Showing 84001 words to 87000 words out of 92772 words

Chapter 29 - KWANTAN BAUNA BOOK 1 COMPLETE by Nana haleema.txt

20 Jul 2024

17698

da girman da yake dashi a idanun mutane, duka ya tsallake su yazo kanki kuma yana tunanin zamu amince da zuciya d'aya yake son ki...?. ga rigimar gidan sarauta musamman ma ta katagum d'in nan da kowa yasan badaqalar da take ciki, Allah ya kawo miki wani daban amma ba shi ba yaje ya samu daidai shi amma ke kam yafi k'arfin ki."




"Sabida tsabar mulki da sarauta bai tab'a min kallon arzuk'i bama sa wani ce yana sona dan kawai suna ganin zamu amince tunda suna da kud'i?, to ba haka muke ba yaje ya nemi daidai ahi nikam a kai a kasuwa."
"Kedai tunda bakya ra'ayi ai shikenan babu wanda zai miki dole, amma yau kiyi addu'a ki kuma yi istikhara kafin ki kwanta wata k'ila akwai abinda Allah ya b'oye wanda mu bamu san dashi ba."


Da to kawai ta amsa ta jingina da bango tayi shiru tana tunanin abubuwan da suka faru tsakanin ta da Asad d'in har kawo wanda ya faru yau sai taji tsigar jikin ta ta tashi har gashin kanta sai taji abin.


Da daddare Asad yana zaune ya dafe kansa yana kallon wani waje daban b'acin ran da Mama take ciki gabad'aya ya dame shi ko yaya ya motsa ita yake gani tana kuka akan abinda yake da ikon rabuwa dashi, kuncin sa ya shafa ya tuna marin da tayi masa wanda ko yana yaro baya tunanin ta tab'a marin sa amma sai gashi yau sabida wata mace daban ta mare shi.
"I'm sorry mah" ya furta a hankali yana sauke numfashi zuciyar sa nayi masa d'aci da k'una.


Hydar ne ya shigo d'akin nasa ya kalle shi ya ganshi sanye da doguwar riga kalar orange mai hula a baya tayi masa kyau sosai yace, "Deaf ko zamu iya zuwa wani waje mu dawo?." Asad zai musa yayi saurin katse shi yace, "Please yanzu zamu dawo kaima kuma zaka ji dad'i stress d'in nan da kake ciki." Mik'ewa kawai yayi suka fita suka shiga mota Hydar yaja Asad bai san inda suka nufa ba.




Babu zato yaga sun tsaya a k'ofar gidan da suka ajjiye su Rauda d'azu kafin Asad yace wani abu Hydar ya fita daga motar a lokacin Baba ya fito ganin su ya saka ya k'araso da fara'a yana fad'in, "A'a Hydar kaine tafe?."


Hydar yace, "Eh, tare muke da Asad ma, ka fito mana" ya fad'a yana kallon glass d'in motar dole Asad ya fito badan yaso ba. Baba yace, "to ku shigo mana ciki ai bakwa tsaya a waje ba." Daman abinda Hydar yake so kenan suka yi gaba Asad ya tsaya a baya bai da niyar tawowa Baba yace, "Asad baza ka shigo ba kai?."
Jin hakan sai ya tako ya biyo bayan su yana jin sa wani iri kamar bashi ba.


Rauda na zaune da hijjabi tana nunawa Ummulkhairi assignment kasancewar gidan akwai hasken wutar sola ba duhu ko ina haske tarr suka ji sallama, amsawa sukayi kafin su kalli wanda suke shigowa. Asad shine k'arshe shigowa yana shigowa ya had'a ido da abar sonsa nan take yaji duk wata damuwa na yayewa a zuciyar sa a hankali tana tafiya kamar daman bata samu mazauni a ransa ba.


"Lah Yaya Aliyu." Ummulkhairi ta fad'a tana kallon sa da murmushi ya kalle ta amma baice komai ba kafin tace, "Ance kaine ka kawo mu sabon gida mai kyau har da wuta ga tv ma, kai mun gode sosai" ta fad'a kamar yarinya k'arama.


Ya murmusa kad'an baice komai ba kafin Baba yace, "ku zauna mana."
Kafin Asad yace wani abu Hydar ya zauna Hydar ya kalli Rauda yace, "ya jikin? Ina Mama ya jikin ta?" Ya fad'a a tare yana kallon ta a nutse. Dumm haka Rauda taji a zuciyar ta tana ji tana yi mata zillo kamar tana rawa ta daure tace, "Umma ta kwanta bata jin dad'i jikinta."
"Ayya" ya furta daga nan shima yayi shiru.


Baba ya kalli Hydar yace, "Nikam Asad baya magana ne?." Hydar yayi murmushi yace, "yanayi amma ba sosai ba gaskiya, baya son magana bai k'i a kai gobe a haka babu wanda yace wani abun ba, haka Allah ya yisa magana bata cikin tsarin sa sosai." Baba yace, "Allah sarki." Hydar yace, "yace na rako shi su gaisa da Rauda amma naga duk ya canja kamar ba shine yace muzo ba" ya fad'a yana kallon Asad da shima kallon sa yake cikin mamakin k'aryar da ya yi masa.


Baba farin ciki ya kama zuciyar sa ya washe baki yace, "To ai sai mu basu waje su gana" ya fad'a yana tashi Hydar ma ya tashi ya fita yana d'agawa Asad gira ya fita aka barsu daga shi sai ita dan Ummulkhairi ma ta shiga ciki wajan Umma.


Shiru wajan yayi babu wanda yace kanzil a cikin su ita ta zuba ido taga k'arshen izza da k'asaitar tasa shi kuma yayi shiru dan bai san me zaice mata ba gabad'aya dan bashi ya kawo shi ba. An kwashe mintina a haka kafin ta yunk'ura zata tashi tana neman sandar ta ta mik'e tsaye tana fad'in, "Ina da abin yi ba zama nazo yi ba." Jin abinda tace sai ya kalle ta yace, "ya jikin ki?." Komawa tayi ta zauna tana hararar sa ta gefen ido tace, "Oh ashe kana magana." Shiru ya kuma yi baice komai ba itama bata amsa abinda yace mata ba.


Tunawa da abinda mai martaba yace dak'yar Asad ya iya tattaro kalaman bakin sa ya had'e waje guda yana ji kamar ana turo kalmomin daga zuciyar sa yace, "I'm in love with you, but no forcing, no begging and no competition." Rauda da take kallon sa bata lokacin da ta furta, "ikon Allah!" tana kallon sa jin abinda yace. Mik'ewa tsaye yayi ya kalle ta itama shi take kallo dukkan su k'irjin su bugawa yake yi ba kamar shi da yake ji kamar ana jijjigo ta daga mazaunin da Allah ya ajjiye ta yace, "good night!" yana fad'a ya fita ta bishi da kallon mamaki mai d'auke da rainin hankalin da yayi mata.




_K'asaitar so d'in kenan sunan wani littafi._⛹‍♀️🤣🤣






#Vote
#Comments
#Share.


*KWANTAN ƁAUNA*
Fitattubiyar 2023


©️ *Nana Haleema.*


*Book 1*
*024.*


Asad baiga Baba ba da ya fita a mota ya tarar da Hydar kawai ya shiga ganin hakan Hydar yaja motar ya tafi yana satar kallon Asad da yake murmushi mai kyau kana gani kasan zuciyar sa fari tas take a wannan lokacin. Shima murmushi Hydar ya mayar da hankalin sa kan tuk'in kana yace, "in aka ce min deaf zai so wata mace lokaci d'aya haka bazan amince ba, amma sai gashi na gani na kuma tabbatar kana cikin soyayyar da baka san iyakar ta ba." Hannu Asad ya saka ya shafa kansa yana kallon titi shi kansa mamakin kansa yake yi domin bai tab'a d'auka akwai soyayyar wacce zata yi masa kamu lokaci guda kamar ta ba, bai kuma d'auka akwai macen da zai yiwa wannan son na farar d'aya haka ba sai gashi ya tabbata yana kuma kan faruwa a lokacin.


"Ka fad'a mata kana sonta face to face dai ko?." Asad ya girgiza kansa alamun a'a Hydar yace, "to meyesa baka ce mata ba? Meye amfanin zuwan da mukayi?, dan fa ka sanar da ita kana sonta ya saka na d'auko ka muka zo nan."
"Oho" ya furta ya shafa fuskar sa yana lumshe idanun sa. Hydar yace, "gashi ai yanayin ka ya dawo daidai da kazo ka ganta, kana cikin damuwa amma gashi daka ganta ka dawo normal. But da ka sani kayi mata bayanin yadda kake sonta, ina so ka sani Asad lokaci yayi da zaka ajjiye wannan rashin maganar taka, ka san ita soyayya ba ruwan ta da mulkin ka ko nasabar ka ko kud'in ka, a iya kwanakin da ka fada tarkon sonta nasan ka tabbatar. Ka fuskanci abinda zuciyar ka take so in ba haka ba zaka iya rasa ta, soyayya tana son kulawa sosai."


Kallon sa yayi idanun sa a bud'e sosai yace, "babu maganar rasata" ya fad'a yana cize bakin sa cikin jin zafin kalmar rasa ta da yace zaiyi. Hydar yayi y'ar dariya kana yace, "na sani shiyasa nace ka dage Asad, a kan idon ka aka nuna mana wanda yake sonta zai iya kwace ta in ya fika iya kula da ita, na farko kai ga yanayin nature d'in ka ga kuma yadda abin yazo in ba mayar da hankali kafi ba zaka zama looser, kuma sun saba da wancan kai kuma kalma mai tsaho bata tab'a had'a ku ba." Murmushi kawai Asad yayi bai kuma cewa komai ba ya mayar da hankalin sa kan in ya tuna Mama gaban sa sai ya fad'i yaji komai ya fice masa a rai.


Washe gari.


K'arfe tara na safe Mum tazo ta d'auki Mama a mota suka fita su biyu kacal ko hadiman Mama bata bari sun biyo ta ba babu wanda yasan inda zasu je sai su kad'ai. Tunda ta shiga motar take k'wafa Mum da take tuk'i dai bata ce komai ba domin itama nata ran a b'ace yake sosai sai daga baya Mama tace, "Wai ni Takawa zai yiwa fad'a kamar zai dake ni akan wata banza y'ar matsiyata bayan hak'urin da ya saka na basu?, kamar ni ace na bawa wad'annan k'ask'antun hak'uri....? Me suke dashi a duniya da zan kalle su nace suyi hak'uri....? an cuce ni wallahi" ta fad'a tana dukan jikin motar ranta a b'ace.



Mum dai bata tanka ba tafiya suke yi lokaci kad'an suka shiga wata unguwa da babu jama'a ko kad'an sai gidaje kad'an-kad'an kamar rugar fulani suka faka motar suka fito dukkan su suka shiga cikin gidan.


Wani k'aramin d'aki suka shiga wanda yake baje da magunguna na itace dana gari da turarruka kana dosar d'akin kasan d'akin maganin gargajiya ne, wanda yake zaune a gaban faranti da aka zuba masa yashi da k'aton mudubi a kusa dashi yana ganin shigowar su ya murmusa yace, "Barka da zuwa Fulani." Waje suka samu suka zauna kafin Mum tace, "Malam mun same ka lafiya."
"Lafiya lau Sadiya, ya yara suke?."
"Lafiya lau. Matsala ta taso dole muka zo da kanmu shiyasa nace basai kazo ba zamu shigo nida Fulani."


Mama ta kalle shi bayan ta d'age nikaq d'in fuskar ta tace, "kamar yadda ta maka bayani a waya Sunan yarinyar Rauda inaso a duba min aga kodai asiri ta yiwa Asad har ya furta yana sonta duk da tarin nak'asun dake tare da ita da kuma tarin y'an matan da suke so ya kula su ya tsallake su yaje wajan ta." Jin abinda Mama tace ya jawo farantin gaban sa ya fara dubawa kusan minti d'aya da wani abun kafin ya karkad'e hannun sa yace, "a abinda muka gani bata yi masa asiri ba had'uwar jini ce kawai."
"Ka dai sake dubawa ko wani ne daban yayi masa asiri dan ya sota" Mum ta fad'a tana kallon sa.


Malamin ya kalle su yace, "Kamar yadda na fad'a muku babu batun asiri a tare da lamarin nan soyayya ce daga Allah wacce ya dasa masa ita a zuciyar sa." Mama tace, "To meyesa yake sonta?."
"Ranki ya dad'e soyayya ce da kuma had'uwar jini ce."
"Ban amince da wani had'uwar jini ba dole akwai wani abun a k'asa. Kai kanka da zaka ga yarinyar na tabbatar zaka bada shaidar akwai abinda aka kulla." Mum ta kalle shi tace, "to yanzu ya za'ayi kenan?." Malam d'in ya sake duba farantin sa sannan yace, "Asad yana son yarinyar sosai lokaci guda Allah ya saka masa ita a ransa, yana sonta kamar ya had'd'iye ta. ita kuma yarinyar kamar har yanzu babu wani tsayayyen abu a ranta amma dai......" Mama ta katse shi ta hanyar fad'in, "Amma me..? A datse soyayyar kawai."


Malam yace, "ranki ya dad'e kenan hakan yana nufin a yiwa Asad aiki ko?." Mama tace, "A'a ba tun yau ba kasan bana san a yiwa Asad wani abu a yiwa ita yarinyar amma bashi ba." Malam ya murmusa yace, "Ranki ya dad'e banda abin ki ita da babu abu tsayayye a ranta shine akwai soyayya a ransa sai dai in shi za'a yiwa aikin a cire ta daga zuciyar sa. "Mama ta girgiza kai tace, "A'a ko kad'an bana son hakan, a nemo wata hanyar." Malam ya sake bincikawa ya kalle su yace, "Kun sani bana fad'ar k'arya dan na samu wani abun a wajan kowa, haka zalika bana fad'awa mutum abinda zaiji dad'i koda bana jin dad'in na gani ba, ina fad'ar abinda Allah ya bani ikon gani ne komai d'acin sa. Maganar gaskiya auren yarinyar nan da Asad bazai lalatu ta sauk'i ba akwai wani abu mai k'arfi da yake rik'e dashi."


A firgice Mama ta kalle shi tace, "A lalata shi ta k'arfi, a saka k'arfin da yafi nasu k'arfin a tarwatsa shibana son hakan ta kasance ne ko a mafarki." Malam ya jinjina kai kafin Mum tace, "A yiwa yarinyar asirin da zata ji ta tsane shi gabad'aya taji bata son ganin sa ko kad'an, kaga koda tayi niyar amincewa dashi zata fasa." Malam ya sake dubawa kana yace, "Yiwa yarinyar aiki ba abu bane mai sauk'i, tana da rik'o da ibada fiye da tunanin ki Hajiya Sadiya." Mama ta dafe kai cikin takaici tana cizan yatsa zuciyar ta na tafasa sabida b'acin rai jikin ta har zafi ya d'auka kamar mai zazzaɓi, bata k'aunar talaka ya rage ta balle kuma y'ay'an ta.


Mum tace, "A kashe ta ko a haukata ta!." Malam ya yi murmushi yace, "Kar ayi gaggawa ranki ya dad'e, shawara a nan aje a same ta a tsoratar da ita har a cusa mata tsanar auren tak'i amsawa zata aure shi, a fitar mata da sha'awar auren jinin sarauta a zuciyar ta. A ganina wannan itace kawai hanya mai sauk'i in tak'i sai a dauki mataki." Mum tace, "Kenan mune zamu same ta?."
"Kwarai ku da kanku zaku same ta in akayi sa'a hakan zaiyi aiki, domin indai ba ita tace bata so ba Asad bazai fasa auren ta ba haka mai martaba bazai fasa bashi ita ba."


Mama ta sauke numfashi tace, "ya batun sarautar sa?." Malam ya bincika kana yace, "Tana nan, kamar yadda na sha fad'a miki shine zai mulki katagum har gobe maganar haka take; amma kamar koda yaushe akwai qalubale manya ma wanda suka fi na baya yawa. Na farko maganar auren nan zata sake dagula komai, na biyu wad'annan wanda nake fad'a miki suna aiki a kansa sun sake zage dantse sun k'aro makaman yak'in yak'ar ku, na uku suna gab da yin nasara a kanki da kuma kan Asad d'in." Mama ta sauke ajiyar kana ta sassauta murya tace, "ya batun tsarin jikin sa?."


"Ranki ya dad'e komai lafiya yana k'ok'ari wajan ibada da rok'on Allah shiyasa suka kasa nasara akan sa har yanzu." Kai ta girgiza kafin ta mik'e tsaye tace, "Zamuyi waya, muje" ta fad'a tana yin gaba tare da sakin niqab d'in fuskar ta. Mum ta kalle shi bayan ta tashi tace, "Akwai maganar da zamuyi ma tattauna a waya" ta fad'a tana fita daga d'akin tabi bayan Mama da sauri. Suna shiga motar Mama ta kalle Mum tace, "muje gidan su yarinyar."


Zaro idanu Mum tayi tace, "muje muyi me? Kin manta rashin kunyar ta dana baki labari?; marina fa tayi."
"Zamu je mu gyara komai ne yanzu."
"Kamar ya mu gyara Fulani? Kema in ta maren ki fa?."
"Ko uban uban ubanta bai isa ya tab'ani ba balle ita; dalilin da Malam ya fad'a shine zai kai mu wajan ta."
"Amma fulani......?" Dakatar da ita Mama tayi ta hanyar cewa, "Muje kawai. Zan nuna miki gidan da suka koma."


Shiru Mum tayi zuciyar ta a wuya take tuk'in har suka zo k'ofar gidan su Rauda Mama ta fita daga motar tana kallon gidan ta tabbatar nan ne inda aka binciko mata ta nufi zuwa cikin gidan, juyowa tayi taga Mum bata fito ba ganin tana kallon ta ya saka ta fitowa suka shiga cikin gidan.


K'ofa biyu suka gani suka tsaya suna kallon k'ofar cikin tunanin waccw zasu bi a ciki, bud'e d'aya akayi aka fito hakan ya saka suka kalli wacce ta bud'e k'ofar ta kalle su tace, "Bayin Allah daga ina?" Inna ta fad'a tana kallon su. Mum ta kawar da kanta gefe da alama baza ta bada amsa hakan ya saka Mama tace, "Muna neman wajan su Rauda."


"Gashi nan" ta fad'a tana nuna musu d'aya k'ofar suka wuce ba tare da sun kuma kallon ta ba. Da sallama suka bud'e k'ofar sai gasu a falo Rauda na zaune ita da Umma da kuma Yaya Ummi suka amsa suna kallon su, ido Rauda suka had'a da Mum ta bita da kallo kana tace, "tofa kice shugabar y'an daba ce da kanta ta kuma dawowa, to yau kuma da me kika zo mana...? zauna ki bamu labari" ta fad'a tana kallon Mum cikin sigar rashin mutunci.


Mama ta zauna ta d'age nikaq d'in fuskar ta ta kalli Umma tace, "Sannu ya jikin?." Umma tace, "lafiya lau Alhamdulillah. Amma ban sanki ba." Mama ta murmusa tace, "Sunana Fulani Rabi'atu mata a wajan sarki katagum ya a wajan sarkin Kano, jika wajan sarkin Kano, uwa a wajan sarkin Katagum mai jiran gado" ta fad'a tana kallon su. Yaya Ummi tace, "Allah sarki! To sannu." Mama ta kalli Rauda tace, "wajan ki nazo." Rauda da mamaki ta kalle ta tace, "gani ai kin ganni."


Mama tazo wuya jin amsar da ta bata amma ta jure tace, "d'ana Asad ya furta kalmar so a gare ki a lokacin da ban shiryawa hakan ba, ya nuna ke yake yi kuma na riga da nayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login