo unguwar su tana gab da shiga layin su ta had'u da k'awayen ta guda biyu Walida da Habiba suna fitowa ta tsaya tana kallon su tace, "ku kuma ina zuwa da rana haka?." Habiba tace, "Rauda manyan gari ke daga ina kike?."
"Gidan Yaya Ummi naje."
"Gidan sarki zamu je zan raka Habiba karb'o sak'o" Walida ta bata amsa tana kallon ta.
"Sai kun dawo Allah ya kiyaye." Habiba tayi y'ar dariya tace, "banza matsoraciya, kizo muje."
"Ni y'ar gidan baban mu, rufa min asiri babu inda zani."
Walida tace, "ke kuwa kizo muje mana yanzu fa zamu dawo." Ta rausayar da kai tace, "kin san ni tsoron doki nake kuma wannan dogaran bulalar hannu su na bani tsoro wallahi."
Habiba tace, "to ina ruwan ki da doki muda ba turken su zamu je ba?, dogarai kuma ai ba ciki zamu shiga bafa k'ark'arin mu wajan Gwaggo ta sai mu dawo." Rauda tace, "kedai Habiba dan kin saba dasu ne kina zuwa ni kam tsoro nake ji."
Jan hannun ta Walida tayi tace, "Dallah can muje an fad'a miki baza mu shiga ciki ba ko banza kya kashe kwarkwatar idanun ki dan nasan baki tab'a shiga ba."
Haka suka rankaya tafi suna hira Habiba tace, "Wallahi Rauda ke kam matsoraciya ce meye abin tsoro a doki da dogarai?." Dariya tayi kad'an tace, "to abinda baka saba gani ba mana Habiba ai dole naji tsoro, nifa ban tab'a shiga cikin gidan ba tunda nake, zaki ga ko hawan sallah ake bana lek'owa sabida tsoron doki kar yayo kaina."
"Shiyasa muka ce kizo muje ai" Walida ta bata amsa suna cigaba da tafiya. Sun yi tafiya mai d'an nisa kafin suka iso babban gate d'in farko na gidan sarki.
Ganin Rauda zata bayar dasu jiki har ya fara rawa ya saka ta suka rik'o ta suka shiga ciki, gate d'in farko suka fara wucewa na cikin masarautar suna ta tafiya domin da nisa kafin kaje gate na biyu, sun wuce gate na biyu suka zo wajan dokuna zasu wuce Rauda ta tsaya cak a wajan idanun ta na kawo ruwa tana girgiza musu kai, "Habiba tace, "kizo mu wuce Rauda babu abinda zasu yi miki."
Kai take girgizawa tana kallo dokunan tace, "bazan iya ba nidai kuje, bazan iya zuwa ba." Walida ta kalli Habiba Habiba tace, "to ki jira mu a nan zamu je yanzu mu dawo, kar ki motsa." Kai kawai ta d'aga sukayi gaba suna waiwayon ta suka shiga gate na biyu.
Doki d'aya ta gani kamar zai yo kanta ta zabura ta bi wata k'ofa da ta gani a bud'e a guje hawaye yana sakko mata daga idanun ta dan ta tsorata sosai bata son ganin doki ko kad'an hakan ya saka ta gigice har bata ganin abinda yake gabanta hankalin ta ya tafi wajan ganin ta nemi mafaka da zata b'uya. Ba zato babu tsammani tayi karo da mutum kafin ta dawo daidai tasan waye ta bashi hak'uri taji an shararawa fuskar ta mari.........
*KWANTAN ƁAUNA*
FitattuBiyar 2023.
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*005.*
Yadda ta gigice idanun ta ya firfito abin tausayi ne jikinta ya tsananta rawa haka hawayen idanun ta suka cigaba da zuba ta kasa koda d'ago kanta balle ma tasan wanda yayi mata kyakykyawan mari haka. A haukace Aliyu yake k'are mata kallo ransa a mugun a b'ace har wuci yake sabida b'acin rai yana binta da banza kallo yace, "Kuna ina!" Ya fad'a cikin murya mai amo har sai da Rauda tayi baya tana rutse idanun ta sabida yadda taji sautin har cikin zuciyar ta.
A guje dogarai guda biyu suka shigo suka zube a k'asa ya bisu da kallon wulaƙanci yace, "wacece wannan?" Ya fad'a yana nuna musu Rauda da take tsaye idanun ta a rufe. Kallon ta sukayi wani daga cikin su yace, "ke y'ar talakawa durk'usa mana!." Jikin Rauda na rawa ta zube guiwa a k'asa jikin ta na rawa sosai duk tsoro ya gama kama mata zuciya. Kallon sa sukayi suka ce, "Allah ya ja zamanin Yarima ban mu santa ba."
Aliyu ya kuma fusata yace, "kenan daman barin wajan kuke babu kowa duk wanda yazo ya shigo sanda ya ga dama?." Su kansu jikin su rawa yake domin tabbas zai iya sakawa a canja musu wajan zama hakan ya saka a tsorace d'aya yace, "tuba muke ranka ya dad'e, Allah ya wuci zuciyar ka, mun amsa kiran Gimbiya ne."
Tunda suka ce gimbiya yasan Mama suke nufi hakan ya saka shi jan dogon tsaki yace, "ku d'auke ta kuje a hukunta ta tunda bata da bakin bada hak'uri" yana fad'a ya juya ya fita daga wajan a fusace.
Har lokacin jikin Rauda rawa yake yi suka mik'e d'aya daga cikin su ya kalle ta yace, "tashi y'ar talakawa yau kin d'ebo ruwan dafa kan ki." Jikin Rauda na rawa ta mik'e har lokacin kuka take ta kasa cewa komai, ba wai tsoron sa take ji ba a'a tsoron doki da kuma masu bulalan nan shine yake sake hargitsa ta. Fitowa sukayi daga wajan daidai nan Habiba da Walida sun fito da alama neman ta suke yi ganin hakan ya saka tawo wajan da sauri Habiba tace, "Allah ya ja zamanin sarkin k'ofa."
"Habiba kin san tane?" Ya fad'a yana kallon ta.
"Na san ta Yallab'ai, k'awa tace rakiya tayi min tana jin tsoron dokuna shiyasa bamu wuce ciki muka ce ta jira mu."
"Ta yiwa yarima Aliyu laifi yana tafiya ta bangaje shi kin kuma san tunda yace ayi mata hukunci babu wanda ya isa ya hana sai mutum biyu kuma basa nan."
Habiba cikin girmamawa ta kuma cewa, "Wallahi Yallab'ai bata tab'a zuwa gidan nan ba yanzun ma nice na jawo ta dan Allah ayi hak'uri a sassauta mata."
"Habiba ba daga ni bane daga shi ne ke kin san halin sa." Zata kuma magana suka hango shi ya tawo lokaci d'aya suka dare hanya yana zuwa zai wuce Habiba tace, "Allah ya ja zamanin yarima mai jiran gado, Allah yayi maka sarkin katagum, Allah yasa ka gaji mai martaba, kaine sarki na goma sha hud'u da izinin Allah. Ranka ya dad'e muna rok'on alfarma, k'awata ce bata tab'a zuwa gidan nan ba sai yau bata san hanyar da zata bi ba, na tabbata kuskure tayi ta shiga inda kake, ina ita ina yarima katagum?, ina ita ina sarkin mu?, ina ita ina shugaban mu baki d'aya?. Ayi mata afuwa ranka ya dad'e" ta fad'a da girmamawa bayan ta zube a k'asa tana tab'a Rauda da har lokacin jikin ta yake bala'in rawa.
"Allah ya wuci zuciyar ka" abinda Rauda ta iya fad'a kenan murya na rawa jikin ta ma na rawa tsoron ta d'aya kar ya saka a kaita wajan doki. Kirarin da Habiba tayi masa ya shige shi hakan ya saka shi ya motsa yatsun sa biyu alamun su tafi kafin yaji ma mai zasu ce ya wuce ciki a abin sa. Wanda yake kusa da sarkin k'ofa ya kalle su yace, "Kinyi sa'a yarinya, maza ku tashi ku tafi kafin ya fito ya canja shawara."
Ai kamar jira suke suka mik'e a guje suka yi hanyar fita Rauda na kuka sosai lokacin Hydar ya fito yaga gift giftwar su fusksr Rauda kawai ya gani tana hawaye daga nan kuma sai suka wuce. D'an lekawa yayi yana kallon su a ransa yana tambayar ko wacece take kuka oho.
Tafiya suke har lokacin Rauda kuka take yi Walida tace, "mune muka ja miki Kiyi hak'uri dan Allah." Habiba tace, "badan mun tilasta ki ba da yanzu babu abinda ya faru, kiyi hak'uri dan Allah ki daina wannan kukan kinga a kan hanya muke fa sai aita kallon ki."
Rauda kuwa ba kukan marin da yayi mata take ba kawai ita a tsorace take ne gani take kamar dokunan zasu biyo ta su kamata. Habiba tace, "kiyi hak'uri haka halin yarima Aliyu yake, bashi da kirki ko kad'an bai d'auki talaka a bakin komai ba ya mayar dasu kamar k'asar da zai taka ya wuce, yadda baya tausayin k'asa yake taka ta da zafin nama haka baya tausayin talaka. Kowa a gidan nan tsoron yi mata laifi yake domin duk tsufan ka koda furfurar ka tana jan k'asa wallahi sai ya saka an maka hukunci. A haka kuma shine zai zama sarkin garin namu."
Walida tace, "mun shiga uku Habiba, akace d'an uwan sa ne."
"Tabd'ijam naki wasa ne Walida, to yadda yake son mulki babu wanda ya isa ya hana shi mulkar garin nan, ke baki ga kirarin da nayi masa bane ya saka ya k'yale Rauda?, ai wallahi da yadda ya furta hukuncin nan sai ya hukunta ta. D'an uwan shine simple babu ruwan sa wallahi kika gan shi baza kice jinin sarauta bane sabida babu abinda ya dame shi, illar kawai shi bashi da lafiyar kwakwalwar in ciwon sa ya tashi sai yayi sati uku a sume."
"Allah sarki abin tausayi, aka ce kuma y'an uku ne."
"Eh uku ne ban tab'a ganin na ukun ba gaskiya kasancewar shi ba mai hayaniya bane ba, ace sai ya kwana ya wuni baice kanzil ba shiyasa ma baya fitowa sabida baya son gaisuwa. Ke kona ganshi bazan banbance su ba."
Walida tace, "tofa lallai."
"Bari kedai, kuma kinga yadda kika ga Aliyun nan haka babar su take ke tama fi Aliyu izza da k'asaita da saka tsinin takalmi ta murtsuke talaka. yar sarki ce kuma jikar sarki ce gata matar sarki, burin ta d'aya tak d'anta yayi sarki kuma zasu yi tunda sune kawai manya y'ay'an mai martaba maza a gidan."
"In sha Allah baza suyi ba, wannan ya zama sarki ai mun shiga uku, taliyar da muke karb'owa kullum ma sai ya saka an daina bamu."
Habiba tace, "kedai ki tsuke baki kawai dan wallahi in kinga yaran nan basu yi mulkin katagum ba sai dai in Allah ne ya nuna ikon sa, dan matar nan da kike gani sai addu'a kawai."
"Allah muka ce ai muma."
Habiba ta kalli Rauda da tayi shiru da alama har lokacin a tsorace take tace, "kiyi hak'uri Rauda dan Allah."
Kai kawai ta d'aga suna tafiya suna hira sama-sama har aka zo k'ofar gidan su Rauda ta shiga su kuma suka wuce. Da Rahma suka yi karo ta dawo daga siyar da abinci tana ganin Rauda tace, "yau kin samu sake har da tafiya gidan Yaya Ummi ko?." Bata iya bata amsa ba ta wuce d'akin Umma har lokacin k'irjin ta bugawa yake.
Umma da ta ga shigowar ta tana tsaye tana gyara labule tace, "ke kuma lafiya na ganki wujuga-wujuga?." Sai da ta zauna ta sauke numfashi ta kalli Khairi tace, "Khairi bani ruwa." Bata musa ba ta tashi ta kawo mata a kofi ta sha ta dire kofin tana ajiyar zuciya.
Umma tace, "lafiya?."
"Umma gidan sarki su Habiba suka jani na raka su."
"A ina kika gansu?."
"Lokacin da na dawo daga gidan Yaya Ummi suka ce nazo muje tunda ban tab'a shiga ba."
Khairi ta fashe da dariya tace, "to Anty shine kuma kike wannan hakkin?."
Umma taja tsaki tace, "ragwanta irin ta Rauda fa." Rauda tace, "Umma dokuna fa na gani zasu biyo ni na tsorata zan gudu naje na bangaje d'an sarki." Ta bud'e baki tace, "too! Amma dai ba'a yi miki komai ba ko?."
"Marina yayi Umma ya dinga ci min mutunci wai y'ar talakawa ya saka a min hukunci Allah ya kawo Habiba ta dinga yi masa kirari sannan ya hak'ura. Wallahi bashi da Imani bai san darajar d'an Adam ba na tsane shi sam bana son sa. Kuma wallahi badan ina jin tsoron doki ba babu abinda zai hana ban mayar masa da maganar da ya fad'a min ba."
Umma ta murmusa tace, "kedai tunda kin kub'uta Alhamdulillah, batun kina son sa ko bakya son sa ai bai tashi ba daman ke meye naki da zaki so shi? Ai sai kallo daga nesa. Naji ana labarin sa ance bashi da kirki sosai gwara da Allah yasa tsoron doki ya hana ki yi masa tsiwa ai."
"Umma sai ma Habiba na baki labarin sa, nima gashi naga zahiri baya da kirki ko kad'an."
Umma tace, "tunda dai lafiya Alhamdulillah, mari kuma Allah zai saka miki." Khalil da ya shigo yake cewa, "Anty d'azu Rahma tazo tana ta fad'a wai yau baki je siyar da abinci ba." Shiru tayi bata amsa ba ta kwanta a kan katifar Umma har lokacin k'irjin ta bugawa yake fuskar Aliyu na wulga mata a idanun ta.
*☆☆☆*
Mai martaba basu dawo ba sai dare har lokacin babu wanda yasan me suka tattauna a hanyar su, a gajiye Asad yake koda ya raka mahaifin nasa b'angaren sa nasu b'angaren yana shiga ya tarar da Suhail a falon shi kad'ai a zaune. Yana ganin sa ya mik'e tsaye yana fad'in, "Welcome back Prince." Kai kawai ya iya d'aga masa ya shiga cikin d'akin sa ganin hakan Suhail ya murmusa zuciyar sa fal farin ciki ya fita.
Wanka Asad yayi ya canja kaya zuwa marasa nauyi a gajiye yake yana so ya huta amma kiran wayar Mama ya hana shi sukuni tun suna hanya take waya hakan ya saka shi fita ya nufi b'angaren ta. A zaune ya tarar da ita daga ita sai Suhaima ya shiga da sallama. Kallon sa take har ya zauna kusa da k'afafun ta ta kalle shi tace, "kun sha hanya." Idanun sa ya lumshe ya bud'e alamun sosai ma kuwa.
"Me kuka tattauna a hanyar taku?." Kallon Mama yayi kafin ya buɗe baki yace, "Mama bamu yi komai ba."
"K'arya bata tsarin halayyar ka Asad ka fad'a min me kuka tattauna." Juya idanun sa yayi kawai baice komai ba tace, "kafi kowa sanin bana jure wannan shirun naka kayi min magana kun tattauna game da sarautar ka?."
Kamar zaiyi kuka ya kalle ta ya girgiza kai alamun a'a, ta fusata tace, "magana zakayi min malam!, kun tattauna ko a'a?."
"Mama bamu tattauna akan komai ba, inda munyi mahaifiyata tasan bazan b'oye mata ba." abinda ya iya fad'a kenan yana dafe jijiyoyin kansa da suke harbawa a gajiye yake sosai ga maganar Mama tana sake d'ora masa damuwa.
Suhaima da take kallon Mama kamar zata yiwa Yayan ta kuka tasan ya gaji gashi baya son magana ga shi sai tsawa take masa kamar ba ita ba. kallon Suhaima tayi tace, "kawo masa abinci yaci." Mik'ewa tayi ba jimawa ta kawo masa bai musu ba ya karb'a yaci abinda zaici ya bar ragowar ta kalle shi tace, "naji na k'yale ka yanzu amma gobe zaka fad'a min abinda kuka tattauna. Sannan nifa ban amince da Suhail ba mahaifin sa munafuki ne ka kula dashi bana so na gan ku tare dan komai zai iya faruwa, bana son ko meye a duniyar nan da zai kawo tangard'a a cikin sarautar da zata dawo hannun ka."
Rausayar da kai yayi a hankali yace, "Sarauta again!."
"Ehh, itace burina kuma matuk'ar ina raye sai kayi, kaje ka nutsu gobe zamu cigaba da tattaunawa."
Kallon ta yayi ta wara idanun ta a cikin nasa ya sauke nasa k'asa tace, "Asad ko kai baka isa kace baza kayi mulkin nan ba matuk'ar na isa da kai, in kaga baka yi wannan sarautar ba ka tabbatar bana raye ne." Kai ya jijjaga kawai yayi mata sallama mik'e ya kalli Suhaima da take kallon sa ya d'auke kansa ya fita.
Suhaima ma bata ce komai ba ta mik'e ta shige ciki itama Maman mik'ewa tayi ta shirya tsaf sai b'angaren mai martaba. Lokacin da ta isa yana zaune a gefe guda yana duba littafai kamar koda yaushe ta shiga da sallama ya amsa mata ta k'arasa ta zauna tace, "kun sha hanya, barka da dawowa."
"Barkan ki, ya daren?."
"Alhamdulillah, ya k'arfin jikin naka?."
"Mun gode Allah."
Shiru ya biyo baya babu mai magana kafin yace, "Aliyu baya gidan nan ko?."
"Ban gan shi ba." Ya ajjiye littafin hannun sa yace, "ban san meyasa Aliyu yake halayya irin wannan ba, meye ribar abinda yake?, shi ko gudun zagi ma baya yi?. Ace yana daga cikin manyan y'ay'a na ace shine kuma wanda yafi kowa gurb'acewa?." Ajiyar zuciya tayi tace, "ban san meyasa Aliyu yake haka ba, kuma takawa kafi kowa sanin yadda aka sha wahala lokacin suna yara wajan kare su daga mugayen sihirin da ake musu. ni nafi tunanin akwai sihiri a jikin sa."
"Koda yaushe ke Aliyu baya laifi asiri ne a jikin sa bakya duba yanayin dabi'un sa. Meyasa Asad shi baya yin abinda yake?, wanda suka yi asirin Aliyu kawai suka tsana?."
Shiru tayi bata amsa ba ya kuma cewa, "Dabi'un Aliyu suna daga cikin abinda yake sake tayar min da hankali, da kunya ace d'an da na haifa